Sashe 5
Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yana ficewa ta ruf'e k'ofar ta fad'a wanka.....
*SameenaAleeyou....📚*
[12/11, 11:14 AM] +234 810 044 6653: *FUSKA UKU*🏮
*04*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
Zaune suke itada Ayiya a parlorn suna kallon tashan _Discovery Family_ a DSTV da gani zaka gane Asma'u najin dad'in shirin da ake nunawa, Ayiya kam sai kallonta take tana mamakin ina abin kallo a nan domin kuwa wani bature ake nunawa cikin daji babu kalan abincin da baici, dangin su k'wari da sauransu....
Asma'u na sipping tea d'inta tana d'an k'ek'ata dariya take fad'in "Ayiya look zaici d'anyen snail... Ya Rabb ewww!"
Ayiya dai murmushi kawai tayi domin har cikin ranta take jin dad'in taga Nana Asma'u cikin farin ciki...
"Ki canza wannan tasha kafin ki kasa cin abinci...." Ta fad'i tana bud'e mata 'yar k'aramar plate d'in dinner set dake ajiye bisa table...
Sallaman da suka jiyo daga bakin k'ofa ya sanyasu maida hankulansu can...
Murmushin Ayiya ya fad'ad'a domin kuwa sosai take ji da Lamid'o mutum ne da yasan darajan 'yan Adam ba kaman abokinsa Siraj ba....
"A'ah lale-lale da takwaran Sarki, kaine tafe...." Ta k'arashe tana gyara masa kushin...
Murmushi fal saman fuskarsa, fuska a duk'e ya k'araso ya durk'usa saman carpet d'in kana ya soma gaida Ayiya...
Cikin jin dad'i taketa amsawa yayinda bugun k'irjin Nana A ya k'aru don duk sanda taga Uncle Lamid'o hakan ce ke faruwa da ita, gaba d'aya sai ta kasa ci gaba da cin abincin nata...
"Zauna bara na kawo maka karin kummallo ko...." Ayiya tace sanda take k'ok'arin mik'ewa...
"A'a Ayiya wllhi da kin barshi na gode, a k'oshe nake daga gida nake ban wuce Company ba nima, na tsaya ne ko zan iske Siraj bai fita ba...." Ya k'arashe yana duba agogon hannunsa daga durk'ushen da yake...
"A'a Sarki zaka saka wani abin a cikinsa, yau kuma girkin Ayiyar taka, haba kardai muyi haka, jirani minti biyu kacal..." Bata jira cewarsa ba ta shige cikin d'an sassarfa tana ci gaba da fad'in "Gauro kamanka nasan bakaci komai ba....."
Murmushi kawai Lamid'o keyi lokaci guda ya gyara zamansa sosai saman carpet d'in, sai sannan ya kulada Nana A dake faman juya fork da knife cikin plate..
Saida ya murmusa had'i da d'anyin gyaran murya kana yace "Nana ashe kina nan a wajen shine babu ko gaisuwa, toh ni bara na gaisheki good morning..."
Tunda ya soma magana ta sinne kanta sosai tana murmushi...
A hankali ta d'an saita kanta had'i da ajiye plate d'inta saman k'aton wooden center table dake gabanta kana tace "Kayi hak'uri Uncle Lamid'o dama zan gaisheka, Ina kwana....?"
Tayi maganar tamkar wata k'aramar yarinya...
"Murmusawa yayi yana studying d'inta kana yace "Gaskiya ki rik'e gaisuwarki saidama na rok'a..."
D'an fito da idanu waje tayi kana tace "Laa Uncle Lamido wllhi ba haka bane dan Allah kayi hak'uri..."
D'an murmusawa yayi kana yace "Toh shikenan na hak'ura.... Da fatan kina lafiya...."
Fuska cikeda murmushi take jinjina masa kana tace "Lafiya lou, ya aiki...."
Ya amsa mata da lafiya angode Allah sannan ya d'aurada "Ya batun bud'e foundation d'in naki....?"
Saida ta d'an muskuta don idan ta jima a zaune k'afarta nayi mata d'an tsami kana tace "Ana kai Uncle.... Jiya munyi magana da Uncle Siraj yace akwai wani business trip da zaiyi cikin 'yan kwanakin nan so da zaran ya dawo za'ayi bikin bud'ewa...."
Lamid'o ya murmusa kana yace "Da kyau.... Da fatan dai za'a gayyacemu...."..
Saida ta d'an dubesa kafin tayi murmushi mai bayyan hak'wara wanda ya sanya kamaninta da 'yar uwarta Nana H ya kuma fitowa sosai kana tace "Kai Uncle ai kune organizers ma saidai ku gayyata...."
Ya kuma murmusawa yana binta da kallo kana yace "Toh shikenan naji dad'in wannan karamci da aka bani.... Allah ya sanya alkhairi ma cibiyan...."
Kai a k'asa ta amsa da "Ameen...."
Dai-dai lokacin Ayiya ta k'araso wajen hannunta d'auke da tray....
Cikin sauri Lamid'o ya mik'e ya amshe tray d'in yana fad'in "Haba Ayiyarmu ai da kirata kawai kikayi na d'auka...."
Ayiya na murmushi take fad'in "Kai haba Sarki kar ka damu kasan shi gauro lallab'asa ake....."
Sosa k'eya ya soma yana murmushi don yasan Ayiya babu b'oyo abindake cikin ranta take fad'i
"Ayiyarmu na dai kusan kawo maki ita insha Allah..." Ya fad'i sanda yake bud'e plate d'in...
"Kai tafi can sai an laluma aji wayam ko budurwar bakada ita..." Ta basa amsa sanda take k'ok'arin had'a masa ruwan shayi....
Sam bata son zancen Ayiya da Lamid'o domin jinta take wani iri haka nan.... K'ok'arin mik'ewa ta soma tana fad'in "Ayiya I'll be upstairs .... Uncle Lamid'o sai anjima..."
Kallo ya bita dashi yanda take dafa kujera kana yace "Okay Nana A.. Ki kula da kanki...."
Bata sami zarafin amsa sa ba sabida wani irin bugu da zuciyarta tayi jin kalamansa na k'arshe, mai yake nufi ta kula da kanta, kenan ya damu da ita...? Batasan yanda zata samo amsar wannan tambaya tata ba, tana cikin tunanin taji hannun Ayiya na taimaka mata, A dai-dai stirs suka had'u da Ammah da Uncle Siraj suna sauk'owa....
***
*Tambuwal*
Yanda tayi d'aurin kallabin gefen fuskarta ga chewing gum da take faman taunawa uwa uba ga hudin hanci na kunne kuwa kusan huji hurhud'u ne, a ido zakayi tunani kilakice ta k'arshe amma duk d'an iskan da ya nemi tab'a mata mutunci ubansa takeci ta kwana lafiya, yawan kwalliya da takeyi yasa kyaunta ya kuma fitowa sosai samari da manyan mutane da dama sukan kawo mata k'ok'on baransu, amma fa bata isa tayi fira da saurayi ba sai a b'oye domin Daddanta ba bari zatayi ba... Mairo kukeji d'iyar Dadda mai dambe da k'arti....
Yauma mayafinta a kafad'a d'aurin kallabin a sama harda d'amaranta tasha ko a jikinta d'aurin zanin kuwa da kad'an ya d'an wuce k'anjinta harda su sark'an k'afa yau ta saka, Zulai na gefenta tana take mata baya...
Duk yanda suka wuce sai kaji an ambacesu... Mairo ko kan nan a sama take tafiya tana taunar chewing gum har suka iso k'ofar makarantar Malam Balarabe....
Yauma kaman kullum ya kasa ya tsare a k'ofar makarantar tasa sai muzurai yake idanunsa bisa kwalta...
Su Mairo suna isowa Malam yayi gyaran murya ya soma tsine ma karuwai yana la'anta, yana fad'in siffofin shigar da Mairo tayi....
Mairo ta janyo Zulai ta mata rad'a a kunne Zulai ta Shek'e da dariya tace "Hakan za'ayi...."
Zulai ta cire d'ankwalinta tayi wurgi dashi had'i da barbaza suma tamkar mai tab'in hankali ta fad'a ajin islamiyan Malam Balarabe tana tsalle.... Ai a d'ari yara suka soma arcewa wasu ta window wasu ta osin Malam Balarabe...
Malam yayi kan yara yana "Subhanallah... Kai ku dawo, ku tsaya nace...." Inaa ai babu yaro ko guda da ya tsaya....
Malam bai ankara ba saiji yayi an dank'wafo 'yar hularsa tashi ka faye naci.... Malam ya yar da karan hannunsa yana "Subhanallah a kawo d'auki...." Ai kafin ya ankare Mairo ta danna kansa cikin ajin yaran Zulai ta saka sakata ta rufe....
Malam ya gansa a hannun mata, Mairo ta tsaya cak gabansa rik'eda dorinar da yake dukan d'alibai...
Jiki na karkarwa Malam Balarabe yake fad'in "Wa'azi nake Mairoruwa wllhi ban kama suna ba, kumin rai....."
"Mairo ta kuma gyara tsayuwa kana tace "Haka ake wa'azin a gidan uwarka.... Kullum kana bisa kwalta idanunka kan mata ka bar aikin da iyayen yara suka biyaka kayi kana yin wanda ba'a aikeka ba koh... A gidan uwar wa kaga muna karuwancin? Ko kuma ka tab'a ganinmu cikin babbar mota a layin nan... Gacan wad'anda suke saka rigar musulunci suna aikata bad'alansu a gansu sun fito daga gida da shiga ta kamala ashe ciki panko ne babu sitira baka bisu ka la'ancesu ba sai mu koh....? Toh yau la'antar da kake mana zata koma kanka ubanka zakaci gobe zaka koyi yanda ake nasiha da wa'azin, kasan baka biyo hanyar data kamata ba...."
Malam tun na magiya har ya koma fad'in "Wllhi na tuba, Mairo ki rufa min asiri Malami ne ni.... Wayyo wllhi na bar sa ido har abada.... Kuyi hak'uri dan Allah.... Na yarda ban biyo hanya mai kyau ba, wllhi wllhi zan gyara halina, kumin rai kada ku dakeni dan Allah..."
Yanda yake magiya har yaso basu dariya....
Zulai tace "Yo ba dashi kake dukan d'iyoyin jama'a ba, tsoro na me kuma zakaji...."
"Wllhi na tuba....." Ya kuma fad'i yana duk'e gabansu sai faman tattamke hular hannunsa yake....
Zulai ta bud'e masa k'ofa tace "Maza ka fita a guje....."
Ai kaman jira yake suna bud'e k'ofar burut ya fice a guje ko waigowa bayayi... Mai zasuyi banda dariya sun san har abada sunyi maganin sa idon Malam Balarabe...
***
Barr Nasaar ya kuma kai dubansa ga Azeeza wacce keta faman shirya Taheera cikin uniform d'inta don yau Daddy ya huta tunda ga Aunty nan ta samu....
Sauk'e ajiyan zuciya yayi kafin ya maido da dubansa ga Junaid wanda ke rik'eda mug na tea tururi na tashi ciki, daga yanda suke tsaye cikin balcony d'in ya k'urawa garin Abuja idanu motoci da mutane sai safa da marwa suke, sai abinda ya k'aru bayan shekaru kusan hud'u da ya bar garin ba tareda ya kuma lek'owa ba.... Komai ya shiga dawowa kwanyarsa daki-daki.... Muryarta ya shiga yawo a dodon kunnuwarsa sanda take sanar dashi an tilasta mata auren waninsa.... Ya shiga tuna sanda yaji k'aran bindiga alamun an harbeta, sautin k'aranta na k'arshe bai daina yawo cikin kunnuwarsa ba..... Ya tuna lokacin da ya bud'e idanunsa ya tarar k'afafunsa sun zama tarihi A DUNIYAR SA..... A hankali ya lumshe idanunsa zuciyarsa da kwanyarsa na barazanar tarwatsewa.... Wani k'ara ya saki had'i da jifa da Mug d'in dake hannunsa......
Cikin sauri Barr ya tura k'ofar balcony d'in don baiso yaran su fahimci abinda ke faruwa... Mamaki bai gama cikasa ba saida yaji muryar Junaid cikin kuka yana fad'in they killed her.... Those three killed her.... Wllhi bazan huta ba sai na d'aid'aitasu gaba d'aya, sai na gansu a situation d'in da nake a yanzu.... Wllhi duk sai sun d'and'ana...." Ya k'arashe jijiyar goshinsa da take koriyar shar tana kuma fitowa....
Jin k'aran horn d'in school bus d'insu Hammad alamun ta iso yasa Barr saurin fitowa nan kuwa ya tarar Azeeza tana ratayawa yaran school bags d'insu had'i da lunch packs d'insu....