← Book details Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 98

Sashe 84

Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Shut your crazy mouth...!!!" Nasaar ya katseta kafin yaci gaba da fad'in "Wllhi kinji na rantse maki wani abu ya sami Azeeza I won't think twice zan d'auki fansata akan Siraj... You'll never see him again, zan b'atar dashi....!!" Ya k'arashe yana tsananin huci

Murmushi Nana H keyi lokaci guda take wasa da 'yan yatsun hannunta saman fuskarsa... "Alright na jika, nasan kana k'aunarta, amma babban kuskuren da zakayi shine ka aura mata Uncle d'ina..."

Shima murmushin yake sanda yake shafa fuskarta kana ya soma fad'in "Kina tunanin ni Nasaar zan aurawa Siraj Azeeza ne, idan baki sani ba don na mallaki Azeeza cikin sauk'i na amshi ragamar aurenta, Siraj haukansa kurum yake amma ina mai tabbatar maki ranar aurensa zai nemi amaryarsa ya rasa, ya rabu da ita rabuwa ta har abada...."

Murmushi Nana H ta saki cikeda jin dad'i "Na yarda da plan d'inka but make sure babu abinda zai sami Uncle d'ina...."

"You can count on that....!!" Ya fad'i yana mai ci gaba da mata wasu salo, k'aran da wayarsa yayi ne ya katse masa hanzarinsa, ganin mai kiran nasa ya sanyasa saurin saka wayar a silent... Lokaci guda ya janyo Nana H jikinsa suka d'aura daga yanda suka tsaya...

***

Lamid'o yaci gaba da fad'in "Ammah mahaifina already yayi hiring private investigator gameda case d'in Nana K so babu abin damuwa idan Allah ya yarda, komai ya kusan zuwa k'arshe da yardar Allah...."

Mamaki ne ya cika Ammah ganin yanda Lamid'o da mahaifinsa ke k'ok'ari wajen binciko mata jikarta, Allah sarki ashe har yanzu akwai mutane masu kyakkyawar zuciya irin haka... Ita dai ko sanin mahaifin Lamid'o batayi ba amma gashi tinda ya dawo k'asar ya d'auki damuwarsu ya d'ora ma kansa... Allah sarki...

D'an muskutawa Ammah tayi kana tace "Allah sarki, da baka tak'ura mahaifinka ba wllhi sakarcin Siraj ne ya hanasa focussing kan batun nemo 'yar uwarsa,.."

Girgiza kai Lamid'o yayi kana yace "Kar ki damu Ammah, Daddy haka yake mutum ne mai son ganin an k'watarwa mutane hakkinsu, musamman da na sanar dashi matsayin Siraj a wajena da kuma family d'in Siraj, so na tabbata he would do anything he can don ganin ya ceto rayuwar Nana Khadijah..."

Ammah ta jinjina kai kana tace "Allah sarki, Allah dai ya biyaku dakai dashi baki d'aya, bansan ta yanda zan soma maka godiya ba Lamid'o... Kuma insha Allahu ka sanar dani duk wasu kud'ad'e da mahaifinka ya kashe akan wannan case d'in zamu biya da yardar Allah...."

Lamid'o ya kuma girgiza kai kana yace "A'a Ammah ba don a biyasa Daddy yakeyi ba, shi haka nan yake bai damu k'arshen k'wandalansa ta k'are wajen taimakon Al'umma ba koda kuwa baida alak'a dasu...."

"Gaskiya ne, na yarda, kuma samun ire-irensu a wannan duniya tamu yanada matuk'ar wuya... Allah ne kawai zai biyasa... Idan kaje ka gaishesa sannan don Allah idan babu damuwa inaso nazo har gida na masa godiya"

Lamid'o ya d'an jinjina kai kana yace "Babu damuwa Ammah, kuma basai kin tak'ura kanki wajen zuwa ba... Amma dai insha Allah zan sanar dashi yanda mukayi...." Ya k'arashe yana k'ok'arin mik'ewa...

Godiya Ammah ta kuma masa kafin ya fice ya nufi sashen Siraj ko zai cimmasa don har yanzu basu san yanda zasu sami Junaid ba...

***

Kai tsaye office d'inta suka nufa, Ma'ajura na gaba yayinda Zaliha ke biye da ita.... Har lokacin k'irjin Zaliha bai daina bugu ba....

Knocking Zaliha ta soma had'i da sallama, saida tayi hakan sau kusan uku kafin aka amsa mata daga ciki aka bata izinin shigowa....

Cikeda risinawa ta shige cikin office d'in Nana A kuwa na ganinta ta saki murmushi don ta tuna tattaunawarsu ta jiya... Gaisawa sukayi kafin Nana A ta kuma tambayar Ma'ajura abinda ke tafe da ita dukda cewa tana sane da batun amma gwara ta sake tuntub'arta....

"Ma'am dama kan maganar da nazo maki da ita jiya ne..."

Nana A ta jinjina kai tana mai rufe file d'in gabanta kana tace "Ina saurarenki.."

Ma'ajura ta kuma d'an daidaita tsayuwarta kana taci gaba da fad'in "Dama kince mu taho tare yau ayi mata gwaji..."

Nana A ta jinjina kai tana mai furta "Haka ne.... Kun taho tarene yanzu haka...?"

Ma'ajura tayi saurin jinjina kai kana tace "Eh tare muke da ita..."

"Toh babu damuwa ki shigo da ita...." Ta k'arashe tana mai janyo wani file d'in gabanta...

Cikeda risinawa Ma'ajura tai mata godiya kafin ta fice kiran Zaliha.....

Ga tsananin mamakin Ma'ajura bataga Zaliha a yanda ta barta ba.... Haushi da takaici ya lullub'e Ma'ajura, sam Zaliha bama ta ganin duk effort d'in da take akanta, meyasa zata kuma tafiya bayan saida ta shiga ta sanar da Asma'u tare suke da Zalihan.... Itakam tanaga ta gama shiga hidiman nema wa Zaliha aiki tunda kunya take son bata.... A fusace ta juya da zummar komawa ofishin Nana A d'in don sanar da ita abinda ya faru, saidai idanu hud'u sukayi da Zalihan ta fito wani k'ofar daban....

Harara Ma'ajura ta galla mata kana tace "Ai wllhi cewa nake tafiya kikayi yau da kinga rashin mutuncin da zan tsula maki, wllhi ko Umma ma bazata iya rabamu ba..."

Zaliha na murmushi ta k'araso had'i da dafe k'awar tata take fad'in "Haba k'awata baikai nan ba, yi hak'uri wllhi k'aran takun keken d'inki da nake jiyowa ya sanayani lek'awa, gaskiya wannan foundation naku ya birgeni wllhi da yawan nakasassu zasu sami abin dogaro bazasu tsaya yin barace-baracen nan ba...."

Fizgota Ma'ajura tayi suka nufi office d'in tana mai fad'in "Yanzu nidai ba wannan ba mu k'arasa kafin kema a baki ajinki da kuma d'alibanki..."

Da sallama suka doshi office d'in Ma'ajura na masu jagora....

Take ta masu umarnin shigowa yayinda tayi tsaye jikin wani dogon drawer mai d'auke da takardu ta basu baya, ba tareda ta dubesu ba don wasu takardun ne a hannunta tana dubawa ta masu izinin da su zauna saman couches dake d'an gefe kad'an...

Haka kurum muryar matar yayi mata tamkar ta tab'a jin mai irinta a wani waje.... Bugun k'irjinta ya k'aru, burinta kawai matar nan ta juyo ta kalli fuskarta......

Juyowar da Nana A zatayi ya sanya Zaliha mik'ewa babu shiri.... Innalillahi wa inna'ilaihi raji'un... Fuskar aminiyarta ce ya bayyana b'aro-b'aro a gabanta... Fuskar Maironta, Mairo aminyarta da akullum take kwana da ita take kuma tashi da ita, take kuma fatan su sake ganin juna idan da rabo....

Ganin irin duban da Zaliha keyiwa Asma'u ya sanya Ma'ajura saurin mik'ewa itama, tana mai k'ok'arin d'an janyo hannun Zaliha alamun kallon nata yayi yawa...

Murmushi saman fuskar Nana A take k'ok'arin gaisar da Zaliha... Baki na rawa ta iya gaisar da Nana A bayan Ma'ajura ta d'an tab'ata alamun ana mata magana....

Dukda cewa Nana A ta lura da irin kallon da bak'uwar ke mata bai hanata masu alamu da kujera ba cewa su koma su zauna....

Da k'yar Zaliha ta iya zama saman kujeran amma for second ta kasa daina duban Nana A ... Tambayoyi Nana A ta shiga mata kan sana'ar nata, yayinda Zalihan ke amsata da k'yar da k'yar cikin sark'ewar murya... Mairo kawai take gani a gabanta, gani take tamkar Mairo ce amma tak'i nunawa ta santa... Meyasa Mairo zata mata haka... Toh amma anya itace kuwa...? Kodashike wannan tanada alamun sanyi ba kaman Maironta da ta sani ba, sannan wannan tanada tsananin wayewa fiyeda Maironta.... Toh kodai a d'an watannin da sukayi ba tare bane har ta zamto haka....??? Muryar Nana A ya kuma katse mata tunanin nata yanda take ci gaba da fad'in "Ma'ajura zata rakaki wajen Aunty Lami ita zata baki d'alibanki da kuma ajin da zaki d'auka...."

Ko godiya Zaliha ta kasa yi saidai Ma'ajura ce ta iya yin magana.... Ko motsawa Zaliha kam ta kasa sai kallon Nana A da take bugu da k'ari hoton Nana A d'in dake ajiye gefen table d'inta harta murmushinta irin ta Mairo ne, kai wannan aka jera maka su biyu d'in itada Mairo zakace mutum guda ne..... Har Ma'ajura ta janyo hannunta suka fice daga office d'in Zaliha bata dawo daidai ba...

"Ke wai lafiyarki kuwa, wai meke damunki, kinga yanda kike kallon Madam kuwa.... Ko kin santa ne....?"

K'uri Zaliha tayiwa Ma'ajura tamkar mai tunanin wani abin, lokaci guda ta shiga girgiza kai alamun a'a, bata san mai zata soma fad'i ba, bata san ta yaya zata soma bayani ba, jikinta gaba d'aya yayi wani irin sanyi, ita tunda take bata tab'a ganin kamanni irinta Mairo da wannan matar ba.....

Har lokacin tashi yayi Zaliha bata fahimci komai ba, haka koda suka koma gida hoton Mairo dake cikin wayarta ta hasko tana mai tsananin mamakin kamanninsu, ta tuna hoton Nana A data gani a ofishinta babu abinda ya raba da wannan hoton Mairo da take kallo a yanzu, a haka Umma ta shigo ta isketa....

Ita kanta Umma shirun Zalihan ya dameta a yau, tinda ta dawo gida ta lura da yanayin nata, gaba d'aya ta koma wata irin sukuku, k'uri Umma ta mata nan taga hotan Mairo ce tai mar k'uri babu ko k'yafta idanu... Zama Umma tayi gefenta tana mai ci gaba da dubanta....

"Zaliha wai lafiyanki kuwa, kin saka hoton Mairo a gaba kina kallo tun d'azu, kiyi hak'uri idan da rabon ku sake had'uwa zaku sake had'uwa, ni inaga yanda kika damu da Mairo haka kike tunaninta haka k'ila tama mance dake itakam tinda dama sud'in tamkar makiyaya suke, yau su yada zango a nan gobe su yada a can... Ki kwantar da hankalinki ki cire tunanin Mairo cikin ranki ki natsu kiyi sana'arki da kyau....." Umma ta k'arashe cikin murya mai kwantar da hankali

"Umma.....!!" Sai kuma ta d'anyi shiru....

Umma ta kuma dubanta kana tace "Ina jinki menene....?"

"Umma wllhi wllhi Mairo na gani yau.... Umma naga Mairo...."

K'uri Umma ta mata kana ta d'an murmusa tace "Toh ai ba abin mamaki bane don kinga Mairo tunda dama su d'in yawo suke wa gari wa gari, mai yuwa da suka baro can nan suka taho...."
Chapter 84 · 0% Book details