Sashe 91
Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shi kuwa Sabi'u tsoron Nana H ya cika masa ciki musamman da tayi maganar Ahidjo, gani yake tamkar zata gane shine silan mutuwar mijinta, amma mai yasa ta d'aura alhakin mutuwar nasa kan Lamid'o, kai wannan abu akwai rikitarwa, kodai ba shi kad'ai bane ya farauci rayuwar Ahidjo...? Sabon firgici ya cika masa zuciya, muryar Bulama da ya sinkayo ne ya kuma d'an zaburar dashi kafin yayi k'ok'arin saita kansa...
Bulama yaci gaba da fad'in "Young lady amsoshin tambayoyinki gaba d'aya naga kakarki ki tambayeta zata sanar dake komai, ga dukkan alamu ta jima tana b'oye maku sirrika, amma wannan ba hurumina bane, hakkinta ne ta sanar daku ko ita d'in wacece.... Abu na gaba, dama ni taimako nayi niyyan yi dukda bansan su waye nake taimakon ba, amma tunda ita ta kasa magana har ke kinyi, na gode maki k'warai kuma zan janye wannan bincike da nakeyi sannan zan hukunta d'anah Lamid'o akan abinda kika fad'i muddin nayi bincike na gano laifinsa.... Na gode..."
Yakai dubansa ga Ammah dake tsaye tamkar ruwa ya shanyeta kana ya d'an murmusa yace "Har bayan shekaru kina nan da kyaun ki Mairo... Na barku lafiya, muje Detective ...." ya k'arashe yana duban Sabi'u wanda dama alla-alla yake su mik'e su bar gidan domin kuwa sosai idanun Nana H suka basa tsoro, gaba d'aya gani yake kaman zata gane shid'in amintaccen mijinta ne a wajen aiki sanda yake raye...
Har ya kai k'ofa yana d'an dogara sandarsa kana ya juyo yana duban Ayiya dake tsaye wajen tana faman rarraba idanu...
"Aishatu kunyi 'yanmatantaka tare kun kuma tsufa tare.... Lallai kun rik'e amanan juna... Saidai nayi matuk'ar mamaki da banga cikon ta ukun ku ba...." Daga haka bai kuma cewa komai ba yayi ficewarsa yana gyara babban rigarsa...
Wani sabon mamaki ya kama Nana H, mai yake nufi Ammah sunyi 'yanmatantaka da wannan mere servant d'in kuma sun tsufa tare, dama sunsan juna ne...?? Lokaci guda tabi bayan Alhaji Bulama gudu-gudu tana fad'in "Alhaji mai kake nufi, wancan matar fah mahaifiyarmu ta kawota gidan nan sanda ta haifemu amma ba Ammah ba..."
Murmushi Bulama ya saki sanda ake bud'e masa marfin mota kana yace "Young lady shiyasa nace maki da alama kakarki ta b'oye maku abubuwa da dama, amma idan hakan tace maku su d'in basu tab'a sanin juna ba kije ki bincikesu na tabbata zakiji komai......"
Daga haka bai kuma sauraren Nana H ba ya buge babbar rigarsa ya shige mota, zuciyarsa na masa wani irin dad'i musamman da ya kula ya gama dulmiyar da tunanin Mairo ya kuma had'ata fad'a da danginta wanda babu mai iya warwareta ciki...
***
"Deejoh! Deejoh!! Deejoh!!! " Sunan da yaketa ambata kenan, idanunsa a rufe ruf har lokacin ba tareda ya bud'esu ba,...
Baba Malam da Hafiz suna tsaye kansa suna karanto masa addu'o'i, abun tamkar shafan aljanu, duba da irin mafarkan da yake yawan yi ga kuma sunan da yau ya kama sai ambata yake....
"Hafiz anya bazaka kira Dr Sahal ba kuwa...?" Mama Azumi ta fad'i tana mai duban Hafiz d'in..
"Mama ai dama Dr Sahal yace mana zai dinga yin wasu abubuwa abnormal sabida yunk'urin dawowa da tunaninsa keyi, k'ila wannan suna da ya ambata nada alak'a da bayansa ne...."
Baba Malam dai shiru yayi yana mai ci gaba da tofawa Ali addu'o'i ba tareda ya amsa su ba... Lokaci guda kuma Ali ya daina ambaton sunan da yake sai wani dogon numfashi da ya shak'a, idan ka gansa a haka dole ya baka tausayi, ga mutum har mutum a kwance amma jinya ke cinsa ta ciki...
Baba Malam ya shafe masa fuska da ruwan addu'a kafin ya maido da dubansa ga Hafiz "Hafizu kabi maganar mahaifiyarka kaje ka kirawo Dr Sahal watak'ila akwai abinda zai iya yi wanda mu bamuda iliminsa, wannan bawan Allah tun safe yake kwance yana jin jiki..."
Hafiz ya jinjina kai cikeda risinawa kana yace "Toh Baba zanjeni yanzu insha Allahu...." Lokaci guda ya fice cikin sauri ya nufi yanda Babur d'insa take ajiye....
*SameenaAleeyou📚**FUSKA UKU*🏮
*60*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
Hafiz na ficewa Mairo da Umma Marie sukayi sallama gidan, kasancewar Baba Malam na tareda Ali ya sanyasu zaman jiransa a b'angaren Mama Azumi, sam bata sanar dasu ga abinda ke faruwa ba ta dai sanar dasu yana wani hidiman ne...
Umma Marie tace "Ai babu komai Yaya Azumi zamu jirasa ba sauri muke ba...."
Mama Azumi ta mik'e domin kawo masu abin tab'awa...
***
A wani checkpoint aka tare Sadiq anai masa tambayoyi da ya dangancin driving license d'insa, akayi rashin sa'a motar dake bayansa boys d'in Bulama ne, tun daga wannan checkpoint d'in da suka fahimci shine mutumin da suke nema suka soma binsa gadan-gadan, saidai basuyi yanda zai gane sud'in binsa suke ba....
***
"Answer me Ammah, who was that man... Mai yake cewa... Ammah who are you, mai kike b'oye mana tsawon shekarun nan....? Just spell it out...!!" Ta k'arashe tamkar zata gaurawa Ammah mari, sai faman firfito da idanu waje take....
Har lokacin Ammah bata daina kuka mai sauti ba, ga numfashinta dake k'ok'arin d'aukewa....
Ganin haka yasa Ayiya saurin matsowa kusan Ammah ta rik'eta had'ida zaunar da ita saman kujera, ta dubi Nana H da murya mai sanyi take fad'in "Nana Hafsat kiyi hak'uri ki sassautawa kakarki, ki dubi halin da take ciki na rashin lafiya, kinsan tanada matsalan numfashi...."
Kallo Nana H take bin Ayiya dashi kafin ta fashe da wani irin dariya, saida ta kuma gyara tsayuwarta tana mai ci gaba da k'arewa Ayiya kallo kana ta soma fad'in "Impressive, yau kece kike min magana da taushi haka, sabida kar na gano munafuncinku, you don't want me to find out your devilish secret.... So you two are allys, Ammah I thought this woman was our Nanny.... And now she turned out to be your accomplice.... Ammah wllhi gwara ki sanar dani kafin na sani da kaina.... Kinga mutumin nan da ya fita wllhi sai na bishi naji komai...."
Sai sannan zuciyar Ammah ta kuma harzuk'qa, lokaci guda ta mik'e had'ida wanke Nana H da wata lafiyayyar mari....
Ayiya tabi Ammah da kallon mamaki yayinda Nana H ta dafe k'uncinta tana mai duban Ammahn shaye da mamaki itama...
Ammah taci gaba da nunata da d'an yatsa hawaye bai daina kwararo mata ba take ci gaba da fad'in "You've no respect, nayi danasanin tayar dake bisa gurb'aracciyar tarbiya, duk abinda kike so tun kina k'arama baki nakeyi, bana ganin laifinki sabida na d'auki son duniya na d'aura maki, 'yar uwarki is nothing like you.... Nana H bakida kunya bakida mutunci kuma kinji na rantse maki kika kuskura kika bi wancan mak'aryacin mutumin da ya fice wllhi nida ke ne a gidan nan... Shashasha kawai wacce batasan ciwon kanta ba...." Ta k'arashe tana tsananin huci...
Ga tsananin mamakinsu dariya sukaji Nana H ta fashe dashi tamkar mai tab'in hankali, lokaci guda take nuna Ammah da d'an yatsa tana mai ci gaba da dariyar take fad'in "Who do I take after...? I take after you, ke na gada wllhi, yanzu nasan yanda na samo duk d'abi'una da ba'a so... Ashe dai a nan na d'auko.... Let me tell you this Ammah, you might be my father's mother amma ke ba uwa ta bace, idan kinmin baki bazai bini ba.... So for all I care ki fad'i worse than that akaina.... Kuma barikiji na fad'a maki, what so ever you're hiding, I'll find out..... And idan naji yanada alak'a da mutuwar iyayena wllhi kinji na rantse maki you gonna hear it from me, kuma barikiji na fad'a maki, zan tafi yanzun nan na sanar da Nana A komai kafin wannan tsohuwar munafukar k'awar taki tayi brain washing d'inta, Uncle kuma bayada lokacin ki yanzu, kuma na tabbata shima yaji abubuwan da kika aikata sai ya tsaneki, you'll lose us all..." Ta k'arashe tana mai hura hanci had'ida kad'a yatsa a fuskar Ammah... Lokaci guda ta juya ta fice daga gidan cikin sauri....
Ayiya sam bata ankara da Ammah dake k'ok'arin zubewa k'asa ba, tabi bayan Nana H tana kiranta, Nana H kuwa ko saurarenta bata tsaya yi ba ta fice.... Juyowar da Ayiya zatayi ta hangi Ammah zube a k'asa tana tamke k'irjinta numfashinta na fita da k'yar da k'yar... Hankali tashe Ayiya ta shiga k'wallawa ma'aikatan gidan kira tana k'ok'arin d'auko inhaler d'in Ammah.....
***
"Gaskiya ni Zaliha bazan iya yin shiru ba sai na tambayi Nana A ko sunada wata 'yar uwa mai kama dasu haka itada Nana H, wllhi kema kinsan bakina bazaiyi shiru ba... Sai na nuna mata hoton nan..... Kamannin yayi yawa...."
Girgiza kai Zaliha tayi kana tace "A'a nidai gaskiya mubi abun nan a sannu, nima na soma zargin ko Daddah sato Mairo tayi tinda dama kullum cikin hijira suke gari zuwa gari, gaskiya Ma'ajura ina tunanin Nana A 'yan uku ne, Mairo ce cikaton ta ukun nasu tinda kinga a shekaru ma kusan dai-dai suke, komai nasu ya nuna haka...."
Ma'ajura ta jinjina kai kana tace "Kuma shine kike so muyi shiru, who knows, wayasan tsawon shekarun da suka d'iba suna neman 'yar uwarsu... Wannan fah taimako zamuyi, Zaliha Allah kad'ai yasan dalilin da ya kawoki garin nan har kika samu aiki a wannan foundation d'in, k'ila ta sanadin ki zasu san yanda 'yar uwarsu take...."
Shiru Zaliha tayi tana jinjina maganar Ma'ajuran cikin zuciyarta kana tace "Kuma fah haka ne kinyi gaskiya Ma'ajura, amma wani hanzari ba gudu ba, kinga dai ni bansan yanda su Mairo suka koma ba tunda kafin mu baro Tambuwal sun k'aura....."
Jikin Ma'ajura ya d'anyi sanyi, ta d'anyi shiru kaman bazatace komai ba sai kuma tayi saurin d'ago fuskarta tace "We shouldn't lose hope, Na tabbata Allah bazai kawoki cikin rayuwarsu babu dalili ba, na tabbata akwai b'oyeyyen Al'amari, mudai sanar dasu kinga mun fita, kuma idan aka tsananta bincike k'ila a samosu tinda kinga sunada kud'in da zasu iya wannan binciken...."
Zaliha ta jinjina kai kana tace "Hakane Ma'ajura... Tashi muje, muje mu sami Nana A mu sanar da ita komai, mu nuna mata hoton Mairo...."
Ma'ajura na murmushi ta mik'e had'i da kamo hannun Zaliha tace "Muje k'awata...."