← Book details Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 98

Sashe 82

Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

D'ago kan da zaiyi yayi idanu hud'u da Asma'u, tana sanye cikin doguwar riga 'yar dubai wanda ya b'oye nakasan dake jikinta, Asma'u tanada kyau irin mai tafiya da nutsuwar nan, gaba d'aya d'ingishin nata ma sai ya zame mata tamkar ado, yanayin sanyinta zaisa kayi tunanin shiyasa take tafiya a hankali cikin tsanaki, komai nata a natse take gudanar dashi, Lamid'o ya kasa ci gaba da magana sai kafeta da idanu kurum da yayi, yama mance gaba d'aya Ammah na wajen, itako sam batama san yana parlorn ba don bata tsaya sauraren Ayiya dake cewa kada ta fice bataci abinci ba, gaba d'aya bataji dad'in lattin da tayi ba, tasan makara a barcin nata nada nasaba da rabin kwana zaunen da tayi a daren jiya ne....

Ammah takai dubanta yanda Lamid'o ya kafe idanunsa, Asma'u ta hango tana sauk'owa daga staircase, lokaci guda tausayin Lamid'o ya rufe Ammah tun bayan abinda ya faru... Badon tayi alk'awari bazatayiwa Asma'u katsalandan cikin manemanta ba da ta umarceta da ta auri Lamid'o domin kuwa tsan-tsan soyayyar jikar tata take hangowa cikin idanunsa....

"Ammah....!!" Ta ambata murya a d'an bud'e don batamayi zaton Ammahn na parlor ba.... Kafin Ammah ta sami zarafin amsawa Asmau tayi idanu hud'u da Lamid'o.. Zuciyarta ta shiga mata zogi, ta shiga tuno maganganun da Nana H ta sanar da ita, yanzu kam k'yamar Lamid'o takeji sosai domin kuwa tabbas idan har abubuwan da Nana H ta fad'i akansa gaskiya ne toh ya cancanci a k'yamacesa....

Cikin sauri ta d'auke idanunta daga barin dubansa ta k'arasa ga Ammah tana gaisheta sauri-sauri... Bata wani tsaya b'ata lokaci ba ta nufi k'ofa tana fad'in "Ammah ni na wuce foundation I'm late already..."

"Bazaki saka komai a cikin ki ba haka zaki tafi...." Ammah ta fad'i cikeda kulawa

"No Ammah babu damuwa zan samu a can..." Bata jira cewar Amman ba ta fice cikin sauri tana fad'in "Ammah sai na dawo...."

Ammah dai amsata kurum tayi had'ida mata fatan sauk'a lafiya.... Yayinda Lamid'o ya b'ace shiru a wajen, kallo guda zaka masa ka fahimci babban abu ke damunsa, baisan ya kamu da tsananin soyayyar Asma'u ba har haka, inama bawa na iya goge past d'insa tabbas da ya goge nasa... A hankali ya d'an sauk'e fuskarsa k'asa ganin Ammah ta maido da dubanta garesa...

A b'angaren Asma'u ma tinda taga Lamid'on zuciyarta bai daina bugawa ba, har suka d'auki hanya itada Malam Sile zuciyar tata na abu guda, tabbas yakishe Lamid'o cikin zuciyarta ya zame mata dole musamman da yanzu ta kuma sanin ko shid'in waye....

A can foundation kuwa Zaliha ba don taso ba ta mik'e zata tafi, duk magiyan da Ma'ajura ke mata kan cewa ta d'an k'ara hak'uri ko Madam d'in nasu zata iso hak'urin Zaliha ya gaza... A dole Ma'ajura ta mik'e domin raka Zulaiha....

*SameenaAleeyou📚**FUSKA UKU*🏮

*55*

*©Sameena Aleeyou...✍🏽*

Kasancewar Central Area ne yasa bazasu sami abin hawa kai tsaye ba, dole su sauk'a can k'asan bridge bakin tasha kafin su sami motar da zata kaisu unguwarsu.... Suna tafe suna fira Ma'ajura na mitan meyasa Zaliha bazata k'ara hak'uri ba tinda sune masu nema, kuma tasan akwai dalili mai k'arfi da ya sanya Madam yin latti koma ya hanata zuwa gaba d'aya, duba da cewa a kwanakin dama Madam d'in tasu batada lafiya cikin 'yan kwanakin....

"Yanzu sai ki koma gida kicewa Umma mai...?" Ma'ajura ta bid'a sanda suke tsallaka babban kwalta...

"Na ce mata sai gobe mana tinda yau bata zo ba, Ma'ajura bazaki gane bane wllhi nidai tsakanina da Allah tinda na shigo wannan foundation d'in naku gabana ke fad'uwa, k'irjina sai bugu yake jikina na bani wani babban Al'amari zai faru, k'ila ma idan Madam d'in taku ba d'aukata aikin zatayi ba, wllhi sam banji a jikina abin arziki zai faru a wajen nan...."

Cikeda mamaki kurum Ma'ajura ke dubanta sanda suka k'arasa bus d'in da zai kaita Suleja... Nan ta umarceta data shiga ta kuma sanar da ita duk yanda akeyi... Bus ta cika Ma'ajura bata bar wajen ba tana kallonsu har sun soma shirin barin wajen kwatsam ta hangi motar Nana A na shiga close d'in foundation d'insu.... Ai a tamanin ta soma bubbuga bus tana fad'in su tsaya.... Aiko driver na tsayawa batayi wata-wata ba cikeda murna ta shiga janyo hannun Zaliha tana fad'in "Ke gata nan ta iso, ta iso wllhi sauk'o muje...."

Jama'a sai dubanta suke uwa mai tab'in hankali, inaa itakam ko takansu bata biya ba sai k'ok'arin janyo Zaliha take, cikin sauri suka soma sassarfa suka nufi foundation d'in k'irjin Zaliha bai daina bugu ba....

***

"Ka fad'a min ina take, ina ka kaita... Ina ka b'oyeta..wllhi wllhi kaji na rantse maka bazan bar wannan shegiyar yarinyar ta kusanci Uncle d'ina ba... Wllhi bazan bari I'll do everything... I mean everything....!!!"

"Shut your crazy mouth...!!!" Nasaar ya katseta kafin yaci gaba da fad'in "Wllhi kinji na rantse maki wani abu ya sami Azeeza I won't think twice zan d'auki fansata akan Siraj... You'll never see him again, zan b'atar dashi....!!" Ya k'arashe yana tsananin huci

Murmushi Nana H keyi lokaci guda take wasa da 'yan yatsun hannunta saman fuskarsa... "Alright na jika, nasan kana k'aunarta, amma babban kuskuren da zakayi shine ka aura mata Uncle d'ina..."

Shima murmushin yake sanda yake shafa fuskarta kana ya soma fad'in "Kina tunanin ni Nasaar zan aurawa Siraj Azeeza ne, idan baki sani ba don na mallaki Azeeza cikin sauk'i na amshi ragamar aurenta, Siraj haukansa kurum yake amma ina mai tabbatar maki ranar aurensa zai nemi amaryarsa ya rasa, ya rabu da ita rabuwa ta har abada...."

Murmushi Nana H ta saki cikeda jin dad'i "Na yarda da plan d'inka but make sure babu abinda zai sami Uncle d'ina...."

"You can count on that....!!" Ya fad'i yana mai ci gaba da mata wasu salo, k'aran da wayarsa yayi ne ya katse masa hanzarinsa, ganin mai kiran nasa ya sanyasa saurin saka wayar a silent... Lokaci guda ya janyo Nana H jikinsa suka d'aura daga yanda suka tsaya...

***

Lamid'o yaci gaba da fad'in "Ammah mahaifina already yayi hiring private investigator gameda case d'in Nana K so babu abin damuwa idan Allah ya yarda, komai ya kusan zuwa k'arshe da yardar Allah...."

Mamaki ne ya cika Ammah ganin yanda Lamid'o da mahaifinsa ke k'ok'ari wajen binciko mata jikarta, Allah sarki ashe har yanzu akwai mutane masu kyakkyawar zuciya irin haka... Ita dai ko sanin mahaifin Lamid'o batayi ba amma gashi tinda ya dawo k'asar ya d'auki damuwarsu ya d'ora ma kansa... Allah sarki...

D'an muskutawa Ammah tayi kana tace "Allah sarki, da baka tak'ura mahaifinka ba wllhi sakarcin Siraj ne ya hanasa focussing kan batun nemo 'yar uwarsa,.."

Girgiza kai Lamid'o yayi kana yace "Kar ki damu Ammah, Daddy haka yake mutum ne mai son ganin an k'watarwa mutane hakkinsu, musamman da na sanar dashi matsayin Siraj a wajena da kuma family d'in Siraj, so na tabbata he would do anything he can don ganin ya ceto rayuwar Nana Khadijah..."

Ammah ta jinjina kai kana tace "Allah sarki, Allah dai ya biyaku dakai dashi baki d'aya, bansan ta yanda zan soma maka godiya ba Lamid'o... Kuma insha Allahu ka sanar dani duk wasu kud'ad'e da mahaifinka ya kashe akan wannan case d'in zamu biya da yardar Allah...."

Lamid'o ya kuma girgiza kai kana yace "A'a Ammah ba don a biyasa Daddy yakeyi ba, shi haka nan yake bai damu k'arshen k'wandalansa ta k'are wajen taimakon Al'umma ba koda kuwa baida alak'a dasu...."

"Gaskiya ne, na yarda, kuma samun ire-irensu a wannan duniya tamu yanada matuk'ar wuya... Allah ne kawai zai biyasa... Idan kaje ka gaishesa sannan don Allah idan babu damuwa inaso nazo har gida na masa godiya"

Lamid'o ya d'an jinjina kai kana yace "Babu damuwa Ammah, kuma basai kin tak'ura kanki wajen zuwa ba... Amma dai insha Allah zan sanar dashi yanda mukayi...." Ya k'arashe yana k'ok'arin mik'ewa...

Godiya Ammah ta kuma masa kafin ya fice ya nufi sashen Siraj ko zai cimmasa don har yanzu basu san yanda zasu sami Junaid ba...

***

Kai tsaye office d'inta suka nufa, Ma'ajura na gaba yayinda Zaliha ke biye da ita.... Har lokacin k'irjin Zaliha bai daina bugu ba....

Knocking Zaliha ta soma had'i da sallama, saida tayi hakan sau kusan uku kafin aka amsa mata daga ciki aka bata izinin shigowa....

Cikeda risinawa ta shige cikin office d'in Nana A kuwa na ganinta ta saki murmushi don ta tuna tattaunawarsu ta jiya... Gaisawa sukayi kafin Nana A ta kuma tambayar Ma'ajura abinda ke tafe da ita dukda cewa tana sane da batun amma gwara ta sake tuntub'arta....

"Ma'am dama kan maganar da nazo maki da ita jiya ne..."

Nana A ta jinjina kai tana mai rufe file d'in gabanta kana tace "Ina saurarenki.."

Ma'ajura ta kuma d'an daidaita tsayuwarta kana taci gaba da fad'in "Dama kince mu taho tare yau ayi mata gwaji..."

Nana A ta jinjina kai tana mai furta "Haka ne.... Kun taho tarene yanzu haka...?"

Ma'ajura tayi saurin jinjina kai kana tace "Eh tare muke da ita..."

"Toh babu damuwa ki shigo da ita...." Ta k'arashe tana mai janyo wani file d'in gabanta...

Cikeda risinawa Ma'ajura tai mata godiya kafin ta fice kiran Zaliha.....

Ga tsananin mamakin Ma'ajura bataga Zaliha a yanda ta barta ba.... Haushi da takaici ya lullub'e Ma'ajura, sam Zaliha bama ta ganin duk effort d'in da take akanta, meyasa zata kuma tafiya bayan saida ta shiga ta sanar da Asma'u tare suke da Zalihan.... Itakam tanaga ta gama shiga hidiman nema wa Zaliha aiki tunda kunya take son bata.... A fusace ta juya da zummar komawa ofishin Nana A d'in don sanar da ita abinda ya faru, saidai idanu hud'u sukayi da Zalihan ta fito wani k'ofar daban....

Harara Ma'ajura ta galla mata kana tace "Ai wllhi cewa nake tafiya kikayi yau da kinga rashin mutuncin da zan tsula maki, wllhi ko Umma ma bazata iya rabamu ba..."

Zaliha na murmushi ta k'araso had'i da dafe k'awar tata take fad'in "Haba k'awata baikai nan ba, yi hak'uri wllhi k'aran takun keken d'inki da nake jiyowa ya sanayani lek'awa, gaskiya wannan foundation naku ya birgeni wllhi da yawan nakasassu zasu sami abin dogaro bazasu tsaya yin barace-baracen nan ba...."
Chapter 82 · 0% Book details