Sashe 75
Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Innah na murmushi take dubanta yanda ta masu tsaye aka baki a ture, don yanzu tinda akace babu Yaya Ahidjo aka daina ganin fari'arta dukda cewa bata yarda ya rasun ba... kana tace "D'iyata yaya dai ko kina son wani abin ne...."
Langab'e kai tayi jikin gini kana tace "Innah kifin da Baffah ya sayo min jiya nake son ci...."
Innah da Baffah suka kalli juna murmushi saman fuskokinsu kana ta d'an sassauta murya tana duban Baffah tace "Toh Baffah kaji fah tinda ka sakalta d'iyar taka da kwad'ayi fitar dare ta kama ka...."
Baffah ya kuma murmusawa don yanzu kullum zai dawo daga kasuwa sai yayowa Deejoh sayayyan kayan kwad'ayi irinta masu juna biyu a talakance...
"Toh gashi kuma babur d'in babu mai, gobe ma idan Allah ya kaimu saidai na tura zuwa bakin kwalta, kiyi hak'uri suyar sassafe sai a sayo maki koh...."
"Baffah ni wllhi wllhi shi zanci, ni inba haka ba kuma zanjeni da k'afata na sayo..." Ta k'arashe tamkar mai shirin yin kuka... Duk fah wannan bidiri sam Deejoh koda wasa batasan cewa juna biyu gareta ba don har yau babu wanda ya sanar da ita tsakanin Baffan da Innar....
Ai Innah babu shiri ta mik'e tana fad'in "Yi shiru abinki karma ranki ya b'aci zan sayo maki yanzun nan...." D'aki ta nufa da niyyan d'auko mayafi yayinda Baffah ma ya mik'e yana fad'in "A'a Bilki baza'ayi haka ba ki zauna da ita a gida k'ila ta buk'aci wani abin bayan kin fita.. Ni zanje bakin kwalta d'in na sayo mata..." Ya maido da dubansa ga Deejoh da tayi zaune gefen shimfid'in nasu kana yace "Bayan kifin akwai abinda kike so... Ko kina son balangu....?"
Washe baki Deejoh tayi harda 'yar tsallenta kana tace "A'a Baffah Balangu sai gobe, amma harda lemun gora zan sha..." Baffah ya d'an murmusa kana yace "Toh an gama, ki kula ki daina tsalle-tsalle kinji koh kinga likita yace babu ishesshen lafiya jikin ki...."
Jinjina masa kai tayi cikeda farin ciki kana tace "Toh Baffah, na gode Baffah, a dawo lafiya....."
Innah ta k'araso murmushi fal fuskarta kana ta d'an dafa Deejoh tace "Duk abinda kike so ki sanar damu kinji koh..."
Nan ma Deejoh jinjina mata kai tayi kana tace "Innah yau saura wata guda Yaya na ya dawo, nayi mafarki ya sanar dani saura wata guda ya dawo.. Innah nawa ne ma wata guda a lissafe.....?" Ta k'arashe tana mai k'irge da 'yan yatsun hannunta....
Tausayinta ya cika zuciyar Innah bata iya ce mata komai ba sai d'an kauda kanta gefe da tayi tana matsan k'wallan da yazo idanunta...
A bakin layin Sabi'u ya had'u da Baffah sai sauri yake yana neman abin hawa... Hasken motarsa ce da ya haska ya fahimci Baffah ne.....
*SameenaAleeyou...📚**FUSKA UKU*🏮
*51*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
Horn Sabi'u yayiwa Baffah wanda ya sanya Baffahn tsayawa yana lek'en mai masa horn d'in...
"Baba barka da dare...." Sabi'u yace daga cikin motar sanda yake zuge bak'ar glass d'in motar...
Muryarsa Baffah ya d'auko lokaci guda ya saki murmushi kana yace "A'ah barka Malam Sabi'u ashe baka koma ba....?"
Sabi'u ya jinjina kai "Eh Baba ban koma ba dama akan sai gobe idan Allah ya kaimu... Baba ina ka nufa...?"
"Bakin babban kwalta na nufa, ka k'arasa gidan yanzu zan dawo ba da jimawa ba insha Allah...."
"Baba muje na kaika mana a nan ai bazaka sami abin hawa ba duhu ya soma shigowa..." Ya k'arashe yana bud'ewa Baffah marfin d'aya b'angaren na mai zaman banza....
"A'a Malam Sabi'u kar ka damu fah zan iya zuwa...." Cewar Baffah dake tsaye b'angare guda...
"Baba dan Allah ka min izini na kaika, idanma aike ne ni zan iya zuwa maka, amma bazan iya barinka a nan haka nan ba...." Ya k'arashe uwa mutumin arzikin gaske...
Murmurshi Baffah yayi kana yace "Allah sarki D'an nan na gode k'warai dama suya kifi ne zan sayowa Deejoh bakin kwalta d'in ungo karb'i kud'in ka sayo mata...." Ya k'arashe yana zura hannu cikin aljihun gaban rigarsa yana ciro 'yan canjin da suka rage masa...
Sabi'u murmushi kurum yake yana dubansa kana ya girgiza kai yace "Baba idan dai don wannan ne babu matsala, dan Allah ka bar kud'inka ka koma gida ka huta...."
Baffah ya girgiza kai yace "A'a Malam Sabi'u baza'ayi haka ba ungo karb'i..."
Sabi'u ya kuma girgiza kai yana murmushi kana ya tada motar yana fad'in "Yanzu zan dawo Baba insha Allah..." Bai kuma jiran cewar Baffah ba ya soma tafiya da motar tasa... Ala dole Baffah ya nufi gida murmushi bai bar saman fuskar sa ba...
Haka Baffah ya shigo gida ya tadda Deejoh da Innah sai faman zuba shiriritarta take, sosai yake tausayin Deejoh da abinda ke cikinta, Allah sarki su kuma irin tasu k'addarar kenan a duniyarsu...
Ba'a d'auki wani lokaci ba Sabi'u ya dawo da kaya nik'i-nik'i, lemun goran ma sink'insa guda ya sayo, Baffah yayita masa fad'an kashe kud'in yayi yawa, k'arshe suka masa godiya shida Innah...
Deejoh kam tana ganin Sabi'u ne ya shigo tayi kicin-kicin da fuska, itakam ta tsanesa ta tsani ganinsa, gashi kaman maye ya tak'ura masu da zuwa, harga Allah dukda kyautata masu da yakeyi da zaran ta gansa take tuna shine ya kawo labarin wai Yayanta Ahidjo ya mutu... Har abada bazata tab'a yafewa wannan mutumin ba, ita koma mutuwar ne yayi da yayi zamansu bai fad'i masu ba da ya fiye mata, suyita zaman jiransa har Allah ya dawo dashi tinda dama ya saba tafiya ya jima d'in...
Koda Innah ta nuna mata suya kifin kicin-kicin tai da fuska kana tace ta k'oshi, ba tareda ta jira cewar kowa cikinsu ba ta shige d'aki abinta, Sabi'u ya sha jinin jikinsa don ya lura duk sanda yazo gidan Deejoh shigewa d'aki take rai a b'ace, anya zata yarda dashi ta amince masa wa buk'atarsa... Koda shike yarinyace shakaf shawo kanta ta amincewa buk'atarsa sam bazai masa wuya ba musamman idan ya nusar da ita cewa Ahidjo ya tafi ba dawowa zaiyi ba...
D'an risinawa yayi kana yace "Baffah ka min izini na shiga nai mata magana inaga kaman gani na ne a gidan bata so..."
Dubansa sosai Baffah yayi kana ya d'an gyara zamansa yayinda Innah tayi saurin bin bayar d'iyarta....
"Malam Sabi'u kenan kar ka damu, tabbas Deejoh har yanzu mutuwar mijinta na jikinta duba da yanayi na k'arancin shekaru irin nata dole sai an d'au lokaci sosai kafin ta dawo dai-dai.."
Sabi'u ya jinjina kai kana yace "Haka ne Baffah,..." Shiru ya d'an gifta kafin Sabi'u ya soma k'ok'arin mik'ewa yana fad'in "Toh Baba gobe zan wuce insha Allah... Ga wannan ko Deejoh zata buk'aci wani abu...."
Girgiza kai Baffah yayi kana yace "Allah ya kiyaye maka hanya amma bazamu karb'i komai naka ba... Abubuwan alkhairi da kayi ubanguji ya biyaka, mun gode k'warai...."
Sabi'u yayi shiru yana jinjina dattako irin na iyayen Ahidjo, a dole ya tafi da kud'insa don Baffah k'in karb'a yayi...
Har Sabi'u ya fice daga layin bai daina tunanin Deejoh ba, har wani cikowa ta kuma yi a 'yan kwanaki biyun, gashi babu hali ya furta k'udirinsa cewa son Deejoh yake alhalin tana cikin Iddah, ga dukkan alamun su Baffah sun san addini sun san cewa nema cikin Idda haramun ne, inama ya samesu irin gidahuman jahilan nan ne masu kwad'ayin abin duniya tabbas da yayi amfani da wannan damar ya mallaki Deejoh, a duk sanda ya ganta sabuwar sha'awarta ke taso masa, shi bama wannan ba wai ciki ne da ita iddah kuwa sai ta haife abinda ke cikinta kafin ta fita.... Sabi'u ya fuzar da iska don baijin zai iya bari Deejoh ta gama Iddah bai mallaketa ba koda kuwa ta haramtacciyar hanya ce, Wa'iyazubillah.....
***
*Abuja*
Siraj ke driving yayinda Nana A ke zaune mazaunin mai zaman banza, Nana A taci gaba da fad'in "Uncle I'm pretty sure if you get to know him zakaji dad'in zama dashi... Wllhi Junaid yanada kirki sosai Uncle , kaga duk lokutan da nake cikin damuwa shike mantar dani ta hanyar kalamai masu k'arfafa gwiwa da kuma kwantar da hankali... And you know what Uncle nida shi mun had'u da k'addara kusan iri guda a wannan rayuwar...."
Tinda ta soma magana bai saurarenta burinsa kawai su isa foundation d'in ya samu ya iske Junaid, amma jin kalamanta na k'arshe ya sanyasa rage speed kafin ya juyo yana dubanta...
"Wait... mai kikace... meye labarinsa, mai ya sanar dake....?" Ya tambaya curiously....
"Kaga shima a had'arin mota ya rasa k'afafunsa dukda cewa jijiyoyin ne kawai suka daina aiki amma k'afarsa garau take a ido tamkar baida wata lalura... Sannan shima ya rasa iyayensa saidai shi a halin yanzu baida kowa a nan don gaba d'aya danginsa suna Cameroon.... Sosai na tausaya masa sabida shi baida kowa gwara ni I still have you ga kuma Nana H ga Ammah ga Ayiya.. Sannan gashi soon zamu kuma kasancewa da Nana K...." Ta k'arashe fuskarta fal murmushi wanda basai ance maka na jin dad'i bane....
Fuzar da iska Siraj yayi had'i da kai dubansa gefen window d'insa.. Wato Junaid bai sanarda Nana A asalin labarinsa ba, bai sanar da ita what really happened to his legs ba, ya tabbata sune silan rasa k'afafun Junaid, ya tabbata wannan kurum ya ishesa dalili ya dawo d'aukan fansa kansu tinda a baya su suka tasamma kashesa... Abinda ya shige masa duhu har yau shine toh waye duk waye sila, waye silan mutuwar Zeenat idan dai ba Junaid bane...? Muryar Nana A ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya tafi...
"Uncle lafiya.... Wani abu ke damunka....?" Ta tambaya cikeda kulawa...
K'ak'aro murmushi Siraj yayi kana yace "Oh no no sweetheart babu komai, naji labarin Junaid amma kinsan dole na masa wasu tambayoyi na kuma yi bincike kansa don bazan d'aukeki haka kurum na basa ba, sabida muna sonki kuma mun damu dake...." Ya k'arashe murmushi mai sanyi saman fuskarsa da har wani dashewa ta d'anyi sabida tsananin damuwa...