Sashe 72
Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Lamid'o tsaye kurum yayi yana duban Nana H da rianannun idanunsa, ji yake tamkar ya jawota ya mak'ureta musamman idan ya tuna damages d'in da ta haifar wa rayuwarsa..... Cikin sauri ya maido da dubansa ga Nana A dake tsaye tana zuban hawaye...
K'ok'arin matsowa kusanta yake yana fad'in "Asma'u bazan tafi ba har sai na sanar daku abinda ke tafe dani.... Nana A ki yarda dani wllhi ba haka kawai na b'ace...."
Dakatar dashi tayi ta hanyar d'aga hannu yayinda Nana H ta tare gabansu tana mai ci gaba da watsa masa wulak'anceccen kallo had'ida huci take fad'in "You heard her right, get yourself outta here before things get worse.... Ka fice aka ce....."
Tarin da Ammah keyi bayan Ayiya ta kawo inhaler d'inta ta mik'awa Siraj ya saka mata a baki ya sanya hankulan su Lamid'o harma dasu Nana's d'in ya koma garesu....
Cikin sauri Ayiya ta kuma mik'o ruwa cikin glass cup ma Siraj d'in ya shiga baiwa Ammah a hankali yanai mata sannu.... Nana H da Nana A ma k'arasowa sukayi sunai mata sannu sanda Siraj ya mata masauk'i saman doguwar kujera mai d'aukan mutum uku.....
Lamid'o na k'arasowa wajen Nana H ta kuma harzuk'a tana fad'in ya fice masu a gida kafin ya kashe masu grandmother....
Siraj yayi saurin rik'o Nana H yana fad'in "Sweetheart let me handle this please...." Ya kuma kai dubansa ga Lamid'o kana yace "Kayi hak'uri ka tafi kaga condition d'in da mahaifiyata ke ciki.... Kaje ni zanzo na sameka muyi maganar...."
Ai baikai aya ba Nana H ta katse sa da fad'in "Uncle kar ka yarda da k'aryar wannan mak'aryacin, kawai ya rasa wani k'arya zaiyi a yarda dashi bayan cin amana da yaudara da yayiwa innocent Nana A shine yace bari ya b'ullo ta wannan hanyar tinda yasan wannan ne kawai zaisa ya kuma samun yardar kowa a family d'in nan... Uncle please do not trust him kaji uncle....."
Kafin Siraj ya sami zarafin magana Lamid'o dake duban Nana H ido cikin ido gajeriyar murmushi saman fuskar sa ya soma fad'in "Zan tafi amma nasan gaba za'a buk'aci aji daga gareni... And let me remind you this, ina son Nana A, yes ina sonta dukda lalurar dake jikinta, dai-dai da rana guda ban tab'a jin soyayyarta ya ragu ba.... Sannan idan komai yayi settling Al'amra suka daidaita zamu kasance tare insha Allah... Nana Khadija zata halarci aurena da Nana A Alqawari nayi wa Nana A koda ban furta mata ba, 'yar uwarta da kukayi tunanin ta mutu zata halarci bukin aurenta insha Allah... Kuma ke baki isa kiyi komai ba....." Yana ida fad'in haka yasa kai zai fice.... Saidai kafin ya isa k'ofa Ammah ta mik'e tana fad'in "Kaga dawo dan Allah dawo ka sanar dani yanda jikata take...." Ta k'arashe hawaye naci gaba da kwaranya mata....
"Ammah no dan Allah ki barsa ya tafi, Ammah bayan duk abinda yayi zaki kuma yarda dashi.. Wllhi na tabbata this only one of his lies... Ammah kar ki yarda dashi kiga daga zuwansa ya jefaki cikin rashin lafiya....." Nana H ta k'arashe tana mai jijjiga hannayen Ammahn....
Girgiza kai Ammah tayi kana tace "K'yaleni na sauraresa Nana Hafsat, idanma k'arya yake wannan karan he won't get away with it I promise....."
Murmushi Lamid'o ya saki yana mai duban Nana H kafin ya k'arasa d'aya daga cikin kujerun ya zauna yana mai godiyawa Ammah had'ida gaidata...
Gaba d'aya waje suka samu suka zauna yayinda Nana H taci gaba da sak'e-sak'enta a zuciyarta... Tayi tunanin shikenan Nana K bazata kuma dawowa rayuwarsu ba tinda Ahidjo dake yak'in fafutukan dawo da ita cikin danginta ya mutu sai gashi Lamid'o ya kuma bayyana da zance iri guda.... Tirk'ashi idan Nana K ta dawo yanda Uncle da Ammah ke sonsu haka zasu nuna mata k'aunar da basu nuna mata ba sama da shekaru ashirin da sukayi ba tareda ita ba... Hankalin kowa zai koma kanta, kai a gari gaba d'aya zancenta za'a keyi ita kuma ta zama tsohon zance bayan wannan gadonsu za'a kuma kacancanawa harda Nana K... Kai idan ta bari Nana K ta shigo rayuwarta tabbas zata iya k'wace soyayyar kowa nata daga gareta gwara tayi da gaske taga bata dawo ba.... Muryar Lamid'o ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da tayi nisa ciki sanda yaci gaba da fad'in "Da farko inai mana ta'aziyan rashi da mukayi na d'an uwa kuma aboki a gareni wato Ahidjo... Ubangiji ya masa rahama yasa ayyukansa na alkhairi su bisa, kurakurensa Allah ya yafe masa yayi rahama a garesa...." Gaba d'aya suka amsa da ameen idan ka d'auke Nana H dake aika masa muguwar kallo, da zata sami dama da ta shak'e Lamid'o ta huta...
Lamid'o yaci gaba da fad'in "Tabbas nasan zaku nemeni a lokacin da na b'ace, toh kaman yanda na sanar da Siraj saceni akayi aka kuma rufeni sama da wata guda a lokacin da nasan cewa Nana Khadija tana raye.... Na soma bincike ne sa'ilinda naci karo da hotonta wayar wani abokina mai suna Nazir..." Baikai aya ba Ammah ta katsesa da fad'in "Ina yake, ina abokin naka... Yaya kamannin Nana Khadija yake a yanzu, na tabbata zatayi kama da 'yan uwanta domin tun suna jarirai kamanninsu guda babu abinda ya rabasu.... Dan Allah ka kaini wajenta na ganta... Ka kaini naga jikata....." Ta k'arashe sabbin hawaye suna gangaro mata... Siraj ya k'arasa ya d'an rik'eta yanai mata alama da ido kan tayi hak'uri su gama sauraren Lamid'o
Lamid'o ya gyara zamansa had'ida d'anyin gyaran murya sannan yaci gaba da fad'in "Ammah Nana K babu abinda ya rabata da 'yan uwanta, kamanninsu guda... FUSKA UKU garesu iri guda, hasalima kamannin na gani na tabbatar itace domin a baya Siraj yakan sanar damu ya rasa niece d'insa guda a had'arin mota ba'a gawarta ba wacce akayi zaton ruwa ne ya tafi da ita.... Toh a lokacin ban sanar daku ba sabida nima ban gama tabbatarwa itace ko ba itace ba sai nayi bincike musamman duba da yanayin shekaru da aka shafe babu ita, toh ina cikin bincikena ne na fahimci Nana K saceta akayi tsawon shekarun nan kuma Mace ce ta saceta ta maidata mallakinta don bata san cewa ba matar bace ta haifeta....." Ammah ta kuma katse sa da fad'in "Wanene wannan matar...? Wllhi ko wacece ita.. Ko wacece sai yanda k'arfina ya k'are wllhi sai na d'aureta a gidan yari rabani da jikata da tayi tsawon shekaru...."
Ayiya ce tayi k'arfin halin zaunar da Ammah tana fad'in ta kula da lafiyarta yayinda murmushi ya wanzu a fuskar Nana A dukda hawaye dake kwaranya mata, tama rasa hawayen bak'in cikin sake ganin Lamid'o ne ko kuwa na farin cikin labarin da take ji ne cewa 'yar uwarta tana raye bata mutu ba.... Wayyo Allah, Allah nuna mata wannan rana da Nana K zata bayyana a gabansu suga juna su rungume juna... Ita kad'ai sai sakin murmushi take tama kasa d'auke idanunta daga barin duban Lamid'o...
Lamid'o yaci gaba da fad'in "Matar tanada had'arin gaske, domin a lokacin data fahimci akwai mai bincike kan d'iyarta wacce ta rad'a mata suna Mairo sai ta kame abokina Nazir nima kuma tasa aka kamani aka kulle.... Da dabara na sami waya dukda ina rufe, na rasa waye zan kira na sanar dashi labarin Nana K sabida ku idan na sanar daku zan iya jefa rayuwar Nana K cikin garari koma na jefa rayuwar ahalin gidan nan cikin had'ari.... Ahidjo shine ya fad'o min a rai kuma shine mutumin da ya cancanta na kira na sanar dashi tinda shid'in jami'in tsaro ne... Na kirasa na sanar dashi amma na gargad'esa cewa kada ya sanar da kowa koda Siraj ne bayan na basa hujjoji na nayin hakan...." Muryar Lamid'o ta soma rawa sanda yaci gaba da fad'in "Heedj..... Heedj ya min alk'awarin nemo Nana K, ya min alk'awarin dawo da Nana Khadija cikin danginta.... A d'akin da aka kulleni ashe akwai camera sun gama ganin komai sunji wayar da nayi... Wanda na tabbata tafiyar da Ahidjo ya tasamma kenan shima sukayi ajalinsa kaman yanda sukayi ajalin Nazir......" Ba Lamid'o kawai ba harta Siraj kuka yake, kai d'aukacin mutanen parlorn kukan ne suke idan ka d'auke Nana H wacce gabanta yaci gaba da fad'uwa... Wato bayan ita kenan akwai wad'anda sukayi farautar rayuwar mijinta Ahidjo... Toh wai wacece wannan matar data sace Nana K, meye take nema daga garesu... Kenan tana iya yuwa ba Nasaar bane yayi nasaran kashe Heedj wasu ne daban.... Gumi ya shiga keto mata dukda saying AC dake tashi a parlorn.... Take taji wani k'arfin hali na sauk'o mata, lokaci guda ta fashe da wani irin kuka ta nufi Lamid'o tana jijjigasa take fad'in "Kai ka kashe shi... Kai ka kashe min miji... Meyasa zaka jefa rayuwar Heedj cikin had'ari..? Mai ya maka da tsanani.... Mai yasa zaka tura mijina a kashe shi, you monster you'll pay for this.." Sosai take kuka tana jijjiga Lamid'o da k'yar Siraj ya iya janyeta shima kukan yake don sai yanzu abubuwa da dama suke dawowa kwanyarsa... Ya tuna sanda Heedj yazo ya taddasa yace dashi akwai maganar da yake so suyi... Ya kuma tuna maganganun da sukayi da Heedj d'in akan Lamid'o, ya tuna yace yana so ya sanar dashi wani abu.. K'ila abinda zai sanar dashi kenan... Meyasa? Meyasa bai saurari Ahidjo ba.... Ya k'arashe tunanin nasa sanda Nana H ta rungumesa ta shige cikin jikinsa sosai tana kuka take ambaton sunan Ahidjo tana fad'in Lamid'o ya kashe mata miji....
Gaba d'aya 'yan gidan suka taru kanta suna lallashi suna bata hak'uri, da k'yar Nana H ta tsagaita da kukan da take kafin Lamid'o yaci gaba da sanar dasu yanda sukayi da Ahidjo...
Shiru na wasu 'yan lokuta ya d'an ratsa parlorn kafin Siraj ya jefo wa Lamid'o tambaya...
"Yaya akayi kayi escaping daga hannun matar, sannan kana iya tuna kamanninta....?"