Sashe 58
Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A'a aiko Dr ya kuma shigar dasu duhu.. Daddah na zaro idanu tace "Auna jini ni Bintu... Ke Marie ina ne nan anya ba wajen 'yan shan jini ba yaya daga zuwa zasuce a auna jinin mu... Mairo matso daga kutiri na...." Ta k'arashe tana janyo Mairo gam jikinta...
Gaba d'aya kallo sukabi Daddah dashi itako ko a jikinta batama san tayi ba. Umma Marie dai abin mamaki ya bata, ta shiga binsu da kallo d'aya bayan d'aya...
Hafiz ya dubi Iyayensa kafin yace "Baba inaga Umma Marie ya kamata ta sani tinda ita kad'aice danginmu a garin nan, sannan ko bamu sanar da ita ba nan gaba zata sani..."
Yaya Azumi ta jinjina kai kana tace "Hakane Hafiz..."
Take Hafiz ya sanar dasu komai duk abinda ke faruwa...
Sosai su Umma Marie suka tausaya ma wannan mutumi sannan suka buk'aci likita da ya auna jininsu idan yayi a d'iba tunda ceton rai ne... Nan fah Daddah tace bataji ba bata gani ba babu mayen da zai d'ibi jininta dana d'iyarta, saida Mairo ta nuna mata b'acin ranta sosai kafin ta amince...
Wani ikon Allah kuwa cikinsu gaba d'aya jinin Mairo ce yayi dai-dai dana wannan mutumi, take aka kuwa d'iba aka k'ara masa, saidai ba'a barsu sun shiga sun gansa ba don har lokacin bai farka sannan zai iya d'iban kwanaki kafin ya farfad'o....
*SameenaAleeyou📚**FUSKA UKU*🏮
*44*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
Mairo na kwance saman gadon da aka d'ibi jininta su Daddah suka shigo, dan Likitocin sun buk'aci karta tashi har sai ta sami hutu sosai domin kuwa ba k'ank'anin jini aka d'iba a jikinta ba, Daddah tana shigowa ta fad'a kan Mairo tana tambayarta yaya takeji....
D'an murmusawa kurum Mairo tayi kana tace "Banjin komai Daddah sai rashin k'arfin jiki ki kwantar da hankalinki kinji, banso ki damu lafiyata lou...."
Daddah na rik'eda hannunta take fad'in "Dole hankalina ya tashi d'iyata, duk abinda zai sameki a duniyar nan zanyi fatan ta sameni amaimakon ke...."
Murmushi Mairo take tana duban yanda Daddah ta d'aga hankalinta kuma ta damu, tabbas Daddanta tana sonta shiyasa wani sa'in koda tayi wani abin takan mata uzuri duba da yanayin halinta da kuma shekaru da suka soma sauk'o mata... Su Umma Marie su Yaya Azumi da Baba Malam duk suma sun shigo sun mata sannu tareda k'ara mata godiyan jihadin da tayi domin wannan dangin jihadi ne, gata mace mai rauni da kuma fitar da jini duk wata hakan baisa tak'i baida jininta ga wannan bawan Allahn ba domin ceto rayuwarsa...
Hafiz ne yayi sallama ya shigo d'akin hannunsa d'auke da bak'ar leda, gaisar da Mairo shima yayi kana ya isa gefen Daddah ya mik'a mata bak'ar ledar yana mai fad'in "Likita yace ta shanye duka biyu domin ta sami k'arfin jikinta..."
Daddah ta jinjina kai tanai masa sannu kafin ta shiga bud'e ledar ta ciro gwangwanin maltinar guda biyu....
Wasu 'yan awanni Mairo tayi a kwance kafin Dr Sahal yace zata iya tafiya saidai zuwa dare ma idan son samu ta sake shan Maltina koda gwabgwani guda ne, sannan ake mata pate ko miyan ganyen inyamurai ta Singapore ci har na tsawon sati guda...
Kota kan wannan bawan Allah su Daddah basubiba suka nufi gida da Mairo domin ita kanta tana buk'atar jinya....
Hafiz ma bai iya zaman asibitin ba dole yabi sawunsu don hankalinsa sam bazai kwanta ba sai yaga halin da Maironsa ke ciki....
***
*Tambuwal*
Kwance ta hangi Zaliha har lokacin bata mik'e ba kaman ta mance yau d'in nan zasu tafi, saida Umman Zaliha ta shigo d'akin sosai idanunta suka sauk'a kan sark'an bead wanda tasan shakka babu Mairo ce ta bata.... D'an murmusawa Umma tayi kafin ta k'arasa ga Zaliha ta d'an dafata
"Zali ki tashi ki shirya kinga Babanki yace motar k'arfe biyu zamubi yanzu kuwa d'aya ma ta gauta...." Ta k'arashe tana mai janyo akwatin Zalin...
Share k'wallan da suka zubo mata Zaliha tayi kana tace "Umma wllhi ji nake kaman kar na tafi kaman nayita zama k'ila wata rana su Mairo zasu dawo, zamu sake ganin juna.... Ga Nazir ma tunda ya tafi shiru bai kuma waiwayomu ba, wai shin haka rayuwar take, kana sanin mutane kuma suna barin rayuwarka, Umma wllhi yanzu har tsoron sabo da mutane nake, wai Umma Abbah bazai iya canza aikin nan nasa ba kawai ba sai mun bar garin nan ba, kinga bamu tab'a zaman wani gari bafa sai nan..." Ta k'arashe tana mai jefa sark'ar cikin jakan kayanta....
Umma ta kuma murmusawa kana ta kamo hannun Zaliha tace "Ki kwantar da hankalinki Zaliha idan da rabo wataran zaki kuma had'uwa da Mairo sannan wajen aiki su suka zab'i su canzawa mahaifinki kuma kinga bazaice ya ajiye aikinsa ba kawai dan iyalansa basa son barin garinsu, wannan aiki dashi yake nema mana abinda zamuci, ki kwantar da hankalinki kinji koh...."
Jinjina kai Zaliha tayi kana ta rungume Ummanta tana addu'an Allah ya amshi bakin Umma watarana ta sake had'uwa da k'awarta Mairo....
Mahaifin Zaliha Gandiroba ne yanda aka masa transfer daga garinsa zuwa garin Suleja ta jihar Niger domin ci gaba da aikin kulada fursunoni a can prison na garin Suleja..
***
*Abuja*
Kaman yanda suka tsara yau ce ranar da Junaid zai fuskanci family d'inta, dan already ta sanar da kowa yau d'in tanada bak'o daga foundation d'insu wanda a wajenta ya wuce abokin aiki kurum, yanada matsayi babba cikin zuciyarta, kowa a gidan saida ya fahimci hakan....
Daga saman bene Nana H ke hangosu sanda Malam Sile ya ida parking motar kana ya k'araso da sauri yana bud'ewa Junaid front seat yayinda Nana A ta fito daga bayan motar tana mai k'ok'arin janyo wheelchair d'insa da aka nad'e a gefenta sabida shiga mota da zaiyi, cikin sauri Malam Sile ya k'araso ya amshi wheelchair d'in yana mai fad'in "Haba Hajiya ai da kin bari zan d'auko masa..."
Nana A na murmushi take fad'in "A'a babu komai Malam Sile ai zan iya...."
Batakai aya ba suka jiyo muryar Nana H daga saman bene ta window tana fad'in "Kai Malam Sile bakaji mai tace bane, zata iya... Besides Sister gwara ki soma koyon taimakon gurgun mijin naki kafin kuyi auren... Gaskiya kin burgeni Nana A...." Ta k'arashe tana mai tafe hannaye had'ida furta "Bravo...!"
Malam Sile dai girgiza kai kurum yayi kafin ya ware kujeran Junaid ya saka masa yayinda Nana A ta d'an girgiza kai had'ida fuzar da iska, wani sa'in idan Nana H tayi wani abin sai suga kaman mutuwar mijin nata bai dameta ba, bacin haka yaya za'ace mata mai takaba ce wannan...
Shiko Junaid k'uri ya mata daga saman benen kafin ya dawo da dubansa ga Nana A wacce ke k'ok'arin had'o kalma domin basa hak'uri garin irin ta na farko da ya samu a gidansu...
Cikin sauri ya shiga girgiza mata kai kyakkyawan murmushi saman fuskar sa kana yace "It's okay, kar ki damu na ganeta tun ranar da muka had'u a foundation, dole a gida a samu irin haka wani sa'in, kar ki damu kinji..."
D'an langab'ar dakai tayi kana tace "But dole na damu, ai ni na kawo ka...."
Girgiza mata kai ya kumayi kana yace "Ban damu ba gorgeous and idan kina son ganin damuwata shine ki shiga damuwa nan ne zakiga hankalina ya tashi..."
D'an murmusawa tayi cikeda jin dad'i kafin ta soma turasa a wheelchair d'in suka nufi cikin gida....
Aiko suna shiga ta shiga rangad'awasu Ammah da Ayiya kira, Rabbeca ce ta fito daga hanyar da zai sadaka da kitchen tanai masu sannu da zuwa... Lokaci guda Nana ta nufi upstairs tana mai sanar da Junaid she'll be right back... Jinjina mata kai yayi yana mai k'arewa gidan kallo yanda aka kashe Naira tamkar a turai....
Yana cikin kalle-kallen ne Nana H ta sauk'o cikin takunta na isa, ko mayafi babu jikinta wai sunan mai takaba.....
"Hello cripple.... Barka da zuwa, naga alama 'yar uwata ta aminta dakai although ni ban yarda dakai ba I'm quite sure you're after her money, you don't love her... I'm sure of it...." Ta fad'i tana mai murmusawa had'i da k'arasa shigowa cikin parlorn, lokaci guda take jinjina kai alamun tana tabbatar da abinda ta fad'i....
Kallo Junaid ya bita dashi kana shima ya murmusa yace "Barkanki, kinyi kama sosai da Nana A saidai FUSKARKU ne kurum iri guda amma kowa da halinsa, a zahiri Nana A itakeda nakasa amma a b'angaren hallaya taki halin ne nakashasshiya don na tabbata da za'a baki hoton d'abi'arki kiga yanda yake looking tabbas bazakiso ba, bayan gurgu ne haka nan yake da muni ba kaman yanda fuskarki keda kyau ba, and yes na saye zuciyar 'yar uwarki kaman yanda kika gani, and there's absolutely nothing you can do about it..." ya k'arashe yana mai d'aga mata gira guda
Mutuwar tsaye kurum Nana H tayi tana kallon wannan shegen gurgun yanda yake watsa mata bak'ak'en maganganu... Bata ida shan mamaki ba ta jiyo muryarsa yana fad'in "Oh by the way, I heard that you lost your husband...." Ya d'an tab'e fuska kana yaci gaba da fad'in "What a pity..." Lokaci guda kuma ya saki murmushi ganin looks d'in da takedashi a fuskarta kana yaci gaba da fad'in "Kodayake kaman mutuwar bai dameki ba balle na mik'a maki ta'aziyata k'ila mutuwarsa ke kanki ya fiye maki rayuwarsa ne.... Am o right...?" Ya k'arashe murmushi saman fuskar sa...
Huci Nana H kurum take don tama rasa mai zata fad'i, isowan su Ayiya da Nana A ya sanya Junaid tura kekensa ya nufesu, cikeda rusunawa yake gaida Ayiya, Cikeda jin dad'i Ayiya tayi hanyar kitchen don kawo ma Junaid abin tab'awa, lokaci guda take umartansa da ya saki jikinsa....
Nana A takai dubanta ga Nana H da ko juyowa ta kasa yi domin bata ida had'iyan maganganun da Junaid ya gama watsa mata ba... Lokaci guda Nana A ta maido da dubanta ga Junaid d'in kana tace "Lafiya dai ko...?" Ta tambaya ta mai dubansa daga shi har Nana H d'in...
Murmusawa Junaid yayi kana yace "Lafiya lou, nayima 'yar uwarki ta'aziya ne na babban rashi da tayi, hak'ik'a rasa masoyi babban rashi da bai misaltuwa, na tausaya mata sosai...." Ya k'arashe damuwa fal fuskar sa...