← Book details Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 98

Sashe 57

Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana mai daidaita zaman suit d'in jikinsa yake fad'in "Wllhi Estates d'in da bamu jima da saya bane wuta ya kamasu, yanzu haka fire service sunata iya k'ok'arinsu wutan tak'i cinyewa, Allah yasa babu kowa cikin gidajen.... Zan tafi yanzu, and please office d'ina na hannunki don bansan yaushe zan dawo ba..." Daga haka ficewa yayi cikin sauri wani wayar na shigo masa....

Komawa kurum Azeeza tayi ta zauna cikin kujera had'ida dafe kanta, itakam anya zata iya zama tanaji tana gani ana cutar da Siraj, gaskiya bazata iya ba, gwara ta tattara ta koma Damaturu k'ila can tafi samun kwanciyar hankali....

Kafin ta bar office d'in saida ta tattara masa duk wasu takardunsa dake bisa table tayi ta maidasu cikin folder a gefe, gaba d'aya Azeeza wani iri take jinta, zuciyarta ta cika da damuwa sosai.. Daga office gida ta wuce straight....

Tindaga bakin gate ta hango yayanta Junaid zaune a farfajiyan gidan da alama dawowarta yake jira, take wasu sabbin k'walla suka ciko idanunta, tausayin yayanta ya shiga ratsa zuciyarta, take zuciyarta ta soma tuhumarta da laifin cin amanar Yayanta d'an uwanta d'aya tak da ya rage mata.... Babu yanda ta iya dole ta tafi ta barsu daga shi har Siraj muddin tana so ta sami nutsuwa cikin zuciyarta

Hannu tasa tana share hawayen da suka zubo mata kafin ta k'arasa gaban Yayan nata tana mai ci gaba da share hawayen dake zubo mata d'aya bayan d'aya

Bai iya ce mata komai ba sai k'ura mata idanu da yayi....

Cikin kuka Azeeza ta soma fad'in "Yaya I'm sorry, I'm sorry Yaya Junaid, but I can not do this anymore.... Yaya kayi hak'uri I failed you...." Kuka ya hanata ci gaba da magana....

Girgiza kai Junaid yake yana mai ci gaba da dubanta kana yace "I don't get you Zeeza, what exactly do you mean... Mai kike nufi....?"

Kallonsa ta kumayi wani kukan na zuwa mata kana tacI gaba da fad'in "Yaya you see, I was about to tell Siraj the whole truth... But then something came up.. And....." Bata kai aya ba Junaid dake faman hura hanci cikin bugun k'irji ya turo wheelchair d'insa gabanta had'i da kamo hannayenta duka biyu, cikin tsananin d'aga murya yake fad'in "Zeeza and what....? Tell me Zeeza did you tell that imbecile about my plans... Did you....?" Ya k'arashe idanunsa na tsarto da wani irin ruwa....

Girgiza kai take ba tareda ta iya furta koda kalma ba....

Shima Junaid d'in hawaye ke fitowa daga idanunsa sanda yaci gaba da fad'in "Zeeza you're so reckless, baki san cewa idan Siraj yasan gaskiya ba harda ke abin zai shafa sannan zakiyiwa Nasaar asarar aikinsa, idan kikayi haka baki kyautawa Nasaar ba...."

Cikin d'aga murya tace "That's exactly why I want to leave, that's why I want to disappear.... Yaya wllhi bazan iya ba, I'm leaving to Damaturu right this moment...." Ta k'arashe tana mai shigewa cikin gida cikin sassarfa tana mai share hawayen da suka wanke mata fuska...

Cikin sauri Junaid ya take mata baya yana ambato sunanta, k'ok'arin tattara kayanta take sanda Junaid ya paka daga gefe yana dubanta, hawaye masu zafi basu daina fitowa daga idanunsa ba....

A hankali ya soma fad'in "Are you really leaving me Azeeza, da gaske zaki tafi ki barni, kar ki manta bakida kowa saini sannan banida kowa sai ke.... Azee don't leave me..." Ya k'arashe yana kamo hannayenta

Girgiza kai take tana dubansa kafin taci gaba da fad'in "Yaya learn to love yourself please.... Matsalarka shine ka kasa son kanka, ka kasa accepting k'addarar da mahalaiccinka ya d'auro maka, shin Yaya baka tab'a sanin idan mutum bai mutu ba Allah bai gama masa halitta ba, bayan wannan Zeenah bazata tab'a wuce tata k'addarar ba itama.... Haba haba saikace babu zuciya cikin k'irjinka, karfa ka mance mun rasa iyayen mu, waye zamu kuma rasawa kamarsu a duniyar nan... Yaya don Allah open your eyes and see, kar ka bari shed'anin dake jikin ka yayi nasara akanka..." Ta k'arashe cikin kwantar da murya had'ida tausasa harshe....

Gefe guda yake duba lokaci guda maganganun Azeeza ke yawo a kwanyarsa.... Juyowa yayi yana dubanta fuskar sa tayi ja gaba d'aya sanda ya soma fad'in "No Azeeza, I won't back down, not, never.... Until I get justice for my self and my Zeenah..... Those three most pay for what they did... And you've to help me finish what we've already started..... If not zaki rasani for good, your only brother, your only family left....."

Kallonsa kurum take tana girgiza kai kafin ta silale k'asa tana mai ci gaba da kuka... Ko takanta Junaid bai kuma bi ba yayi ficewarsa daga d'akin, can k'asar zuciyarsa yana jin babu abinda zai hanasa k'arasa abinda ya fara only then zai zama free daga alk'awarin da yayima Zeenah.....

***

*Damaturu*

Bayan shud'ewar wasu awasu awanni Dr Sahal ya fito daga d'in tiyatar yana mai share zufan dake bisa goshinsa da farin handkerchief...

Cikin sauri suka mik'e gaba d'aya suka nufi Dr Sahal, take ya buk'aci yayi magana da Baba Malam, ya kuma umarcesu dasu kwantar da hankulansu domin anyi aikin cikin nasara kuma da ikon Allah zai sami lafiya, ... Da wannan batu na Dr Sahal Hafiz da mahaifiyarsa suka sami natsuwar zuciya, shi kuwa Baba Malam takewa Dr Sahal baya yayi suka nufi office d'insa...

Bayan ko wannensu ya daidaita saman kujera Sahal yayi gyaran murya kana ya soma fad'in "Baba anyi aiki cikin nasara da yardar Allah, mun godewa Allah don ban zaci abin zai zo mana da sauk'i kaman haka ba, abinda yasa bamu kaisa can babban asibitin gwamnati ba shi sai anyi wasu cike-cike sannan zai d'auki lokaci kafin ayi aikin tunda asibiti ne na gwamnati kuma kaga ga yanayin case d'in nasa wannan dalili yasa muka kawo majinyacin asibitin abokin aikina wanda ba na gwamnati ba, da kuma taimakonsa muka gudanar da aikin...."

Baba Malam ya jinjina kai kana yace "Haka ne Likita, ai babu abinda zamu iya biyanku dashi saidai muce Allah ya biyaku da mafificin alkhairi..."

D'an girgiza Kai Sahal yayi kana yace "Babu komai Baba amfanin likita kenan cikin Al'umma, abinda nake son sanar dakai shine wannan mutumi ya sami raunuka cikin jikinsa kaman yanda na sanar daku daga farko,.."

Baba Malam ya jinjina kai yana mai fad'in "Haka ne likita.."

Sahal ya kuma jinjina kai had'ida d'an fuzar da iska kana yaci gaba da fad'in "Baba a zahirin gaskiya jini ya zuba sosai a jikinsa, sannan jini ya d'an tab'a kwanyarsa kad'an wanda mukayi nasarar cirewa cikin yardar Allah... Amma kuma wani hanzari ba gudu ba... A gaskiya Baba koda wannan majinyaci ya sami lafiya dole ya iya rasa d'aya ko fiyeda d'aya cikin abubuwan da zan lissafo maka, kodai ya rasa hankalinsa ma'ana ya sami tab'in hankali ko kuma ya rasa jinsa ko ganinsa ko ya rasa tunaninsa ma'ana tunaninsa ka iya shafewa sabida ikon Allah ne kurum zai raya mutumin nan, don tunda nake aikin likitanci ban tab'a gamuwa da mutumin da ya sami mummunar had'ari irin na wannan mutumin ba.... Sannan abu na k'arshe munada buk'atar jini cikin gaggawa a k'ara masa, don cikin mu biyu dagani har abokin aikina babu wanda jininsa ya dace da nasa, kai Baba girma ta sauk'o maka balle mu auna naka idan ya dace mu d'iba amma...."

Cikin sauri Baba Malam ya katse sa da fad'in "A'a likita ceton rai ne, ka auna nawa idan baiyi ba ka auna na iyalai na, fatanmu Ubangiji ya tada kafad'un wannan bawa nasa, kar kaji komai likita...."

Jinjina kai Dr Sahal yayi kana yace "shikenan Baba zamuyi yanda kace zamu auna...." Daga haka mik'ewa sukayi a tare suka fice daga office d'in...

Koda aka auna jininsu babu wanda nasa ya dace da na wannan mutumin, ana haka su Umma Marie suka iso hankali tashe, Mairo da Daddah sai dannan Umma Marie suke suna fad'in insha Allah babu abinda zai sami Kawunta Baba Malam....

Sosai Hafizu yayi mamakin hangosu Umma Marie suna k'ok'arin shigowa reception sai sannan ya tuna sanda sukayi waya Umma Marie ta tambayeshi asibitin da suke kuma bai sanar da ita wani mutumin suka kawo ba, tabbas dole hankulansu ya tashi don jiya ce masu yayi Baba Malam na nemansa cikin gaggawa dole suyi zaton k'ila Baba Malam d'in ne babu lafiya ko Mamansa Yaya Azumi.... A hankali ya dafe kansa don tun jiya d'in basu sami natsuwa ba daga shi har iyayensa...

Turus su Umma Marie sukayi ganin su duka ukun a reception...

Baba Malam ya mik'e yana tambayarsu lafiya yaya ya gansu haka....?

Daddah baki sake tace "Yo ai ku zamu tambaya bawan Allah, jiya Malam Hafizu bai mana karatu ba ya tafi afujajan cikin tsananin tashin hankali yana mai sanar damu kana neman sa cikin gaggawa.... A daren hankalin Mariya ya tashi taso zuwa muka danneta mukace ta bari gari ya waye, haka dai muka kwana muna dannarta don ta sanar damu jikinta na bata wani abin ne ya sami kawunta, toh safiyar yau d'in nan muka nufi can gidanka bamu taddaku ba, shine muka yanke shawarin ta kirawo Hafizu ta tambaya, Hafizu ko yace kuna asibiti kaji dalilin da yasa muka taho...." Ta k'arashe koro bayanin tana mai zama saman kujera....

Baba Malam ya girgiza kai kurum yana mamakin shirirta irinta Hafizu bacin haka yaya zai sanar dasu suna asibiti gashi tun jiya basuji daga garesu ba ga halin da ya barosu ciki ai dole hankali ya tashi....

D'an girgiza kai Baba Malam yayi kana yace "Ku kwantar da hankulanku babu abinda ya samemu lafiya lou muke...."

Umma Marie na share ragowar hawayen idanunta take fad'in" Amma Kawu wajen wa kuka zo asibiti gaba d'ayanku tun safe tinda nasan danginmu gaba d'aya basa garin nan suna Taraba...."
Gaba d'aya suka dubi juna, Baba Malam Hafiz da kuma Yaya Azumi... Kafin su sami zarafin magana Dr Madi abokin aikin Dr Sahal ya k'araso yana tambayar "Kuma kunzo a auna jinin naku ne ko za'a sami wanda yayi....?"
Chapter 57 · 0% Book details