← Book details Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 98

Sashe 24

Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sanye take cikin doguwar riga ta atampa kalan shud'i mai manyan zane, ta yafa mayafi kalan hoda wanda ya tafi da kalan jikinta... Idanunta a k'asa sanda Siraj ya k'ura mata dogayen idanunsa akanta, so yake ya d'auke idanunsa daga dubanta amma ya kasa,...

Saida ta iso dai-dai bakin table d'insa taja ta tsaya sihirtaccen murmushi saman fuskarta...

"Barka da safiya Sir... May I....?" Ta k'arashe tanai masa nuni da kujerar dake gaban table din had'i da juya idanu

*SameenaAleeyou📚**FUSKA UKU*🏮
*FUSKA UKU*🏮

*17*

*©Sameena Aleeyou...✍🏽*

Ko motsa idanunsa daga kan Azeeza ya kasa, k'yam ya kafeta da idanu babu ko k'yaftawa fuskar nan nasa kuwa lokaci guda ya had'eta gaba d'aya....

Azeeza tasha jinin jikinta domin fuskar Boss d'in nata yafi kama da a kirasa Tyrant.... A hankali ta zame hannunta daga jikin kujeran tana d'an gyara mayafinta had'i da yin gyaran murya....

Sai lokacin Siraj ya dawo daga duniyar tunanin da yayi nisa cikinta, gyara zamansa yayi saman kujerarsa ta alfarma kana ya mata nuni da kujeran dake gaban table d'in

"Please sit down...!" Yayi maganar babu alamun wasa a fuskar sa...

Murmushin yak'e kawai Azeeza tayi kana ta zauna tanai masa godiya. ..

Ya jima yana wasu 'yan rubuce rubucensa ba tareda yace mata kanzil ba, har dai Azeeza ta saduda cewa wannan Tyrant d'in baida niyyan mata magana.... Kaman kuwa yaji zancen zucin nata mik'ewa yayi yana daidaita zaman suit d'insa kana ya soma tafiya ya nufi k'ofa waya mak'ale a kunnensa..

Baki sake Azeeza ta bisa da kallo, lallai wannan ya cika d'an rainin hankali toh mai yake nufi da zamanta a nan ita da ta shigo interview yayi tafiyarsa ya barta, what does this mean....? Babu mai bata amsa tambayarta, kaman daga sama ta jiyo muryarsa yana fad'in

"Get my things over there and follow me...." daga haka sa kai yayi ya fice daga office d'in...

Azeeza tabi bayansa da kallo kafin ta maido da dubanta ga table d'in nasa tana lissafin toh waima wasu stuff yake nufi, file d'in kenan hala.... Cikin sauri ta shiga had'e takardun tabi bayansa cikin sauri kafin ya b'ace mata, da shike kana iya hango wajaje da dama cikin Company d'in abinka da ginin da yasha kwalliya da glass...

Daga office d'insa ya hangota rungume da file sai sauri take tana bin bayan Siraj, k'irjinsa ya buga, ta yaya Siraj zai fita da Azeeza daga soma aikinta a company d'in... K'irjin Nasaar ya shiga masa zafi sosai, meyasa ma tun fari ya aminta Azeeza tayi aiki da Siraj, anya baiyi kuskure ba? Kai dole yasan abin yi he loves Azeeza so much bazai iya barinta ma kowa ba, Azeeza tashi ce.... A hankali ya shafi naman goshinsa yana tunanin tun wuri gwara ya sanar da ita abinda ke cikin zuciyarsa kafin yayiwa kansa sakiyar da ba ruwa....

Gaba d'aya files d'in neman watsewa kawai suke a hannunta, kuma sabida tsaban mugunta subi ta lift basu biba, ta matakala Siraj yabi dasu, ta gaji iyaka gajjiya,....

Da k'yar take numfashi sabida yanda ta jigata, a wahalce ta soma fad'in

"Sir! Please Sir wllhi na gaji, dan Allah kace mun iso floor d'in, wayyo Allah na wllhi na gaji bazan iya ci gaba da tafiya ba....." Ta k'arashe tana durk'usawa wajen gashi takalamin k'afarta wedge ne mai tudun gaske....

Juyowa yayi yana dubanta yanda ta durk'usa a wajen alamun gajjiya, a hankali ya tako ya dawo da baya had'ida d'an kwanto da kansa dab yanda take a durk'ushe kana ya d'an rage murya yace "You have to... You must, if you really need this job.... This is also part of your interview... Oya tashi muje, we almost there...." Yana ida fad'in haka ya mik'e yana mai ci gaba da tafiya....

Harara kurum ta rakasa dashi tana nan durk'ushe a wajen, lokaci guda ta tuna she's doing this for her only brother, she promised not to let him down... She really need to put up with this Tyrant, lokaci guda ta mik'e taci gaba da binsa, ganin ya kusa b'ace mata ya sanyata k'walla masa kira tana binsa cikin sauri....

Saida suka kusa zagaya cikin kampanin tana biyeda Siraj wanda ko a jikinsa da jigatan da tayi wayarsa ma yakeyi, da alama bai fin mintuna goma bai d'aga waya ba....

Saida suka iso dai-dai wajen wasu kujeru na shak'awata Siraj ya k'arasa saman guda d'aya ya zauna, waya manne a kunnensa yake mata nuni da kujeran gefe...

Saida ta juya idanu had'i da jan k'aramin tsaki kana ta ajiye file d'in saman table d'in da iya k'arfinta kafin ta zauna had'i da hard'e k'afafu d'aya kan d'aya, fuzar da iska tayi ta shiga bin Kampanin da kallo, tabbas babba ne sabida koda zasu zo bata nan suka shigo ba....

Wani ma'aikaci ne mai sanye da farin uniform ya k'araso da tray a hannunsa glass cup guda biyu bisa, ya ajiye masu saman table d'in had'i da gaida Azeeza, ko amsa sa batayi ba don gaba d'aya wani irin haushin Siraj take ji.... Saida ya shafe mintuna kusan talatin yana wayar kafin ya d'an sarara da wayar nasa, idanunsa naga wayar yake fad'in

"K'arfe takwas nake shigowa building d'in nan, before 8am my coffee must be ready ko wace rana, sannan ba'a k'aramin komai kan schedules d'ina idan suka riga suka zama ready... Abu na gaba I don't tolerate coming late, and.... You also need to prioritize your job, bana d'aukan excuses....." Lokaci guda ya d'auki glass cup d'aya ya kurb'a yayinda Azeeza ke faman binsa da kallon mamaki....

Murya a d'an dake tace "Naji dokokinka Sir and insha Allah zan kiyaye...."

Batakai aya ba ya katseta da fad'in "Abu na k'arshe bana tolerating kawo samari wajen aiki, as far as kina wajen aiki babu kula samari koda a waya ne sai lokacin tashi yayi... Kin fahimta...?" Ya k'arashe yana ware mata dogayen idanunsa a fuskarta wanda tuni ya sanyata sadda nata idanun k'asa...

A hankali ta shiga jinjina masa kai, dole ta masa biyayya idan ta tuna wa Junaid take duka wannan.... Lokaci guda ta jiyo muryarsa yana ci gaba da fad'in "Good, so now Janet zata nuna maki komai.. Congratulations once again Miss Azeeza...." Ya k'arashe yana mik'ewa tsaye...

Yanda ya ambato sunanta babu ko gargada ya sanayata kuma dubansa saidai tuni ya bar wajen cikin tafiyarsa da tafi kama da sassarfa...

Azeeza tabi bayansa da kallo, ya bar wayansa guda a wajen ga shirgin takardun da ya sanayata tattarowa, uwa uba ita batama san ta yanda ta nufa ba a wannan huge building d'in.... D'an fuzar da iska tayi sanda tunanin Nasaar ya fad'o mata kafin ta ciro wayarta cikin jaka ta shiga dialing layin Nasaar....

***

*Misau*

Shikam yanzu har ga Allah yarinyar dariya take basa tama daina basa takaici, murmushi mai bayyana hak'wara yayi sanda ya tuna safiyar yau yanda ta shigo masa d'aki gaba gad'i babu ko sallama balle neman izinin shiga wai ita a dole ta kawo masa abin kari, yanda ta gansa daga shi sai gajeren wando ya sanyata k'walla ihu wanda saida su Baffah da Innah suka nufo wajen, abinda zai kuma baka dariya sai tsalle take tana rintse da idanu tana fad'in D'angayu kayi hak'uri wllhi Innah ce ta aikoni, wllhi ba laifina bane..... Har saida Innah ta kad'ata d'aki kafin tayi shiru ta daina tsalle-tsalle da rintse idanun, shi baima san yanda Innah ta samo yarinyar ba don ko d'azu da ya tambayeta yanda ta samo yarinyar sai ce masa tayi zata sanar dashi komai, shi sam ji yayi bai sake da zaman yarinyar a gidan ba...

Wata iriyar yarinya mai ban takaici da dariya... Girgiza kai kurum yayi kafin ya janyo wayarsa ya shiga dialing layin matarsa....

Bugu biyu a na uku ta d'aga har lokacin bata daina kukan abinda Uncle Luv yayi mata ba..

"Hello Heedj...!" Kasa ci gaba da magana tayi sai sabon kuka da ta fashe masa dashi...

Hankali tashe Ahidjo ya mik'e had'i da ficewa cikin sauri sabida k'aranci service na waya dake cikin gidan...

Daga yanda Deejoh ke shanya ta hango fitarsa cikin sauri, sauri-sauri itama ta take masa baya..

Daga d'aya b'angaren cikin kuka Nana H taci gaba da fad'in "Heedj I just can't stand them all anymore... Dan Allah ka dawo wllhi duk sun tsaneni a gidan wariya suke nuna min.... Heedj ka dawo dan Allah bazan iya rashinka na tsawon kwanaki ba...." ta k'arashe cikeda kuka irinta makirci..

Ahidjo ya shafi naman goshinsa cikin sigan lallashi ya soma magana....

"Alright sweetheart, I'm sorry OK, ki kwantar da hankalinki ki daina kuka I'll soon comeback to you insha Allah OK... As soon as I'm done with this investigation zan dawo kinji sweet...."

Cikeda shagwab'a tace dashi "I love you my Heedj..."

Murmushi ya d'anyi soyayyar matarsa na kuma dabaibaye zuciyarsa kana yace "And I love you too Sweet... So much... Ki daina kuka ki kulamin da kanki kwanan nan zan dawo kinji koh...." Ya k'arashe cikin sigan lallashi

Kalamansa na k'arshe kurum Deejoh taji, toh da waye D'angayu ke waya, da gaske har zai kuma tafiya ya bar Innah... Allah sarki ta taya Innah murnan dawowarsa sai gashi kuma kwana d'aya tak yayi yana maganar komawa.... Lokaci guda taji jikinta yayi sanyi sosai... Cikin sauri ta juya zata shige cikin gida saidai tuni Ahidjo ya ganta, mamaki ya cikasa, maike damun wannan yarinyar? Lab'e take masa kokuwa mai.. Lallai gwara ya saita ta tun wuri kafin ta jik'a masa aiki....

A d'ari ya take mata baya taku kad'an ya cimmata a dai-dai zauren shiga cikin gidan, lokaci guda yakai mata damk'a....

Deejoh uwar tsoro zata saki ihu Ahidjo yayi amfani da hannunsa guda ya toshe bakinta... Giran sama da k'asa ya had'e yana watsa mata mugun kallo lokaci guda ya sungumeta ya nufi sashensa da ita...

Deejoh sai faman wutsil-wutsil take tsoro ya cikata domin kuwa tun ba yanzu ba Innah tasha fad'i mata kada ta yarda wani namiji yakai hannu jikinta, don namiji na tab'aka zakayi abin kunya abin nunawa a gari, shikenan ta shiga uku ta mutu ta lalace shikenan D'angayu ya tab'ata wayyo Allahnta, shisshiginta ya janyo mata....

Bai direta ko ina ba sai d'akinsa...
Chapter 24 · 0% Book details