Sashe 36
Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Innah ta kuma murmusawa had'i da girgiza kai kana taci gaba da fad'in "Gaje ba mahaifiyar Deejoh bace kishiyar mahaifiyarta ce, mahaifiyar Deejoh ta rasu da jimawa, mahaifinta kuwa bashida ta cewa a gidansa sai abinda Gaje tace.... Deejoh marainiya ce wacce ta tashi cikin tsananin maraici... Tausayi da k'ok'arin ceto rayuwar Deejoh daga hannun muguwar nan yasa muka nema maka aurenta domin bamuda zab'i, hakan ne kawai zai fitar da ita daga k'angin data tsinci kanta ciki.... Kaji tak'aitaccen tarihin Khadijatu...."
Jinjina kai yayi cikeda tausayin Deejoh kana ya mik'e yace da Innah "Idan ta gama karatun ta kawo min shayi d'akina..."
Innah ta jinjina kai tace "Toh Babana zata kawo maka...."
D'an rusunawa yayi had'i da amsawa kafin ya nufi verandar Baffah ya gaidashi dukda a ciki-ciki yake amsa masa...
Tinda ya shige d'aki tausayin Deejoh da tunaninta ya cika zuciyarsa, shi harga Allah a tsarinsa idan ya tafi da ita ba'a matsayin matarsa zai tafi da ita ba saidai ya tafi da ita matsayin 'yar aiki da aka tilasta masa zuwa da ita daga gida don harga Allah baisan ta yanda zai soma sanar da matarsa aure aka masa ba, auren ma da k'aramar yarinya wanda da yayi aure da wuri da ya haifeta.... Shi bama wannan ba, tausayi yarinyar take basa ya zaci Fulani sun daina wannan auren wanda shi a wajensa child abuse ne ashe dai basu daina ba.... Shafe sumarsa yayi had'i da d'an fuzar da iska.... Sallaman ta ya katse masa tunanin da yake...
Idanunta a k'asa har ta k'arashe shigowa d'akin yayinda Ahidjo ya shiga bin duk wasu b'angarori na jikinta da kallo... Bai tab'a k'arewa jikinta kallo ba sai yau, shi kansa baisan dalilinsa na yin hakan ba, iyaka dai yasan so yake yaga yanayin girman jikinta da har za'ayi tunanin mata aure don shi kullum fuskarta kawai yake kalla....
Gefensa ya nuna mata yace ta dawo wajen ta zauna.... Ba tareda ta kawo komai cikin zuciyarta ba ta komo wajen ta zauna.... Ahidjo yaci gaba da kurb'an shayinsa yana kuma k'are mata kallo.... Ji yake wani abu na tsargar masa cikin jikinsa.... Tunda ya soma bin jikinta da kallo yake jin wani abu nai masa yawo... Saurin rintse idanunsa yayi yana k'aryata zuciyarsa dake gaya masa wani abu gameda Deejoh....
Deejoh kam gaba d'aya ji tayi yau d'in bata sake dashi ba... Ji tayi tsikar jikinta na tashi musamman data d'ago idanu taga irin duban da yake mata.... Gabanta ya yanke ya fad'i lokaci guda.... Ta d'an yunk'ura zata tashi, harda d'an rawar murya take fad'in "Barin je kar Innah ta nemeni..." Saidai kafin takai aya taji hannunsa cikin jikinta ya rik'ota...
Dubansa ta d'anyi cikeda tsoro saidai kafin tayi magana ta jiyo muryarsa na fad'in "Innah bazata nemeki ba tasan kina wajena.... Kuma kin mance nace yau zakimin labarinki...."
Itakam wani irin kunyarsa da nauyinsa takeji.... Bata iya cewa komai ba sai zama da tayi wannan karan daga can gefe ta zauna....
A hankali yaci gaba da sipping shayinsa lokaci zuwa lokaci yana dubanta, ko wannensu da abinda ke sak'awa cikin zuciyarsa....
Koda ya gama shan shayin ma kasa sakin jiki tayi dashi, shi kad'ai ya dinga mata labarai dana ban dariya da kuma na wajen aikinsa, k'arshe har hiran matarsa saida ya mata, abubuwan da take so da wad'anda bata so, kalan soyayyar dake tsakaninsu da sauransu.... Dukda Deejoh batasan meye kishi ba amma saida taji wani abu cikin zuciyarta...
Batasan sanda tace "nuna min matar taka naga hotonta..."
Wayarsa ya janyo dashike itace saman screen ya d'an danna power buttom ta kawo haske, kyakkyawan fuskar Nana H ya bayyana... Jikin Deejoh yayi sanyi, domin kuwa duk yanda 'yar gayu takai ga gayunta matar Yaya Ahidjo takai...
Kallo Ahidjo ya bita dashi ganin yanda yanayinta ya canza lokaci guda kana yace "Yayadai? Ko bata maki kyau bane....?"
Murmushin yak'e Deejoh tayi kana tace "Tamin kyau sosai, ta iya gayu itama kaman kai....."
Ahidjo ya murmusa kana yace "Kar ki damu idan mun tafi Abuja har gayu zata koya maki dan naga kema kina son kwalliya da gayu...."
Cikeda jin dad'i ta shiga wage baki tana fad'in "Nima zan zama 'yar gayu....?"
"Ahidjo ya kuma jinjina mata kai kana yace "Sosai kuwa zaki zama 'yar gayu kema kawai ki tayani rok'on Baffah ya amince mu tafi...."
Deejoh ta kuma jin dad'i gashi zata shiga makaranta gashi zata koyi gayu ai tuni tace "Da sassafe insha Allah zan tambayi mana Baffah..."
Ahidjo yace "Yauwa Deejah ta, ki dage cewa ke mijinki kike son bi kinji... Ki dage kina so mu tafi don ki fara zuwa makaranta...."
Deejoh ta jinjina kai tace "Haka zance masu shida Innah dama sun san ina son makaranta sosai..."
Murmusawa yake yana dubanta had'ida jinjina yarinta irinta tata kana yace "Muje na rakaki d'aki toh...."
Babu musu ta mik'e suka nufi k'ofa... Har d'akin Innah ya mata rakiya, basu sami Innah a d'aki ba don har ta wuce b'angaren Baffah...
Ahidjo ya mata rakiya har cikin d'akin kafin ya juya zai fice... Juyowa yayi ya d'an dubeta had'i da sakar mata murmushi kafin ya fice...
Deejoh ta kwanta saman gado had'ida rintse idanu zuciyarta naci gaba da bugawa da sauri da sauri...
Shiko tunda ya koma d'akinsa kasa barci yayi sai faman juyi yake saman katifa ba tareda sanin abinda ke damunsa ba.....
***
Wasa-wasa shak'uwa da sabo sun shiga tsakanin Ahidjo da Deejoh sosai a 'yan kwanakin, duk sanda suka keb'e tsintar kansa yake cikin yanayi na tsananin buk'ata, baisan dalili ba amma kam idan bai k'aryata zuciyarsa ba sha'awar Deejoh ke d'awainiya dashi, shi kansa abiga abin sha'awar a jikinta ba amma ko yaushe suka keb'e sai yaji hakan, ba abin ya avoiding d'inta ba plan d'insa ya b'aci...
A b'angaren Lamid'o da Nana A abubuwa basu tafiya yanda ya kamata domin kuwa Nana H ta kasa ta tsare duk wani yunk'urin da Lamid'o yayi sai ta toshesa, shi kansa Siraj yak'i approving d'insa har yanzu...
A b'angaren Junaid kuwa ko yaushe k'ok'arin janyo hankalin Nana A yake garesa, shak'uwa da amintaka na musamman ta kuma shiga tsakaninsu, duk yanda ka gansu a foundation toh tare suke, har wasu a foundation d'in suka soma zargin ko soyayya suke, Aunty Lami da kanta saida ta fad'i hakan... Murmushi kawai Nana A da Junaid keyi sai yace shi k'anwa ya d'auketa...
Zaune suke wajen da suka saba zama har Malam Sile yazo d'aukarta, fuskarta kawai zaka duba kasan tana cikin tsan-tsan damuwa...
Junaid ya kuma dubanta yana karantarta kana yace "Asmah that guy is your Uncle's friend.... look I'm not saying you should reject him or something.... Abinda nake nufi Uncle Siraj yafi kowa sanin Lamid'o maybe yanada reasons d'insa da yasa baya sonki dashi... Sannan Nana H abokin mijinta ne kaman yanda kika fad'a min, so kinga itama ta yuwu tasan wasu abu da dama gamedashi wanda ke baki sani ba...." Ya kuma marairaice fuska had'ida kwantar da murya kana yaci gaba da fad'in "Look Asmah.... I care about you and I don't want you getting hurt.... Think about this please..... Kinji.."
D'an murmusawa tayi cikeda jin dad'in yanda Junaid ke mata magana kana tace "Shikenan Junaid. I'll think about it I promise you..."
Murmushi shima ya sakar mata kana yace "Murmushi yafi kyau da kyakkyawar fuskar ki...." Ya k'arashe yana binta da wani irin kallon k'urillah wanda ya sanyata murmusawa had'i da rufe fuska tana fad'in "Ni daina ka daina kallo na haka..."
"Why, am I not allowed...?" Ya tambaya teasingly
Hararan wasa ta aika masa kana tace "Kai ba.... Kana son wasa ko a wajen aiki.."
Murmusawa ya kumayi sanda ya shiga tura tayun wheelchair d'insa yake fad'in "Believe me wa ke kad'ai kawai nake wasan....."
Nana ta bisa da kallo cikeda tausayin sa duk sanda ta tuna bashida kowa....
Suna a wajen ta hangi motar Nana H yauma ita tazo d'aukarta...
Murmushi kwance saman fuskar Nana A
take duban Junaid kana tace "Finally yau zanyi introducing d'inka wa 'yar uwata Nana Hafsatu..."
lokaci guda k'irjin Junaid ya buga sanda yabi Nana A da kallo... Bai sami zarafin magana ba sai k'aran parking d'in motar Nana H da sautin ya dira cikin kunnuwarsa...
D'ago idanun da zaiyi sukayi ido hud'u da Nana H tana takowa cikin k'asaita da yanga kaman yanda ta saba....
Tana k'wrasowa wajen Nana A ta k'arasa tayi hugging d'inta cikeda jin dad'i tana fad'in "Sistu yauma kin tuna dani, naji dad'i sosai..."
Nana H bata sami daman amsata ba sai duban Junaid da take babu ko k'yafta idanu...
"Asma'u wanene wannan....?"
Nana H ta tambaya idanunta akansa yayinda shima nasa idanun k'ur akanta...
*SameenaAleeyou📚**FUSKA UKU*🏮
*26*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
*Fatan Alheri Aysha Sada Machika Novels...💖*
Lokaci guda Junaid ya sakarwa Nana H murmushi kana yace "You must be Nana H...?"
Yatsina fuska kurum tayi tana binsa da kallon k'ask'anci kafin ta sami zarafin magana muryar Nana A ya katse ta...
"He's Junaid my coworker....." Ta kuma maido da dubanta ga Junaid kana taci gaba da fad'in "Junaid wannan itace Nana H 'yar uwata da nake baka labari..."
Kallon Nana H kurum Junaid yake yana jinjina kai kana yace "I see, Barkanki Nana H is a pleasure meeting you, naji labarunki da dama daga 'yar uwarki......" Ya k'arashe murmushi kwance saman fuskarsa
Kallon tuhuma Nana H ke bin Nana A dashi kana tace "Wait... Wait Nana A wai kina nufin har ma irin wad'annan shirgin kike bada labarina na.... Niko mai zai had'ani da nakasassu da zakizo foundation d'inki kina labarina... Kar ki sake banaso, banson komai yayi associating d'ina da nakasassu kin fahimta koh..." Ta k'arashe tana kuma yatsina fuska...
Sosai jikin Nana A yayi sanyi da irin cin zarafin da Nana H taiwa Junaid, cikeda fushi take fad'in "Haba Nana H, meyene haka, meye laifin mai nakasa, shin mu muka so muga kanmu haka? Ba Allah bane ya jarabcemu, kema fah bakifi k'arfin Allah ya jarabceki ba... Kuma idan kana raye tabbas ba'a k'are maka halitta ba... This is...."