← Book details Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 98

Sashe 43

Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaje kuwa tana daga k'ofa tana hangensu ta ramin k'ofa tana faman tab'e tab'en baki... Saida taga Ahidjo ya ciro kud'i cikin aljihunsa yana mik'awa mahaifin Deejoh ya sata sake baki tana duban damin kud'in... Babban abinda ya bata takaici shine yanda Malam Ard'o yak'i amsar kud'in yana cema Ahidjo "Wllhi D'ana ka bar kud'inka mun gode sosai...."

Gaje kuwa daga yanda take lab'e take fad'in "Ard'o yau zamuyi daru muddin baka amshi kud'in nan ba...." Don ko fitowa ta kasa sabida wani irin tsoron Ahidjo da Allah ya d'aura mata...

"Baba dan Allah ka karb'a idan ka d'aukeni D'a..." Ahidjo ya fad'i yana kuma damk'awa Malam Ard'o kud'in....

Da k'yar da sid'in goshi Malam Ard'o ya amshi kud'ad'en da Ahidjo ya basa.... Daga nan Ahidjo sallama ya masa kana ya fice daga gidan...

Malam Ard'o ya bisa da kallo zuciyarsa na masa sanyi ko babu komai Deejoh d'an mutunci ta Aura ba kaman yanda mutanen gari suka d'auka ba.....

Gaje kaman jira take yana ficewa ta k'araso ta wawashe kud'ad'en daga hannun Malam Ard'o tana faman washe baki...

Malam Ard'o dai kallon mamaki ya bita dashi yana mamakin hali irin na Gaje....

Ahidjo na fitowa gidansu Deejoh wayar Lamid'o ya shigo masa, saida k'irjinsa yayi wani irin bugawa ba tareda sanin dalili ba, don harga Allah ya mancewa kowa cikinsu a 'yan kwanakin harta matarsa Nana H bai tunawa, duk abinda yake ciki Deejoh kawai yake tunawa....

"Hello Bro.... Kwana da yawa..." Ya fad'i yana rage girman idanunsa sabida hasken rana da ya fito.... Jin muryar Lamid'on cikin wani irin yanayi yasa Ahidjo nutsuwa sosai..

Daga d'aya b'angaren Lamid'o yaci gaba da fad'in "Heedj I really need your help..... Nasan babu wanda zai min sai kai...."

Ahidjo yace "Ina jinka Lamid'o wai meke faruwa ne.... Just go straight please..."

Lamid'o ya sauk'e ajiyan zuciya kana yace "Alright.... Heedj, kana jina....?"

Gajeren tsaki Ahidjo yayi kana yace "Lamid'o wai menene dan Allah ka fad'a min...."

"Heedj Nana K is alive.... She's alive...."

Gaba d'aya Ahidjo yama rasa wacece Nana K, a hankali ya shiga nanata sunan

*SameenaAleeyou📚**FUSKA UKU*🏮

*31*

*©Sameena Aleeyou...✍🏽*

"Nana Khadija 'yar uwar matarka data b'ace 20years back....." Lamid'o ya nanata cikin wata irin murya mai sanyin gaske....

Girgiza kai Ahidjo yayi kana yace "Lamid'o wace irin magana kake, lafiyarka kuwa, Nana K ta jima da rasuwa kowa yasan wannan da tayi surviving accident d'in da tuni an sani kuma da ta dawo wajen family d'inta, I'm pretty sure wata dai kawai ka gani mai kamadasu Nana H amma ba Nana K ba...."

Girgiza kai Lamid'o yayi tamkar Ahidjo na ganinsa kana yace "Heedj ya kake magana haka, wllhi Nana K na gani da idanuna, dukda a hoto na ganta but wllhi tllhi na tabbata itace bazan zauna inai maka rantsuwa kan abinda banida tabbas akai ba...." Yayi maganar sounding serious...

Sosai Ahidjo ya nutsu kana yace "Toh mai kayi, ka sanar da Siraj ne da familynsa ko kuwa....?"

Kai Lamid'o ya kuma girgizawa kana yace "Banida wannan ikon Heedj da nayi..."

"Kamar yaya....?" Ahidjo ya tambaya cikeda mamaki...

Fuzar da iska Lamid'o yayi kana yace "Is a long story Heedj, babu time sannan bazai yuwu na sanar da kai a waya ba... Alfarma nake so ka min...."

K'asar bishiya Ahidjo ya samu ya zauna kana yaci gaba da fad'in "Umhum ina saurarenka.... So kake na sanar da Siraj..?"

Cikin sauri Lamid'o ya girgiza kai alamun a'a kana yace "Heedj ina cikin matsala yanzu haka mutumin da yayi kidnapping Nana K years back nima ya kamani ya tsareni da ya fahimci ina bincike akansa, ya fahimci nasan sirrinsa shiyasa ya kamani ya rufeni don kar na cimma burina na dawo da Nana K wajen real family d'inta...."

Shafa kansa Ahidjo yayi kana yace "Now I get you, mutumin kake so a kama, zaka iya sanar dani location d'inka yanzu zamu tura mutanen ...."

Saurin katsesa Lamid'o yayi da fad'in "No Heedj kai kafi kowa sanin case irin na kidnap haka ba'a saurin involving police, Heedj abinda yasa na kiraka so nake ka k'arasa abinda na fara kar ka damu dani I'll be fine I promise... Ahidjo Siraj is our brother koda ace baka auren niece d'insa Siraj d'an uwanmu ne na sani shekarun baya mun tab'a jefa rayukanmu cikin had'ari a sabida Siraj.... Nasan baka mance abinda ya faru 4years back ba.... Bana fatan irin wancan tragedy d'in ya kuma faruwa... But we need to do this Heedj, Nana K ta cancanci ta dawo cikin family d'inta, na tabbata zasuyi farin ciki maras misaltuwa,..." Fasali ya d'anja kana yaci gaba da fad'in "Idan na sanar da Siraj yanzu zai zargi wani abu shiyasa na soma sanar da kai and please kar ka sanar dashi har sai ka damk'a Nana K hannun family d'inta, Suna can garin Damaturu ta jihar Yobe..... Please Heedj nasan ka fahimceni a matsayinka na D'ansanda...."

Sauk'e ajiyan zuciya Ahidjo yayi kana yace "Na fahimceka Lamid'o, insha Allah zan k'arasa aikin alkhairin daka soma, and da zaran na maido da Nana K gida insha Allah kaima zan fitar da kai and wancan mutumin will face justice...."

A hankali Lamid'o ya saki murmushi kana yace "Alhamdulillah, na gode Heedj, Ubangiji ya baka nasara...."

"Ka daina min godiya Lamid'o kar ka mance koda ace bana auren d'iyar Siraj hakki na ne kare Al'umma tinda nayi rantsuwa zan rik'e aikina bisa gaskiya da amana...."

Jinjina kai Lamid'o yayi lokaci guda yaji hwaye na neman ciko idnunsa sabida cin amanan Ahidjo da sha yi a bayan idanunsa.... Wasu irin k'walla masu zafi suka zubo masa, lokaci guda yaji ya tsani kansa, bai tab'a jin nadama irinta yau ba....

Murya na rawa Lamid'o ke furta "Heedj... Please forgive me... Dan Allah ka yafe min brother...."

Jikin Ahidjo yayi sanyi lokaci guda duk a tunaninsa sabida aikin da Lamid'o ya saka sa ne yake rok'onsa gafara tinda yasan dole akwai had'ari cikin aikin.....

"Haba Lamid'o ka daina bani hak'ura and insha Allah kaima zaka fita daga wannan taskon just trust me bro....."

Kasa furta komai Lamid'o yayi sabida wani irin kukan nadama da yaji na taso masa, tabbas Nana H ta cucesa, da ace bata persuading d'insa wajen suyita aikata masha'a ba da bai ci amanan abokinsa ba.... Kasa ci gaba da magana yayi lokaci guda ya kashe wayar had'i da durk'usawa saman gwiwoyinsa yana kuka sosai shar-shar da hawaye Wanda bai tab'a yin irinsa ba a rayuwarsa.....

Yana durk'ushe wajen yana kuka yaji an banko k'ofa an shigo ana tafe hannaye.....

"Bravo..! Bravo Smart boy....!!!" Muryar Alhaji Bulama ya daki dodon kunnuwansa....

A zabure Lamid'o ya mik'e yana goge hawayen fuskarsa lokaci guda yake hura hanci had'ida watsawa Bulama mugun kallo....

"You think you're smart right....?" Bulama yace yana mai murmusawa idanunsa kan Lamid'o, gurds d'insa majiya k'arfi sun saka sa a tsakiya....

A zuciye Lamid'o yayo kansa zai kai masa capka yake fad'in "I'm gonna kill you, you worthless....." Saidai kafin yakai aya K'artin nan sun kwantar dashi da duka....

D'aga masu hannu Bulama yayi alamun su k'yalesa kana ya k'arasa yana bubbuga wayar data tarwaste daga hannun Lamid'o a k'asa da sandarsa ta dogarawa.... Lokaci guda yake murmusawa yana fad'in "Lamid'o kenan.... Wato k'ok'arinka na matuk'ar birgeni.... Akwai ka da k'wazo da k'ok'ari, saidai kuma matsalan you such an idiot.... K'aton jiki gareka saidai kuma k'aramar kwanya gareka... Take a look of this....." Ya k'arashe yana k'ok'arin d'ago fuskar Lamid'o da sandar dake hannunsa, yayinda fuskar Lamid'on ke kife k'asa yana d'igan jini.....

Wani d'an rami ya nuna masa jikin k'ofar d'akin wanda idan ba ka kula ba bazaka zaci camera bace 'yar k'arama mak'ale a wajen....

Bulama ya kuma murmusawa kana yace "You think I'm stupid, kana tunanin zan barka haka kurum ne bayan nasan kaida Nazir kunci amanata.... You're very much mistaken dear Son.... Na tsufa amma kwanyata bata tsufa ba, tafi ta matashi d'an shekaru talatin aiki.... Da sanina, ni da kaina na d'auki waya na baiwa Barde nace ya kawo maka don nasan dole Nazir ya sanar dakai wani abu.... Fine... Na sami information d'in da duk nake nema, and now kwanakin wancan traitor d'in k'irgaggu ne, tinda yaci amanata amfaninsa ya k'are.... Sannan ina welcoming sabon victim da ka jefosa cikin wannan mess d'in... Your good friend Ahidjo....."

Girgiza kai Lamid'o yake yana wasu irin hawaye sanda ya isa har jikin k'afafun Bulama da rarrafe ya kamo k'afafun Bulama yana kuka sosai yake fad'in "Daddy please no.... Dan Allah Daddy na rok'eka kar ka kashe Nazir da Ahidjo..... Daddy please don't..... Dan Allah kada kayi komai ma Ahidjo.... He's innocent, wllhi ni na saka shi baisan komai ba, please Daddy ka kasheni kawai ka huta amma dan Allah banda Ahidjo.... Na jima ina zaluntarsa a baya idan ka kasheshi yanzu a dalilina bazan tab'a yafewa kaina ba.... Daddy Dan Allah no..... I beg of you please.....!" Ya k'arashe cikin tsananin kuka yana mai k'ank'ame k'afafun Bulama...

Dariyar rainin hankali Bulama ya kece dashi kana ya sauk'ewa Lamid'o sandar hannunsa a gadon bayansa... Lokaci guda Lamid'o ya saki k'aran azaba yayinda Bulama yasa kai ya fice daga d'akin yana fad'in "Fool...!"

Har Bulama ya fice Lamid'o bai daina kuka yana rok'onsa kada ya cutar da Ahidjo ba....

***

Daren ranar Deejoh rungume cikin jikinsa take yana mai ci gaba da lallashinta yana sanar da ita dole ya koma Abuja koda su Baffah basu amince ya tafi da ita ba sabida nemansa da ake cikin gaggawa a wajen aiki....

Deejoh ta kuma goge k'wallan da suka zubo mata cikin murya mai rawa sosai tace "Tafiya zakayi ka barni.... Dan Allah kada ka tafi ka barni kaji...." Ta k'arashe sabbin hawaye suna zubo mata....
Chapter 43 · 0% Book details