← Book details Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 98

Sashe 10

Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin yanda jijiyar goshinsa ta fito sosai ya sanya k'irjin Barr bugu, k'ak'aro murmushi yayi kana yace "Kana tareda yardata Junaid bazan ci amanarka ba da yardar Allah...."

Junaid ya jinjina masa kai dai-dai lokacin da Azeeza ta shigo hawaye na safara a fuskarta...

Kallo take kan faman binsu dashi yayinda Junaid ya soma k'ok'arin saita kansa donyima k'anwar tasa magana...

Girgiza masa kai ta soma tana fad'in "Yaya u don't have to explain..... I've heard everything, so that was the reason.... Yaya why? Meyasa... Haba Yaya Junaid shin Fansa ya kamace ka, shin A DUNIYARKA babu hak'uri.... Yaya I can't bazan iya ba... And I'm going back to Damaturu immediately.... Bana cikin burin Fansarka....." Tana kaiwa nan tasa kai zata juya cikin tsananin huci... Saidai kafin takai k'ofa Junaid ya isa ya rik'o hannunta...

Juyowa tayi suna kallon juna hawaye na ci gaba da ambaliya a fuskarta....

"Azeeza you must.... You must help me.... Babu komawa da baya sabida na riga na fara....."

Tsugunawa tayi suna fuskantar juna su duka biyun.... Kasa magana tayi sai wani sabon kukan da ya b'alle mata... Cikin sauri Junaid ya rungumeta cikin jikinsa shima hawayen na neman ciko idanunsa....

Barr ya bisu da kallo cikeda tausayawa....

****

*Tambuwal*

Kaman kullum suna zaune tsakar gidan suna sana'arsu ta sark'an beads itada Zaliha da k'awarsu Hanne yayinda Dadda ke bayi tana wanka da shike hantsi ta sako kai sanyi ya d'anyi sauk'i...Abinka da Dadda tana bayin tana wankan tana 'yan wak'e-wak'en ta.... Tun daga bayin taji ana bugun k'ofar gidan ana k'wantara sallama....

Uwar tsaki taja don tasan yanzu haka bazai wuce masu karb'an sark'an amarya bane gashi su Mairo sun sake kid'an Barmani Mai Choge a tsakar gidan tasan bazasu saurari bugun k'ofarba....

Tsaki taja tana goga soso take fad'in "Wai wayene mai bugun k'ofar nan ne....?" da shike bayin ba wani ratar kirki bane garu ne ya raba tsakaninsa da wajen gidan....

Daga yanda suke tsaye sai jiyo muryoyinsu tayi suna fad'in "Daga ofishin Hisbah ne...."

Ai a d'ari Dadda ta wanke sabulun dake idanunta tana fad'in "Na'am... His mene...?"

D'ayan ya k'ara cewa "Hizbah..."

Cikin sauri ta janyo zaninta saman garu ta d'aura a k'irjinta tana fad'in "Toh lafiya dai koh, ko kunyi zaton nan d'in gidan Magajiya ne...?"

"Ko mu shigo ne....?" d'ayan ya kuma tambaya...

"Kai gani nan zuwa ku jirani, ina tafe..." Ta k'arashe tana d'aukan kwandon wankarta.... A filin tsakar gidan ta tarar dasu Mairo an sha kallabi a gefen kai jai rangaji da kai ake ana zura beads jikin d'an robar tsark'ar da gani suna jin dad'in sana'ar tasu... Batabi takansu ba sai hijabinta data d'auka saman igiya ta nufi k'ofar gida...

Aiko tana bud'ewa taga mutum biyu da Uniform jikinsu da dorinai ga kuma Malam Balarabe a gefensu yana muzurai yana hura hanci....

"Toh lafiya dai ko...?" Ta tambaya tana yarfe sauran ruwan fuskarta...

"Hajiya kin gane wannan.? " Guda d'aya ya tambaya yana nuna mata Malam Balarabe da dorinar hannunsa..

Yatsina fuska kurum Dadda tayi kana tace "Yo na ganesa mana, ba yaron nan ba d'an gidan Tale d'an bana sauk'e kawai ya soma malamta ko ba shine ba....?"

"Hajiya toh a gidan nan naki munji labarin akwai karuwai kina tara 'yanmata da sunan kina koya masu sana'a ashe kawalci kike., kuma tabbas gashi muna jiyo sautin gurmi daga cikin gidanki na tashi don haka yanzu zamu shiga muyi kame..."

"Bantan uba...." Ta furta tana tattaro hijabinta, kafin ta ankara sai gani tayi sun shige gidan Malam Balarabe yana fad'in "Ku dai shiga suna ciki watsatsun amma ku rintse idanu...."

A d'ari Dadda ta take masu baya tana ruwan bala'i had'i da tafe hannaye....

Su Mairo kam zumbur suka mik'e ganin maza cikin gidansu rik'e da dorina...

Dadda fad'i take "Wata doka ce ta baku dama ku shigo min kan iyalai na 'yan mata... Toh wllhi sai munyi shari'a daku...."

Malam Balarabe suna had'a idanu da Mairo yayi bayan jami'in hizbah guda d'aya yana fad'in "Ka gansu nan suna asharalle dama na fad'a maku koda na masu wa'azi mutunci na sukaci harda cewa zasu bugeni...."

Jami'in Hizbah ya d'aga dorina yana fad'in " Ya subihanallah.. Ku wuce muje... Muje nace, baku iya komai ba sai bad'ala da cin mutuncin Malamai...."

Abinda ya basa mamaki shine babu wanda ya motsa daga Mairo har k'awayenta... Kallo d'aya kurum tayi wa k'awayen suka fahimci mai take nufi.... Kafin su ankare tuni Hanne ta gark'ame k'ofa itako Zulai tuni ta rarumo igiyan guga ganin haka yasa Dadda murmusawa don tasan mai suke shirin yi... Tuni ta yaye hujabinta daga ita sai d'aurin k'irji... 'yan hizbah suka soma rintse idanu suna a'uzubillahi Hajiya kanki d'aya.... Ai mai maganar bai ankara ba sai ji yayi an sharb'osa k'asa... Malam Balarabe na ganin haka ya nufi katanga a d'ari lawurje har tana neman kwancewa ya haye katangar... Ko waigowa bayayi fatansa kurum ya tsira...

Tuni Dadda ta zaune d'ayan tana fad'in "Hanne bani muciya a kitchen..." Hanne ta tafi a guje d'auko muciya

Mario da Zulai kuwa dorinar 'yan hizban suka amsa suka shiga kewayasu bakajin komai sai ihun k'artai..... Sai suka masu lilis da k'yar suka tsira hannun su Mairo...

"Gobe ku sake shiga gidan wasu babu bincike sai an maku fin haka, su saka rigar addini kuna tsiyarku, baku tafi bayan gari kama karuwai ba sai cikin gari tsakiyar unguwa gidan wasu... Gobe ma ku dawo..." Ta k'arashe tana jifa masu dorinar su...

Hula a hannu suka tsere suna tsinewa abokinsu Malam Balarabe, da alwashin sai sun kira ogansu na Hisbah wannan cin zarafi da aka masu bazai tafi a banza ba.....

***

*Misau*

Innah Balki tayi shiru tana duban k'awar tata Larai kana tace "Toh yanzu Larai kinaga naje gidan Malami nace amin kiranye Malam bazaice nayi shirka ba... Anya Larai kinaga babu komai.... Gaskiya ina tsoro nidai a ganina kawai muci gaba da addu'a kuna tayani har Allah yaji k'aina ya karkato da hankalinsa ya dawo gida, nidai duk turasa karatu k'asar Arna da Malam yayi shi ya jawo mana wannan musiba sam Hidjo na bai sami ishesshen karatun addini ba...."

Larai ta kuma duban Innah Balki kana tace "Balki nifa taimaka maki nakeda niyyanyi... Idan kuma baki son taimakon kinga tafiyata bariki kuma yanzu d'anki ya soma zama cikinta k'adangarun bariki na lashesa muddin bazakiyi wani hobb'asa ba.... " Ta k'arashe tana yafa mayafinta take fad'in "Ni kinga tafiyata tunda ke 'yar dad'i miji ne komai sai kin sanar dashi baki san ki tashi ki taimaki kanki ba, toh wayema yace maki kiranye shirka ne, addu'a kawai da sadaka Malam zaiyi cikin yardar Allah d'anki ya dawo amma tunda baki son taimakon ni kinga tafiyata...."

Cikin sauri Innah Balki ma ta mik'e don A DUNIYARTA babu abinda take muradi tamkar ta sami hankalin d'anta da kulawarsa....

"Larai muje kiyi hak'uri kada ki tafi...."

Larai ta kad'a kai tace "Ah toh duniyar nan kowa da kika gani na buk'atar addu'a .. Yanzu Sunusi d'an gidan Iya Dumba da yabi makiyaya da masu farauta yak'i gida ba Malam d'in bane ya masa kiranye ya dawo gida, gashi yanzu yayi aure harda 'ya'yansa, nake baiwa Malam labarinki ya tausaya maki sosai yace zai taimaka shine ke zakice baki so ko...."

Cikin sauri Innah Balki ta kuma girgiza kai tana fad'in "A'a wllhi ai nace muje, Ubangiji dai yasa mu dace.... Bara kiga na shiga d'aki na d'auko mayafi....." Ta k'arashe tana shigewa uwar d'akin

****

Zaune take saman k'aton gadon nata cikin yalwataccen d'akinta wanda ya k'unshi kayan more rayuwa da dama... Hannunta rik'eda wani k'aton hoto wanda ya k'unshi kusan mutane biyar.... Wad'anda suke daga tsaye Mace ce da kuma namiji wanda basai ance maka mata da miji bane, na zaune saman kujera kuwa 'yan mata ne yara guda uku masu fuskoki iri guda, kamanninsu d'aya tamkar an tsaga kara, a hoton yaran bazasu gaza shekaru biyu zuwa uku ba, kyawawa dasu ko wacce an kame mata sumarta da ribbon kana ganin yaran kasan sunji hutu sun gaji, ba sai ance maka 'yan uku bane ma'ana triplets ne...

Har Ayiya ta fito daga bathroom Nana A bata daina murmushi tana shafa hoton ba. A haka Ayiya ta k'araso ta sameta itama murmishi kwance saman fuskarta....

Nana A ta d'ago tana duban Ayiya da zamanta kenan gefenta, cikin sanyin muryarta tace "Ayiya insha Allah suna Aljannah..... Mummy Daddy da kuma NANA K.... Ayiya sometimes nakanji cewa da ace 'yar uwata Nana K tana raye k'ila da tayi kama irin tamu nida Nana H k'ila da yanzu FUSKA UKU iri guda ne a gidan nan.... Ina son Nana K kuma bazan tab'a kyautar da toys d'inta ba har abada ina ganin 'yar uwata a jiki......" Tana kaiwa nan ta lumshe idanunta had'ida rungume hoton...

Ayiya da tausayin Nana A ya ratsa zuciyarta batasan sanda ta rungumota ba tana share mata hawaye...

Bata jima da shigowa gidanba daga bakin k'ofar d'akin ta tsaya tana kallonsu makirin murmushi kwance saman fuskarta.... Cikin zuciyarta take fad'in _Ohh my poor crippled sis.. I wish you too didn't survive the accident so that bazan sharing Uncle Luv d'ina dake ba, na sami soyayyarsa ni kad'ai .. Daga shi har Ammah... But.... Anyways You still lost your leg... Ta d'an tab'e fuska had'i da furta "Oh oh oh What a pity ,..... I'm still the queen don munada FUSKA iri guda doesn't mean munada kyau iri guda.... and yes I still love you baby sis sabida Momy da Daddy sun tafi sun barmu saura mu biyu....._ Ta k'arashe tunanin nata tana watsawa Ayiya kallo lokaci guda ta saita kanta taci gaba da tafiya mai k'wark'wasa saman bene tana k'wallawa Ammahnta kira....

*SameenaAleeyou📚*
[12/15, 5:59 AM] ‪+234 806 231 4322‬: *FUSKA UKU*🏮

*08*

*©Sameena Aleeyou...✍🏽*

Tunda suka dawo daga gidan Malam Tsalha ta rapka uban tagumi tana tunanin ta yanda zata soma b'ullowa lamarin, Malam yace saidai ayiwa Ahidjo aure a garin muddin tana so kiranyen da za'a masa yayi tasiri, amma idandai ba aure aka masa ba kwanaki kad'an zaiyi yayi tafiyarsa.... Ko motsawa daga kujeran da take bisa Innah Balki ta kasa balle tayi tunanin d'aura sanwar miyan dare....
Chapter 10 · 0% Book details