Sashe 11
Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A haka Baffah ya shigo gidan ya taddata, abin duk ya damesa da ganin yanayin da ta shiga duk a zatonsa tunanin halin da Deejo ke ciki take, yasan halin Balkisu da saka abu a ranta yanzu haka wannan tunani shi ya hanata sukuni...
Bayan sallan isha suna zaune saman tabarmarsu ta azara suna cin tuwonsu ta surfeffiyar masara miyar busheshiyar kub'iya sai k'anshin manshanu ke tashi ga radio d'insu gefe suna sauraren zab'en dare, abinda zai baka sha'awa da wad'annan ma'aurata shine tsananin soyayyar juna da kulada juna da suke, Allah sarki saidai nasu jarabawan kan d'ansu ne, dama kowa da yanda Allah zai jarrabesa A DUNIYAR SA....
Innah ta musk tana duban Baffah dake faman santin tuwonsa tace "Nikam Malam nace ba...."
D'agowa yayi yana dubanta kana yace "Kika ce mene Inna wuro....?"
Abin duniya duk ya dami Innah gani take batabi hanyar da ya dace ba amma batada zab'i domin Ahidjo shine mata d'anga guda tak komai zata iya yi domin ta sami soyayyarsa.... Baffah ya katseta da fad'in "Ina jinki badai tunani Deejo kike ba.... Allah sarki yarinyar abin tausayi ne d'azu da zan wuce sallan magariba saida na jiyo kukan yarinyar nan, abin tausayi, na rasa ta yanda zanyi na amso yarinyar nan ta dawo hannunmu Gaje bazata tab'a bari ba... Ko gidan Mai Unguwa zan tafi gobe da sassafe...."
Ya k'arashe yana duban Innah wacce damuwa ya kuma nunawa sosai a fuskarta lokaci guda wani tunani ke shigowa zuciyarta, toh kodai hakan zatayi ne...? Bata ida tunanin nataba ta kuma jiyo muryar Baffah yana fad'in "Balkisu wai lafiyarki bakiji abinda nake fad'i ba... Wai meke damunki ne ki fad'a min Bilki na....."
Innah ta gyara zama sosai kana ta soma fad'in "Malam ina tausayin Deejo sosai ina jinta tamkar d'iyar da na haifa ta cikina, yanzu cewa da kayi ka jiyo kukanta har cikin raina naji ciwon hakan, ina fata mu cireta cikin wannan k'angi da k'unci da take ciki.... Malam nikam nace ba mai zai hana mu nema wa Yaron nan auren Deej....." Kafin ta dasa aya Baffah ya cire hannunsa daga cikin tuwon yana dubanta cikeda mamaki da gaske take maganar abinta....
"Bilki lafiyarki kuwa? Kanki d'aya...? Ta ina wannan Al'amari zai soma yuwuwa.... Deejo ta wahala a rayuwarta zata buk'aci jin dad'i a rayuwarta, bata cancanci miji irin d'anki ba... Yaron da baisan mutuncinmu ba balle na wacce za'a aura masa? ..... Ko kin mance acan barikin yanda ya tareda rayuwarsa yanada aurensa... Kawai mu d'auki Deejo don son zuciya irin tamu mu aura masa.... Haba Bilki wannan magana bata kamaceki ba...." Ya k'arashe yana jawo kwanun sha dake cikeda ruwa...
Innah ta d'an b'ata fuska had'i da yin rau-rau da idanu kana tace "Amma Malam....." Baffah yayi saurin dakatar da ita da fad'in "Bana son jin komai, wannan magana bamai yuwuwa bane ALIYU bazai auri yarinyar nan ba...."
Cikin sauri Innah ta d'ago tana dubansa domin a iya saninta rabon Malam da ya kira Ahidjo da asalin sunansa idan bata b'ata tunani ba tun sanda ya masa rad'in suna sai gashi yau ya ambato sunan b'aro-b'aro lallai tunda kaga haka tura ta kai bango.... Bata k'ara cewa komai ba har Malam ya mik'e daga saman tabarman, hankalin Innah ya kuma tashi matuk'a ta shiga tunanin wani hanyar da zata kuma bi, domin ita a ganinta dama ce ta sameta....
***
Gaba d'aya suke zaune a wargajejen dining table d'in mai k'unshe da kujeru goma sha biyu, Nana H 'yar gaban goshin Uncle Siraj hannun su mak'ale cikin na juna sai zuba masa shagwab'a da sangarta take Ammah na kuma riritata....
"Haba Uncle Luv wllhi har kunya nakeji na shiga cikin k'awaye da motata wllhi ta tsufa sosai yau fah shekara tim baka canza min ba ai k'awayena sai su rainani....." Ta k'arashe tana kuma turo baki gaba....
Daga yanda Lamid'o ke zaune ya kafeta da idanu sihirtaccen murmushi kwance saman fuskar sa.
Siraj ya ajiye fork d'in dake cakalan abincin dashi ya kaikaito sosai yana dubanta kana ya soma fad'in "Baby I'm sorry okay... You know I've been very busy kwanakin nan, nasan ya kamata a canza maki mota kiyi hak'uri please akwai noticing da za'a shigo dasu k'arshen December d'in nan sai ki d'auke wacce ta maki kinji..." Ya k'arashe yana shafa kanta kaman k'aramar Baby....
Turo baki ta kuma yi cikin da shagwab'a tace "Uncle nidai naka nake so please...."
Siraj ya dubeta cikeda mamaki kana yace "Baby nawa fah kika ce...."
Kai tsaye ta shiga gyad'a masa kai alamun eh ta k'arada idan kuma bazaka bani ba shikenan bana so...."
Siraj ya matso da kujeransa kusan nata sosai kana ya rik'e hannayenta alamun lallashi ya soma fad'in "Sweetheart bawai banason baki mota ta bace akwai important documents da na adanasu cikin different safes a cikin motar and....." Baikai aya ba sai gani yayi ta mik'e daga table d'in tana fad'in "You know Uncle I just lost my appetite..... And bana son motar ka rik'e abinka....."
Cikin fushi ta soma tafiya Ammah na kiranta...
Excusing kansa yayi yabi bayanta....
Ayiya da isowarta wajen kenan hannunta rik'eda bowl da alama wani abin zata serving d'insu baki sake take dubansu kafin ta shiga tafe hannaye take fad'in "Oh ni Bintu naga salo wannan shi ake kira SHAK'UWA SABON SALO.... Toh Allah shi kyauta ya yaye maku...." Ta k'arashe tana duban Nana A dake faman juya spoon cikin plate kana tace "'Yar Albarka na zuba maki 'ya'yan itaciyan ko...." D'an k'ak'aro murmushi Nana A tayi had'i da girgiza kai kana tace "A'a Ayiya na riga na k'oshi....." Bata kai aya ba ta jiyo muryar Lamid'o yana fad'in "Fruit is good to your health especially da dare ki sha ko kad'an ne...." Ya k'arashe murmushi kwance saman fuskar sa....
Batasan dalilin da ya sanyata amimcewa ba lokaci guda ta shiga murmusawa had'i da jinjina masa kai tana fad'in "Toh Uncle zan sha....."
Ayiya taji dad'in hakan tana lura da irin sadda kai da Nana A keyi da kuma kallon da Lamid'o ke mata murmushi mai kyau kwance saman fuskarta, itakam Allah sa hasashenta ya tabbata sai tafi kowa farin ciki domin Sarki da 'yar Albarka ba k'aramin dacewa zasuyi ba.... Ana haka Ammah da tuntuni hankalinta bai wajen tana tunanin fushin da Nana H tayi, k'ok'arin mik'ewa ta soma yi tana fad'in "Shima dai Siraj son neman fitane dashi, yanzu idan tayi fushi ta tafi sai mu shafe sati bamu ganta ba a gidan nan mai akayi akayi mota da zai hana d'iyarsa inyi.. Haba ni banason irin haka..."
Gaba d'aya kallo suka bita dashi jin irin fad'an rashin gaskiyar da take faman yi akan Nana H....
Kafin Ammah ta k'arasa mik'ewa Siraj da _Hetch_ (in Shawty's voice😂) suka dawo parlorn tana mak'ale cikin jikinsa alamun sun shirya, tuni annuri ya cika fuskar Ammah fad'i take "Hafsatu na ki kwantar da hankalinki mota ce dole ya baki...."
Murmusawa Siraj kawai yayi yana mai k'ok'arin gyarawa Nana H kujera domin zama yake fad'in "Ammah ai kinsan Baby idan ba'ayi abinda take so ba toh babu zaman lafiya...."
Nana H kuwa jin haka yasa kanta sai kuma fashewa yake, toh ta yaya ma zata bari Uncle luv yayi aure, duk wannan kulawar da yake bata wa matarsa zaike bayawarwa sannan idan yayi aure na nufin zai sami nasa 'ya'yan kenan da suka fito daga asalin tsatsonsa dole kenan duk wannan soyayya da yake mata ya tashi ya koma kan 'ya'yansa....
Wayar Ammah ne yayi k'ara ta soma yunk'urin mik'ewa Ayiya tayi sauri tace "Hajiya ki bari na kawo maki..."
Ammah tace "A'a barshi kawai Ayiya dama ina son mik'ewa..."
Ammah na barin wajen Ayiya tayi caraf ta sako zance don bataso Siraj da Nana H suci gaba da k'untatawa 'yar Albarka...
"Sarki ya kamata ka kawo min matar nan taka na saka mata albarka, don na tabbata mai hankali zaka kawo wacce ta iya zama a gida ta kula da miji ba mai gantali a saman kwalta ba kullum...."
Ai Ayiya tana kaiwa aya Nana H ta shak'a tasan ko ba'ace ba Ayiya da ita take, tak'i jinin wannan tsinanniyar mata mai suffan mayu, gashi dai tun mutuwar iyayensu take rainonsu amma ta tsaneta kaman ta fatattaketa daga gidan haka kullum takeji, bacin kinibibin Nana A da tuni ta koreta koda tsiya koda arziki, itace mutum guda dake neman tak'ura rayuwarta tun tana yarinya....
Lamid'o murmusawa kawai yayi yana shafa wuya yake fad'in "Ayiya na kusa insha Allah...."
Ayiya ta watsa wa Siraj harara kana tace "Yauwa ai ya fiye maka kada kabi na wannan abokin naka wanda aljana ta auresa ta hanasa ajiye iyali... Idan nace a kamashi aje a masa karatu shida mahaifiyarsa ba yarda zasuyi ba... Ai sai ka zauna a haka, ita wacce ka lik'e matan naga dai babu aure tsakaninku ehe, kuma dole ranar daka ajiye naka iyalin ta sarara maka dun babu macen da zata d'auki wannan iskancin... K'atuwar mata god'e-god'e da ita kullum tana mak'ale jikinka wai kai Ankul loof koh.. Toh Allah yasa wata da Zara ne ku maga ta k'arya randa kayi aure....."
Tunda ta soma magana suke dubanta, Siraj daina abinda yakeyi cikin waya yayi yana duban Ayiya yanda ta zak'e sai tsefesu take, Nana H kuwa ta kumbura sosai tamkar ta fashe, ji take kaman ta tashi ta rufe Ayiya da duka....
Burin Ayiya ya cika ta k'untata masu kaman yanda suka k'untatawa 'yar Albarka... Ganin Nana H na shirin magana yasa Nana A saurin mik'ewa tana fad'in "Ayiya zan tafi d'aki..." Don tasan k'arshe abin bazaiyi kyau ba muddin suka ci gaba da zama wajen don Nana H ba hak'uro zatayi ba yanzu zata wawwatsa wa Ayiya rashin kunya son ranta babu mai k'wabarta, ta kuma san sabida ita Ayiya tayi hakan....
"Uncle wllhi idan ba'a kori matar nan daga gidan nan ba wllhi sai ta cusawa Nana A tsanarmu kasan sakaryace batasan mai k'aunarta ba.. Uncle kaji irin maganganun da take, kaida Ammah ne kuke cewa a barta sabida Nana A wllhi da tani ce da tuni bata gidan nan tunda babu gadonta ciki...."