← Book details Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 98

Sashe 94

Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bata ida rufe baki ba wayarta ta soma ruri... Ayiya ce mai kiranta, da murnarta ta d'aga wayar da niyyan sanar da Ayiya daddad'an labarin saidai yanayin da taji Ayiya ciki yayi masifar tayar mata da hankali....

Murya na rawa Nana A ke fad'in "Ayiya Ammah ta... Ayiya mai ya sameta, ina kuke yanzu.... OK ok gamu nan zuwa...." Cikin sauri ta dubi Nana H dake sak'e-sak'en next move d'in da zatayi cikin zuciyarta kana tace "Nana H it's Ammah.... Tana asibiti unconscious..." Ganin irin kukan da Nana A keyi ne ya sanyata rungumota ba wai sanar da ita ciwon Ammah da tayi ba don tasan a halin da ta tafi ta bar Ammah ciki hakan ka iya faruwa...

Cikeda tashin hankali tamkar gaskiya Nana H ke fad'in "Muje, muje Asma'u..... Oh no we can lose our grandmother...."

Basu kuma bin takan su Zaliha ba suka nufi motar Nana H cikeda tashin hankali, itakam Zaliha tafiyarsun ya fiye mata don dama gaba d'aya jinta take tamkar wacce take aikata abu maras kyau tana tsoron a ganta, batasan dalilin da yasa Daddah ke guduwa da Mairo gari zuwa gari ba shiyasa ma gaba d'aya sai take ji tamkar Daddah na hangota....

Cikin sauri itama ta janyo hannun Ma'ajura tace su fice daga foundation d'in....

Daga yanda Junaid ke lab'e yana sauraren duk abubuwan da suka faru, wani tunani ne ya shiga bugawa a kwanyarsa, yaga reaction d'in Nana H, yagani daga k'wayar idanunta yanda sam bata k'aunar a samo 'yar uwarsu, yaji irin abubuwan da take fad'i.... Baisani ba amma yaji yana son taimakon Nana A yaji a jikinsa akwai wani babban Al'amari dake faruwa a family d'insu Nana A, yana son sanin ko menene wannan abun, yana son sanin komai... Cikin sauri shima ya fice ya tari cab ya umarci mai cab d'in da subi bayan motar can.... Ya masa nuni da taxi d'in dasu Ma'ajura suka shige.....

***

Da k'yar aka samu Ali ya saki hannayen Mairo amma bai daina ambaton ita d'in matarsa bace, duk yanda suka so fahimtar dashi abu yak'i cin tura, itako Umma Marie hankalinta gaba d'aya a tashe yake sanin cewa Daddah ta dawo gida zuwa wannan lokacin.... Turk'ashi wannan shine ana wata ga wata, sunje gidan Baba Malam kan matsalan Mairo saiga wani matsalan ya kunno kai, ikon Allah shi kuwa wannan k'ila jinyar k'aramar hauka yake da ita, amma sam baiyi kama da mahaukacin ba, duk wannan tunani cikin adaidaita take yinsa, itama a b'angarenta Mairon ta kasa yak'ishe tunanin cikin zyciyarta, da fari ta razana sosai da lamarin mutumin damin itama tafi basa matsayin mai tab'in hankali saidai har yanzu tana jin alamun hannunsa cikin nata, tunda take a tarihin rayuwarta tsawon shekarunta a duniya babu namijin da ya tab'a koda tab'a mata 'yar yatsa ne, don idanma taga take taken ka kenan tuni zata ci maka mutunci idan bakaiyi sa'a ba ma kasha ruwan duwatsu, a lokacin tana Mairon Daddah kenan.... Wai ita ce yau namiji ya rik'e mata hannaye ta kasa masa komai saima wani irin tausayinsa da takeji, ga tsikar jikinta da ya dinga tashi, wannan wani irin mutum ne ? Mai yasa ya ambaceta da matarsa.....

*SameenaAleeyou📚**FUSKA UKU*🏮

*62*

*©Sameena Aleeyou...✍🏽*

Tak'ure take jikin garu kaman dai yanda ta saba, idanunta duk sunyi luhu-luhu, gaba d'aya ta koma abin tausayi, ita a halin yanzu tafi tausayin halin da Siraj ka iya kasancewa ciki fiyeda ita, wayasan wani mugun abu Yayanta Junaid da kuma Nasaar zasu masa, tabbas idan wani abun ya sami Siraj itama mutuwa zatayi, gwara kawai su kasheta itama ta huta, badon tasan hukuncin wanda ya kashe kansa ba a shari'a tabbas da ta committing suicide da wannan zaman uk'uba da take, shi fansa babu alkhairi ko kad'an cikinsa, inama Yayanta zai fahimci hakan, inama zai kasance mai yawan afuwa da yafiya, inama zaiyi koyi da annabawa da mutanen k'warai, tabbas bazata gusheba tanaima yayanta addu'an shiriya koda zai kasance ranarta ta k'arshe kenan a duniya.... Tab'a k'ofar da akayi ne ya sanyata saurin lumshe idanu tamkar mai bacci...

Nasaar ne ya shigo d'akin had'ida k'ura mata idanu, shi kansa yana tsananin tausayin halin da take ciki saidai idan ba hakan yayi ba bazai tab'a mallakanta ba...

A hankali kaman mai tsoron kada ya tasheta daga baccin yake k'ok'arin k'arasowa kusanta, tsugunawa yayi had'ida k'ura mata idanu, kyakkyawar fuskarta ya zamto very pale, kallo guda zaka mata tayi tsananin baka tausayi, yakai dubanta ga abincin da ya sayo mata bada jimawa ba, janyo pack d'in yayi ya bud'e ta d'anci kad'an wanda da gani ba don dad'i tacisa ba saidon tsoron kada yunwa ya mata lahani....

Nasaar yaci gaba da duban Azeeza daga yanda take tak'ure, so yake ya gyara mata kwanciyarta ya d'aurata saman gado amma yasan idan ta bud'e idanu ta gansa zata kuma tsanarsa ne.... D'an fuzar da iska yayi ya soma k'ok'arin mik'a hannunsa da niyyan d'agata saidai kafin hannun nasa ya k'arasa jikinta wayar salularsa ta soma ringing, Bulama ne mai kiran nasa... Cikin sauri ya d'aga wayar yana sauraron mai Bulaman yake sanar dashi, lokaci guda ya shiga jinjina kai yana mai fad'in "OK, ok Sir, I'll be on my way right now..." Daga haka katse kiran yayi cikin sauri ganin Azeeza na mosti kaman zata dungura ya sanyasa saurin aje wayar a gefe yayi k'ok'arin tallafota.... Aiko bud'e idanun da zatayi ta shiga kwad'a ihu tana turesa daga jikinta...

Nasaar a rikice ya soma fad'in "I'm sorry Zeeza is not what you thinking , I'm sorry please kinji...." Bata ko kulasa ba sai kukan da ta ci gaba da yi tana kuma tak'urewa jikin garu... Tunawa da yayi Bulama na nemansa cikin gaggawa ya sanyasa mik'ewa ya fice cikin sauri had'i da kullo k'ofar...

Nan idanun Azeeza ya sauk'a kan wayar Nasaar da ya mance...

Hannayenta har suna rawa ta janyo wayar, wani ikon Allah sa'ar data samu shine wayar ba'a lock take ba, take ta soma tuno lambobin mutane dake kanta wad'anda zata kira su kawo mata d'auki....

Bata iya recalling lambar kowa sai ta Umma Marie, dama daga lambar Yayan Junaid sai na Umma Marie sune kawai akanta tinda sune her only family...

Saida ya fice da motarsa daga cikin gidan ya shafa aljihunsa yaji baiji wayarsa ba, sabon tashin hankali, ai a d'ari Nasaar ya fice daga motar ya nufi cikin gidan a guje..

***

Tunda ta dawo gidan bata taddasu ba hankalinta bai kwanta ba, bata san dalili ba amma a 'yan kwanakin tana wasu ire-iren tunani kaman an kusa rabata da Mairon ta, rabata da Mairo yana nufin rabata da rayuwarta ne, Mairo ce farin cikinta Mairo ce sanyin idaniyarta, tunanin irin korar kare da mahaifanta da danginta suka mata a wancan lokacin bayan ya shiga zuwa mata, bata da kowa sai Mairo bata da dangi sai Mairo, wasu hawaye suka shiga gangaro mata sanda ta tuna lokacin da ta koma Bulkacuwa ta tarar iyayenta babu ko guda, sun mutu da bak'in cikinta, bak'in cikin laifin da sam babu nata a ciki.... Dangi babu mai d'aga idanu ya kalleta balle yayi fatan ace ita d'in tashi ce... Mas'ud shine mutumin da ya fad'o zuciyarta, mutumin da sukayi soyayya tun yarinta, mutumin da yaso bata rayuwa irin wacce ta rasa, tabbas dole ce ta sanyata dawowa mace mafad'aciya ta kuma yi alk'awarin koyar da Mairo k'watan 'yanci a wajen koma wanene don kar a zama da ita saniyar ware kaman yanda aka ruguza mata tata rayuwar.... Wasu hawaye suka zubo mata.... A hankali ta mik'e ta shige uwar d'aki jiki a sanyaye tamkar ba Daddah ba....

Mai adaidaita yana ajiyesu suka yada zango a waje ganin yanayin Mairon har yanzu bai canza ba....

D'an fata Umma Marie tayi kana ta soma fad'in "Mairo are alright...?"

Hannu Mairo tasa had'i da goge ragowar hawayen dake gangaro mata kana tace "Umma bansan meke faruwa dani ba, Umma rayuwata gaba d'ayanta bansan koni wacece bace, bayaga irin mafarkan da nake Umma yanzu kuma kwatsam na had'u da wani mutumi da ya kuma shigowa rayuwata.... Umma kodai....." Bata kai aya ba wayar Umma Marie ya soma ringing....

K'ok'arin ciro wayar take daga cikin jakka saidai kafin tayi nasaran ciro wayar ta yanke ta zamto missed call, lokaci guda wani kiran ya kuma shigowa bak'uwar lamba...

Ta k'urama wayar idanu, lokaci guda take k'ok'arin d'agawa...

A dai-dai lokacin Nasaar ya banko k'ofar d'akin ya shigo, d'if Azeeza ta kasa magana ga Umma Marie ta d'aga sai faman fad'in Hello hello take shiru ba'a amsata ba.... Cikin sauri ya fuzge wayar had'i da katsewa yana mai watsa mata wata irin muguwar kallo..

Umma Marie ta dubi Mairo data mata k'uri kana tace "Kinga bak'uwar layi ce kuma basuce komai ba...."

Mairo ta d'an murmusa kana tace "k'ila irin masu had'a lambar nan ne suyita kira ko zasu dace da samari ko saurayi...." Ta d'an k'arashe cikeda barkwanci..

Tak'aitaccen dariyan Umma Marie ma tayi kana tace "Aiko sunji muryar tsohuwa bazasu kuma kira ba, mu k'arasa ciki nasan Daddah na nan na jiranmu...."

Mairo ta jinjina kai kana tace "Aifa kafin ta tsilemu da tambayoyi...."

***

"Answer me, who did you just call...?" Ya kuma tambaya yana tsananin huci

Har lokacin kuka take ba tareda furta masa koda kalma ba....

A zuciye Nasaar ya k'araso had'i da kamo wuyarta yana mai ci gaba da huci yake fad'in "Don't push me to hurt you Azeeza, I love you and I hate seeing you in this situation, please stop being stubborn...." Ya k'arashe yana mai rage murya ganin kukan nata k'aruwa yake sosai...

Cikin kuka take fad'in "Idan kana sona kaman yanda kake cewa don Allah ka fitar dani a nan.... Kaji don Allah ka fitar dani...."

Tsugunawa Nasaar yayi suna fuskantar juna har lokacin bata daina tak'urewa jikin garu ba....

"Azeeza I've plan for us, ki daina hanzari don bazaki tabbata cikin nan ba, idan na fiddaki yanzu Junaid zaiyi tunanin naci amanarsa ni kuma banaso na sami matsala da Yayanki...."
Chapter 94 · 0% Book details