← Book details Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 98

Sashe 49

Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Siraj yaci gaba da fad'in "Haka Nana H take and especially akaina saboda basu san wani uba ba sai ni, shak'uwata da ita tun tana k'arama ya samo asali so sai take ganin kaman idan nayi aure matar will steal me from her kin gane... Amma tanada kirki sosai itama, and I'm pretty sure you'll soon get along with her too..."

Cikin sauri ta shiga girgiza kai kana tace "No no I don't wanna get along with her.."

Ba tareda ya dubeta ba murya cikeda umarni yace "You must cos she's your husband's fav...."

Girgiza kai kurum Azeeza tayi kana tace "Stop fooling yourself I'm not your wife..."

Murmushi ya kumayi kana yace "In the future..." Girgiza kai kurum tayi don ta soma sabo da halin Siraj

Lokaci guda ta shiga Juya maganganunsa akanta, Nana H bata so yayi aure, bata son ganinsa da mace, tabbas akwai wani b'oyeyyen Al'amari da ya shige duhu...

Tayi nisa duniyan tunanin sanda taji muryarsa yana fad'in "We are here..."

Sai sannan ta kula har sun iso Siraj ya iya falfala gudu a mota sam bai ganin nisan unguwannin Abuja... Hannu tasa zata bud'e marfin motar kafin taji Siraj ya Kira sunanta

Juyowa tayi tana dubansa yanda ya kafeta da madaidaitan idanunsa masu yalwan suma, gabanta yayi wani irin fad'uwa lokaci guda ta sauk'e idanunta k'asa

Murmushi Siraj yayi don abinda yake son gani kenan if she feels something for him.... shopping bag d'in da Ammah ta bata ya mik'a hannu backseat ya d'auko kana ya mik'a mata

D'an kallonsa tayi had'i da mak'e kafad'a

"Why...?" Ya furta yana dubanta

"Ka maida Ammah kayanta Barrister zaiyi fad'a

Siraj ya d'an gyara zamansa kana yace "Bzaiyi fad'a ba cos soon zan fad'a masa about us, and idan baki karb'a ba Ammah zatayi fushi, ki karb'a kinji.... Shed'an ne mai maida kyauta..."

D'ago idanu tayi tana dubansa taga murmushi saman fuskar sa, a hankali ta mik'a hannunta ta karb'a kana tace "Na gode Sir...."

Har ta fice daga motar Siraj bai bar wajen ba saida ta isa k'ofar gida ta jiyo muryarsa yana fad'in "Banda latti, and my coffee should be ready before my arrival.."

Murgud'a masa baki tayi kana tasa kai ta wuce...

Ya rakata da kallo murmushi mai bayyan hak'wara saman fuskarsa kana ya d'an bud'e murya ganin ta bud'e gate zata shige yace "See you tomorrow...."

Bata amsa sa ba sai waiving da ta masa had'i da sakar masa murmushin yak'e...

A hankali ya furta "I love you...." Kafin ya tada motarsa ya bar wajen...

Cak Azeeza ta tsaya jiyo sautinsu da tayi suna magana cikin fad'a..

Nasaar yaci gaba da fad'in "Because of your selfishness kana neman jefa rayuwar k'anwarka cikin garari, kan wani banzan revenge naka, you don't even care ko meye Siraj zai aikata da k'anwarka.....!"

Cikin tsananin d'aga murya da huci Junaid yake fad'in "You shut up, and don't you dare raise your voice on me... Who the hell do you think you're, just because you helped me out, sai kayi tunanin zaka shiga rayuwar mu nida k'anwata and think you can decide for us... Azeeza is my sister she's my sister, and I know her well, nasan bazata tab'a yin abinda kake fad'i ba.... I raised her well nasanta nasan abinda zatayi nasan wanda bazatayi ba... Na fad'a maka ka ajiye kishinka a gefe don ni na saka Azeeza tayi playing idiot d'in I know she'll never fall for him....!" Ya k'arashe yana tsananin huci...

Jinjina kai Nasaar yake shima d'in hucin yake kana yace "Fine... Naji, amma ka sani I love Azeeza I love with all my heart, and I can't sit back watching you ruining her life because of your stupid revenge, I'll protect her koda da rayuwana ne...." Yana ida fad'in haka yasa kai ya fice daga d'akin yana huci...

Azeeza dake lab'e bakin k'ofar kuka ne yazo mata sosai, tabbas Siraj na tsananin buk'atarta ta lura wani ne mai laifi yake b'uya a bayansa, kafin Yayanta ya cimma burin fansarsa kan Siraj dole tayi iyaka k'ok'arinta wajen kub'utar dashi.... Lokaci guda ta wuce d'akinta batama bari suka san ta dawo gidan ba....

***

*Misau*

Batasan ya shigoba sai hancinta da ya jiyo mata k'amshin turarensa, a hankali ta juyo da dubanta garesa...

Murmushi ne kwance saman fuskarsa kana ya soma takowa ya shigo. a hankali ta d'an mik'e daga kwancen da take ta zauna....

Ahidjo ya k'araso gefenta ya zauna had'i da k'ura mata idanu.... Kallon da yake mata har saida ya bata tsoro don kallon yayi yawa har tayi tunanin ko wani abu ne a fuskarta....

Ganin tana shafa fuskarta alamun tana neman abinda yake kallo yasa Ahidjo d'an murmusawa kafin ya kamo hannayenta ya rik'e

A hankali ya furta "Ki barni na kalli fuskarki ta yuwu kallon k'arshe kenan, gobe zan tafi Deejoh....."

Gabaki d'aya yinin yau kalamansa karyar mata da zuciya suke, gaba d'aya ta koma sukuku... Girgiza masa kai tayi kana tace "Yaya zaka dawo, nasan zaka dawo ka tafi dani kamar yanda kace...." Ta k'arashe k'walla na ciko idanunta

Murmushin k'arfin hali yake yana dubanta lokaci guda ya saka 'yan yatsunsa yana share mata hawayenta yake fad'in "You're so special here..." Yayi nuni da k'irjinsa kafin yaci gaba da fad'in "You're so special to me Dee, and last night was something special.... just unforgettable.... You're now part of me Dee..."

Kuka kawai Deejoh take dukda ba gane abubuwan da yake fad'i take ba, lokaci guda take girgiza masa kai kana tace "Dan Allah ka min magana yanda zan gane, kace min zaka dawo kaji Yaya...."

Matso da ita yayi ya rungume cikin jikinsa had'i da kwantar da kanta saman k'irjinsa tana jin bugun zuciyarsa yanda yake da sauri da sauri... A hankali ta lumshe idanu tsananin k'aunar mijinta na fuzgarta

Saida yaji kukan nata ya lafa cikin k'irjin nasa kafin yaci gaba da fad'in "Dee promise me idan na tafi bazakiyi kuka ba, kinsan idan kikayi kuka daga duk yanda nike zanji...."

Bata iya cewa komai ba sai jinjina masa kai da tayi

Ahidjo yaci gaba da fad'in "I'll miss you Dee, so much.... Ki kula min da kanki kinji...."

Nan ma kai kurum ta jinjina masa a hankali kafin tace "Toh yaushe zaka dawo...?" Tayi tambayar cikin sark'ewar murya

"Just two weeks sati biyu kawai zanyi insha Allah..."

Jinjina kai ta kuma tana goge ragowar hawayen idanunta, amma cikin zuciyarta kukan zuci take shid'inma da zai samu yayi kukan da wani abin ya ragu masa sabida yanda yake ji can k'asar zuciyarsa, a hankali ya gyara masu kwanciyarsu ya d'an kishingid'a yayinda Deejoh ta zamto samar k'irjinsa...

A haka Innah ta lek'o da zummar shigowa saidai ganinsu a haka da tayi ya sata fasa shiga d'akin, a hankali ta koma sihirtaccen murmushi saman fuskarta....

***

*Damaturu*

Baje-baje Daddah tayi tsakar gida tana basu labarin gudun data kwasa, idan taji an buga k'ofa sai ta soma dafe-dafen mik'ewa tana neman hanyar gudu saidai taji ashe almajirai ne masu bara sai ta koma ta zauna tana haki...

Mairo na dariya take fad'in "Wllhi Daddah naji ina son auren mai saka uniform ko don saboda ke...."

"Ya kawo min raini ubansa zanci ke nifa ba tsoro nikeji ba, shi sojan ma da nake shayi nasan ana masu alluran mahaukata ne shiyasa, kuma idan wannan allurar ta motsa toh fah basu sanin mi suke yi, wato rabona da irin wannan gudu tun ina matashiya 'yar shad'aya da na sayin fad'an wata k'awata ana ce mata Dumba, ta zubda wata yarinya tallanta ni daga zuwa aka saida min fad'ar sile guda don ni da saidai na sayi fad'a ba'a nemata, toh shine yayan yarinyar mafarauci ne ya kwance mana karnukansa na farauta nayi gudun famfalak'i.... "

Umma Marie mai zatayi banda dariya...

Mairo ma dariyar take kana tace

"Aiko ni kika bari da tsaro zance ma k'aton arne wllhi har k'aryata ta k'are na rasa mai zance masa, gashi harda masa kwtancen k'arya don ce masa nayi ba shagon su Dakura muke aiki ba...."

Daddah ta bud'e baki tana dariya kana tace "Ai wllhi gobe gobe zan nemi gidansu wancan kututturiyar don sai naga yaya jikinta ya kwana..."

Gaban Umma Marie ya fad'i jin fad'an Daddah bamai k'arewa bane... Cikin lallama tace da Daddah "Ni kuwa Daddah da kin hak'ura ma had'u da ita dai a centre..."

Daddah tace "Inaa ai bataci ta fitowa Santa (centre) ba yanda ta lallasu, gwara muje mu mata gaisuwan ban gajiya, ko ya kikace Mairo ta..."

Lokaci guda Mairo ta jinjina kai tana fad'in "Haka ne Daddah ta..."

Umma Marie dai tsoro lamarinsu ya soma bata ta soma tunanin idan zata iya ci gaba da zama da wad'annan mutane masu sayo fitina da kud'insu.....

***

A ranar cikin jikin juna sukayi bacci shida Deejoh, wani irin bacci mai cikeda shauk'i da ni'ima ya had'u da sanyi maras cutarwa dake kad'awa a garin, Asubahin fari kafin ayi kiran farko Ahidjo ya farka yaji Deejoh cikin jikinsa, wayarsa ya lalumo ya haske fuskar Deejoh dake bacci da ita, a hankali ya saki murmushi kafin yakaiwa lips d'inta sunba, ganin ta d'an soma motsawa ya sanyasa saurin gyara mata kwanciyarta kafin ya mik'e a hankali ya nufi d'akinsa... Cikin sauri ya shiga kimtsa kayayyakinsa....

Ya jima yana duban Deejoh rik'eda jakarsa kafin ya k'araso ya shafi fuskarta a hankali, turarensa da yake amfani dashi ya ajiye mata gefenta kafin a hankali ya furta "I'm sorry Dee... I'm sorry, Allah yaso saduwarmu...." Ya k'arashe muryarsa na tsananin rawa, a hankali ya mik e bayan ya kuma gyara mata bargonta kafin ya rataya jakkarsa ya fice....

*SameenaAleeyou📚**FUSKA UKU*🏮

*35*

*©Sameena Aleeyou...✍🏽*

A hankali Deejoh ta bud'e idanunta, nan taga haske ya haske labulen d'akin alamun ta makara sallan asuba.... Waigawa gefe da gefenta tayi taga bataga Ahidjo ba, k'irjinta yayi wani irin yankewa ya fad'i.... A firgice ta mik'e k'irjinta naci gaba da bugawa ta nufi sashen Ahidjo, cikin sauri ta dad's d'akinsa gabanta naci gaba da fad'uwa tana addu'an Allah sa mafarki take bai tafi ba....
Chapter 49 · 0% Book details