← Book details Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 98

Sashe 71

Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bai kai aya ba Siraj ya katsesa "Hey hey Cut it out, will you...." lokaci guda kuma Siraj d'in ya Fuzar da iska idanunsa kan Lamid'o hannayensa rik'e da kunkuminsa sosai yanayinsa zai tabbatar maka a gajjiye yake da al'amra masu rikita lissafi... Lokaci guda ya soma girgiza kai kana yaci gaba da fad'in "He was here... He was right here, don't tell me kai ka turosa ya nemi Nana A to get his revenge on me?? ...." Ya k'arashe jijiyoyin wuyansa da goshinsa suna kuma tashi...

Da mamaki Lamid'o ke dubansa domin Siraj d'in ya koma tamkar wani zautacce....

"Ban....fahimceka ba Siraj, mai kake nufi... Waye kenan....?"

Siraj ya kuma shafe kansa data cunkushe masa kana yace "Lamid'o that imbecile was here.... Bai mutu ba, Yana raye and.. And I'm pretty sure da biyu ya soma aiki a foundation d'in Nana A, yanzu haka maganar da nake maka soyayya suke...."

Wani irin bugu k'irjin Lamid'o yayi ya shiga ganin walk'iya na gifta k'wayan idanunsa...
.
Girgiza kai ya soma kana yace "No Siraj, you must be mistaken, Junaid ya mutu saidai wani mai irin sunansa mai kama dashi ka gani amma bashi ba...."

A hasale Siraj ya katse sa da fad'in "Ya kake magana haka Lamid'o... Ina fad'a maka na gansa, na gansa da idanuwa na... Dole mu zama ready I'm pretty sure revenge ya dawo d'auka akanmu...."

Shafe goshinsa Lamid'o yayi yana mai jinjina kai ga k'irjinsa dake bugu cikin da sauri da sauri kana yace "Idan kuwa haka ne he must be after the three of us, yana neman Nana A domin yayi ruining d'inmu nida kai....."

Cak Siraj ya tsaya wani tunani na yawo a kwanyarsa sanda ya tuna kalan mutuwar da Ahidjo yayi.... Saurin d'agowa yayi yana duban Lamid'on kana yace "Shi ya kashe Ahidjo.... Na tabbata shi ya kashe sa.... Shine ya soma mana d'auki d'ai-d'ai... Ya soma da Ahidjo, and nida kai zaiyi amfani da Nana A ya ruining d'inmu.... I swear I'll not allow him to come near my niece.... Lamid'o we need to do something right away...." Ya k'arashe tsananin tashin hankali na nunawa a fuskarsa....

"Whatttt!!!!! Ahidjo ya mutu....
Ahidjo fah kace Siraj....?" Ya k'arashe cikin tsananin nuna tashin hankali

Jinjina masa kai Siraj yayi kana yace "I'm sorry kaji abin gatsau amma dole ka sani... We lost our dear friend..... Ahidjo my brother my friend my in-law is gone.... Kayi hak'uri Lamid'o...." Ya k'arashe sanda Lamid'on ke matso k'wallan da suka mak'ale cikin idanunsa lokaci guda ya dafe kansa saman k'irjin Siraj wanda shima tuni zuciyarsa ta kuma karaya... Sam basu san sanda Al'amra zasu daidaita masu a rayuwarsu ba...

Cikin juriya Siraj ke dafa kafad'un Lamid'o yake fad'in "You need to be strong yanzu da al'amra suka fara bayyana... Lamid'o bazamu kuma maimaita irin laifukan da muka tapka a baya ba.... Idan munaso rayuwa ta daidaita mana tabbas sai munbi komai hanyar data dace.... Kayi hak'uri..." Ya k'arashe suna masu rungume juna sanda su dukansu biyun sukayi bursting cikin kuka..... Allah sarki idan ka gansu a haka dole su baka tausayi...

Jikin Lamid'o yayi sanyi sosai, tabbas ya sani Ahidjo da Siraj basuda alhakin mutuwar Zeenat, ta yaya zai bayyana wa Siraj ga dalilin mutuwar Ahidjo, ta yaya zai fad'i wa Siraj ya san gaskiyar abinda ya faru da Zeenat four years back... Ta yaya Ahidjo zai tab'a yafe masa yanzu da baya nan... Dole ne ma yayi kuka, a cikin su ukun yanaji yafi kowa zunubi, ta yaya ubangijinsa zai tab'a yafe masa....

Da k'yar Siraj ya iya basa baki kafin ya d'an saita kansa, amma kam zuciyarsa na tsananin masa zogi da rad'ad'in abubuwan da ya aikata a rayuwarsa wanda duka ba kowa bane sila illa Bulama...

K'aran da wayar Lamid'o yayi ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya tafi.... Ganin mai kiransa ya sanyasa fuzar da iska kana yace "Siraj there's something you also need to know...."

Kallonsa Siraj yayi da jajayen idanunsa kana yace "Don't tell that imbecile was the one who kidnapped you...."

Girgiza kai Lamid'o yayi kana yace "I don't think he has anything to do with my disappearance...."

Da mamaki Siraj d'in ke dubansa kana yace "Ban gane ba...."

Sauk'e ajiyan zuciya Lamid'o yayi had'ida share fuskarsa ya d'an gyara tsayuwarsa "Siraj your niece.... Nana K is alive....."

Kallonsa kurum Siraj yake cikin tsananin bugun k'irji... "What!!!!" Lokaci guda kuma ya d'an murmusa kana yace "Kar mu dawo da wannan zancen Lamid'o Nana K ta mutu samada ahekara ashirin... Ko a baya Ammah da tayita saka ma ranta jiikar tata bata mutu ba wata rana zata dawo garemu k'arshe ta hak'ura da ta fahimci da gaske d'in ta mutu..."

Girgiza kai Lamid'o ya kuma yi kana yace "Siraj wllhi Nana K 'yar brother d'inka mai rasuwa tana raye, sannan wannan shine dalilin da yasa na b'ace kuma ina zargin shine dalilin mutuwar Ahidjo.....!!!"

Wani irin bugu k'irjin Siraj yayi wanda yasa k'iris ya rage bai kifa k'asa ba....

Lamid'o ya tallafosa ya rik'osa kana yace "Mu shiga ciki Siraj ayi komai gaban su Ammah...."

Tamkar rak'umi da akala haka Lamid'on ya shiga janyo Siraj suka nufi cikin gidan...

***

*Damaturu*

Da dafe bango ya mik'e ya d'an tsaya still k'afafunsa suna d'an rawa alamun har yanzu babu k'arfi jikinsa...

Daga Hafiz har Baba Malam annuri ne ya cika fuskokinsu, lokaci guda suke furta Masha Allah.....

Shima Alin murmushi ne saman kyakkyawar fuskar sa wanda ya k'ara haske sabida rashin fita da yakeyi....

Baba Malam ya dubi Hafiz kana yace "Mik'a masa sandar Hafizu...."

Cikeda risinawa Hafiz ya mik'awa Ali sandar ya d'an soma takawa murmushi bai bar saman fuskokinsu ba sanda Ali kewa Hafiz godiya...

Sosai sukaji dad'in takawa da Ali yayi Hafiz na biye dashi a baya tsoron kada ya fad'i...

Mama Azumi ce ta k'araso itama fari'a fal fuskarta take mik'a godiyarta ga Allah, ta k'arada "Lallai yau zaka raka k'aninka wajen karatu da alama ka kusa soma tuk'aku a babur d'inma...."

Murmushi Ali yake kana yace "Mama inajin k'afafun sunmin nauyi sosai..."

Mama ta jinjina kai kana tace "Ai dama hakan zakaji, kar ka damu sannu a hankali zai warware idan kana d'an motsasu.... Hafiz ku d'an fice koda bakin lungu ne amma kada kuyi nisa sabida komai kad'an kad'an ake d'iba..."

Hafiz ya amsa mata lokaci guda Baba Malam da kansa ya d'auko sabon takalmi slippers ya ajiyewa Ali Hafiz ke k'ok'arin taya Alin sakawa.. Yanda gaba d'aya suke rawar jiki akansa sai ya sanyasa k'walla, shin a rayuwarsa ta baya har yanada iyaye da 'yan uwa masu k'aunarsa irin haka, tabbas idan har shi d'in basu suka haifesa ba duniyar nan cike take da mutanen k'warai... A haka suka fice bakin lungu Hafiz na biye dashi na tayasa hira, kaman kuwa had'in baki nan suka had'u da Dr Sahal yazo duba patient d'insa....

***

A parlor Lamid'o ya zauna yayinda Siraj ya nufi upstairs kiran Ammah....

Sam bai sanar da ita tafe yake da Lamid'on ba sabida yasan kalan fushin da Ammah keyi dashi Lamid'on, don ko bayan ranta ne tace bata yarda Lamid'o ya kuma taka k'afarsa a gidan ba balle family d'inta su kuma accepting d'insa...

Hango Ammah da Lamid'o yayi tana sauk'owa daga stirs ya sanyasa saurin mik'ewa tsaye.....

Tun daga nesa Ammah ta soma huci tana nunasa da yatsa take fad'in "Mai ya kawo wannan mutumin gidan nan.... Har kanada k'arfin halin da zaka kuma nuna fuskarka a nan bayan abinda kayi...."

Siraj yayi saurin tare Ammah yana fad'in "Ammah dan Allah kada ki kori Lamid'o ki tsaya kiji da mai yazo, please Ammah...."

A fusace ta kuma fad'in "Na fad'a maka bana son sake ganin wannan fuskar tasa a gidan nan.... Ya wuce ya fice min a gida...."

Tsawan da Ammah tayi yayi dai-dai da fitowarsu Nana A da Ayiya...

Hango Lamid'o tsaye a parlorn ya sanyasu daskarewa...

Siraj yaci gaba da fad'in "Ammah you need to calm down kiji da meye Lamid'o yazo...."

Cikin tsananin fad'a ta kuma fad'in "Banaso naji da meye yazo, bana k'aunar sake ganin wannan fuskar tasa, my granddaughter has already moved on babu abinda zatayi da macuci mayaudari mak'aryaci irinsa..."

Cikin tsananin b'acin rai Siraj da ya gama zama exhausted yace "Koda maganar ya shafi jikarki da kikayi zaton ta mutu sama da shekaru ashiri... Koda ace maganar ya shafi Nana Khadijah.....!!!"

Gabaki d'aya k'irajensu suka shiga bugu a dai-dai lokacin da Nana H ta k'araso parlorn, da alama taji duk abinda Siraj ke fad'i... K'irjinta bai k'arashi bugawa ba saida taga Lamid'o tsaye gabanta.... Wani irin birki tayi yayinda jiri ya kusan kifata k'asa......

*SameenaAleeyou📚**FUSKA UKU*🏮

*49*

*©Sameena Aleeyou...✍🏽*

Cikin kuka Ammah taci gaba da girgiza kai tana fad'in "Siraj ta yaya zaka yarda da wannan mayaudarin, na tabbata wannan d'aya ne daga cikin k'arerayin da ya saba, Nana Khadija ta rasu ta rasu, na tabbata da ace jikata tana raye da ta dawo gareni....." Kukan Ammah ya tsananta yayinda numfashinta yaci gaba da fita da k'yar da k'yar, lokaci guda take k'ok'arin yin collapsing Siraj yayi saurin rik'ota yayinda Nana A da Ayiya suma sukayi kanta....

Huci kurum Nana H take tana duban Lamid'o wanda shima ya nuna tashin hankalinsa da ganin irin yanayin da Ammah ta shiga.... Cikin sauri Nana H ta k'arasa gabansa tana mai ci gaba da huci take dubansa, lokaci guda ta soma fad'in "Mai ya kawo ka mai ya dawo dakai, azzalumi macuci mayaudari maci amana... Ka dawo ne ka yaudari 'yar uwata da sabon k'arya cewa Nana K na raye.... Ko kuma zuwa kayi ka k'arasa mana Kakarmu.... Nana A bata buk'atarka ta sami madadinka, you better get lost kafin kaga abinda zan maka...." Ta k'arashe tamkar sabuwar kamun hauka tana neman abinda zata d'auka ta kwad'awa Lamid'o, hankalin Siraj kam na kan mahaifiyarsa da tayi collapsing a wajen... Nana A ce tayi k'arfin halin rik'e Nana H ta k'araso ga Lamid'o tanai masa wani irin duba na tsana da Allah wadan mai hali irin nasa, cikin hawaye take fad'in "Dan Allah ka tafi, kar ka kuma dawowa rayuwarmu, everything is alright now... Bamu buk'atarka... Ka tafi dan Allah...."
Chapter 71 · 0% Book details