← Book details Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 98

Sashe 52

Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

K'uri ya mata yana dubanta kafin ya rungumota cikin jikinsa, lallashinta yake yana mai ci gaba da fad'in "Sweetheart I thought you're used to this already, haba Nana ta ki bani k'arfin gwiwa please, kin rigada kinsan abinda zan tafi nema..."

Jinjina masa kai tayi tana mai share hawayenta take fad'in "Hakane Heedj, you're the best Allah ya taimakeka ka dawo mana da Nana K safe and sound...."

Hannayenta ya kama kana yace "Ameen sweetheart, don't ever forget how much I love you okay...."

Jinjina masa kai tayi tana murmushi take masa addu'an kariya kana tace "You take care okay..."

Shima jinjina mata kai d'in yayi had'i da manna mata peck gefen chick d'inta kana ya rataya jakkarsa....

Har mota ta masa rakiya tanai masa waving kafin yana wucewa ta komo cikin gida tamkar zata kifa da k'asa ta d'auki wayarta ta shiga dialing layin Nasaar.....

Nasaar na ganin kiranta yayi saurin d'agawa dama ita d'in yake jira...

"Kana jina, he just left the house get ready and don't you failed me, zan turo maka brand d'in motar in short kawai zan turo maka hoton motar right a way...." Bata ko jira cewarsa ba tayi saurin katse kiran tana k'ok'arin tura hoton motar Ahidjo...

Da shike a speaker ya saka masu wayan shida Bulama suna gama saurare Bulama ya kece da wata iriyar dariya kana yace "Nana Hafsatu kenan ba don ke jinjin Mas'ud bane sai nace musanyenki akayi da nawa jinin, koda baki kashe shashashan mijin naki ba ni nan zan kashe maki shi, sannan zan kuma d'aura alhakin mutuwarsa a wuyarki tareda dalilai masu k'wari...." Ya kuma duban Nasaar kana yace "Aikinka yana kyau sosai...."

Lokaci guda Bulama ya mik'e yana mai kiran yaransa....

Nasaar kuwa dafe kansa yayi yana tambayar kansa shin mai ya aikata....

***

"Sabi'u ban yarda Nana H tasan inada wata mata ba acan gida, na yarda da kai kuma nasan ko ban dawo ba zaka kular min da family na, akwai rayuwa akwai mutuwa shiyasa na sanar dakai gameda Deejoh...."

Jinjina kai Sabi'u yake yana dubansa kana yace "Kar ka damu DT you can always count on my support, insha Allah...."

Jinjina kai Ahdijo yayi had'ida masa godiya kana yace "Ni zan wuce yanzu Allah ya k'addara saduwarmu....."

Jinjina masa kai kawai Sabi'u yayi kafin ya masa rakiya har wajen motarsa ya shige had'ida barin wajen....

jikin wandon Sabi'u 'yar k'aramar abin sauraren magana ne wanda daga can yanda Junaid yake ya saurari komai yanda duk Sabi'u da Ahidjo sukayi, a hankali Junaid ya shiga matse hannunsa yana tunanin harbi uku ya jiyo sanda yaje ceton Zeenat, wanda ya tabbata cikin FUSKA UKU ko wannensu harbi guda yayi mata... A hankali ya furta "Zaka mutu yau kaman yanda ka kasheta...."

Tunda ya soma driving yake tsintar kansa da wani irin fad'uwar gaba, ga wani irin gudu da bai tab'a yin irinta ba shi yake falfalawa bisa hanyar, tafiya tsakanin Abuja da Yobe ba tafiya bane mai sauk'i kasancewar shid'in d'ansanda ne yasa duk checkpoint d'in da ya iso suna ganin ID d'insa suke sara masa su basa hannu, yawan checkpoints dake tsakanin Jos to Bauchi yasa basu cimmasa ba sabida tashin tashin na hankula da ake yawan samu bisa hanyar, sannan Bauchi to Damaturu shima akwai checkpoints sosai sabida Al'amarin tsaro dake bisa yankin.... Duk wannan tafiya da Ahidjo keyi baisan ana biye dashi ana farautar rayuwarsa ba, gari ya soma duhu sanda ya shiga garin Damaturu baisan ina ya nufa ba first saidai yasan hoton Nana H da Nana A dake tafe dashi zaisa ya samu nasaran abinda ya kawosa cikin yardar Allah tunda su duka ukun are identicals....

Basu cimmasa ba sai a garin ta Damaturu

A dai-dai wani duhuwa ya hangi wata mota ta sha gabansa yayinda wasu k'artai suka nufo motarsa suna masa nuni da bingogi suke fad'in kada ya motsa....

D'aga hannayensa sama kurum yayi yana tambayarsu su fad'i mai suke nema daga garesa.....

Fad'i suke idan yayi motsi zasu harbesa, lokaci guda d'aya daga cikinsu ya shige k'asar motar, Ahidjo yanaji suna k'ok'arin fasa wajen wucewar man fetur baida halin motsawa don sun pointing bindiga saitin kansa yana motsawa zasu harba....

Lokaci guda fuel ya soma kwarara, tabbas yaji warin fetur amma baiji k'aran zubanta ba sai wuta da ya kama lokaci guda....

Yanaji yana gani wuta na k'ok'arin had'awa dashi don har ya soma galabaita sanda ya soma k'ok'arin ceton kansa.... A dai-dai lokacin wasu mutane sanye da kayan Soji suka iso wajen don basa d'auki yayinda wad'ancan 'yan ta'addan suka gudu....

Sanda Sojin nan suka cirosa haki kawai yake yana k'ok'arin k'arasa cire rigarsa da wuta ya kama, farin fatarsa duk yayi bak'i sabida azaba... Suna cirosa kuwa motar ta kama gadan-gadan kan kace mai tai exploding....

Can gefe suka matsa suna kallon yanda motar ta kama da wuta... Sai sannan Ahidjo ya sami zarafin d'ago kai yana dubansu da zummar masu godiya saidai babban abinda yafi basa mamaki hango wani mutumi da yayi tsakiyar sojojin shi kad'ai ne sanye da jampa sannan mutumin dattijo ne sosai, lokaci guda kansa ya kuma d'aurewa yana mai ci gaba da tarin hayak'i daya turnuk'esa....

Bai ankara ba yaji sauk'an k'otar bindiga a wuyarsa... Dukansa suka shiga yi sanda wannan mutumin ya masu alama, jina jina sukayiwa Ahidjo kafin Dattijon ya k'araso kansa yana dubansa....

Cikin murya mai fita da k'yar Ahidjo ke tambayarsa "Wanene kai, me kake nema daga gareni, waye yasa ka min wannan aikin...." Yayi maganar tamkar mai koyon magana sabida tsananin azaba da ya sha.... Sandar hanunsa tsohon ya kuma kwad'a masa mari da ita wanda saida ya gautar masa da fuska... Lokaci guda yasa k'artan suka d'ago masa Ahidjo da ko tsayuwa bai iyayi sabida azaba kana ya saka hannu ya d'ago fuskar Ahidjon dake nishi da k'yar kana yace "Matarka, matarka Nana Hafsatu ita ta biyani na kashe ka, sabida bataso ka dawo da 'yaruwarta gida, sannan she never loved you, sabida kawunta ta aureka ba soyayya ba.... And now zaka mutu...." Ya k'arashe yana kuma kai masa naushi a ciki

Da k'yar Ahidjo ke girgiza kai yana fad'in Nana H bazata tab'a masa haka ba don tana k'aunarsa...

Dariya mutumin yayi kana yace "Shiyasa nace you're fool, Ka fad'a trap d'inta..." Lokaci guda ya janyo dutsen dake gefensa kafin ya bugama Ahidjo a k'eyarsa nan wani sabon jini ya kece..... Da k'arfin gaske ya kuma tokarinsa ya fad'i gefe babu alamun numfashi a jikinsa....

Bulama ya kece da dariya kana ya furta "Babu wanda ya isa ya bayyana Mairo sai lokacin dana so yayi....." Daga haka shida yaransa suka bar wajen cikin motocinsu, suka bar Ahidjo mace a wajen....

***

Murmushi take daga saman benen tana mak'ale da wayar a kunnenta a hankali ta furta "Very well, ka tabbata motar ta k'one k'urumus....?"

Daga d'aya b'angaren Nasaar yace "I promise you Ahidjo ya zama tarihi tokarsa ma baza'a samu ba....."

Nana H ta kuma murmusawa cikeda jin dad'i kana tace "You know this calls for celebration ya kamata kazo muyi murna a gida...."

Daga haka katse wayar tayi dai-dai sanda ta sauk'o parlor ta zauna bisa kujera tana mai fashewa da wani irin dariya "Heedj heedj heedj you such an idiot, Oh my dear husband I'm truly sorry but you've to die, wannan shine kawai hanyar da zai hana Nana K dawowa garemu, nayi imani idan ina numfashi Ammah da Uncle kai da duk wani dangi namu babu wanda zaisan Nana Khadija na raye balle ta dawo garemu, yanzu na soma toshe duk wata k'ofa da zai sadata da asalin danginta...." Wani dariyar ta kuma fashewa dashi kafin ta soma k'wak'ulo kuka tana fad'in "Yeah yeah, I've to cry for you Heedj, I must cry for you....." Ta k'arashe tana dariya amma hawaye ne ke sauk'owa daga idanunta....

***

Sanda Sabi'u ya sanar da Junaid cewa Ahidjo ya mutu sakamakon tabbatar masa da yaransa sukayi cewa sun k'onesa cikin mota, maimakon yayi farin ciki yaji dad'i sai akasin haka, gaba d'aya sai ji yayi zafin da zuciyarsa ke masa babu abinda ya ragu saima wanda ya k'aru, d'aki ya k'ume yana kuka sosai tamkar k'aramin yaro yana mai tuna Zeenat da alk'awarin da yayi mata na d'aukan fansa akan FUSKA UKU.....

***

*Damaturu*

Wajajen k'arfe biyar suka isa gidan Baba Malam, shashen su Yaya Azumi suka fara biyawa suka gaisa kafin suka k'araso wajen Baba Malam, gaisawa sukayi sosai kafin Baba Malam ya tambayi Mairo ko ta kama addu'an da ya koya mata, tiryan-tiryan kuwa ta soma karanto masa, sosai Baba Malam yaji dad'i ya lura Mairo nada saurin kama karatu, gashi karatun da ya bata shekaran jiya har ta kama...

Baba Malam ya kuma gyara zama yana dubansu kana yace "Maryama inaso ki sanar dani matakin karatunki...."

Mairo tayi shiru tana tuna yaushe rabonta da makaranta na boko ma balle na islama wanda da yawan iyaye muke sakaci dashi mubada k'arfi ma karatun boko bayan wannan karatun addini shine zai taimakemu ranar gobe domin da zaran bawa ya mutu ayyukansa sun tsaya cak, ba hujja bace a yanzu yanda ilimi ya shiga lungu da sak'o kajewa ubangijinka a matsayin rashin sani, kar mu mance tabi'ai da wad'anda suka rigayemu sun sha wahala sosai wajen neman ilimi, mu a yanzu ilimi ya wanzu mana ko ina ya ratsa ko ina, zama babu neman ilimin addini ba k'aramin kuskure bane, don Allah mu gyara mu baiwa lahirarmu himma domin itace rayuwa dawammemiya

Girgiza kai Mairo ta d'anyi kana tace "Malam rabona da makaranta inaga tun muna wata gari mai Rafin zurfi a can ta k'asashen yamma, shid'inma a aji uku na tsaya a sakandare lokacin da muka bar garin ban kuma shiga wata makaranta ba, sannan islamiya kuma nasan a baya mukanje ta allo shima tunda muka baro garin Kazaure na daina zuwa...."
Chapter 52 · 0% Book details