Sashe 38
Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wani munafukin murmushi Nana H tayi kana ta dubi Nana A da kanta ke kife saman cinyarta tana kuka mai tsuma zuciya kana tace "Wllhi bazan barshi haka nan ba, wllhi sai na ci masa mutunci shi bai isa ya wulak'anta 'yar uwata ba yayi tunanin he can get away with it...." Ta k'arashe maganar nata cikin tsananin huci sai ka rantse iyaka gaskiyarta kenan.... Lokaci guda ta nufi cikin gidan Lamid'o mayaudarin murmushi saman fuskarta...
Nana A kam ko zarafin amsata bata samu ba don batama fahimci mai take nufi ba, sautin budurwar Lamid'o data jiyo ya kasa b'acewa daga kunnuwarta...
Nana H na shiga gidan ta dubi su Linda da Bash dake faman bunka sigari, lokaci guda ta ciro check cikin jakanta ta wurgi Bash dashi kana tace "Make sure you tidy up this mess kafin ku bar gidan nan... Kuyi sauri yana iya dawowa any moment....." Tana ida fad'in haka ta fice cikin sauri...
Bash da Linda harda ihun murna sanda sukabi check d'in da kallo...
***
Kallonsa take yanda yaketa jidan kaya wanda akasarin kayan abaya ne irinta larabawa.... Idan tayi magana ma ba amsata yakeyi ba balle taji dalilinsa na mata shopping... Lokaci guda ta b'ata rai sosai murya cikeda tsiwa tace "Sir wllhi wllhi kaji na rantse ko ka saya min kaya bazan saka ba tinda bace maka nayi banida kaya ba...."
Karkatowa Siraj yayi yana dubanta kana yace "A haka kike tunanin zan barki ki dinga ratsa cikin maza kina saka d'inkin atampa riga da skirt ko wani gardi na ganin jikin ki, banson ki dinga janyo hankalin employees d'ina kanki don dokar Kpaninmu ne ba'a soyayya..."
Shaye da mamaki take dubansa, wai kishinta yake ko mai.... Bata kai ga samo amsa ba yaci gaba da umartan masu kantin da su fito masa da designers dogayen riguna 'yan dubai....
Wayarsace tayi k'ara ya d'aga lokaci guda yana mai ambatan sunan Nasaar.... Lokaci guda yake furta "What!!!!.... Okay okay I'll be there in a bit... Kar ka bar wajen just keep an eye please...." Daga haka katse kiran yayi had'i da robbing nape d'insa warily....
Kallo ta bisa dashi kana tace "Problem....?"
D'an dubanta yayi kana yace "An emergency happened in the office, my presence needs there immediately, so zan kira niece d'ita Nana H ta kaiki gida, kar ki bar wajen nan kinji koh, just wait here...." Ya k'arashe yana zira wayarsa a aljihu cikin sauri ba tareda ya jira amsarta ba ya isa yayi settling bills ya fice a fujajan yana neman layin Nana H...
Kambuu wannan matar zai kira wai ta kaita gida... Azeeza ta fad'i cikin zuciyarta... Lokaci guda kuma ta shiga tunanin toh waima wani emergency ne ya faru? Tinda taji Nasaar ne ya kirasa tasan bazai wuce kishi irin na Nasaar bane kurum, yayi hakan ne don b'ata masu fitar tasu.... Toh kodai ta tafine kar ta jira wannan mahaukaciyar niece d'in tasa... Wata zuciya tace jirata kurum tinda yace haka.. Waje ta samu ta zauna tana mai kiran layin Yayanta Junaid...
***
Nana H na ida parking wayar Siraj ya shigo mata, kafin ta sami zarafin sanar dashi abinda ke faruwa tsakanin Nana A da Lamid'o Siraj ya soma sanar da ita buk'atarsa...
Wani irin bugu da k'irjinta yayi k'iris ya rage wayarta bai sullub'e daga hannunta ba....
*SameenaAleeyou📚**FUSKA UKU*🏮
*27*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
Cikin gida Nana A ta shige har lokacin hawaye bai daina zarya saman fuskarta ba... Ammah da Ayiya suna parlor ta wucesu ba tareda tace dasu komai ba...
Gaba d'aya hankulansu tashi yayi ganin yanayin nata, Ayiya tabi bayan Nana A tana tambayarta abinda ya faru, inaa Nana A sam bata sami zarafin amsata ba, hankalin Ayiya idan yayi dubu ya tashi... Cikin sauri ta fice daga parlorn tana rangad'awa Malam Sile kira, bata hangi kowa ba sai Nana H da tayi zaune cikin mota ta rasa meke mata dad'i...
A d'ari Ayiya ta nufi Nana H tana fad'in "Ni dama nasan za'a rina... Muguwa mai mugun hali uwar mai kika mata....?" Ta k'arashe tana fincikan marfin motar Nana H
Wani banzan kallo Nana H ta watsa mata irina banida lokacinkin nan kana ta karkato da kyau tana duban Ayiya dake faman huci kana tace "Wannan shine lokacin da nake jira yazo... Barikiji na fad'a maki Nana H ta wuce duk wani tunaninki, tuggunki da kuma makircinki... Sannan da kikazo kina min shouting akai mai yasa baki tsare d'iyar taki kin tambayeta ba....?" Ta kuma murmusawa kana taci gaba da fad'in " Kije ki tambayeta mai Lamid'o Sarki naki ya mata na tabbata daga nan zaki sami cikakkiyar bayani don ni banida lokacinki...." Tana ida fad'in haka ta finciki motar ta tayi gaba
Ta bar Ayiya tsaye a wajen tana faman tururi
***
Shafa kansa Lamid'o yayi had'i da fuzar da iska kana ya kuma damk'e wayar yana mai ci gaba da fad'in "Look zan biya ko nawa ne.... Just tell me wani aiki kake wa Bulama...."
Nazir ya shafi kansa yana muzurai kana yace " Kaman nawa zaka biyani....?"
Cikeda jin dad'i Lamid'o yace "Ka fad'i amount d'in da kake so...."
Nazir baki sake yace "Haba rankashidad'e don't take me for a fool mana... A waya fah muke maganar nan.. Naji alert kafin na baka duk wani information da kake nema gameda Mairo, I'll send my bank details ka fahimta...."
Lamid'o ya murmusa kana yace "Babu matsala sai na jika daga yanzu zuwa anjima..." Daga haka katse kiran Lamid'o yayi had'i da sakin murmushi, zuciyarsa tana kuma tunzurasa wajen sanin wacece MAIRO....
Suna ida waya Nazir ya kuma ficewa ya nufi gidansu Zaliha ko an sami wani labari gamedasu Mairo, don tunda su Mairo suka bar garin cikin neman yanda zai samesu yake wayoyinsu gaba d'aya baya shiga...
***
*Damaturu*
Cikin tsananin fushi Mairo ta kuma duban Daddah kana tace "Daddah fisabilillahi mai yasa zaki karya min SIM d'ina mai yasa zaki min haka, haba Daddah shin kina kyautawa rayuwata kenan...?"
Daddah dai tinda ta soma magana tab'e baki kurum take ba tareda ta furta koda kalma ba k'arshe da abin ya isheta mik'ewa tayi tana duban Mairo kana tace "Wai kin mance duk garin da muka baro toh doka ce mu canza layi...? Mairo wai meke damunki ne, shin karya layin waya yau ya zamto bak'on abu a wajenki ne... Sanin kanki ne bazamu tab'a canza gari bamu canza layi ba.... Idan da sabo ya kamata wannan ya zame maki jiki...." Ta k'arashe tana janyo kayan sana'arta kasancewar yau zasu fara halartar shagon d'inkin su Umma Marie don tuni ta sama masu gurbin aiki a wajen....
Mairo kaman ta fashe ta dubi Daddah tayi k'wafa kana tace "Amma dai kinsan cewa akwai mutane masu mahimmacin a rayuwata da muka baro a Tambuwal, yanzu fisabillillahi ina zan sami Nazir da Zaliha....?"
Tsuka Daddah taja bayan ta sake baki tana dubanta kana tace "Yo sai mai, ke duniyar nan da kike gani mutum ba abin yarda bane ka gama rayuwa da wani yana nan yana binka da sharri, ki ciresu a ranki idan da rabon ku sake had'uwa wani lokacin sai kiga Allah ya had'aku..... Karma kiyi hushi Mairamu na, Allah sa haka shine alkhairi don layin waya kam tun muna kwalta na tauneta...."
Girgiza kai kurum Mairo tayi cikeda takaici kana ta isa saman carpet ta suri Jakarta ko takan Daddah bata kuma bi ba tayi ficewarta, dai-dai lokacin Umma Marie ta iso tana tambayar Daddah ko sun shirya...
Daddah na washe baki take fad'in "Mun shirya Mari 'yar aljannah ke kawai dama muke jira.."
Umma Marie ta murmusa cikeda jin dad'i kana tace "Madalla mu k'arasa waje toh kar lokaci ya k'ure mana...."
A waje suka tadda Mairo d'aurin kallabinta a goshi don yau a sama take jinta tinda Daddah ta takaleta, k'iris kawai take jira..
Suna fitowa Mairo tayi gaba abinta, tana tafiya tana 'yan wak'e-wak'enta, Umma Marie sai murmushi take don tasan bazai wuce Daddah bace ta takali Mairo, a d'an zamansu tare har ta fahimci su duka biyun mafad'ata ne amma suna birgeta sosai, har cikin ranta take jin k'aunarsu....
Dakura ce zaune bakin shagon sai faman fetsa rashin kunyarta ga duk wanda taga dama take, dama haka nan Dakura take akwaita da fad'an rashin gaskiya harta Hajiya Yagana mai shagon d'inkin tasan halin Dakura, gashi ta zame mata k'arfen k'afa ta kasa korarta, Dakura masifeffiya ce ta k'arshe, da yawan customers da suka daina kawo d'inki Dakura ce ta koresu....
Tinda su Daddah suka shigo Dakura ke binsu da kallon banza haka nan tak'i jinin Umma Marie sam basu shiri, saidai Umma Marie mace ce mai tsananin hak'uri da kai zuciya nesa wannan dalili yasa bata kula Dakura koda ta takaleta da fad'a....
Wasu kujeru Umma Marie ta nunawasu Mairo tace su zauna kafin Hajiya Kaltume mai Masana'artan ta iso....
Mairo da Daddah suka nemi waje suka zauna suna bin shagon da mutanen ciki da kallo, lokaci guda Daddah ke karantar kowa.... Kowa a wajen ya masu sannu da zuwa idan ka d'auke Dakura dake faman d'age-d'agen hanci tanai wa mutane kallon banza.... K'wafa kurum Daddah tayi tana addu'an Allah sa wannan mai zubin muciyar ta takaleta.....
***
Tana ida parking a k'ofar boutique d'in ta hangeta ta cikin glass tana zaune ta hard'e k'afafu tamkar wata sarauniya..... Nana H ta murmusa had'i da bud'e marfin faran Range Rover d'inta ta fito tana takunta cikin yanga da isa kaman yanda ta saba....
Tana isowa wajen ta tab'e baki tana bin boutique d'in da kallo don kantin wasu Labani's ne wanda sai ka cika kafin ka saya kaya a wajen, lokaci guda ta soma fad'in "Shidai matsiyaci bai iya samun waje ba sai yayi k'ak'a gida... Bacin haka nasan Uncle d'ina is a decent man babu abinda zai had'asa da karuwa har ya fita shopping da ita idan ba ita ta cusa kanta ba....." Ta k'arashe tana hard'e hannaye a kunkuminta...