← Book details Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 98

Sashe 76

Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushin itama tayi kana tace"Ina sonka Uncle ina fata ka kasance cikin farin ciki har k'arshen rayuwarka... Sacrifices d'inka garemu bazasu tab'a k'irguwa ba, na tabbata da ace Daddy yana raye iyakacin gata da soyayya da zai nuna mana kenan... Uncle inai maka addu'an ka sami farincikin LA soon...." Ta k'arashe guntun hawaye na sauk'o mata...

Murmushi ya kuma saki kafin ya saka d'an ysatsan sa ya goge mata hawayen kana yace "Na gode... Na gode da addu'o'inki sweetheart..."

Girgiza masa kai tayi still murmushi saman fuskarta kana tace "Bayan duk abubuwan da kake mana this is the least I can do, I can't wait naga aurenka da Anty Azeeza na kuma d'auki 'ya'yayenku a kafad'una..."

A hankali murmushin dake bisa fuskarsa ya soma gushewa tabbas Azeeza ta mallaki wani gurbi cikin zuciyarsa wanda bai tab'a mallaka ma wata mace ba, sai yanzu ya yarda duk matan da ya nema a baya ashe ba soyayya yake masu ba, yanzu yakeji rayuwa zata iya kasance masa impossible muddin ya rasa Azeeza.. A hankali ya maida fuskarsa ga kwalta ba tareda ya iya sake cewa komai ba...

Jikin Nana A ya d'anyi sanyi sai tanaji dama bata masa maganar Azeeza ba don tasan ta d'ago masa wani mik'i ne cikin zuciyarsa....

Shiru itama tayi bata kuma cewa komai ba har suka isa foundation d'in....

Har Nana A tayi settling a office d'inta babu Junaid babu alamun sa, lokaci zuwa lokaci Siraj ke duba agogon hannunsa don anjima kad'an sukayi zasu had'u shida Lamid'o....

Harta Aunty Larai saida tayi mamakin kasancewar Siraj d'in yau a foundation d'insu, Nana A tayi dialing wayan Junaid bai shiga, hankalin Siraj idan yayi dubu ya tashi.. Dubanta ya kumayi kana yace "Sweetheart bakisan gidansa ba, bakisan unguwar da yake ba...."

Dubansa tayi da mamaki yanda ya zama very desperate kana ta d'an murmusa tace "Kai Uncle what's with the rush na tabbata anything 9am zai iso don Junaid baya latti dukda lalura irin tasa saidai da dalili....

Siraj bai kuma cewa komai ba sai mik'ewa da yayi yana d'an zarya cikin office d'in yayinda Nana A ta ci gaba da duba takardun da bata dubasu ba a 'yan kwanakin da tayi bata zuwa sabida rashin lafiya da tayi...

Knocking d'in da akayi a k'ofa ne ya sanyasu maida hankalinsu k'ofar k'irjin Siraj naci gaba da bugu jira kurum yake yaga Junaid ya turo k'ofa ya shigo...

Wata budurwa ce ta shigo da sallama... Nana A ce kurum ta iya amsa mata sallaman yayinda budurwar tace "Oh sorry Ma'am bansan akwai mutum ba zan dawo anjima..."

Murmushi saman fuskar Nana A tace "A'a Ma'ajura shigo mana babu komai...."

Ma'ajura ta ida shigowa tana godiyawa Nana A lokaci guda take gaida Siraj.... Ko iya amsata baiyi ba saima haushinta da yaji, duk a zatonsa Junaid ne zai shigo...

Fita yayi daga ofishin ya nufi waje ko Allah zaisa ya had'u da Junaid ya taresa tun daga waje....

Wasu takardu Ma'ajura ta ajiye saman table d'in Nana A kana taci gaba da fad'in "Ma'am ga list d'in abubuwan da ake buk'ata kaman yanda kika ce na rubuto...."

Nana A ta karb'a tana dubawa dangin kayayyakin d'inki ne da aka buk'ata... Jinjina kai tayi kana tace "Yayi kyau Ma'ajura, zuwa gobe insha Allah duka za'a sayosu, ko kuma zan baki kud'in idan yaso sai kuje da Malam Sile ku duba a kanti..."

Cikeda rusunawa Ma'ajura ta jinjina kai kana tace "Toh Ma'am Allah ya kaimu..."

Nana A ta amsa da ameen sanda take maida kanta ga file d'in gabanta...

Har Ma'ajuran takai k'ofa sai kuma ta d'an tsaya ta dawo da baya...

Nana A ta d'ago kai tana dubanta kana tace "Akwai wani abin ne....?"

Ma'ajura ta d'an shiga 'yan kame-kame tana son sanar da Nana A d'in abinda ke tafe da ita...

Ajiye pen d'in hannunta tayi tana duban Ma'ajuran da kyau kana tace "Idan akwai wani abin buk'atar just don't hesitate to tell me ok...."

D'an girgiza kai tayi kana tace "Ma'am komai zai wadata insha Allah... Dama...." Sai kuma ta d'an ja birki..

"Umhum ina saurarenki dama me..." Nana A ta fad'i murmushi wanda ya kasance d'abi'arta kwance saman kyakkyawar fuskarta....

"Ma'am dama akwai wata 'yar uwatace basu jima da dawowa garin nan ba, sannan tana irin sana'ar hannu na bead shine nace dama Ma'am mai zai hana tinda ga wasu sabbin d'alibai mun d'iba idan sunada buk'atar koyon sana'ar bead sai ta soma koyar dasu domin bunk'asa sana'ar hannun ga 'yan uwa masu lalura.... Amma Ma'am shawari ne kuma 'yar uwar tawa tana buk'atar aikin sosai shine nace idan da hali ko za'a d'auketa take koyarwa..."

Shiru Nana A tayi tamkar mai nazari kana tace "Kinada sample d'in sark'a ko 'yan kunne da ta tab'a had'awa...?"

Cikin sauri Ma'ajura ta jinjina kai kana ta shiga bud'e zip d'in side bag d'inta tana fad'in "Eh akwai a nan nazo dashi ma...." Ta k'arashe tana warware sark'ar gaban table d'in Nana A...

Juya sark'ar Nana A ta shiga yi tana binta da kallo yayinda Ma'jura ta cika da fargaban kar boss d'in tata tayi rejecting alfarmarta koda shike tasan Madam d'in tasu akwai kirki da sanin darajan d'an Adam...

Lokaci guda Nana A ta shiga jinjina kai kana tace "Yayi kyau matuk'a Ma'ajura, babu komai kina iya zuwa da ita gobe idan Allah ya kaimu...."

Farin ciki ya cika Ma'ajura, haka tayita godiyawa Nana A har ta fice, Murmushin nan ne dai saman fuskar Nana Asma'u...

***

"Think about it Junaid, idan ka bari Azeeza taci gaba da ganin Siraj things might get worse.... And especially now da Siraj yasan cewa kana raye.. Kana tunanin bazai iya sanin cewa Azeeza k'anwarka bace ko kuwa me... Com'on Siraj think about it... Duniyar nan fah k'arama ce...."

Yanda Nasaar ke magana zaka fahimci cikin tsananin tashin hankali yake...

Junaid da fuskarsa ke duban wani b'angaren fuzar da iska yayi kana yace "In that case zamuyi fixing auren a tsakankanun sati biyun nan... Ka sanar da Siraj cewa ka samu Azeeza amma bazai ganta ba sai ranar da ka yanke domin d'aura masu aure.. Period, na tabbata yanda yake mutuwa da soyayyarta zai amince cikin gaggawa..."

Girgiza kai Nasaar yake yana duban Junaid kana yace "What about me...? Ya kake magana haka Junaid, banida kishi ne ko kuwa me da zaka wakiltani na bada auren Azeeza, Junaid ta yaya zan iya... Sanin kanka ne ina son k'anwarka with all my heart ina son aurenta, ina son kasancewa da ita for the rest of my life, ina so ta zamto new mother wa 'ya'ya na... But then mai ka aikata, kama kasa bari na sami kusanci da ita balle na gina nawa soyayyar cikin zuciyarta, kasa na d'auketa da hannayena na kaitawa Siraj... And now kana maganar na baiwa Siraj aurenta... What do you take me for... Are you using me or what....huh...?" Ya k'arashe cikin tsananin d'aga murya jijiyoyin wuyarsa na tashi...

"You need to calm down first idan kana so muyi magana ta fahimta... Nasaar I know exactly what I'm doing, do you think banjin zafin had'a tilon 'yar uwata da mutumin da nafi tsana a Duniya ne.. Huh... Don't be ridiculous Nasaar, kaima kasan auren Azeeza da Siraj bamai d'orewa bane, sannan za dai ayi taron ne amma baza'a d'aura ba don kafin a d'aura zan cika k'udirina....."

Fuzar da iska Nasaar yayi kana yace "Fine, na fahimceka, zan wuce company yanzu na tadda Siraj d'in a can...."

Junaid ya murmusa domin yasan shi kuma damar samun tafiya foundation yayi idan Nasaar ya kira Siraj ya sanar dashi abinda ke tafe dashi...

***

Kasancewar Siraj d'in ya sanar dashi yana foundation ya sanyasa nufa wajen kai tsaye can k'asar zuciyarsa wani irin sanyin dad'i ke masa zai saka farin cikinsa Nana A a k'wayar idanunsa...

*SameenaAleeyou📚**FUSKA UKU*🏮

*52*

*©Sameena Aleeyou...✍🏽*

A farfajiyan foundation d'in ya iske Siraj sai faman zarya yake daga wannan angle d'in zuwa wancan... Gaisawa sukayi sama-sama su duka biyun babu wani mai kyakkyawan natsuwa cikinsu idan ka kallesu dole ka fahimci hakan...

"Har yanzu baizo ba...?" Lamid'o ya tambaya yana mai duba agogon dake d'aure left hand d'insa...

Girgiza kai Siraj yayi kana yace "Jikina na bani bazai dawo ba tinda yasan na gansa, what if yaje yayiwa Nana A wani abin a b'oye ba tareda saninmu ba... Lamid'o I'll never ever forgive myself if something bad happens to her...."

Girgiza kai kurum Lamid'o yake yana k'ok'arin calming Siraj yake fad'in "No no Siraj nothing bad will happen to her insha Allah... I'll protect her with my life... Wllhi bazan tab'a barin wani ya cutar da Nana A ba muddin ina numfashi...."

Fuzar da iska Siraj yayi zuciyarsa nai masa zafi kafin ya d'ago rinannun idanunsa yana duban Lamid'o lokaci guda ya shiga pointing d'insa da yatsa yana fad'in "Ban maka izinin kaje kusan Nana A ba after what you did...." Katsesa Lamid'o yayi da fad'in "But Siraj...."

"No no but.... Kar muyi wannan maganar yanzu Lamid'o mu focussing kan abinda ke...." K'aran da wayarsa tayi ne ya katse masa zancen nasa, ga tsananin mamakinsa sunan Nasaar ne ya fito b'aro-b'aro jikin screen d'in.. Cikin sauri ya d'aga don jikinsa ya basa it must be something about Azeezah...

Daga d'aya b'angaren Nasaar yaci gaba da fad'in "Siraj let's talk in person, maganar bata waya bace.... And it's about Azeeza...."

Saida Siraj ya zabura da jin haka, bakinsa har na rawa yake furta "Nasaar ka sameta ne... Ina Azeezah... Is she fine...? Please tell me nothing bad happens to her..."

Jin yanda ya wani daburce yasa zuciyar Nasaar ci gaba da tafarfasa, ji yake kaman ya shak'o wuyar Siraj ta cikin wayar kurum ya huta.. He hates him like hell...

"Siraj calm down, Azeeza is quite fine... Kawai ka sameni a company muyi maganar...."

Cikin sauri ya shiga jinjina kai kaman Nasaar d'in na ganinsa yake furta "Alright, alright Nasaar I'll be on my way...." Daga haka bai jira cewan Nasaar d'in ba ya katse wayar.... Daga d'aya b'angaren kuwa huci kawai Nasaar yake yana duban wayar kafin ya furta "Imbecile!"
Chapter 76 · 0% Book details