← Book details Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 98

Sashe 26

Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Junaid ne ya d'an turo wheelchair d'insa kusansu sosai kana ya soma fad'in "A tunanina mu k'aro yawan machines d'in tunda mun riga munyi register ma wasu bazamu barsu babu aiki ba, sannan kud'in nan dole daga Company zai fito ba daga aljihun Uncle d'inki ba, besides shi kansa Uncle idan yaji abinda za'ayi da kud'ad'en zai farin ciki.... Ko yaya kuka gani.....?" Ya k'arashe yana dubansu da innocent face d'insa....

Aunty Lami da Asma'u suka kalli juna kafin suka murmusa, Aunty Lami tace "Gaskiya ne Junaid, kayi gaskiya kuma na gamsu da shawarinka...."

Murmushi kawai Asma'u tayi tana duban coworkers d'in nata, har cikin zuciyarta take jin dad'i tun bayan da ta gama jami'a ta zama bored a gida bata zuwa aiki amma yanzu tana jin dad'i sosai, zuwa Foundation yakan sakata farin ciki da mutanen dake ciki..... Tuni itama ta amince da shawarin Junaid ta kuma tabbatar masu cewa yau d'in nan da zaran ta koma gida da yardar Allah zatayiwa Uncle maganar washe gari ta taho masu da feedback.... Akan haka suka samu matsaya ko wannensu cikeda farin ciki....

Shi kad'ai yake duban Nana A yanda take murmushi yana sak'a abubuwa da dama cikin zuciyarsa, he's gonna use her and ruined Siraj completely......

Koda Lamid'o ya Krista don zuwa d'aukarta sai sanar dashi tayi zata dawo da Aunty Lami don zasu biya duba kayayyakin da ya kamata su k'aro a foundation d'in nasu...

Aiko nan driver d'in Aunty Lami ya kwashesu gaba d'aya Junaid na gaba yayinda Aunty Lami da Nana A ke zaune a baya, sai raha suke gaba d'ayansu, sosai suka sake da juna, store daban daban suka biya...

***

Fasa shiga motar yayi tunda tace masa basai yaje d'aukarta ba, lokaci guda ya rufe motar yana k'ok'arin komawa cikin gida yaji mutum rungume dashi ta baya.... Ko ba'ace masa ba yasan itace....

A fusace ya juyo yana k'ok'arin b'anb'areta daga jikinsa yake fad'in "Let go of me you piece of garbage....." Saidai kafin ya ankare ta soma sunbatarsa ta ko ina kaman tsohuwar mayya...

K'ok'arin k'wace jikinsa yake yana fad'in "Nana H what do you think you are doing.... Just... Let go of me.... Ki sake ni nace...."

Kaman cewa yake ta k'ara, fad'i take "No darling I know you want this.... Just don't deny it... Don't you miss me.... Abunda muka saba ne Lamid'o.. I told you can't get rid of H so easily.... Mu ci gaba kawai daga yanda muka tsaya...." Ta k'arashe tana kuma masa wasu salo...

Da k'arfin gaske ya murd'e hannayenta had'i da fincike jikinsa yana fad'in "You really are insane.... Bakida hankali Nana H... Sau nawa zan sanar dake I love your Sister, I love her so much... With all my heart... Get this pls....."

Huci take tana dubansa lokaci guda hawaye ya ciko idanunta, cikin zafin rai ta soma fad'in "Lamid'o you can't do this to me... I know you love me... Wllhi kana sona, you're only confused, dan Allah kar ka juya min baya, wllhi bazan iya jure rashinka ba.... Please don't... I love you wllhi..."

Cikeda tausayi yake dubanta yana tunanin duk yanda akayi kwanyarta nada matsala, girgiza kai yake still na rik'eda kafad'unta kana ya soma fad'in "Nana H, you're sick, you really need to see a doctor... Or if you want I'll talk to Siraj kina buk'atan likitan kwanya.... Please Nana H ki yarda kiga likita, ta yaya zaki makance akan Maza uku duka ke kad'ai.... Wllhi na jima da sanin soyayyar da kikewa Siraj ya wuce na Kawu kawai, soyayyar da bazai tab'a faruwa tsakaninku ba kike masa.... Nana H you can't go on like this... Na rok'r arzikinki dan Allah ki barni na jarabba soyayya da Nana A for the first time in my life.... Dan Allah... Wllhi na sani kamuwan Allah ne ya jefa min soyayyar Asma'u cikin zuciyata tunda a baya banza bola na d'auki mata, sai gashi soyayyar macen dake da nakasa jikinta ya hanani sukuni bayan dubun 'yan matan dana wulak'anta abaya duk a dalilinki... Nana H I beg of you ki rabu dani dan Allah..."

Kuka sosai ta fashe dashi had'i da fad'awa cikin k'irjin Lamid'o.....

*Hetches ina gaisuwa😎*

*SameenaAleeyou📚**FUSKA UKU*🏮

*19*

*©Sameena Aleeyou...✍🏽*

A hankali ya cire jikinsa daga nata yana binta da kallon tausayi yanda take kuka sosai...

"Look Nana H ki rik'e mijinki and try to change for the best, Ahidjo na k'aunarki sosai pls kar kiyi wasa da damanka, oya let me walk you out...." Ya k'arashe yana mai nuna mata hanya...

Lokaci guda taci gaba da huci tana dubansa...

"Lamid'o bazanyi abinda kake umartana ba, bazan fita daga rayuwarka ba, sannan idan baka d'aga idanunka kan 'yar uwata ba I'm afraid things might get worse, I'm.... capable of doing anything,...." Daga haka ciro shades d'inta tayi ta rufe idanunta dashi ta fice daga gidan....

Kallo yabita dashi har ta fice kafin ya fuzar da iska ya nufi cikin gidansa.... Shi kad'ai ya kifa kansa yana tunani... Ya kamata ya takawa mahaukaciyan nan birki before she does something drastic, and especially to Asma'u... Yasan Nana H bata hankali zata iya yin komai d'in kaman yanda tace.... Lokaci guda ya mik'e ya kuma suran car keys d'insa ya fice a gidan....

***

Zaune suke a parlor shida Ammah suna tattauna wasu 'yan lamra, dowawarsa kenan shima d'in ko sashensa bai nufa ba.... Ko sallama babu tasa kai ta shigo gidan har lokacin shades d'in manne idanunta...

Ko kollon arziki basu isheta ba balle su sami darajan gaisuwa ta nufi up stirs abinta.... Daga Ammah har Siraj kallo suka bita dashi, Siraj yayi saurin mik'ewa ya isa gareta yana kirawo sunanta, inaa ko kulasa batayi ba tasa kai abinta har saida ta shige d'akinta... Zata maida k'ofan ta rufe Siraj yayi saurin rik'e k'ofan ya shige d'akin...

"Uncle please not now...." Ta fad'i tana ajiye jakanta had'i da kwab'e dogayen takalmanta....

"Nana H, Sweetheart are you still mad at me? Look I'm sorry, kiyi hak'uri kinji... Ina sonku both you and your Sister and bazan bari inaji ina gani na bari wani abu ya cutar daku ba, idan har na bari hakan ta kasance toh kuwa ina mai tabbatar maki bazan tab'a yafewa kaina ba.... I'll never ever stop being over protective... Sabida a idanuna har gobe ku yara ne, yaranda nake d'auka a kafad'una, sannan dukda banida cikakken hankali da girma sanda mahaifanku suka rasu bazaisa nace kud'in ba amana bace a hannuna.... I love both so much... Like my own..."

Tunda ya soma magana take dubansa da idanunta da suka kuma yin rau-rau, lokaci guda ta k'arasa cikin sauri had'i da rungumesa ta shiga rera kuka....

Lallashinta Siraj yake yana bata hak'uri, Nana H taci gaba da fad'in

"Uncle please kar kayiwa kowa irin soyayyar da kake min cikin zuciyarka, Uncle please don't ever stop loving me... Kaji Uncle, wllhi idan ka daina sona mutuwa zanyi...."

Dafe da bayanta Siraj yake fad'in "That will never happen, never ever Sweedy... You are my Favorite Niece, and you'll always hold that special place in my heart...." Ya k'arashe yanai mata nuni da k'irjinsa murmushi kwance saman fuskar sa.....

Murmushin itama take dad'i ya mamaye zuciyarta...

Siraj na murmushi yana kuma calming d'inta yake fad'in "Let's have lunch outside... I'll just get changed OK..." Ya k'arashe yana fad'ad'a murmushinsa...

"Oh really Uncle... Oh you the best.... I love you...." Ta fad'i tana tsalle had'i da rungumesa...

"Anything for my precious.. Mu jira Nana A ta dawo sai mu fita gaba d'aya koh... Ko ya kika gani....?"

Nan da nan tayi kicin-kicin da fuska baki a ture take fad'in "Uncle nidai just the two of us ya isa besides bamusan yaushe zata dawo ba, and I'm starving already...."

"Alright fine, barin canza I'll be down in a bit...."

Cikeda murna ta masa rakiya har k'ofan d'akinta kafin ta dawo da baya had'i da lumshe idanu.... "Uncle Siraj is the most kindhearted person I've ever known...." Ta fad'i idanu a lumshe, sauri-sauri itama ta canza shigar nata zuwa wani silk material d'inkin doguwar riga wanda ya kwanta a jikinta sosai kana iya ganin suran jikinta yanda ya bayyana tamkar ba d'iyar musulmi ba... Kaico Allah ka wadatamu da karatun addini.....

***

Tafe suke a mota bayan sun tashi a aikin, donma ta d'an tsaya ta jira Nasaar ya kammala wasu ayyukan a nasa a office d'in, kallonta da wistiyar idnu yayi yaga gaba d'aya hankalinta bai wajen, da alama bata ji dad'in aiki da Siraj ba a ranarta na farko....

D'an gyaran murya yayi kana yace "So how did it go.... Ya kika sami boss d'in naki, mai kirki ko kuwa akasin haka....?" Ya tambaya idanunsa naga kwalta...

D'an fuzar da iska tayi kana tace "Not too bad.... Dama nayi tunanin hakan zata rina faruwa, what matters is that I got employed sannan zanyi amfani da damata na taimakawa d'an uwana ya cika burinsa, it breaks my heart seeing him spending the rest of his life on that wheelchair...." Ta k'arashe had'i da sauk'e nannauyan ajiyan zuciya kafin ta d'ago ta dubi Siraj sosai fuska cikeda damuwa take fad'in "But do you think I'm doing the right thing.. Kanaga ban taimakawa b'arna ba... What if Allah ya tuhumeni, mai zance wa ubangiji na.... Anya banyi kuskuren taimakawa Junaid ya d'auki fansarsa ta hanyar da bata dace ba.... I'm afraid... Wllhi ina tsoron kar abubuwa su zama worse ta dalilina...."

Rage speed yayi had'ida d'an dubanta kafin ya maida idanunsa ga kwalta yana mai ci gaba da fad'in "Zeeza you're not doing anything wrong.... FUSKA UKU sun cutar da Junaid cuta mafi muni a duniyarsa, kuma kaman yanda Junaid ya fad'i a wannan duniya tamu ko kace zakayi shari'a da mai kud'i bazakayi nasara ba, wannan shine hanya mafi sauk'i da zai rama abinda aka masa tunda bazai iya yafewa ba...."

Murya na rawa Azeeza take fad'in "But Barrister meyasa shi bazai zamto daga cikin bayin Allah masu yafiya da hak'uri ba, Allah fah yana son masu afuwa..... Da ace iyayenmu suna raye na tabbata da bazasu goyi bayan wannan fansa da Ya Junaid ke neman d'auka ba.... Barrister pls stop him kaji dan Allah...."
Chapter 26 · 0% Book details