← Book details Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 98

Sashe 20

Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmusawa ta kuma yi tana dubansa kana tace "Really.... Meye had'inka da 'yar uwata don't tell me kaima ta siye zuciyarka da salihancin nata.... Oh'o 'o h Darling I don't get you.... What are you trying to say...?"

Fuskarta ya d'ago suna duban cikin idanun juna yake fad'in "I love your Sister Nana H.... I love her so much, and I'm ready to build my own family with her....."

Dariyan rainin hankali ta fashe dashi kana tace " You're deluding yourself here darling, na lura tun ranar da aka bud'e foundation d'inta kake binta da mayen kallo..." tayi wani murmushi kana taci gaba da fad'in "Nayi mata kwalliya irin nawa shiyasa kake ganinta tamkar ni, nasan idan ka sami chance na kashe mijina zaka kashe shi for us to be together..... Lamid'o you love me... I know you does..." Ta k'arashe tana kuma shafan fuskar sa...

B'anb'areta yayi daga jikinsa kana yaci gaba da fad'in "Look Nana H I know we made alot of mistakes in the past... Na cutar da abokina nabi matarsa sannan na cutar da d'aya abokina nabi niece d'insa da aurenta.... But.... things are different now, dan Allah na rok'ek'i mu mance duk abinda ya faru a baya wllhi I'm serious I love Nana A... I love her so much.....kin fahimta....?" Ya k'arashe yana duban cikin idanunta...

Cikeda mamaki take dubansa kafin ta soma girgiza kai tana fad'in "You gone insane Lamid'o, you're unbelievable.... After all that had happened between us, kana tunanin zan bari ka auri 'yar uwata...? Lallai kayi hauka... Wllhi kayi hauka Lamid'o, wllhi baka isa ka auri wata mace ba alhalin ina raye...."

Kallonta yake yanda take faman huci kafin ya kwashe da dariya yana mai dubanta, lokaci guda ya saita kansa kana ya soma fad'in "Kar kiyi tunanin zan biki da lallama, bari kiji na fad'a maki ni ba Siraj bane sannan ni ba Ahidjo bane.... Tsakanin FUSKA UKU bakisan wa kike so ba, you're so selfish, kin raba Ahidjo da danginsa kin hana Siraj aure sannan kina tunanin ni Lamid'o zaki min abinda kika masu ne....?" Yayi wata murmushi kana yaci gaba da fad'in "Nafi k'arfinki wllhi kuma idan ina numfashi sai na auri Nana A saidai ki mutu randa kika ganta a gidana a d'akina muna shan soyayya and there's absolutely nothing you can do about it darling...."

Murmusawa tayi tana dubansa kana ta janyo necktie d'insa fuskokinsu dab da juna take fad'in "I like to mess with other people, that's my personality.... Allah baka sa'a gaka ga Nana A...." Tana ida fad'in haka ta suri handbag d'inta ta shiga taku tana kwarkwasa ta bar masa gidan....

Kallo ya bita dashi had'ida fuzar da iska, bazai bari Nana H ta hanasa samun farin cikinsa Asma'u ba, he would do everything in his power to stop her.... Da wannan tunanin ya mik'e ya nufi kitchen d'insa don samawa kansa abinci....

***

Kallo tabi Ahidjo dashi sai faman shirya kayansa yake cikin jaka, a hankali ta k'araso ta rungumesa ta baya idanunta sunyi rau-rau

"Sweet da gaske tafiya zakayi, toh yaushe zaka dawo? Kasan bazan iya jure rashinka ba...."

Juyo da ita yayi suna fuskantar juna kafin ya masu masauk'i saman gadon, fuskarta ya d'ago ya shiga share mata hawayenta kana yace "Sweet I promise bazan jima ba, besides tafiyar nan daga office ne badon haka ba da bazan yita ba.... Hafsat ko ina naje always remember that you are here in my heart..." Ya k'arashe yana nuni da k'irjinsa...

A hankali ta furta "I love you my Detective..."

Rungumeta yayi cikin jikinsa had'ida lumshe idanu kafin shima ya furta "I love you too Sweet...."

Shirya kayan da ba'a k'arasa ba suka lula duniyar ma'arauta...

***

Tafe suke cikin foundation d'in suna zazzagawa ko wani fanni suna gani, kama daga fannin masu koyan d'inki da masu koyon had'a takalma da dai sauransu... Nana A ita ke tura Junaid dake saman Kekensa, idan ka gansu sai sun burgeka yanda suke cikin farin ciki... Aunty Larai ta bisu da kallo fuskarta d'auke da murmushi, abotan Nana A da Junaid abin burgewa ne, lokacin sallah nayi zasu bar duk wani aikin dake gabansu su tafi sallah, duk yanda zasu zaga cikin foundation d'in tare suke zuwa, a d'an kwanaki biyun sabo ne sosai ya shiga tsakanin Nana da Junaid...

Dai-dai k'asar wata bishiya ya d'ago yana dubanta fuskarsa d'aukeda murmushi kana yace "Aren't you tired... Ki tsaya mu huta a nan don nasan kin gaji da turani...."

Murmusawa itama tayi kana tace "Kaman kuwa kasan na gaji... Kasan yanayin tafiyar tawa sai a hankali..."

Murmushi Junaid ya kuma yi kana ya isa ya janyo mata kujera suka zauna k'ark'ashin bishiyan, dubanta yayi yana mai gyara zamansa cikin kekensa yake fad'in "Umhum ina saurarenki, kina bani labarinki...."

Nana A ta murmusa "Haka ne ina baka labarina.. Inama na tsaya...?" Ta d'an murmusa had'ida sadda kai k'asa kana taci gaba da fad'in "Yauwa na tuna... Kana ji ba..."

Jinjina kai kurum yayi yana dubanta babu ko k'yafta idanu sanda taci gaba da fad'in

"Mu Uku Mummyn mu ta haife mu, Ni Nana Asma'u da kuma 'yan uwana guda biyu Nana Khadija da Nana Hafsat... A lokacin da aka haifemu anyi babban buki a family d'inmu, yara uku 'yan mata lokaci guda gashi mahaifiyarmu dama bata tab'a haihuwa ba wannan dalili yasa soyayyarmu yayi tasiri a zukatan kowa cikin danginmu, haka muka taso cikin soyayya tsakanin iyayenmu 'yan uwa da kuma abokan arziki.... A lokacin munada shekara uku mahaifinmu ya tattaremu gaba d'aya family d'insa harda Momyn mu, Daddy kaman yanda Ammah kakarmu ta bamu labari mutum ne da baya so wani driver yake tuk'asa, duk nisan waje haka yake zuwa babu driver dukda cewa a lokacin shi yake running Kampanin Kakan mu marigayi Mas'ud Laushi, Daddy bai ragewa Uncle Siraj komai ba, haka shima Uncle Siraj bai yarda da d'aukan driver ba, su kuma ra'ayinsu kenan.... A wannan tafiyar k'addara ta had'arin mota ya auka mana yanda motar Daddy ta kufce ta fad'a k'asan bridge.... A wannan had'arin motar muka rasa mahaifanmu gaba d'aya...." Hawaye suka zubo mata, lokaci guda Junaid ya mik'a mata handkerchief, ta dubesa had'ida k'ak'aro murmushi kana ta karb'i handkerchief d'in tana furta "Na gode..."

Saida yayiwa iyayenta addu'an samun rahama ta d'an sami nutsuwa kana taci gaba da basa labari...

"Daddy da Momy suka mace a wannan had'arin, muka rasa 'yar uwarmu guda d'aya Nana K wanda ko gawarta ba'a gani ba, hasalima ana tsammanin ruwa ne ya tafi da ita... Ni kuma Nana Asma'u kaji sanadin rasa k'afata guda da nayi... Nana Hafsat ce kawai bata sami ko k'warzani ba a wannan had'arin kaji ikon Allah...." shiru ya d'an biyo baya kafin taci gaba da fad'in "A haka muka taso mu biyu gaban Kakarmu Ammah da kuma Uncle d'inmu Siraj sai kuma Nanny d'inmu Ayiya wacce nake jinta tamkar uwa a gareni... I love her dearly, kaji tak'aitaccen tarihin Nana Asma'u....." Ta k'arashe kwantaccen murmushi saman fuskarta...

*SameenaAleeyou📚*[12/28, 9:38 AM] ‪+234 802 741 0766‬: *FUSKA UKU*🏮

*15*

*©Sameena Aleeyou...✍🏽*

Daga nesa ta hango wasu samari zaune k'asar wata rumfa nan fah Deejoh ta k'ara sauri tana karanto duk addu'an da yazo bakinta, k'ila da tabi maganar Innah da ba haka ba, wayyo Innarta... Ire-iren abubuwan da ta rink'a tunowa kenan. Tsabagen tsoro ji tayi kaman sun mik'e sun nufota

Ai a d'ari Deejoh ta kwab'e takalmanta ta rungumesu a hannu ta shiga falfala gudu da 'yan k'afafunta...

Dai-dai bishiyar dake k'ofar gidan nasu yayi parking motarsa, ya d'aga kai yana kallon yanayin garin lokaci guda yaji murmushi na zuwa fuskarsa, haka kurum wani irin sanyi yaji zuciyarsa na masa, lokaci guda yaji burin sake ganin iyayensa ya k'aru cikin zuciyarsa...

A hankali ya soma tafiya ya nufi zauren mahaifin nasa, cak ya tsaya cikin zauren yana k'arema wajen kallo yana tuna abubuwan da suka faru shekarun baya lokacin yana yaro kafin ya tafi karatu cikin yaran masu hannu da shuni har wani tunani ya gifta kwanyarsa, lokaci guda Ahidjo yaji jikinsa ya masa sanyi sosai, a hankali ya soma d'aga k'afafunsa da niyyar shiga cikin gidan saidai kafin ya sauk'e k'afa guda yaji an banko k'ofar zauren an shigo a guje...

Kira kawai take k'wand'arawa Innah tana fad'in tazo ta ceceta saiji tayi ta fad'a jikin mutum... Gaba d'aya bata fahimci waye ta runguma ba itadai kawai nata tunanin Innah ce, sosai ta k'ank'anemasa tana tsalle tana "Innah ki rufe k'ofar wllhi su Lado ne dasu Muntala, Innah bazan sake maki taurin kunne ba wllhi bazan sake fita ba tareda izininki ba...."

Duk wannan zuban da take bata saki Ahidjo ba wanda ya rasa abin fad'i ga duhu balle yaga wacece wannan yarinya iyakaci dai yayi tunanin k'ila gamo yayi...

Tun daga bayin take jiyo ihun Deejoh tasan za'a rina hakan Deejoh gidan k'awaye ta wuce shiyasa bata dawo ba ga d'an karan tsoro, girgiza kai kurum Innah tayi ta nufi zauren tana fad'in "Wai dama ina kika tsaya ne, Deejoh bakijin magana, ina kike ki k'araso ki sameni yau nida ke ne...."

Gaban Deejoh ya yanke ya fad'i jiyo muryar Innah daga cikin gida, toh waye wannan ta rik'e kodai Baffah ne, amma ai da ya mata magana, wayyo Allahn ta kodai su Lado ne suka biyota suka lab'e a zaurensu... Sai lokacin ta lura wannan ai yama fi Innarta girma, jikinta ya d'auki rawa ta kasa sakinsa sai rawa da jikinta keyi....

Isowar Innah zauren tana kiran Deejoh alamun tana nemanta taga tamkar mutane a tsaye amma basa motsi, toh kodai idanunta ne... K'arasa shigowa zauren tayi tana gyara d'aurin kwalinta takai hannu jikin k'wan wutan ta d'an motsa sa don ya b'aci dama sai an d'an tab'a yake kamawa....

Ai Innah na kunna wutan Deejoh ta d'ago kai tana kallon mutumin data rik'e shima idanunsa k'ur akanta... Wani k'ara ta saki lokaci guda ta shikashi... Shid'inma matsawa gefe yayi a razane yana tunanin gamo yayi da gaske, domin yanda k'wan wutan ya haske fuskarta baka ganin komai sai k'walk'walan idanunta da tsoro ya cikasu ga uwar ja gira saikace muciya aka zana, shi bai tab'a ganin irin kwalliyan ba yayi zaton kwalliyan aljanu ne....
Chapter 20 · 0% Book details