← Book details Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 98

Sashe 48

Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin sauri ta rik'o hannunshi tana share fuskarta suka komo cikin parlorn.... Suna tafe wayar Siraj ta soma ruri cikin sauri ya cire hannunsa daga cikin hannun Nana H ya koma waje yana amsa wayar....

Aiko tana komowa cikin parlorn ta hangi 'yan gidan gaba d'aya sai nan nan da Azeeza suke babu kaman Ammah wacce tuni Azeeza ta shige zuciyarta, Nana A kuwa sai janta da fira take Ayiya na basu dariya, da alama suna jin dad'in firan nasu... Azeeza ko saurarensu kawai take amma hankalinta na wajen su Siraj da Nana H wanda har yanzu bataga shigowarsu ba tinda suka fice.... Itakam ta soma razana kardai Siraj neman niece d'insa yake.... Subhanallah bata fatan hakan ya tab'a kasancewa...

"My Uncle is a wonderful man, ina mai tabbatar maki zai kula dake fiyeda tunaninki..." Nana A ta fad'i murmushi fal saman fuskarta....

Azeeza koh murmushin yak'e tayi ganin duk yanda suka zata Siraj masoyinta ne kana tace "Ah ai....." Isowan Nana H ya katse mata maganan nata..

"Ce maku tayi ita girlfriend d'in Uncle ne.... Well she's his secretary, and according to Uncle hanya ce ta biyo dasu ta nan shiyasa suka tsaya don naje office ban samesa ba shine ya biyo gida ya tadda meyasa nake nemansa bayan ya riski sak'ona..." Ta maido da dubanta ga Azeeza tanai mata murmushin na fiki iya bariki kana tace "Am I right....?"

Murmusawa Azeeza tayi kana tana dubanta saidai kafin ta sami zarafin magana Ayiya ta katseta da fad'in "Sabida ke baki gane abubuwa ba.... Idan na miji na bada kulawa irin haka soyayya ce... D'iyata ki taimake mu ki korar mana aljanar data aure Sirajo kinji, mutum ya girma ya girme har yana neman zama tuzuru...."

Kan Azeeza a k'asa tana kuma janyo mayafi tana rufe fuskarta take murmusawa kana tace "Ayiya bansan gidan nan zai kawoni ba don da ban yarda ba, mu Al'adanmu budurwa bata bin saurayi gidansu kafin aure koda gaisuwa ce sai ta kama dole...."

Ayiya ta kuma murmusawa cikeda jin dad'i don taga irin kallon da Azeeza da Nana H ke watsa wa juna tasan tabbas wannan yarinya ita zata masu maganin Hafsatu kana tace "Kai amma Al'adanku abin burgewa ba kaman irinta wagga gida ba da aka ari Al'adan yahudu aka yafa....."

Tamkar ta k'arasa ta shak'e Azeeza da Ayiya haka take ji, sai hura hanci take tana binsu da mugun kallo, kasa ci gaba da tsayuwa tayi a parlorn cikin tsananin k'una da k'irjinta ke mata ta fice....

Nana A kuwa dad'ine ya kuma cika zuciyarta jin Azeeza budurwar Uncle Siraj ne, tinda maganganun Azeeza hannunka mai sanda ne....

Nana H na fitowa ta hangi Ammah da Siraj suna magana can k'ofar bayan parlorn.... Cikin sauri ta lallab'a ta k'arasa kusan wajen had'i da kasa kunnuwa tana sauraro komai...

Ammah taci gaba da fad'in "amma su waye iyayenta.....?"

Siraj ya d'an murmusa kana yace "Marainiya ce Ammah, bata da kowa a nan sai mijin 'yar uwarta da take zaune da yaransa, ta rasa kowa nata a Maiduguri...."

Cikeda tausayawa Ammah tace "Allah sarki gata yarinya ce sosai... Kuma da alama tanada hankali sosai...."

Siraj ya kuma murmusawa yana jinjina kai kana yace "Azeeza nada hankali sosai Ammah, banso na bayyana abinda ke tsakaninmu ma jama'a tun yanzu kinsan matsalata...."

Jinjina kai Ammah tayi kana tace "Gaskiya ne, kayi gaskiya Siraj, har yanzu mak'aryaci mayaudarin yaron nan bai bayyana ba koh...."

Siraj ya D'angelo shafi kansa kana yace "Wai Lamid'o...."

Ammah ta jinjina kai tace "Who else...."

Siraj ya d'an fuzar da iska kana yace "He hasn't showed up Ammah, but we have no business to do with him anymore, don ko ya dawo bazan barshi yaci gaba da aiki da companyn mu ba.... hakan yafi mana, nasan Lamid'o bazai bayyana kansa nan kusa ba haka yake min ko a school ne muddin ya min laifi toh shi yake d'auke k'afa daga wajena, sannan Alhamdulillah Nana A ta watsar da sha'aninsa bata bari abin ya affecting d'inta sosai ba...."

Ammah ta jinjina kai kana tace "Haka ne Siraj, barin k'arasa ciki mu gaisa sosai da sirkar tawa...."

Siraj ya kuma murmusawa kana yace "Toh Ammah..."

Lokaci guda Ammah ta shige ciki ta k'ofar bayan yayinda Siraj ya nufi sashen sa don canza kayan jikinsa zuwa masu sauk'i... Nana H dake matsan hawaye cikin sauri ta take masa baya....

Yana k'ok'arin zame rigar jikinsa Nana H ta banko k'ofar ta shigo....

Shaye da mamaki ya rik'e rigar a hannu yana dubanta... Cikeda tsananin mamaki yake furta "Ke...! Lafiyarki, wai meke damunki....

Wani kuka ya kuma taso mata jin irin kalaman da a yanzu Uncle ke mata wanda sam a baya baya mata irinsu....

Cikin kuka take fad'in "Uncle did you hear yourself now... Uncle kaji yanda kake min magana, tun kafin ka aureta ta rabamu dakai, and you know what hurts me the most...... You lied to me, kace min ba budurwarka bace and I over heard your conversation with Ammah... Uncle har ka fara b'oyemin abubuwa.....?" Ta k'arashe cikin tsananin muryar kuka...

Zura rigarsa Siraj yayi kafin tako dab da ita, cikin muryar kwantar da hankali ya soma magana...

"Were you eavesdropping again? Ba na hanaki sauraren maganar da babu ruwanki ba.... Well tinda kinji, eh ina son Azeeza, I love her with all my heart like I've never loved anyone before..... Kuma ina fatan ta zamto abokiyar rayuwata..."

Girgiza kai Nana H take cikin rashin yarda da abinda kunnuwarta ke jiyo mata kana tace "Uncle you might put her life in danger.... If you really love her then don't marry her.... Uncle kar ka mance irin iftila'in da suka faru baya.... Uncle do you want that tragedy to repeat itself..." Ta k'arashe tana girgiza kai hawaye naci gaba da zubo mata

Zeenat ne ta fad'o zuciyar Siraj da abinda suka aikata shekaru hud'u baya shida abokansa wanda sam baison tunowa, cikin sauri ya finciko hannun Nana H yana mata wani irin mugun kallo da idanunsa da suka sauya launi yake fad'in "Kar na sake jin magana makamanciyar haka daga bakinki, you have no right to decide for me... Just get out of here, get out of my room...." Ya k'arashe yana fitar da ita daga d'akin da k'arfinsa....

Mamaki ya kuma cika Nana H, da gaske ita Uncle ke treating this way akan mace... macen ma low class irin Azeeza lallai idan batayi da gaske ba tana gab da rasa Uncle Siraj d'inta.... Bata koma cikin gidan ba ta wuce garden zuciyarta naci gaba da mata k'una tana tunanin hanyar da zata b'ullawa lamarin...

Siraj kuwa dafe kansa yayi yana tuno yanda ya tilasta wa Zeenat aurensa yayi amfani da k'arfin dukiyarsa da ikonsa ya tilastawa mahaifin Zeenat aura masa Zeenat.... Zeenat bata sonshi haka ya aureta.... Amma babu shakka saurayin da take so shi yayi ajalinta tinda shi suka tadda da ita, shi kuma saurayin sun kashe sa ba tareda bincike ba wannan dalili bazai tab'a barin Siraj ya huta ba idan ya tuna ran saurayin Zeenat da suka d'auka shida abokansa... But what if shi saurayin shine ya kashe Zeenat...? Take b'angare na zuciyarsa ta basa amsa da baku da laifi fansan ran matarka ka d'auka.... A hankali ya fuzar da iska kafin ya shirya cikin k'anan kaya ya nufi sashen Ammah yanda ya samu gaba d'aya sun saka Azeeza a tsakiya kowa na nan nan da ita, da alama itama tana jin dad'insu ta d'an saki jiki dasu... Murmushi Siraj ya saki soyayyar Azeeza na ratsa b'argo da tsokarsa...

Jikinta ne ya bata Siraj yana bakin k'ofa aiko tana d'ago kai ta hangesa cikin shigar da bata tab'a ganinsa dashi ba, k'ananun kaya kyakkyawan murmushi saman kyakkyawan fuskarsa, kullum cikin suit take ganinsa yau da ya saka k'anun kaya sai ya mata kyau sosai k'uruciyarsa ta fito ba kaman yanda suit yake maidasa babban mutum responsible ba....

Waving ya mata had'i da kashe mata idanu.... Sam bata kulada Nana A dake faman zuba gefenta ba....

Sai sannan Nana A takai dubanta ga k'ofa nan taga Uncle Siraj tsaye yana sakarwa Azeeza murmushi, murmusawa Nana A tayi salon soyayyarsu na burgeta....

Sallama yayi ya shigo parlorn Ayiya na faman masa tsiya ya wani shasshanyewa...

Wajajen biyar Siraj ya umarci Azeeza da ta tashi ya kaita gida, Nana A kam bata ma so tafiyar Azeeza ba don wani k'awancene ke shirin shiga tsakaninsu.... Ammah kuwa shopping bag babba ta sakawa Azeeza atampa super da leshi mai kyaun gaske had'ida turare Arab oud mai kyau da tsada... Sam Azeeza tak'i amsa saida Siraj ya amsa yace zai bata a mota.. Dole tayiwa Ammah godiya kafin ta masu sallama suka fice...

Har bakin k'ofa Nana A da Ayiya suka raka Azeeza, Ayiya bata daina yiwa Siraj tsiya ba tana fad'in "Haka mijin naki yake kaman mai juju shi kad'ai yayita b'ata rai... Allah yaso ke ba irinsa bane...."

Murmushi kawai Azeeza keyi yayinda Siraj ke raka Ayiya da mugun kallo, matar sosai ta tak'urawa rayuwarsa, shi baiso ma ta sake da Azeeza...

Nana H daga yanda take zaune ta hangesu, lokaci guda taji kuka na kuma zuwa mata... Take ta soma baiwa kanta k'arfin gwiwa.. "You're strong and tough Nana H....." Bata kai aya ba kukan ya kuma zuwa mata ganin Siraj da kansa ya bud'ewa Azeeza k'ofa... Lokaci guda taci gaba da fad'in "But is okay to cry when you hurt... Azeeza you'll be next, I promise..." Tana ida fad'in haka tasa kai ta wuce cikin gida had'ida fad'awa d'akinta ta kulle gaba d'aya.....

***

"So yaya kikaga in-laws d'in naki...." Ya fad'i sanda yake sharan kwana

D'an kallonsa tayi had'i da kauda kanta ga duban window kana tace "Your are so kind.... Guda d'aya ce dai bata yo halinsu ba I guess halinka tayi, don itama ta iya wulak'anta mutane, and is like jealous of you...."

D'an dubanta yayi gajeren murmushi saman fuskarsa had'ida girgiza kai kana ya maida dubansa ga kwalta yace "Hey am I that tyrant... C'mon don't be rude...."

Tab'e baki ta kuma yi ba tareda tace komai ba...
Chapter 48 · 0% Book details