Sashe 67
Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gyara zama Baba Malam yayi kana ya soma fad'in "Wato a lokacin da Hafizu ya tsinceka gefe dakai kad'an ya tsinci wani kati wanda kuke ce masa ID card, toh wannan kati ta k'one sosai rubutun jiki gaba d'aya sun shafe sai harafi uku ne basu shafe ba, wad'annan haruffa uku kuwa sune ALI, sanda muka tambayeka sunanka kace baka sani ba sai muka yanke shawarin mu kiraka da wad'annan haruffa ukun.... Kaji yanda ka samo sunan Ali..."
Jinjina kai Ali yayi had'i da d'an murmusawa kana yace "Baba banida abinda zan biyaku dashi sai addu'a, ubangiji ya biyaku da mafificin alkhairi..."
Baba Malam ya d'an murmusa kana yace "Babu godiya d'ana, koda ace mun sami asalinka gaba har kullum zaka kasance d'a a wajen mu Yaya ga Hafizu...."
Ali ya murmusa cikeda jin dad'i dai-dai lokacin da Mama Azumi tayi sallama hannunta rik'eda abinci tana tambaya ko Baba Ali ya tashi...."
Murmushi ya cika fuskokinsu sanda ta ida shigowa d'akin, Baba Malam na mata sannu yayinda Baba Ali ya soma gaisheta yana fad'in "Mama nidai kina shagwab'ani da yawa bacin haka abincin nan d'azu fah kika bani naci...."
Murmushin itama take tana mai zuba abincin cikin plate take fad'in "Yo ba dole na shagwab'a ka ba tinda fatana kenan ka sami lafiya sosai ka soma takawa... Maza cinye wannan tass had'i b'argo na maka domin ya k'ara maka k'arfin k'ashi....." Ta ida maganar tana tura masa plate d'in abincin gaban sa....
Cikeda jin dad'i Ali ya d'au abincin ya soma ci yayinda suka ci gaba da fira gaba d'ayansu Kai kace d'ansu ne da suka tsuguna suka haifa....
Sallaman Hafiz ne ya katse masu firan tasu...
"A'a Malam Hafizu an dawo kenan....."
Baba Malam yace sanda yakai dubansa ga Hafizun dake k'ok'arin shigowa bayan sun amsa masa sallaman sa....
"Eh Baba na dawo yaya na sameku....." Cewar Hafiz dake k'ak'arin zama daga can gefen Ali....
"Lafiya lou Hadizu yaya Ummar taka da sauran d'aliban naka..."
Murmushi saman fuskar Hafiz yake fad'in "Lafiya lou suke Baba, aiki ne ma ya masu yawa can masana'artan tasu shiyasa basu samu sunzo sun gaida Yaya Ali ba kasan ranar sunzo su amma yayi dai-dai da ranar komawa asibiti basu taddasa gida ba, amma zuwa gobe ko jibi idan aiki ya ja baya zasuzo insha Allah...." Ya k'arashe yana mai maida dubansa ga b'angaren mahaifiyarsa had'ida gaidata... Amsa masa tayi yayinda Baba Malam yaci gaba da fad'in "Allah sarki, ai babu komai, komai sai Allah ya nufa.." Mik'ewa Baba Malam d'in yayi yana fad'in "Barin k'arasa daga ciki, Azumi idan kin gama da yaran naki a kawo min nawa abincin...."
Mama ta amsa masa tana mai k'ara abincin plate d'in Ali sabida Hafiz yace tare zasuci shida yayansa Ali....
Cin abincin kurum suke amma hankalin Ali naga budurwan nan data sadaukar da rayuwarta ta basa jininta, gashi ranar da suka zo basu samesa ba, fatansa ya sami lafiya sosai ya taka yajesa har yanda take ya mata godiyan babbar kyautar data masa wanda sam bashida abinda zai biyata duniyar nan sai addu'an alkhairi....
Hafiz yana hankalce dashi yanda ya k'urama waje guda idanu kana ya d'an muskuta bayan ya had'iyi abincin da ya kai bakinsa yace "Yaya Ali ka kwantar da hankalinka insha Allah tunaninka zai dawo kuma zaka san ko kai wanene tinda Likita yace idan had'ari makamancin abinda ya sameka ya kuma samunka akwai yuwuwar tunaninka ya dawo..."
D'an murmusawa Ali yayi kana yace "Kayya Hafiz da ace kasan yanda nakeji a kwanyata da bakiyi tunanin zan iya tuna wani abu nan gaba ba.. Hafiz ji nake bansan kowa ba sai ku, duk iya runtse idanuna da nakeyi wani sa'in har na kasa bacci duk domin na tuna wani abu gameda rayuwata a baya sam banayi saidaima ciwon kai mai tsanani da yake haifar min, shiyasa na yanke ma kaina cewa kune nawa a halin yanzu ni kuma tawa k'addarar kenan rayuwa biyu zanyi a wannan duniyar, a baya bansan koni waye bane amma a halin yanzu sunana Ali Yayan Hafizu kuma d'a ga Mama da Baba Malam, kasan tunanin da nake...?"
Hafiz ya girgiza kai alamun a'a. Ali ya kuma mik'e k'afafunsa kana yace "Wannan budurwar da kace ta bani jini nake so na ganta itama nai mata godiya domin gaba d'ayanku kunyi tarayya wajen ceto rayuwata, Allah biyaku da mafificin alkhairi...."
Murmushi Hafiz yayi domin an ambato masoyiyarsa Mairo dukda cewa batasan yana yi ba kana yace "Allah sarki Mairo kenan,... Ai Mairo ta wuce duk yanda kake tunani wajen kirki sannan da fari tak'i aminta a sanar dakai cewa ita ta baka jini saidai tak'urani da kayi yasa na sanar dakai..."
"Mairo...!" Ali ya maimaita a hankali kafin ya saki murmushi yana mai kallon wani gefen, baisan mai yaji gameda sunan ba amma haka kurum yaji kaman yanaso ya tuna wani abin, jin kansa na neman sarawa ya sanyasa kawar da tunanin daga cikin kwanyarsa... Muryar Hafiz ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya tafi...
"Yaya idan ka gama cin abincin sai mu d'aura karatunmu, yanzu na tabbata bakada matsala a fannin tsarki alwala da kuma sallah...."
Cikeda jin dad'i Ali ya jinjina kai kana yace "Alhamdulillah na ganesu gaba d'aya dama yau kace zaka d'aura min kan Azkar na shiga ban d'aki da sauransu...."
Hafiz ya jinjina kai kana yace "Allah Yaya kwanyarka tana saurin kama abu ga dukkan alamu kaid'in mai ilimi ne a baya, insha Allah kafin ka bar gaban Baba Malam sai Ka zamto babban Malami...."
D'an dubansa Ali yayi kana yace "Hafiz babu yanda zanje Baba Malam shine Baba na, nan shine gidanmu..."
Hafiz ya murmusa kana yace "Haka ne Yaya na amma bazanso ka tabbata a haka ba, ina fatan watarana zaka san kanka domin bamusan mai ka bari a baya ba....."
Shiru yayi baice komai ba yana jinjina maganganun Hafiz d'in cikin zuciyarsa....
***
*Suleja*
Zaune take saman Tabarma misalin k'arfe 7:30am tana faman had'a bead d'inta sana'ar da suka tashi bisa itada k'awarta Mairo, ita kad'ai sai murmushi take tana tuna wasu memories da suka sharing tare, ciki harda saita Malam Balarabe shugaban sa'idinawa kaman yanda suka rad'a masa, fad'a da 'yan hizba da dai sauransu, kai wato police stations na garin saida suka saba dasu sabida tsananin kawo k'arasu da ake... A hankali ta furta "Oh Mairo ina zan ganki, Allah sa kema kina tunanina kaman yanda nakeyin naki...." Ta k'arashe tana mai saita bead necklace d'in a wuyarta dai-dai sanda Ma'ajura tayi sallama hannunta d'auke da k'aramar jaka da kuma 'yar cooler....
Cikeda fari'a Zaliha ta amsa mata tana fad'in "Kece da sanyin safiyar nan, hallo bashi kika bina ko....?"
Dariya Ma'jura ta d'anyi kana tace "Wllhi shiyasa nake son kasancewa dake all the time kiyita min hausar nan taki dad'i taka min...."
Zaliha ta d'an dara kana tace "Yo gashi kuwa kin d'au hanyar koyo, wai ina zaki da safiyar nan....?"
"Wllhi aiki zan tafi, ina koyar da d'inki wani foundation na musakai haka, toh sun d'aukeni haya suna biyata duk wata ni kuma ina koyar da wasu daga cikin musakan masu buk'atar koyon sana'ar d'inki. Ina Umma ko ita ke kitchen.....?" Ta k'arashe sanda idanunta suka sauk'a saman wuyar Zaliha yanda sark'ar bead d'inta ya zauna yayi d'amar a wuyarta...
"Gaskiyarki kam yafi maki zaman kurum...." Zaliha tace sanda take k'ok'arin mik'ewa tsaye...
Ma'ajura ce ta d'an dafata tana rik'o sark'ar take fad'in "Ke ina kika sayi sark'ar nan tai kyau sosai, kodai Shehu master ne ya kawo don ko yanzu ma da zan wuce bakin kantinsa saida na gansa yana k'ok'arin bud'ewa yace min ina sabuwar k'awata nace yanzu haka ma gidansu na nufa..."
Zaliha ta shafa sark'a tana d'an dariya maras sauti kana tace " Wani Shehu Master ni Zaliha'u rufa min asiri don Allah da samarukan zamani basuda tabbas, ni na had'a kayata...."
Ma'ajura ta kuma dubanta cikin rashin yarda kana tace "Ke haba....?"
Zaliha bata daina dariyar ba tace "Au baki yarda ba koh, toh idan kina so sai na had'a maki sana'ata kenan...."
Ma'jura ta shiga santin sark'ar sosai tana fad'in tai kyau....
"Ki kawo kayan buk'ata kawai na had'a maki, don yanzu ma banida kayayyakin ne wasu na baro su can Tambuwal da na had'a maki...."
Ma'jura taci gaba da juya sark'ar tana mamaki kana tace "Toh idan har kin iya irin wannan mai zai hana na fad'iwa madam d'inmu ta foundation na tabbata zata d'aukeki don irin wad'annan abubuwan ake son koyawa musakai su sami abin dogaro..."
D'an jim Zaliha tayi kana tace "Tab kikace fah har cikin Abuja wannan nisa har ina, ai kud'in ma a abin hawa zai k'are kuma bayan haka sai Abbah ya barni koh..."
Ma'ajura ta jinjina kai kana tace "Wllhi salary mai kyau ake biyanmu ke mai degree ma ya sami wannan aikin namu tuni zaiyi wllhi ni sonki da alkhairi nake kinga sai mu dinga tafiya tare Yaya Safiyanu yana rage mana hanya tinda kabo kabo yake cikin garin Abujan... Amma ki sanarwa Umma kiji ta bakinta ni kuma zan baki kud'i ki sai kayan aikin kiyi kaman guda uku haka sai na kaiwa Aunty ta gani na tabbata zata yaba kuma zatace a kawo ki.. Ko yaya kika gani...."
Nan ma d'an jim Zaliha tayi kana tace "Toh shikenan yanda mukayi da Umma na sanar dake.... Ki tsaya kici k'osai mana...."
D'an girgiza kai tayi tana duban agogon hannunta kana tace "Kiyi hak'uri wllhi na makara kar Yaya Safiyanu ya tafi ya barni ki gaida Umma idan na dawo zan shigo insha Allah...." Ta k'arashe tana mai ficewa cikin sauri...
Kallo Zaliha ta bita dashi har ta fice, tana jinjina kirkin mak'otan nasu gidansu Ma'ajura domin a ranar da suka dawo garin Suleja Mamansu Ma'ajura ita ta basu abincin dare don isowar magariba sukayi, a gaskiya su Ma'ajura sunada mutunci da sanin darajar d'an Adam a haka Umma ta fito ta taddata tana tambayarta ba muryar Ma'jura ta jiyo ba...
"Eh itace Umma ta wuce aiki tana sauri kada ta makara tace a gaidaki idan ta dawo zata shigo...."
"Kai haba Zaliha shine baki d'ibar mata abincin ba taci, ga k'osai na kwashe kwaskon farko..." Umma tace tana mai d'an fad'awa Zalihan...
"Laa Umma wllhi sauri ne take shiyasa fah..."