Sashe 45
Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
D'an d'ago idanu tayi tana dubansa kana tace "Ina ne ribs. ...?"
Kamo hannunta yayi ya manna k'asan k'irjinsa kana yace "Daga nan d'ina aka cireki Dee sabida ke Matata ce..."
Idanuwansu suka had'e waje guda, su duka kallon juna suke, kaman wacce ta tuna wani abu sai juyar da fuskarta tayi....
Murya can k'asa tace "Amma baka sona ai...."
Mamaki maganan nata ya basa yanda ta fad'i har cikin ranta, shi bai mata kallon tama san meye soyayya sabida k'arancin shekarunta...
Juyo da fuskarta ya kuma yi kana yace "Inji wa waye ya fad'a maki haka....?"
"Ba najika kana ce ma Baffah koda baka sona ba.... Kenan wancan matar taka 'yar gayu kake so...." Ta k'arashe baki a ture
Dariya taso basa amma ya d'an gimtse kana yace "Wato bakida daina lab'ewa kina sauraren maganan da ba'a aike ki ba koh? Ba na hanaki ba....." Ya k'arashe fuska babu walwala
Girgiza masa kai tayi had'ida sadda idanunta k'asa kana tace "Kayi hak'uri bazan sake ba...."
Wani irin dad'i ya mamaye masa zuciya, tunda yake baisan mace ta baiwa miji hak'uri don nashi matar batasan wannan ba a rayuwarta.... Murmusawa ya kumayi yana mai ci gaba da duban fuskarta.... A hankali ya gyara masu kwanciyar yana ayyana abubuwa da dama cikin zuciyarsa....
***
Kwance take saman k'irjinsa tana shafa fuskarsa lokaci guda tanai masa wasu salo masu rikita wanda ake masa.... Hannu yasa yana shafa fuskarta kana yace "Mai kike so ayi....."
Murmusawa ta kumayi lokaci guda take yawo da 'yan yastunta saman fuskarsa kana tace "K'anwar matarka ce, kuma k'ark'ashinka take zaune, sannan ina hango soyayyarka cikin idanunta, so abinda nake so kaima zaka so, nasan you want her for yourself ni kuma I want her out of my Uncle's life.... Bana sonta kusan Uncle Siraj ko kad'an...."
A hankali Nasaar ya jinjina kai kana yace "You're right.... I love her so much, kuma bazan tab'a barinta ma kowa ba is a promise...."
Nana H ta kuma murmusawa had'i da gyara kwanciyarta sosai kana tace "Toh ka gani, so kaga I'm quite sure nida kai will make a great team..." ta tak'arashe tana kai masa sunba....
***
Yana fitowa daga sashen Innah bayan ya lallab'a Deejoh tayi bacci don saida ya bata paracetamol sabida d'an zafi da jikinta yayi...
Wayarsa ya ciro ya shiga neman layin Sabi'u bugu biyu Sabi'u ya d'aga...
"DT barka da dare..?" Cewar Sabi'u daga d'aya b'angaren
"Barka Sabi'u, ya aiki...."
"Mungode Allah, DT ya gida ya Family....?"
Ahidjo ya amsa da "Alhamdulillah mun gode Allah..... Inaga nima zuwa gobe ko jibi zan shigo Abuja akwai wani aiki da nake dashi...."
Sabi'u ya gyara tsayuwarsa kana yace "Toh, aiki kuma....? Harda kaine cikin wad'anda AIG zai tura Rivers, I thought hutunka bai k'are ba...."
Shafa kansa Ahidjo ya d'anyi kana yace "No, ina so dama muyi magana dakai amma ba'a waya ba sai na dawo.... Insha Allah gobe ko jibin dai zan shigo....."
Jinjina kai Sabi'u yayi kaman Ahidjo na kallonsa kana yace "Shikenan DT sai na jika...." Daga haka sallama sukayi da Ahidjo ya k'arasa sashensa yana neman layin matarsa Nana H.....
***
*Damaturu*
Gari na wayewa suka soma shirye-shiryen tafiya aiki, Daddah ta kad'a kai a karo na biyu sabida jiya akan idanunta Dakure ke rungume wasu maza, ta lura Hajiya Yagana tana fita Dakura ke maida wajen dandalin hira da samaruka marassa kamun kai gashi babu wanda ya isa ya mata magana sabida ta lura kowa tsoronta yake a cikin shagon....
Cikin zuciyarta take addu'an Allah sa ta tadda wani abu ba daidai ba a shagon..... Da wannan tunani su Mairo da Umma Marie suka k'araso suka isketa kafin suka d'auki hanyar masana'antar tasu.....
Dakura kuwa sauk'arta kenan daga babur ta hangi Soji guda masu tsaron farkon layin yana k'arasowa dama samarukanta ne, wani sa'in idan ta tashi daga shagonsu k'arfe shida wajen Sojojin nan take tsayawa suyita rungume rungume suna abinda ba daidai ba.....
Aiko yana k'arasowa ya soma washe baki yana gyara zanzaronsa ga uwar tumbinsa uwa randar burkutu. Yana tafe yana furta "Dakuura, ka sami isowa.."
D'an yatsina fuska Dakura tayi tana kuma taunar chewing gum had'ida juya idanu.. Lokaci guda take furta "Shi wannan daga zuwata ya wani zo zai soma damuta....." Tana k'ok'arin biyan d'an mashin Sojin ya k'araso da sauri yana zaro kud'i cikin aljihunsa yake fad'in "A'a a'a wannan ai aiki na ne...." Ya k'arashe yana tambayar mai Mashin kud'insa...
Lokaci guda Dakura ta soma murmusawa don ta yanda tafi k'arfi kenan, idonta idon kud'i ne....
"Haba officer ai daka barshi...." ta fad'i tana juya idanu had'ida yin k'araras da chewing gum....
Hannu ya mik'a yana rik'ota yake fad'in "A'a no don't worry, this is nothing.... Yau kunzo da wuri mu k'arasa tent d'inmu before your Madam come...."
Murmushi Dakura tayi kana tace "A'a bazanje tantinku banga su ba...."
Waigawa ya somayi yana dube -dube yake fad'in "Su waye kenan... Are you expecting someone...?"
Dariya tayi irinta 'yan tasha kana tace "Money, kud'i nake nufi...."
Dariya ya kuma yi kana yace "Ahh kudi is not a problem.... Muje..." Ya k'arashe yana kuma kamota
Dai-dai lokacin su Daddah suka sharo kwana..... Mairo da Umma Marie sai labari suke Umma Marie na d'an mata bayanin yanayin unguwar, basu ankare ba sai jin Daddah sukayi tana rangad'a salati tanai masu nuni da Dakura da gardi ya rik'ota... Kasancewar bak'ar riga ce jikinsa bata kaki ba shiyasa Daddah bata fahimci ko waye bane.. A d'ari ta nufesu tana k'ok'arin ciro bulaliyarta da tayi sapiyanta cikin jakanta...
Aiko tana cimmasu ba tareda tace dasu komai ba ta shiga zabga masu bulaliyar nan kace turota akayi....
Daga Umma Marie har Mairo kasa furta koda kalma sukayi sai kallon ikon Allah da suka tsaya yi....
Wandon jikin mutumin da boot d'in k'afarsa kurum Mairo ta hanga ta fahimci Soja ne
*SameenaAleeyou📚**FUSKA UKU*🏮
*33*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
*Gaisuwa tareda Fatan Alheri masoyan Mairo da Daddah sun gode matuk'a😅🤝🏼*
"Tsinannun Allah farar safiya hantsi na kallonku kuna bad'ala ubanku zakuci....." Bata kai aya ba taji an rik'i bulaliyar gam....
Ta d'ago tana huci take duban mutumin wanda idanunsa suka koma tamkar garwashin wuta.... Dakura kuwa sai bala'i take tana tsinewa Daddah tana fad'in "Wllhi yau kashinki ya bushe tsohuwar kawai wllhi kaf danginki sai an kullesu, kuma babu uban da ya isa ya bud'eki...."
"Ke dalla rufe min baki motar haya kurum, kina nan kutittiriya dake uwa gaban gado sai iya shege da iskanci koh, toh wllhi dake da samarukan naki duk idan dai ina nan ubanku zakuci...! Ta k'arashe tana k'ok'arin janye bulaliyarta hannun mutumin.... Karkatowa tayi tana fincikan bulalan take fad'in "Kai kuma ba tsoron pankan pankan nake ba kaji na fad'a maka.. Kaima....." Aya ta saka ma kalaman nata sanda idanunta suka sauk'a k'asa ta hangi wandon kakin dake jikin mutumin wanda ya tsaya mata tamkar gunki, take 'ya'yan hanjin Daddah suka shiga murd'awa... Bakinta ya shiga karkarwa tana girgiza kai lokaci guda ba tareda ta furta komai ba.....
Mairo da Umma Marie da suka koma tamkar ruwa ya shanyesu sai sannan suka nufesu a d'ari.... Umma Marie ta shiga baiwa Dakura dake balbalin bala'i hak'uri yayinda Mairo ta isa ga mutumin tana k'ok'arin janye Daddah take fad'iwa Sojan "Yallab'ai kayi hak'uri bamu jima da dawowa daga jinyar tab'in hankali ba... Dan Allah kayi hak'uri Yallab'ai...."
Banda jinjina kai babu abinda Daddah keyi tana fad'in "Shiyasa ma sam ban lura da wandon jikinka ba Yallab'ai...."
Dakura kuwa sai kuruwa take tana fad'in "Wllhi Oga Bulus k'arya suke maka, tsaban iskanci ne ke damun wannan tsohuwar...."
A duniya Mairo tak'i jinin abinda zai tab'a Daddarta balle a zageta...
Karkatowa sosai tayi tana duban Dakura ta daina bada hak'urin da take kana tace "Idan kika sake zagi min uwa zan watsar zan shirya maki wad'annan wargazazzun hak'waran naki...."
Dakura dake faman tsalle tana ruwan bala'i gata dududu bata wuce kafad'un Mairo ba, tsalle ta kuma dakawa had'i da cire d'ankwalinta ta sha d'amara tana fad'in "Woo wllhi ba'ayi shegiyar da zata zageni ba Dakura nake naci uban kowa na kwana lafiya...." Bata kai aya ba taji sauk'ar bulala a bayanta...
Umma Marie salati kurum take jikinta sai rawa yake sam bata saba da tashin hankali ba... Daddah tana ganin haka don tayi trusting d'iyarta tasan tsaf zata iya da Dakura, ganin sojan nan ya manna waya a kunne Umma Marie na k'ok'arin rabiyar fad'ansu Mairo da Dakura , tasan hankalin kowa baya gareta, a hankali ta soma zame takalmanta cikin sand'a da dabara... Aiko tana kwab'esu ta wawace a guje tana fad'in "Mairo kar kika ragar mata, cimin uwarta da kyau ta yanda gobe idon gardi bazata gani ba...." Tana gudu take wannan maganganun takalma a hannu.... Ai Sojan nan a d'ari yabi bayanta saidai kafin ya cimmata Mairo ta watsar da Dakura cikin kwalbati kace k'ullin kayan wanki aka watsar, cikin sauri Mairo tasha gabansa tanai masa murmushi mai kashesa, lokaci guda ta shiga masa mad'e tana fad'in "Haba my Yallab'ai ba girmanka bane fad'a da mata kana Jarumin Soja..."
Ai Oga Bulus yaga fara kyakkyawa wacce tafi Dakura tanai masa mad'e tuni ya shiga washe baki yana k'are wa Mairo kallo... Mairo ko cikin zuciyarta take addu'an Allah sa kar ya matso kusanta, k'irjinta sai faman bugu yake....
"Yarinya mai kyau....!" Oga Bulus ya fad'i yana kuma washe baki...
Umma Marie kam tuni ta nufi hanyar da taga Daddah ta nufa don sanin halin da take ciki....
Dakura daga cikin kwalbati take faman nishi don ihu mai kyauma ta kasa..... Gashi layin ba mai yawan jama'a bane ya had'u kuma da safiya balle ta samu masu kawo mata d'auki..
Oga Bulus kuwa ganin Mairo ta soma tafiya ya shiga bin bayanta yana kiranta "Yarinya Mai kyau....!"
Suna barin wajen Sojin da ya masu waya suka k'araso da hilux basu tadda kowa wajen ba sai Dakura dake faman nishi cikin kwalbati... Aiko nan suka zaci Dakura Oga Bulus ya turosu su kame.... Nan suka shiga janyota suna k'ok'arin watsa ta bayan Hilux take kururuwa tana fad'in wllhi ba ita bace su tausaya mata... Inaa ko kulata basuyi ba suka watsa ta bayan hilux da alama ko hausar ma basa ji.....