← Book details Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 98

Sashe 8

Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Junaid yaci gaba da fad'in "Siraj....!" Shiru ya d'an biyo baya..... Hannu yasa ya shafe fuskarsa gaba d'aya d'an sauran hawayen duk suka tafi kana yaci gaba da fad'in "Tun lokacin da ya d'aura idanunsa kan Zeenatu ya aukawa soyayyarta.... Bugu d'aya Laushi Group ta amince da had'akar kasuwanci da Datti Investment, nasan zaka iya sanin lokacin tunda kaima kana k'ark'ashin Companyn....?" Ya k'arashe yana duban Barr cikin idanu...

A hankali Barr ya girgiza masa kai kana yace "A lokacin ban fara aiki da Laushi Group ba domin lokacin da na soma aiki dasu lokacin auren Siraj ne....."

Junaid yayi shiru tamkar mai nazari kana ya gyara zamansa saman wheelchair d'insa...

"Baka sanar dani mai ya rabaka da matarka, meyasa kake zaune daga kai sai 'ya'yanka... Shin kaima iftila'i ce ta rayuwa ta auka maka....?"

Shiru Barr yayi yana dubansa kafin ya d'an murmusa ya d'an shafi nape d'insa kana yace "Bai kamata ana bada labari a katse a shiga wani ba idan da mai saurarenmu zai shiga rud'ani...." Ya k'arashe murmushi kwance saman fuskar sa.....

Junaid d'inma murmusawa yayi yana mai karantar Barr kana yaci gaba da fad'in "Kace wani abu.... A ina na tsaya maka ma?"

Tambayar saida yaso baiwa Barr dariya ya kuwa d'an murmusa kana yace "Had'uwar Siraj da Zeenatu..."

Junaid ya murmusa yace "Haka kuwa...." Saida ya kuma saita kansa kana yace "Murmushi ba d'abi'ata bace tun bayan rasa farin ciki na sai gashi yau ka sa sai yinta nake a arha... Da ace Umma Marie da Zeeza zasuga fuskata da murmushi da sai sun maka kyauta....."

Barr ya kuma murmusawa kana yace "Ni fatata ka dawamma cikin murmushi domin sosai take k'arawa fuskarka annuri da kamala...."

Junaid ya shafi k'asunbin sa wanda bai jima da tarawa ba kana yaci gaba da fad'in "Sabo sosai Siraj da Zeenatu sukayi duk a tunaninta sabida kasuwancin da ya had'asu ne sam bata kawo Siraj nada wata nufi na soyayyarta cikin zuciyarsa ba... Wasu lokutan haka kawai zai buk'aci suyi confidential meeting da Zeenat su biyunsu, su fita tare joints parks da sauransu duk akan ana tattauna business ne... A lokacin sai na fara zargin wani abu sam banason keb'ewanta da young tycoon d'in.... Toh sai na fara nuna mata rashin amincewata gashi lokacin Datti Investment ta soma hab'akowa da taimakon Laushi group, a lokacin Zeenat sai ta d'auki abun kishi ne kawai irin nawa, wani sa'in har ta nuna rashin jin dad'inta tunda gashi har mahaifinta na alfahari da ita, you know how business men are... Kasuwancinsu ya fiye masu komai... Ana haka abu ya soma bayyana da gaske dai Siraj soyayyar Zeenatu ne tam cikin zuciyarsa, ni kuma a lokacin sai na soma jin Zeenatu taci amanar soyayyar da nake mata, duk da banso zuciyata ta aminta da zarginta na cin amana amma na kasa... Wasu irin manyan kyauta Siraj yake mata wanda har ita kanta ta soma tsorata da lamarin nasa, koda tazo ta sameni ta sanar dani halin da ake ciki banza na mata, Mahaifiyarta kanta bataso saka Zeenatu da Alhaji Haruna Datti yayi kan hark'ok'in kasuwancinsa ba tinda ita mace ce gashi ita kad'ai Allah ya basu... Shiko Alh Datti ganin kasuwancinsa na hab'aka sai ya mance da komai, sai ya zamana Alh Siraj Laushi bashida wajen hira sai wajen mahaifin Zeenat, wanda shi kansa mahaifin Zeenat gani yake wannan babban nasara ce a gareshi tinda Alh Siraj ya tsallake k'anan Kamfanunuka da dama ya tunk'ari nasa... A haka Siraj ya soma sanar da mahaifin Zeenatu buk'atarsa..." Aya ya d'an saka ya d'ago yana duban Barr kana yaci gaba da fad'in "Kasan meye abin mamakin...?"

Nasaar ya girgiza kai alamun a'a bai sani ba...

Junaid yaci gaba da fad'in "Mahaifin Zeenat ya amince da buk'atan Siraj wanda bani kawai ba harta mahaifiyar Zeenatu da ita kanta Zeenatun saida muka shiga rud'ani.... Ranar wata alhamis Baba Datti ya kirani har parlornsa yake sanar dani _Junaid kayi hak'uri ka amshi soyayyarka da Zeenat a matsayin k'addarar rayuwarka, sannan ka nemo wata yarinyar ko a ina take ni zan tsaya maka a matsayin mahaifi har ka mallaketa, Junaid na riga na amshi kud'in auren 'yar uwarka Zeenatu nanda wani lokaci kad'an za'ayi auren...._ "A lokacin sumewane kawai banyi ba domin duniyar juyamin ta soma yi.. I was like.... Ta yaya Baba zaimin haka, bayan duk mafarkan da mukashayi wajen gina gidanmu da Zeenatu, tare muka girma tare muka gina rayuwarmu da mafarkanmu da komai da komai, bamusan soyayyar kowa ba sai na junanmu, rana d'aya tak ace na rabu da ita... How could that be possible....? Muryata tana rawa nake fad'in Baba lafiya wani abin nayi.. Baba ko baka aminta da tarbiyata bane... Baba dan Allah kar ka rabani da Zeenatu wllhi bansan yaya rayuwata zata kasance ba... Baba please don't do this na rok'eka... Baba ya kalle ni da idanun tausayi kana ya duk'ar da kansa yana girgizawa ya d'ago ya dubeni da k'yar yace _Junaid I'm sorry, ka yafe min d'ana wllhi banida zab'i kasan akan kasuwancina babu abinda bazanyi ba muddin inada halin yi d'in, rayuwata gaba d'aya nayisa ne cikin k'ok'arin gina kasuwanci na.. Kayi hak'uri Junaid kayi hak'uri d'ana..._ A lokacin bansan sanda na mik'e na soma tafiya hanya na hard'e min ba sai ganin Zeenatu nayi gabana cikin shesshek'ar kuka ta rik'eni tana fad'in _Junaid dan Allah kar ka bar Abbah yayi haka... Junaid dan Allah kace ya aura mana juna, please don't let him do this.... Junaid kar ka bari a aura min wanda banaso, ka manta mafarkanamu da burikanmu.... Junaid ka amsa min mai Abbah yace maka....._ Tamkar mutum mutumi haka Zeenat ke jijjigani ina kallon kyawawan idanunta masu zuban ruwa, kasa ganewa nayi zafin kukanta nakeji kokuwa zafin abinda Baba Datti yamin nakeji.... Ban iya ce mata komai ba sai b'anb'are hannayenta da nayi daga jikina... Ina jiyo sautin kukanta yanda na barta a durk'ushe tana rok'ona na dawo amma ban iya juyawaba sabida tsoron kar na zube a wajen nima..." Shiru yayi idanunsa suka kad'a sukayi jazir yayinda idanun Barr ya kawo ruwa sosai wani irin tausayin Junaid yakeji....
Chapter 8 · 0% Book details