← Book details Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 98

Sashe 53

Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ga mamakin Mairo k'walla ta hango idanun Baba Malam, tabbas tana cikin duhu na jahilci ace mace budurwa haka batada ilimin fiqhu toh da meye zata gyara addininta, yaya take wanka, yaya take tsarki, yaya take alwala balle aje maganar sallah, shi bautan Allah sam ba'ayinsa daka, komai da ka gani muddin addini ne toh sai kanada hujjan yinsa ba kawai kai tsaye zakayi ba kace kaga anayi ne... Wllhi wllhi muje mu nemi ilimi, yanda ake bautan kanta kafin ta ta zama karb'ebb'iya, wllhi ubangijinmu zai tambayemu, musamman mu mata masu yin jini na al'ada, mata don Allah mu farga mu fita mu nemi ilimi mu gyara addininmu don wllhi ba'ayin addini daka... Allah ya mana muwafaqa ameen...

Tambayoyi da dama Malam yayiwa Mairo sai ya kula rayuwarta gaba d'aya an ginasa ne wajen dambe da sunan k'watan 'yanci wanda dambe sam ba Al'adan 'ya mace bace, namijin ma ba'a koyar dashi dambe ba balle Mace, ita mace wace halitta ce mai tsananin kima da daraja saidai idan ita ta watsar da darajanta amma 'yar uwa ko yaya kike ki sani Allah ya maki kima da daraja, musulunci ta gama maki komai saidai idan kece kika watsar da kanki toh sai ki nemi wad'an nan kima da daraja naki ki rasa, muyi hattara mata....

Tabbas daga Mairo har mahaifiyarta Daddah sunada buk'atar koyarwa ta addini tun daga littafan fiqhu da tauhidi yanda zasu san Mahaliccinsu su kuma san yaya ake bauta masa, Baba Malam ya yanke shawarin Hafizu ya dinga zuwa har gida yana koyar dasu addini dukda cewa sunsan za'a sha fama sosai da Daddah don har yanzu batasan ina Mairo da Umma Marie ke zuwa ba....

***

Washe gari Nana H ta dawo gida sabida tafiyar da Ahidjo yayi, Siraj d'in kansa baiji dad'in dawowar nata ba, shikam yafi so ta natsu a d'akinta, Ayiya kuwa haka tayita yab'a mata maganganu marassa dad'i wanda sam Nana A batajin dad'in hakan tana matsuk'ar son 'yar uwarta sosai...

Saidai ga tsananin mamakinsu Nana H wannan karan a saliha tazo gidan, don tunda tazo bakaji hayaniyarta ma 'yan aiki ba balle 'yan ahalin gidan...

Haurowa sama tayi bayan sun gama hira da Ammah ta baro Amman tana kallon tashan labaru, tana hango k'ofar d'akin Nana A ta saki murmushi kafin ta soma kwaikwayon yanayin tafiyar Nana A har ta isa k'ofar d'akin.... Tana isa ta soma knocking a hankali, daga yanda Nana A ke zaune saman gado tana waya da sabon chwing gum d'inta Junaid ta bada izinin shigowa a tunaninta ma Ayiya ce...

Ganin Nana H ce ya sanya Nana A sakin murmushi, daga bakin k'ofar murmushin ne kwance saman fuskar Nana H kafin tace "May I... ?"

Jinjina mata kai Nana A tayi kafin tayi saurin yin sallama da Junaid, ta maido da hankalinta ga Nana H tana mai fad'in "Sis shigowa mana..."

Murmusawa Nana H ta kumayi kana tace "Gani nayi kaman 'yar uwar tawa soyayya take na katse mata...."

Nana A ta murmusa cikeda kunya kana tace "Kai Nanatu c'mon, ba soyayya bane, maganar da ya shafi foundation muke...."

K'arasowa take murmushin bai bar saman fuskarta ba had'i da rungume kafad'un Nana A kana tace "I can see it from your eyes Sis, I'm pretty sure you're in love with that guy from the foundation, and you know what wllhi kun dace, he's super handsome although yanada deficiency, amma it doesn't matter idan dai kina sonshi, hankali kwance don nasan bazai tab'a hurting d'inki ba tunda shima yana fama da lalura makamanciyar taki ...." Ta d'an kuma marairaice fuska kafin ta dafa Nana A tace "Sister I really want to see you happy, please give that guy a chance wllhi na hango tsan-tsan soyayyarki a idanunsa sanda naje d'aukoki a foundation, Nana A kar kiyi wasa da damarki bakisan mai rayuwa ta tanadar maki ba, karma kiyi tunanin Lamid'o da abinda ya maki, maza suna suka tara kowa da halinsa, kiga dai yanda muke zaune da Heedj shekara biyu babu yaji balle saki, in fact ba'a tab'a jin kanmu ba sai wanda ba'a rasa ba..." Ta k'arashe murmushi saman fuskarta

Murmushi Nana A keyi tana mai jin dad'in shawarwarin 'yar uwar tata kafin ta rungumeta cikin sauri tana fad'in "Nana H thank you, thank you sister, bansan mai zanyi ba idan babu ke...."

Juya idanu kawai Nana H keyi tana yayyamutsa fuska lokaci guda take bubbuga bayan Nana A kana tace "I love you sister, everything for my only sister...."

Ayiya ce ta shigo tanai magana wa Ammah saidai labarun da ake nunawa ya tafi da hankalin Ammah, k'onenniyar motar Ahidjo aka nuna ana sanarwa an sami motar tasa a k'one k'urumus sannan ba'a sami gangar jikinsa ba, jami'an tsaro sun tabbatar cewa jikin DT Aliyu ta k'one k'urumus cikin motar wanda yasa ba'a samesa ba....

Wani irin k'ara Ammah ta saki a dai-dai lokacin da Siraj yayi sallama parlorn, Nana H da Nana A a gigice suka nufo downstairs... .

*Toh fah masu karatu ga Ahidjo dai anyi ajalinsa, ga Deejoh a gida batasan cewa da takaba akanta ba, shin yaya Deejoh zataji idan wannan labari na rashin mijinta ya risketa, Shin Junaid zai cimma burinsa akan FUSKA UKU, shin yaya rayuwa zata kasancewa Siraj babu abokansa, shin Lamid'o zai kub'uta daga hannun Bulama? Shin auren Siraj da Azeeza mai yuwa ne,? Yaya zata kasance tsakanin Junaid da Nasaar idan yasan cewa ya danne shari'ar Zeenat, Shin Mairo zata dawo gida....?*

*Uwar gayya Nana H😂 one word for her please guys....*

#FU
#SameenaAleeyou
#Nagode

*SameenaAleeyou📚**FUSKA UKU*🏮

*41*

*©Sameena Aleeyou...✍🏽*

*ZBI Zauren kara Zauren mutunci Zauren sharhi fatan alheri gareku gaba d'aya😍🤝🏼*

*Wai haka Heedj keda masoya, yau harda wad'anda bansan suna bin labarin ba sun zuba sharhi kan mutuwar Heedj😂, kar ku damu insha Allah he's in better place.... Na gode da k'aunarku gaba d'aya♥*

Girgiza kai Siraj yake yana kallon abin tamkar almara, no badai Heedj d'insa ba.... He was here,.... Suna tare d'azu'dazun nan... No it can't be him, they must be mistaken, it can't be Heedj... Baisan sanda k'afafuwarsa suka kasa d'aukansa ba yayi wani irin silalewa a wajen zuwa k'asa...

Ammah cikin sauri tana k'ok'arin maida kukanta ta nufi Nana H ta rungumeta sosai yayinda Nana H d'in ke fad'in "Ammah no.... Not my Heedj, Ammah I can't lose him, I already lost a lot of people, Ammah I lost my parents and my Sister, and I.. I just can't lose my husband in such a tragic way like that..... Ammah I just can't...." Ta k'arashe cikin wani irin kuka mai firgitarwa...

Cikin rawar murya Ammah ke sanar da ita tayita karanto innalillahi wa inna'ilaihiraji'un

Dai-dai lokacin Nana A ma ta fasheda wani irin kuka yayinda Ayiya ta k'arasa da sauri ta rungumeta, Allah sarki idan ka gansu dole su baka tausayi....

Zaune kawai Siraj yake dirshan a wajen yana tuno sa'insan da sukayi a safiyar yau, ashe tafiyar kenan, ashe Heedj sallama yazo masa, Innalillahi wa Inna'ilaihi raji'un, meyasa bai saurari Heedj ba da abinda zai fad'a masa, meyasa ya gaggaya masa magana anyhow, meyasa basuyi rabuwa ta dad'i ba.... Meyasa ya rasa abokanansa aminansa.... Why his friends why..... Kuka mai k'arfi wanda Siraj bai tab'a irinta ba a girmansa ita ta kufce masa.....

Kuka yake bilhakk'i da gaskiya yana fad'in "Dan Allah ku fad'a min ba Heedj bane, ni nasan bashine, wllhi kuskure sukayi amma ba Heedj d'insa bane... A guje Nana H ta tafi ta fad'a jikinsa tana wani irin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, sosai Siraj ya rungumeta suna cazgan kuka tare...

Da k'yar Ammah ta iya k'arasawa garesu tana basu baki dukda dai kanaji kasan k'arfin hali kawai take, Allah sarki ta tuna dududu baifi kwana uku da zuwa nan ba har tana masa tsiya asubahin fari daga sauk'arsa ya biyo matarsa sai gashi kwatsam wai yau babu shi tabbas d'an Adam shi ba komai bane idan ya fahimci hakan, yanzu-yanzu ana taredakai anjima mala'ikan mutuwa zai zare ranka, Al'amari na Allah _Kun fayakun_ ne, Sarkin da baida fadawa sai bayi, sarkinda baida mashawarci, sarkin da mulkinsa take dawamemmiya... Allah ka bamu k'arshe mai kyau... Ameen...!

A wannan dare iyalan marigayi Mas'ud Laushi sunga tashin hankali wanda suka jima basuga irinta ba, Siraj dole ya baka tausayi sabida yanda abin yayi affecting d'insa, gashi yayi neman duniya wayan Lamid'o bai shiga, shi kansa yasan a yanzu suna buk'atar juna daga shi har Lamid'o sabida rashin d'anuwansu da sukayi, saidai rashin shigar wayar Lamid'on sosai ya d'aga masa hankali, duk wani layi da yasan zai iya samun Lamid'o ya kira bai samu ba, tunanin maganganun Ahidjo a safiyar ranar ta shiga yawo a kwanyarsa, da gaske kenan Lamid'o kidnapping d'insa akayi.... Wani sabon jiri ya kuma tasowa Siraj da k'yar ya iya k'arasawa sashensa....

Nana H ta tashi zata bi bayansa Ammah ta kamota tana tambayarta ina zata tayi hak'uri...

Girgiza kai Nana H keyi tana mai ci gaba da hawaye take fad'in "Ammah Uncle Siraj needs me, bazan iya jure ganinsa cikin tashin hankali ba....

Baki sake Ayiya ke duban ikon Allah, wai matar da mijinta ya mutu kenan amma tashin hankalin da Siraj ke ciki yafi na mutuwar mijinta, abun sosai ya baiwa Ayiya tsoro ya kuma d'aure mata kai...

Ammah na girgiza kai take fad'in "Nana Hafsat Siraj will be okay kinji koh, ke a yanzu kin shiga takaba maza mu wuce sama ki canza wad'annan tufafi don sunyi kwalliya da yawa sannan ki cire duk wani sark'a da 'yan kunne, ki nutsu waje guda kiyiwa mijinki addu'an dacewa, tabbas mutuwar Ahidjo dole ya tab'aki sosai sabida ganin gawarsa kawai zai iya kwantar maki da hankali saidai muyi hak'uri haka Allah ya k'addara bazamu bisne Ahidjo ba, Allah ya masa rahama ya kuma toni asirin duk wanda keda hannu a mutuwarsa.."

Rungume take da Ammah tana ci gaba da matsan hawaye b'angare na zuciyarta ji take kaman ta shak'e Ammah sabida ta haneta zuwa wajen Uncle, shegen shisshigi ina ruwanta idan ma batayi takaban ba ai mijinta ne, harda wani addu'an Allah tona asiri irin taji dad'in nan.... Ta kumayin tsuka cikin zuciyarta kafin a fili ta kuma fashewa da sabon kuka, da k'yar Ammah ta janyota suka nufi sama....
Chapter 53 · 0% Book details