← Book details Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 98

Sashe 29

Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Daddah idan da sabo na saba da hijira saidai naji mamaki yanda ke kanki kinsan baki adalci wa rayuwata kuma har kina iya fad'in haka... Daddah na sani wani sirrin rufamin da zakiyi zaifimin sama da bayyana min da zakiyi, domin wani abin a barsa a sirrance yafi... Sannan ni Daddah har yau Allah bai had'ani da wanda zan gani nace ya kwanta min ba har wai naji na sami mijin aure.... Abu guda da yafi damuna shine rashin yarda da kanki da kika kasa yi... Daddah idan sabida mahaifina kike hijira gari zuwa gari na rok'i arzikin ki ki barni nayi ido hud'u dashi. Muyi gaba da gaba dashi mu daina wannan wasan b'oyon na rok'eki kimin wannan sadaukarwan dan Allah Daddah....." Ta k'arashe muryarta na tsananin rawa...

Daddah ma tuni idanunta sukayi rau-rau ganin hawaye cikin idanun d'iyarta... A hankali ta janyo Mairo ta rungume tana fad'in "Na kusa sanar dake komai d'iya da izinin Allah... Yanzu tashi mu samu mu isa tasha...."

Mairo ta d'ago kanta daga k'irjin Daddah tana dubanta kana tace "Ina muka nufa yanzu....?"

Daddah na murmushi tace da ita "Gabashin k'asar nan can Jihar Yobe....."

Cikin zafin nama kaman wacce aka takala ta mik'e ta shiga had'a kayanta da na sana'arta... Ta jima tana rik'eda wata sark'ar da Zaliha ta had'a mata tana duba kafin ta saki murmushi ta jefa sark'ar cikin jaka tana mai fad'in "Zanyi kewarki Zaliha...."

***

Tinda ya had'a wayar caji bai kuma bi takanta ba, asubahin fari yaji k'aran waya ya cika masa kunne, nan ya tuna ashe jiya ya d'auko wayar Daddy zaiyi bincike cikinta saidai ya kasa bud'e lock d'in wayar hakan yasa bai kuma bi takan wayar ba, ya bari akan sai zuwa safiya yasan abinyi.... Cikin sauri kaman zai kifa ya isa ga wayar yana kallon lambar da ake kira dashi babu suna... Lokaci guda Lamid'o ya d'aga wayar ya k'ara a kunnensa...

Hankali tashe Nazir da bai jira wata-wata ba ya soma fad'in "Boss wllhi sun tafi an wayi gari ban samesu gidansu ba... Boss Mairo sun bar gari......"

Cikin sauri Lamid'o ya cire wayar daga kunnesa k'irjinsa naci gaba da bugu

A hankali ya furta "Mairo!..."

Dabara ta fad'o masa cikin sauri ya katse kiran ya tura sak'o cewa yana wajen da bazai iya magana ba.... Aiko kan kace mai sak'on Nazir ya shigo...

_Boss there's problem.... wllhi bansan yaya akayi hakan ta kasance ba, kuma bansan ina suka nufa ba, amma yanzu haka tashan motoci na nufa..._

Lamid'o yafi good five minutes yana bin sak'on da kallo kansa na kuma d'aurewa... Toh wacece Mairo... Daddy yankan kai yake ko menene.? Shin kodai Mairo ce silan rasa mahaifiyarsa tinda yasan lokutan baya da wayonsa mahaifinsa na cin zarafin mahaifiyarsa.... He really needs to find out koma wacece.... Lokaci guda ya ajiye wayan ya nufi bathroom donyin alwalan sallan asuba....

*SameenaAleeyou📚*
[1/7, 10:09 PM] ‪+234 803 596 9052‬: *FUSKA UKU*🏮

*21*

*©Sameena Aleeyou...✍🏽*

Sauri-sauri Nazir ya nufi tasha saidai unfortunately ya tarar motar asuba ta bar tasha... Babban abinda yafi damunsa baisan yanda suka nufa ba.... Ya jima yana bulayensa a tashan kafin ya dawo gidan yana kuma dubawa har gari ya soma haske... Lokaci guda ya tuna Zaliha yasan dole Mairo ta masu sallama kuma ta sanar dasu yanda suka nufa...

Cikin sauri Nazir ya nufi gidansu Zaliha yana bugun k'ofa....

***

*Yobe _Damaturu_*

Sauri-sauri ta gama shirin tafiya wajen aikinta, shagon d'inki da wata attajirar mata ta bud'e a unguwar domin taimakawa mata marassa sana'a.... Tana d'aga jakan nata hotonsu ya fad'o daga ciki, tsohon hoto da suka d'auka lokacin Junaid na asibiti.... Murmushi kwance saman fuskarta take shafa hoton fuskar Junaid da Azeeza... A hankali ta furta "I miss you my children...." Lokaci guda ta ciro wayarta ta shiga dialing layin Junaid....

Bugu biyu Junaid ya d'aga kiran da murnansa

"Umma Marie... I miss you sweetheart...!" Ya k'arashe dariyan farin ciki saman fuskar sa...

"Nayi kewarku nima Junaid... Ya kuke ya al'amra suke wakana... I hope kuna cikin k'oshin lafiya....? I worried so much about you..." Ta k'arashe cikin rawar murya

Murmushi ya kuma yi kana yace "You don't have worry... Muna nan lafiya... And everything is going well just like the way I planned.... Umma nayi kewarki..... Please don't cry kinji...."

Murmushi Umma Marie take tana goge hawayen da suka zubo mata kana tace "Ina Azeeza...?"

"Ta tafi aiki, bata jima da ficewa ba...."

D'an jim tayi kana tace "Junaid kardai amfani kake da k'anwarka domin d'aukar fansar ka... Junaid... Anya anya kuwa Junaid... Na fara tsoron Fansar nan taka kada reshe ta juye da mujiya, Junaid dan Allah ka bar komai wa Allah ka dawo...."

Junaid na huci sabida duk sanda aka masa maganar d'aya daga cikin Fuskoki ukun nan sai yaji ya tsani komai a duniyarsa face burin d'aukan Fansa.....

Murya a dashe yake fad'in "Umma Marie Shari'a ma ta aminta da idan an zalunceka ka rama matuk'a bazaka iya yafewa gwargwadon zaluncin da aka maka amma kuma yin afuwan yafi alkhairi.... Umma wllhi wllhi bazan barsu ba har sai na cika burina... Kawai ki ci gaba da min addu'a... Kici gaba da mana addu'a daga ni har Azeeza...."

Shiru ya d'an ratsa tsakani kafin ta jinjina kai tace " Amma kuma shari'a bata amince maka ka d'auki doka a hannunka ba Junaid, shin baka tunanin tarin had'arin dake cikin yin hakan... Sannan zaka iya zaluntar wanda baiji ba bai gani ba duk a dalilin fansar ka... Junaid....."

Katseta yayi da fad'in "Umma must we have to talk about this again.... I'm not backing down... Not until I destroyed them all....!" Cikin tsananin huci yake maganar..

Dan sauk'e ajiyan zuciya tayi kana tace
"Shikenan Junaid tunda dai hakan ka zab'a amma ka sani duk abinda zakayi ka ringa tuna mahalliccinka har kullum wasilcina a gareka kenan..... Ka gaida min Azeeza idan ta dawo ka kulamin da kanku.. I love you both...."

Junaid ya saki murmushi har cikin ransa yake jin k'aunar Umma Marie kana yace "Insha Allah Ummah... We love you too... Sai mun sake magana..."

Suna ida wayan ta zura hijab d'inta ta d'ibi kayan aikinta tayi ficewarta wajen sana'arta...

***

*Abuja*

Tun daga gate yake jiyo sautin dirin mahaifinsa cikin tsananin fad'a ya tara ma'aikatan gidan gaba d'aya...

"Wani sabon iskanci kuka d'auko... Ta yaya za'ace kamata a gidan nan na ajiye abu na nema na rasa.. Waye ma suka gyara parlorn jiya...? Wllhi wllhi kunji na ratse rasa wayar nan na dai-dai da rasa rayuwanku... Idanma akwai d'an lek'en asiri cikin ku ne zan gama daku gaba d'ayanku in seconds.... Ku b'ace a gani dolaye kawai... Awa d'aya tak na baku ku nemo wayar nan yanda ta shiga ta fita idanma a shara kuka saka. .." Cikin sauri ya soma tattara zurmemen jallabiyarsa ya nufi d'aki yana dogara sandarsa...

Yana shigewa Lamido ya shigo parlorn.... Nan da nan ma'aikatan suka soma gaidasa... Saida ya tabbata hakulansu baya wajen kana yayi saurin jefa wayar tsakankanin kujeru... Lokaci guda yake tambayarsu mahaifin nasa nan suke sanar dashi ya shige d'aki... Parlorn k'asa ya dawo ya zauna gami da had'e hannayensa waje guda yana tunanin ta yanda zai b'ulla wa lamarin.....

Wani ma'aikaci guda ne ya k'araso yana tambayar Lamid'o mai za'a kawo masa...

Girgiza kai kurum Lamid'o yayi yana murmushi kana yace "Babu komai Ayuba ci gaba da aikin ka. ."

Ayuba ya risina had'i da amsawa kafin yayi wucewarsa... Dokan gidan Alh Bulama ne mata basa masa aiki tun bayan rasuwar matarsa mahaifiya ga Lamid'o....

***

Ammah na hankalce dashi yanda yake cakalan abinci tamkar baya so, kai da ganinsa kasan wani abu na damunsa.... Ajiye spoon d'in hannunta tayi tana mai ci gaba da karantarsa lokaci guda ta d'anyi gyaran murya kana tace

"Babana wai lafiya, meke damunka?... "

Siraj ya d'an fuzar da iska had'ida shafe goshi kana yace "I'm fine Ammah.. Mai kika gani....?"

"Gaba d'aya gani nayi yau d'in kaman bakai ba, tun d'azu tunani kake ka kasa cin komai sannan yau kayi lattin tafiya office ba kaman kullum ba.... Akwai abinda ke damunka ne.... Share it with me please... Baka da wacce ta fini....."

Siraj ya d'an kuma gyara zamansa cikin kujeran kana yace "Ammah is somehow complicated.... I just don't know... Bansan ta yaya zan soma maki bayani ba but all I can say is that....." Fsali ya d'an ja had'i da fuzar da iska..

Ammah ta bisa da kallo damuwa fal fuskarta...

"Umhum ina jinka Sirajo meke faruwa....?"

"Ammah wata yarinya ce take yunk'urin shiga rayuwata.... Nayi k'ok'arin na mata mugunta ko kuma duk wani wulak'anci don kawai taji bazata iya hak'uri dani ba amma yin hakan da nayi sai naga kaman k'aimi ya k'ara mata wajen matsowa kusa dani... Ammah you know me... You know my problem.... Banso wata rai ta kuma salwanta a dalilina..... And you know the worse part of it is that I can't avoid her... Dole kullum na kasance tareda ita.... Ammah I'm afraid...." Ya k'arashe idanunsa saman plate d'in pancakes d'insa.....

A hankali Ammah ta mik'a hannunta ta rik'o na Siraj tausayinta na ratsa b'argo da tsokarta kana tace "Sirajo a koda yaushe ka tuna kanada family d'inka and we all love you so much...."

Kasa furta komai Siraj yayi sai kallon Ammah da yake yi wasu irin ruwa na neman ciko idanunsa....

Cikin rawar murya ya soma fad'in "Ammah your love is simply enough for me.... But Ammah I'm also human and I've feelings... and......" Kasa ci gaba da magana yayi sabida wani irin nauyin mahaifiyar tasa da yaji...
Chapter 29 · 0% Book details