← Book details Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 98

Sashe 33

Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nana A tayi murmushin jin dad'i kana tace "Ayiya dole ki sosa idan kin gansa, yanada zuciya mai kyau.."

"Allah sarki Allah saka masa da alkhairi kula min da d'iyata da yakeyi, barince ma Sile kin gama yaje ya d'aukoki...."

Nana A ta kuma murmusawa saidai kafin takaiga bada amsawa Ayiya ta hangi motar 'yar uwarta Nana H tazo d'aukarta.... Shaye da mamaki take kallon motar kafin ta d'an saita kanta tace da Ayiya... "Ammm Ayiya shikenan basai Malam Sile yazo ba Nana H tazo d'auka ta...."

Bata jira cewan Ayiya ba ta katse kiran domin already Nana H ta cakka birki gabanta... Lokaci guda ta shiga zuge glass d'in motar murmushi saman fuskarta....

Mamaki bai bar saman fuskar Nana A ba wai da gaske itace Nana H tazo d'auka ko kuwa dai wani uzirinta ya kawota.... Bata ida tunanin ba ta jiyo muryar Nana H cikin k'atuwar Range Rover d'inta tana fad'in "Hello Sis.... Shall we..?"

Still mamaki saman fuskar Nana A, a hankali ta furta "Nana H are you serious you are here to fetch me....?"

Nana H ta murmusa had'i da d'aga giranta guda d'aya kana tace "Sure I'm here to fetch my one and only Sis.. Come on get in the car...."

Murmushin saman fuskar Nana A ya fad'ad'a cikeda jin dad'i ta bud'e marfin motar da shike k'afarta nada matsala da k'yar ta d'an iya kama motar ta shige....

Fuskar Nana H d'auke da alamun damuwa take duban 'yar uwar tata take fad'in "Oh careful Sis... Ko nazo na taimaka maki ne...?" Ta k'arashe tana yatsina fuska...

Cikeda jin dad'i Nana A tace "Kar ki damu Sis zan iya... Na gode da kika tuna dani...."

Mirmushi Nana H tayi lokaci guda tayi key wa motar kana tace "Kai haba Sistu, banida wacce ta fiki duk fad'in duniyar nan kar ki mance mun zauna mahaifa guda for good nine months kafin muzo duniya.... Ki daina damuwa idan na nuna kulawata akanki... Nana A wllhi bakida wanda yafini..."

Nana A ta murmusa dad'i fal zuciyarta kana tace "Gaskiya ne Sister banida wanda yafiki... I love you..."

Nana H ta kuma murmusawa sanda ta maida dubanta ga kwalta kana tace "Shiyasa nake so idan na baki shawari ki d'auka kuma ki yarda dani kan bazan so naga wani abu ya cutar dake ba....." Ta k'arashe fuska fal alamun damuwa

K'aran da wayar Nana A yayi ne ya katse masu firan tasu...

Da fari'arta ta d'aga wayar ganin Uncle Siraj ne mai kiranta...

"Assalamu alaikum... Uncle barka da yamma....!"

Jin da Siraj take waya ya sanya Nana H ta juyo ta bata wani kallo...

Daga d'aya b'angaren Siraj yace "Nana A what happened... Ya akayi baki dawo gida ba har yanzu, yanzu shigowata gida Ammah tace min baki dawo ba... Hope all is well...?" Ya k'arashe murya fal damuwa...

Murmushi ta sakar masa mai d'an sauti kana tace "Uncle har hankalinka ya tashi haka na rashin ganina a gida... Naji dad'i kun damu dani gaba d'aya, d'azu Ayiya ta kira so worried, and Nana H tazo d'aukata na musamman sannan gashi kaima ka kira domin jin lafiyata... I feel loved.." Ta k'arashe cikin tsananin jin dad'i

Banda uwar harara babu abinda Nana H ke aika mata, cikin ranta tayi k'wafa ganin hankalin kowa ya tashi kan wannan gurguwar.... Bata kuma sauraren wayar Nana A da Siraj ba sai ciro wayarta da tayi ta tura sak'owa Lamid'o...

_Super boyfriend, your precious flower is with me... And guess what sweetheart.... I'm the one driving sai yanda naga daman kaita... I told you so.. I can be very dangerous..._

Daga haka ajiye wayar tayi had'i da juyowa ta dubi Nana A ta sakar mata murmushi kana tace "So tell me about you and Lamid'o..."

Murmushi Nana A tayi had'i da d'an bud'e idanu kana tace "Sis kinsan Uncle baiyi na'am dashi ba har yanzu...."

Nana H ta murmusa kana tace "Precisely sabida ya sansa farin sani ne tinda abokinsa ne and he don't want you getting hurt.... Toh amma kefa do you feel anything for Lamid'o...?"

Kallonta Nana A tayi kafin ta d'anyi shiru kaman mai nazari...

"Kar kiji kunyata Nana A idan baki sharing dani ba duk fad'in duniyar nan da waye zakiyi... Do you love him as well...?".

D'an sauk'e ajiyan zuciya Nana A tayi kana ta d'an jinjina kai "Of course Nana H I do feel something for him.... But I'm not really sure if that's love... And quite alright ina respecting d'insa sosai...."

Murmusawa Nana H ta kumayi kana tace "My sister is finally in love... Ko babu komai dai kinji irin dad'in da mace keji idan namiji yace yana sonta tinda babu wanda ya tab'a fad'a maki haka before.."

Lokaci guda Nana A ta d'an b'ata fuska ba tareda ta furta komai ba....

D'an dubanta Nana H tayi taga yanda mood d'inta ya canza lokaci guda alamun maganar ya mata zafi kana tace "Oh... Hey I'm sorry, don't take it personal kinji... Just joking...."

D'an murmushi Nana A tayi wanda yafi kama da yak'e kana tace "Kar ki damu banyi fushi ba besides gaskiya kika fad'i babu wanda ya tab'a cewa yana sona before shiyasa bazanyi wasa da damata ba now that Uncle Lamid'o is in love with me...."

Kalman Nana A na k'arshe sosai ya soya mata zuciya wai wannan musakiyar ma har tasan taso namiji... Ji tayi dama bata kawo maganar ba... K'aran shigowar sak'o a wayarta ya sanyata dubawa tana mai rage speed d'in motar...

_Nana H please don't... Don't hurt her, I beg you.... Na yarda Mu had'u a Gwarimpa by 8 can gidanki but please don't hurt Nana A..._

Tana ida karance sak'on ta saki murmushi had'ida cilla wayar backseat... Fira sukaci gaba dayi da Nana A har suka isa gida....

***

Baffah fuska d'aure yake duban kayayyakin da Ahidjo ya sayo ya kawo gidan, ya kuma duban Innah yace "Zuba masa kayansa ba cewa mukayi muna cikin talauci ba ya ci damu, dama can baisan cinmu ba balle shan mu...."

Jikin Innah yayi sanyi yayinda Ahidjo ya kuma sadda kai....

*SameenaAleeyou📚**FUSKA UKU*🏮

*24*

*©Sameena Aleeyou...✍🏽*

"Baffah dan Allah kayi hak'uri ka yafe min...." Ya fad'i yana kuma sadda kai k'asa....

Idan darduman da Baffah ke bisa ya amsa toh kuwa shakka babu shima zai amsa... Radio ya kunna yana mai kishingid'a kaman baisan da hallita a wajen ba....

Ahidjo ya dubi Innah da tuni idanunta sukayi rau-rau, bai sake cewa komai ba ganin Baffah ya juya masa baya sai mik'ewa da yayi jiki babu k'wari yana shirin barin d'akin...

"Zo nan!... " Muryar Baffah ya katse sa.

"Tattari kayanka ban buk'atar ganinsu a nan...."

"Baffah....!"

"Ka tattara nace koh...."

Bai tattara ba sai durk'usawa da yayi kana ya soma fad'in "Baffah meyasa kaki amsar tuba na, nasan nayi kurakurai da dama a baya amma wllhi na gane kurena Baffah bazan kuma tafka kuskuren da nayi a baya ba.... Baffah dan Allah ka yafe min kaji Baffah na...." Ya k'arashe cikin rawar murya...

"Aliyu tashi ka fice min a d'aki....!" Kalmar da Baffah ya fad'i masa kenan....

Jiki babu k'wari bai kwashi kayan ba ya mik'e ya fice daga d'akin...

Ahidjo na fitowa ya hangi Deejoh ta rafka uban tagumi alamun taji fad'an da Baffah ke masa.... Kallon kallo suka shiga yiwa juna shida Deejoh kafin yasa kai ya nufi b'angarensa... Cikin sauri ta mik'e tabi bayansa

Sanda Ahidjo ya fice Innah ta dubi Baffah sabida sosai ranta ya sosu da abinda Baffan keyi... "Haba Malam, haba Malam yanzu shikenan bazaka sami gurbin yafiya wa yaron nan cikin zuciyarka ba, shikenan fah mana tilo, kuma ya ijiye aikinsa da iyalinsa ya zab'i ya faranta mana yanzu mai kake tunani idan ya koma 'yar gidan jiya...."

Dubanta kawai Baffah yayi fuska babu walwala kana yace "Ni nasan abinda nakeyi, na kuma san halinsa... Idan har da gaske yake ya tuba zamu gani... Jikina yana bani Aliyu wani abin yake k'ullawa, ki d'ibi kayansa ki maida masa nikam bani buk'ata, kuma k'warar shinkafarsa ban yarda a girkata a tukunyan gidana ba kinji na fad'a maki..." Daga haka Baffah ya gyara kwanciyarsa yana mai ci gaba da saita radio d'insa...

Innah ta matsi k'wallan da suka zubo mata cikeda takaicin mijinta na ta d'ibi kayyakin ta fice daga d'akin...

**

Zaune ta samesa waya manne a kunnensa, da alama da abokan aikinsa yake wayan....

Can gefe ta samu ta zauna Ahidjo ya bita da kallo yana mai ci gaba da magana a wayar, lokaci guda kuma ya mik'e ya fice still wayar manne kunnensa....

Yana ficewa ta mik'e ta shiga tattara masa d'akin, kayayyakinsa da suke bisa katifa gaba d'aya ta tattaresu ta kinke, ta fice sashen Innah d'auko tsintsiya.. Innah na ganinta ta d'au tsintsiya da parker ta tambayeta ina zata da tsintsiya..

D'an rakub'ewa tayi kana tace "D'akin Yaya zan share..."

Har cikin ranta taji dad'in hakan, da alama Deejoh da Ahidjo sun soma sakewa da juna, lallai shawarin Hinde ya mata amfani, ga dukkan alamu auren da aka masa zaisa ya zauna dasu sosai...

Tsaf Deejoh ta share masa d'akin, ta linke masa abin sallahn sa harda k'aramar k'ur'ani ta gani saman abin sallar... Ta saki murmushi tana mamakin ashe duk gayun nan nasa dai bai mance mahallicinsa ba, lokaci guda girmansa da take gani ya kuma k'aruwa....

Ya d'an jima tsaye bakin k'ofa yana kallonta yanda ta zage sai gyara d'akin take, lokaci guda ya tsinci kansa da sakin murmushi, ashe dai yarinyar tanada hankali dukda tarin shiririta da take dashi, koda shike yasan shiriritar ma ta yarinta ce, ya tuna tunda sukayi aure da Nana H bata tab'a ganin wani abu nasa ta kintsa ba saidai ta umarce mai aiki tayi shid'inma sai taga bai d'age abinsa bane take umartan mai aikin, talk less of share masa d'aki saidai ma'aikata suyi... Shimfid'arsu kuwa da suka kwanta idan ba shi ya tattare ba toh kuwa shakka babu mai aiki ce zatayi... Ahidjo ya kuma sakin murmushi had'i da girgiza kai....

Juyowar da zatayi kuwa suka had'a idanu dashi yana nan tsaye hard'e da hannaye... Murmushi ya sakar mata yayinda tayi saurin janyo hijab d'inta ta saka...

K'arasa shigowa d'akin yayi yana mai k'arewa d'akin kallo kana yace "Sannu da aiki..."
Chapter 33 · 0% Book details