← Book details Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 98

Sashe 37

Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ya isa da Allah, ba wa'azi nace kimin ba, idan kina iya tafiya kizo mu tafi, idan kuma bazaki tafi ba fine... Ni kinga tafiyata tinda ke bakisan meke maki ciwo a rayuwa ba..." Ta k'arashe tana karkad'an d'an makulin motar har ta isa ga motar tata...

Nana A da jikinta yayi sanyi gaba d'aya juyowa tayi tana duban Junaid da ya raka Nana H da wani irin kallo shi kad'ai yake sak'e-sak'e cikin zuciyarsa... Kafin Nana A ta sami zarafin magana ya sakar mata murmushi kana yace "It's nothing, kar ki damu kinji.... Nasan akwai mutane irin haka so bai dameni ba, kuma banyi fushi ba, ba kowa bane zai iya zama da mai deficiency irin namu bai k'yamacesa ba ko ya nuna masa ya fisa ba.... That's why bazan tab'a auren mace mai cikar halitta ba sabida gudun gori a gaba..."

Kallo Nana A take binsa dashi lokaci guda take auna kalaman nasa... Mai yake nufi da bazaiyi aure ba sai mai nakasa... Kenan itama idan ta auri mai lafiya irin haka ka iya faruwa da ita..? bata kai ga samo amsar tambayarta ba ta jiyo muryarsa yana fad'in "Please kar ki bari wann maganar ya dameki... And promise me bazaki samu sab'ani da 'yar uwarki akan wannan maganar ba..."

K'ak'aro murmushi tayi tana jinjina sanyin zuciya da kyakkyawar d'abi'a irinta Junaid kana tace "I promise you, bazan kuma tada maganar ba..."

Murmushi shima ya sakar mata kana yace "Thank you.... See you tomorrow, you take care Okay...." Ya k'arashe yana tura tayun wheelchair d'insa zuciyarsa nai masa wani irin zafi... Tabbas Nana H batasan su waye sanadin kasancewarsa saman wannan kujera ba da bata soma magana makamancin haka ba, amma itama kwanannan zata tsinci nata mijin saman irin kujeran da yake bisa.... Ya k'arashe tunanin nasa wata irin murmushi mai cikeda ma'anoni kwance saman fuskarsa...

***

Tin daga nesa Nasaar ya hangosu Azeeza na biyeda Siraj yayinda waya ke manne kunnen Siraj, shifah sam baison k'eb'ewar Azeezarsa da Siraj especially now that they're in relationship... Wani irin kishin Siraj yakeji maras misaltuwa, gani yake kaman ya tapka ganganci tinda ya bari Azeeza ta soma aiki a Laushi Group, baida zab'i hakan ne kawai zaisa Junaid ya kuma aminta dashi har ya basa auren tilon k'anwarsa tinda yasan har abada Azeeza bazata tab'a zama mallakin Siraj ba... Shi kansa bazai tab'a bari ba ma, Azeeza tasa ce shi kad'ai... Cikin sauri ya mik'e yabi bayansu...

Dai-dai haraban kampanin suka tsaya lokaci guda wani security ya k'araso da motar Siraj wajen kana ya mik'awa Siraj d'in keys cikeda rusunawa..

Siraj ya bud'e motar ba tareda ya dubeta ba yace "Get in the car..."

Sosai wannan jin kan nasa ke bata takaici idan ta tunawa Junaid take aikin sai kawai ta watsar ta shanye duk wani jidakan da yake mata, abin nasa har mamaki yake bata...

K'arasawa tayi ta bud'e marfin motar ta shige.... Aiko kaman jira yake tana shigewa yayi key wa motar suka bar wajen ba tareda tasan ina suka nufa ba....

Hankalin Nasaar yakai k'oluluwa wajen tashi, cikin sauri ya zaro wayarsa ya turawa Azeeza text yana tambayarta ina zasuje itada Siraj... Take ta masa reply da batasan yanda suka nufa ba don ta tambayesa yafi baki biyar bai bata amsa ba... Nasaar ya kuma tura mata da sak'on ta kula da kanta kar ta bari Siraj ya mata wani mugun abu.... Azeeza ta tura masa da reply kar yaji komai she can take care of herself...

Sauk'e ajiyan zuciya Nasaar yayi yana kuma karanta sak'on Azeeza don shi da niyyan bin bayansu yayi Azeeza ta kwab'esa acewarta kar Siraj yayi suspecting wani abu.... Lokaci guda ya kuma tura mata da wani sak'on

_I love you so much my Zeeza.._

Murmushi Azeeza take tana bin screen d'in wayar da kallo, sak'on da Nasaar ya turo mata, hankalin Siraj rabi naga kwalta rabi naga Azeeza da tuntuni ya fahimci sak'o take karantawa tana kuma maida reply.... Zuciyarsa ta shiga raya masa da saurayi take yi, k'irjinsa ya shiga masa zafi, cikin dakekkiyar murya yace da ita

"Bance maki babu kula samari during working hours ba.... Ke da waye kike chatting...?"

Karkatowa tayi tana dubansa yanda yayi maganar babu alamun wasa a fuskarsa abin har yaso bata dariya... Batakai ga basa amsa ba taga ya mik'o mata hannu yana fad'in "Bani wayar...."

Mamaki ya kuma cikata... "Amma dai Sir cikin rules d'inka baka hana amsa sak'o a rubuce ba amsa Kira ne dai ka hana, so I see no reason da zai sa ka amshe min wayata..." Ta k'arashe tana jujjuya masa maidaidaitan idanunta masu yalwan suma sama da k'asa...

Siraj ya bita da kallon mamaki yanda sam bata tsoronsa dukda k'arancin shekarunta, shi da yawan 'yan matansa tsoronsa sukeji idan ya kafa masu doka basa takawa amma wannan yarinyar ko shakkarsa bataji a matsayinsa na shugabanta... Wata zuciya tace meyasa kake dangantata da sauran 'yan matanka ko ka mance ita employee d'inka ce not your girlfriend.... Mai yasa zai dameka...? Take b'angare na zuciyar tasa ta basa amsa da _Because you love her.._ Saurin rintsa idanunsa yayi had'i da saita kansa kafin ya maida hankalinsa ga driving lokaci guda ya d'an saki murmushi da gefen bakinsa wanda sai ka kula sosai ka gane hakan kana yace "It suits you, ina son mace mai tsiwa..." Yayi maganar can k'asar mak'oshi

Karkatowa tayi tana dubansa mamaki saman fuskarta sai ka rantse bashi yayi maganar ba kana ta d'an murmusa had'i da juya idanu tace "Shiyasa kake son niece d'incan taka.."

Ya kuma murmusawa sanda yake karyan kwana ba tareda ya dubeta ba yace "She's my Fav...."

Azeeza ta murmusa tace "Sir nifa ba tsiwa na maka ba at least sai ka sanar dani yanda zamuje..."

Nan ma idanunsa naga kwalta yace da ita "What if saidaki zanyi....?"

Murmushi ta kumayi kana tace "Ai babu wanda zai iya sayana, tsadace dani...."

Sai sannan Siraj ya maido da dubansa gareta kafin ya maida idanunsa kwalta yana mai fad'in "You sure about that...?"

Ba tareda ta dubesa itama tace "Umhum sosai ma...."

Dai-dai lokacin yayi parking k'ofar wani rantsettsen boutique na mata Wanda ya amsa sunarsa....
Azeeza ta bisa da kallo fuska cikeda alamun tambaya....

Lokaci guda yayi unlocking motar ba tareda ya dubeta ba yace "We're here to buy you new set of clothes... Ya kamata ki canza wardrobe d'inki idan kina son yin aiki dani....." Daga haka sa kai yayi ya shine cikin boutique d'in...

Baki sake ta bisa da kallo tana mamakin k'arfin hali irin na Siraj, toh ita kuma ce masa tayi tana buk'atan canjin wardrobe ko me... Meye ma laifin kayan da take sakawa da zaice she need a change of wardrobe.... Lokaci guda ta shiga bin kayan jikinta da kallo shaye da tsananin mamaki....

***

Nana A ta kuma duban Nana H sabida d'aurewa da kanta yayi kana tace "Ina ne nan, ina kika kawoni....?"

Kamo hannayen Nana A Nana H tayi lokaci guda idanunta sukayi rau-rau kana ta soma fad'in "Sistu..... I..... I don't know how to explain it, kawai gani nayi gwara na kawoki ki gane ma idanunki, don idan na fad'i maki ba yarda zakiyi ba...."

Kan Asma'u ya kuma d'aurewa, girgiza kai ta d'anyi kana tace "I still don't get you... Wai menene ke faruwa Nana H...?" Wannan karan tsoro ya d'an nuna saman fuskarta...

Kamo hannayen Asma'u Nana H tayi suka nufi cikin gidan....

Cak Nana A ta tsaya a k'ofa kana tace "Sistu bazan shiga ba sai kin sanar dani yanda kika kawoni...."

Murmushi Nana H tayi kana tace "Asma'u kin yarda dani, kin yarda bazan tab'a cutar dake ba...?"

Nana A ta jinjina kai a hankali...

"Good.. Nan da kike gani ba gidan kowa bane sai gidan Lamid'o... D'azu Heedj ya turo min sak'o ta wajen Lamid'o, nayita kiransa ya kawo min sak'ona bai kawo min ba shine na yanke shawarin zuwa na amsa da kaina.... Toh da nazo amsa shine naga wani abu... Something terrible... Abinda baki bazai iya fad'i ba...." Aya ta dasawa kalaman nata sabida rawa da muryarta ya soma yi...

Nana A cikeda tashin hankali ta soma hawaye tana tambayar Nana H mai ya sami Lamid'o dan Allah ta sanar da ita....

Bata bata amsa ba sai kamo hannunta da tayi suka nufi cikin parlorn...

Abinda suka soma karo dashi shi yafi komai d'aga hankalin Asma'u... Kwalaben barasa ne kusan kalan biyar a wajen, da wasu shirgin kayan maye... K'irjinta yayi wani irin yankewa ya fad'i.... Ta shiga bin hotunansa dake parlorn da kallo tana addu'an inama ba shi bane, saidai zuciyarta ta aminta mata tabbas gidansa ne....

Wani d'aki suka hanga a bud'e Nana A ta soma tafiya ta nufi d'akin jikinta na wani irin rawa... Saidai kafin ta isa d'akin taja ta tsaya cak sabida wani kayan tashin hankalin da kunnuwanta suka jiyo mata... Muryar mace take ji cikin sautin da bai kamata ba tana ambaton sunan Lamid'o cikin wasu irin sumbatu marassa dad'in saurare wanda dagaji kasan masha'a kurum suke aikatawa.... Jikin Nana A ya d'auki b'ari innalillahi kawai take ambata ba tareda ta iya motsa koda d'an yatsanta ba.... Cikin sauri Nana H ta k'arasa ta Lakota suka nufo waje kana ta rungumeta tana bata baki...

"Kiyi hak'uri Sistu shiyasa banso kika gani ba amma bazan iya b'oye maki ba sabida bana son na cutar dake... Wannan shine Lamid'o wannan ne real identity d'insa... Asma'u Lamid'o bai kamaceki ba, Lamid'o ba irin mijin da ya dace dake bane.... I'm sorry Sister banson ganinki broken....." Tsananin kukan Nana A ya k'aru tanayi tana k'unshe bakinta, lokaci guda ta shiga janyo hannun Nana H tana fad'in "Mu bar wajen nan, dan Allah Nana H mu bar wajen nan kinji...." Ta k'arashe cikin shesshek'ar kuka...

Rungumeta Nana H tayi suka fice daga gidan suka nufi mota...
Chapter 37 · 0% Book details