← Book details Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 98

Sashe 97

Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yaron ya kuma jinjina kai kana ya koma cikin gidan, Umma da Zaliha sai yi suke Zaliha tana fad'in itafa wllhi batasan kowa a wajen ba balle har wani yazo nemanta, Umma na fad'in ta dai je ta duba ta kumaji da mai yazo...

Muryar yaron ya kuma katse su "Wai yace wajenki yazo....."

Kafin Zaliha ta kuma yin magana Umma tace "Kaga jekace masa tana fitowa...."

Zaliha baki a ture take duban Umma kana tace "Fisabilillahi Umma haka kawai bamusan mutum ba kice ina zuwa, Abbah yafah hanani tara masa ko wani irin shirgi k'ofar gida...."

"Eh dai ai nima ba son ganin kina tara shirgin nake ba, amma ai wannan cewa akayi daga wajen aikinku yake bakisan mai ya kawo sa ba, shifa rayuwar nan da kike gani sam babu kyau wulak'anta d'an Adam, maza tashi kije....."

Ba don taso ba ta mik'e ta kuma d'aukan mayafinta fuska babu walwala ta nufi waje....

Saida ta lab'e jikin k'ofa tana hango bak'on nata, mamaki ya cikata don ba kowa bane illa wannan gurgun da kaman idan bata b'ata gani ba shine suka had'u dashi na fitowa ofishin Nana A... Toh meye yazo yi mata? Ta tambayi kanta tana mai faman ci gaba da sak'e-sak'e cikin zuciyarta.... Cikin tsanaki ta soma takowa....

***

K'uri tayiwa Ammah da har lokacin bata farfad'o ba tausayinsu gaba d'aya na ratsa zuciyarta, su kuma haka tasu k'addarar take A duniyarsu, daga wannan sai wancan, daga an d'inke wannan sai wancan ya kuma b'arkewa, yaya zakayi da hukuncin ubangiji saiko godiyar Allah.....

D'an kaikaito da fuskarta tayi tana duban Ayiya data rapka uban tagumi kana tace "Ayiya mai Dr yace...."

Saida ta sauk'e ajiyan zuciya kana ta d'an gyara zamanta "Toh Asma'u har yanzu dai basuce komai ba, sun dai d'auki jininta kashi daban-daban wanda nake tunanin gwaji zasu mata..."

Nana A ta jinjina kai still idanunta na kan Ammah take ci gaba da fad'in "Nazo mata da sak'o mai dad'i ashe bazan taddata idanunta biyu ba.... Ammah Allah ya baki lafiya kiyi tozali da Nana K, jikarki tana raye, kinyi gaskiya da kikace jikinki na baki Khadija na raye, tabbas tana raye, nasan zakiyi farin ciki da ganinta, ta girma ta zamto cikakkiyar budurwa mai kyau....."

Tinda ta soma magana Ayiya ke dubanta, murmushin da batayi zato ba ya kufce mata, hannayen Nana A ta kamo tana mai fad'in "Asma'u da gaske 'yar uwarku na raye, da gaske kin ganta, a ina kika ganta... Nuna min ita....."

Murmushi Nana A keyi dukda hawaye dake ci gaba da zubo mata, lokaci guda ta rik'o hannayen Ayiya "Tana raye Ayiya, na ganta a hoto wanda ya tabbatar mana da shaidar cewa 'yar uwarmu na raye, na tabbata Uncle Siraj da Ammah zasuyi farin ciki sosai....."

Ayiya ta jinjina kai kana tace "Haka ne.... 'yar uwarki ta ganta itama,.... Ina nufin Nana Hafsatu...."

Take fuskar Nana A ya d'an sauya amma ta daure tace "Eh ta ganta itama..."

"Tayi farin ciki....?" Ayiya ta kuma jefo mata tambayar

Dubanta Nana A ta d'anyi tamkar mai karantar yanayinta kana ta d'an girgiza kai alamun a'a... "I don't know, ban sani ba... Ban sani ba Ayiya..... You know how my sister is.... She's somehow unbearable.... But what matters is that she's alive and we'll soon be together insha Allah...." Ta k'arashe murmushi kwance saman fuskarta...

***

Kallo guda Nasaar ya mata had'ida kwashewa da dariya, nunata ya shiga yi yana kuma ci gaba da dariyarsa ganin yanayin shigar tata....

Tsaki tayi had'ida cire k'atoton bak'in gilashin dake rufe saman idanunta kana tace "Stop this will you... You're so annoying...." Ta k'arashe tana bangajesa had'ida shigewa cikin parlorn....

Juyowa ya kuma yi yana mai ci gaba da dubanta tak'aitaccen dariya saman fuskarsa kana yace "What on earth is gotten into you,.... I mean why are you dress like this....."

"Is none of your business, zaka sanar dani dalilin kirana ne kokuwa....?"

Nasaar ya kuma murmusawa yana mai k'arasowa kusanta had'ida kamo hannayenta, cikin kashe idanu yake fad'in "But you still look gorgeous sweetheart..."

Katsesa tayi da fad'in "I'm always beautiful.... So tell me why am I here anyway...."

Murmushi bai bar saman fuskar Nasaar ba yake fad'in "Gaskiya dole Heedj ya makance da soyayyarki....."

Murmusawa tayi tana mai dubansa da gefen idanu kana tace "I rather not discuss this subject you idiot... Ka sanar dani yanda Azeeza take...."

Murmusawa Nasaar ya kumayi yana janyo sumar kanta a hankali yake ci gaba da fad'in "But I still wonder how he cheated on you with a small girl.... A teenager for that matter....."

Lokaci guda ta d'ago tanai masa wani irin duba kana ta d'an murmusa.... "Nasaar ka kirani nan ne domin ka b'ata min rai..... Bari kaji na fad'a maka, Heedj was mine alone, Heedj bai tab'a cin amanar aurenmu ba, Heedj bai tab'a mu'amala da wata mace bayana ba, ka daina fad'in wannan k'aryar, idanma ka kawo wannan topic d'in ne don ka karkatar min da hankali I don't believe you, kuma bari kaji you make your move fast kafin nayi nawa, you know me quite well..... You know exactly what I'm capable of...." Ta k'arashe tana wasa da 'yan yatsun hannunta saman fuskarsa....

Har lokacin Nasaar bai daina murmushi da gefen bakinsa ba yana binta da wani munafukin kallo....

Janyota yayi ta fad'o cikin jikinsa kana yaci gaba da fad'in "Mata kenan.... Kun iya makirci ajin farko, saidai kuna mance wayonku kad'an ne gaban namiji.... Kodashike babu abinda zai dameki tinda ba sonsa kike ba.... So don yayi aure a gida ya d'irkawa matar ciki ba damunki zaiyi ba, amma babban abinda ya dameni shine raina maki wayo da yayi, yayi aure ba tareda saninki ba, sannan har ya bata abinda ya kasa baki.... Ina nufin d'ansa na kwance cikinta....."

Da k'arfin gaske ta turesa daga jikinta tana wani irin huci take fad'in "No... No no that's not true, Heedj bazai tab'a min abinda kake fad'i ba, you're ridiculous..."

Nasaar ya kuma fashewa da dariya kana yace "You better stop deluding yourself darling, I'm telling you the truth...."

Mik'ewa tayi tsam sanda wani irin kishi ya tokare mata mak'oshi, har itace Heedj zai wulak'anta haka, itace zai rainama hankali, yaje yayi aure and he even impregnated the girl.... This is unacceptable, even though he's dead she needs to take her revenge, ji take inama zataga Heedj a gabanta data shayar dashi mamaki, data nuna masa no one messes with her..... Kallon Nasaar dake zaune saman kujera ya d'ora k'afa d'aya saman d'aya kana tace "If you're telling the truth take me to her right this moment...."

Murmusawa ya kumayi yana mai ci gaba da karkad'a k'afafu kana yace "Mai zan samu in return...?"

Shafe goshinta tayi tana mai ci gaba da huci had'ida kai komo cikin parlorn kana ta maido da dubanta ga Nasaar.... "I need to see her right now..." Ta k'arashe hawaye na gangarowa daga idanunta had'ida durk'ushewa wajen, iya rayuwarta bata tab'a tsammanin Heedj zai mata haka ba.... Heedj ya mata k'arshen wulak'anci wanda bata tab'a tsammani daga garesa ba.....

A hankali Nasaar ya dafata, lokaci guda ta d'ago tana dubansa sai kuma ta rungumesa cikin tsananin kuka take furta "Bazan tab'a yafe masa ba, bazan tab'a yafe masa ba... He got what he deserved......" Ta k'arashe tana goge ragowar hawayen idanunta...

***

Juyawa ta kuma yi zata shige gida Junaid yayi saurin tare gabanta.... "Dan Allah ki saurareni...."

Katsesa tayi da fad'in "Mai kake so kaji ne wai na fad'a maka ni bansan abinda kake magana akai ba, ka k'yaleni dan Allah...."

Junaid ya d'an kuma fuzar da iska kana yace "Nasan kin sani, kin kuma san abinda nake magana akai, Ki sani idan wancan matar sace Nana K tayi kema kinda laifi muddin kika rufe abinda kika sani.... Dan Allah ki sanar dani yanda zan sameta...."

K'uri Zaliha ta masa tana dubansa kana tace "Toh wai kai bawan Allah meye naka a ciki, meye naka na damuwa harda biyoni gidanmu, anya bakayi shisshigi da yawa ba....."

D'an murmusawa yayi kana yace "I'm doing this for Nana A, na sani samun 'yar uwarta farin ciki ne a gareta shiyasa nayi alk'awarin samo mata ita dukda lalurar da nake d'auke da ita....

Jikin Zaliha ya d'anyi sanyi, don harga Allah kalamansa na k'arshe sunyi tasiri cikin zuciyarta....

A hankali ta d'an gyara tsayuwarta kana tace "Shikenan zan sanar dakai komai iyakacin abinda na sani kuma insha Allah zan taimaka maka mu samo Mairo...."

Murmushi Junaid ya sakar mata kana ya furta "Na gode..... Na gode sosai...."

Tak'aitaccen murmushi itama tayi ba tareda ta kuma iya dubansa ba kana tace "Zan shige gida idan Allah ya kaimu goben sai ka dawo amma dan Allah kada ka sanar da Nana Asma'u wannan maganar sabida banso 'yar uwarta tasan komai gameda k'udirinmu...."

Jinjina kai yayi kana yace "Insha Allah...."

Har Zaliha ta shige gida Junaid bai bar k'ofar gidan ba, saida ya tabbata ta shiga gida kafin ya juya ya soma tura wheelchair d'insa....

Zaliha kuwa tana shigewa gida tsaye tayi jikin k'ofa had'ida lumshe idanunta, tunda take bata tab'a tsintar kanta a yanayi irinta yau ba, mai hakan yake nufi....? Saurin bud'e idanunta tayi had'ida shigewa cikin gida kafin Abbanta yazo ya taddata wajen.....

***

Washe gari Nana A bata sami zarafin zuwa foundation ba sabida jikin Ammah, har yanzu bata farfad'o ba, ga Uncle Siraj shiru basu samesa ba, ga Nana H ma tinda ta fice bata dawo ba... Abin yama Nana A yawa ga tunanin 'yar uwarta da take ji a jikinta tana gab da bayyana.... Sosai ta baiwa Ayiya tausayi haka ta rungumeta ba tareda ta iya koda rarrashinta ba sabida batasan mai zata soma fad'a mata ba, iyakaci ta sani duk randa sirrin da suke b'oye masu ya bayyana zata rasa Asma'unta.... A hankali ta lumshe idanunta siraran hawaye suka gangaro mata, Allah kurum take ambato cikin zuciyarta tasan shine kawai zai iya kawo masu d'auki....
Chapter 97 · 0% Book details