Sashe 54
Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ayiya da Asma'u zaune sukayi bisa kujera Asma'u na hawaye take fad'in "Ayiya da gaske Uncle Heedj ya tafi, Ayiya rabona dashi tun kafin yayi tafiyar can da ya d'an jima, Ayiya Uncle nada kirki shikad'aine zai iya zama da 'yar uwata sabida hak'urinsa da kirkinsa.... Ayiya ina tausayin 'yar uwata, ta rasa mijinta a k'aramin shekaru... A kullum ina hangosu zasu hayayyafa su kuma tsufa tare ashe kana naka Allah yana nashi.... Na Allah shine dai-dai.... Allah yajik'anka Uncle Heedj kyawawan d'abi'unka su bika.... Tabbas ka barmu da kewa na rashinka....." Ta k'arashe cikin kuka sosai... Ayiya ta rungumota tana lallashinta cikin daurewa zuciyarta cikeda damuwar sam bata kyautawa Ahidjo ba sanda yake raye sabida rashin jituwa da Nana H dake tsakaninsu saida ya shafi Ahidjo sanda ya soma neman auren Nana H ta d'auki kulawarta ta maida kan Lamid'o wanda batasan shine zaici amanar d'iyarta Nana A ba, Allah sarki Ahidjo tabbas yafi matarsa kirki, zata jima tanajin zafin abubuwan data masa a baya....
Siraj kuwa yana fad'awa d'aki hotonsu da suka d'auka su uku tare a makaranta can United States ya d'auka yana gani, sun dafe juna su duka FUSKA UKUN, Siraj na tsakiya yayinda Ahidjo da Lamid'o ke gefe-gefe....
K'ura ma hoton idanu yayi wasu irin sabbin kuka suna taso masa, a hankali ya zauna had'ida rungume hoton cikin k'irjinsa, lokaci guda ya janyo wayarsa ya shiga neman layin Azeeza, bugu ta d'aga don ita yanzu har firgita take idan taga wayar Siraj tunda tasan Yayanta na farautar rayuwarsa..
Saidai kafin ta sami zarafin magana tajiyo sautin kukansa, sosai hankalinta ya tashi tabbas ba k'aramin abu bane zai saka namiji kaman Siraj kuka, take kawai taji kuka na zuwa mata itama gashi ya kasa fad'in komai sai kuka...
Cikin kuka itama take fad'in "Sir... Siraj lafiya, meke faruwa ne dan Allah ka sanar dani...." Ta k'arashe tana k'ok'arin mik'ewa had'ida neman takalmi zata fice bata damu da duhu da gari yayi damuwarta kawai Siraj ya zama safe..
Junaid daga balcony ya hangeta cikin sauri ya turo kekensa ya fito had'ida shan gabanta....
Sosai Azeeza ke kuka tana tambayar Siraj ya sanar da ita abinda ke faruwa...
"Dan Allah sir ka sanar dani yanda kake wllhi yanzu zanzo, please ka sanar dani...." Ta k'arashe cikin shesshek'a...
Cikin rawar murya Siraj dake tak'ure waje guda yake fad'in "Azeeza ABOKAINA abokaina Azeeza, na rasa su gaba d'aya.... Azeeza na rasasu... Heedj ya tafi ya tafi Azeeza tafiya ta har abada, dan Allah kice min zasu dawo zamu kuma rayuwa tare A DUNIYAR MU kice min zasu dawo kinji...." Ya k'arashe cikin wata irin sanyin murya...
Wani irin sanyi jikin Azeeza yayi don tasan k'udirin Yayanta akan FUSKA UKU. A hankali ta silale saman tile tana mai watsawa Yayanta Junaid wani irin duba da rianannun idanunta...
***
Washe gari kan kace mai labari ya riske ko ina, Sabi'u shi yayi duk wani cuku-cuku aka bada report na boge cewa tsagerun boko haram su suka k'ona Agent Aliyu cikin motarsa kasancewar da yawan mutane sun kwana da sanin rayuwar duk wani force a yankin arewa maso gabas yana cikin had'ari babba.... Da wannan k'akk'waran dalili yasa Siraj basu tsananta binkice ba sannan Nana H ma ta nuna batason binciken don bazata juri wasu unnecessary stupid interrogations daga jami'an tsaro ba sabida tana fama da jimamin mutuwar mijinta...
A b'angaren Azeeza sosai halinda Siraj ke ciki ya dameta, a ranar kwana na biyu ta fito cikin shiri zata tafi gidansu Siraj ta'aziya don koda ace basu jituwa da Nana H tasan matsayin Ahidjo a wajen Siraj, sannan su Ammah sunada mutunci sun cancanci gaisuwa, lokaci guda kuma ta tuna toh waima ta yaya zata soma gaisar da Siraj, ta shiga gidan ta gansu cikin k'unci da kuka tace mai? Yayanta ne silan komai kokuwa mai zatace....? Lokaci guda wasu sabbin hawaye suka shiga gangaro mata tausayin Siraj na ratsa b'argo da tsokarta...
D'ago kan da zatayi sukayi idanu hud'u da Junaid yana dubanta babu alamun wasa a fuskarsa....
"Zeeza kukan mai kikeyi....?" Ya tambaya yana dubanta
Kauda kai gefe tayi wasu hawayen na kuma zubo mata lokaci guda taji bazata iya zuwa ta'aziyan ba don koda taje kuka zatayitayi....
Har cikin ransa Junaid kejin kukanta a hankali ya k'arasa gareta yana mai tura kekensa, ganin k'anwarsa cikin tashin hankali sai ya kuma jefa zuciyarsa cikin k'unci....
"Zeeza ki daina kukan nan kina jina....."
Jiyowa tayi cikin tsananin kuka tana dubansa had'i da girgiza kai take fad'in "Yaya vengeance has turned you into something else... Yaya this is not you.... Why why meyasa ka zab'i zama maras yafiya, shin kaji dad'i a ranka sanda ka riski labarin mutuwar Ahidjo.... Meyasa ka kasheshi...?"
Cikin daka tsawa idanunsa na fitar da wani irin ruwa ya katseta da fad'in "Because he killed her, that imbecile killed my Zeenah, and look at me Zeeza, Zeeza rayuwata saman keken guragu batada wani amfani, have I ever told you sabida d'aukan fansan Zeenah akan FUSKA UKU nake rayuwa, ban tab'a fad'a maki ba koh toh yau ki sani, randa burina ya cika nima zan tafi Zeeza, zan tafi na sami Ammi da Baaba.... And Zeenah zamu kasance tare har abada..." Ya k'arashe hawaye masu zafi naci gaba da kwaranya masa...
Lokaci guda Azeeza ta soma jada baya tana tunanin tabbas Yayanta Junaid ya sami tab'in kwanya...
Da k'yar Nasaar dake tsaye bakin k'ofa ya gama saurarensu tsaf ya iya juyawa kansa na masa wani irin nauyi, sam ji yake zuciyarsa tamkar zata fito waje ta fashe, soyayyar Azeeza na neman tarwatsa masa rayuwa, shin Azeeza kukan mai take irin haka, shin kukan kauce hanya da Yayanta yayi take ko kuwa ma Siraj take wannan kukan..? Mutum d'aya ce tak zata iya amsa masa wannan tambayar kuma ba kowa bace face ita Azeezar...
Cikin sauri ya fice daga gidan ya nufi motarsa ba tareda sanin yanda ya nufa ba, tambayar kansa yake maiyasa yake zama looser a kullum, mai yasa yake tura mota ta tafi ta barsa da k'ura a kullum.... Gefen hanya Nasaar ya samu ya paka motarsa had'ida kifa kansa jikin steering wheel k'irjinsa naci gaba da masa wani irin zogi, tabbas wannan karan kam bai shirya barin Azeeza ma kowa ba, he'll fight for her love even if it will cost him his life.....
***
Bayan sati biyu da faruwan wannan Al'amari jigum Ayiya tayi tana kallon irin rayuwar da ake a gidan marigayi Mas'ud Laushi wai da sunan musulmai, ace Ahidjo ya mutu amma su kasa neman iyayensa da danginsa su sanar dasu, basu san ko iyayensa na raye ba, ko suna mace, Nana H dake lab'e jikin staircase tana sauraren Ayiya da Ammah cikin sauri ta nufo downstairs tana mai matso hawaye ta fad'a jikin Ammah a guje tana fad'in "Ammah yanzu shikenan daga mutuwar mijina an soma zancen a nemo danginsa ko wata mijina baiyi ba za'a soma d'aga min hankali da nemo danginsa, Ammah da wanne zanji da zafin mutuwar mijina koda nemo danginsa Ammah dan Allah kada ki biye wannan matar ko kuma wllhi nima mutuwa zanyi idan aka tak'urani....." Ta k'arashe tana kuka sosai..
Lallashinta Ammah ta shigayi tana sanar da ita bazata kuma jin maganar ba har sai ta dawo cikin hayyacinta.... Nana H kuwa jin haka ta d'ago idanunta ba tareda Ammah ta kula ba tana mai watsawa Ayiya mugun kallo had'ida sakar mata makirin murmushi...
Girgiza kai kurum Ayiya tayi tana mamakin yanda son zuciya yayi tasiri tsakanin Al'umma a wannan duniya tamu, tabbas akwai gyara sosai cikin rayuwan gidan Mas'ud Laushi, sabida tsananin takaici Ayiya bata iya furta komai ba sai mik'ewa da tayi ta bar parlorn, Nana Hafsatu ita ke juya gidan yanda taso, kuma babu mai taka mata birki... Wannan abu sosai yake k'ona zuciyar Ayiya, tasha attempting barin gidan amma sabida Nana A sai ta fasa, tasan idan ta tafi Hafsatu zata iya cutar da ita sannan sam su iyayen basa ganin hakan, fatanta Allah ya wankar masu da idanu su soma ganin wacece d'iyar tasu....
***
Yau kusan kwanaki kenan daga Deejoh har Innah suna wasu irin mafarkai barkatai gameda Ahidjo, Innah kullum cikin addu'a take tana rok'on Allah ya tsare mata d'anta a duk yanda yake, ita kuwa Deejoh k'uryar d'aki shine wajen yinyinta don tinda Yayanta kuma mijinta Ahidjo ya tafi walwalarta ya tsaya a gidan, kullum rungume da kwalban turaren da ya bata take bacci ko fesawa batayi tsaban taltala turaren da take tana kallon mijinta a jiki, a kullum zuciyarta bai tab'a karaya cewa Yaya Ahidjo bazai dawo ba tasan tinda ya mata alk'awari tabbas zai dawo d'in, wannan take tunawa taji ta sami natsuwa sosai cikin zuciyarta...
A can Abuja kuwa Sabi'u gaba d'aya ya rasa wanne zaiyi, shin ya tafi can gida Misau ya sanar masu ne ko kuwa, wata zuciya tace cin amanar taka zaiyi yawa idan bakaje ka duba mahaifansa da kuma iyalinsa da ya barta, take Sabi'u yaji zuciyarsa na raya masa washe gari yayi asubanci zuwa garin Misau ta jihar Bauchi
****
A garin Damaturu kuwa da k'yar da sid'in goshi aka shawo kan Daddah ta yarda Hafizu yake zuwa yana basu karatu, duk bayan lisha suke karatun a farfajiyan gidan Umma Marie, tuni Daddah ta tilastawasu Dakura suma suka soma zuwa karatun, idan ka zauna a majalisin karatun ko ka k'i sai kayi dariya, Malam Hafizu kam nashan fama, gashi da alama idanunsa sun sauk'a kan Mairo saidai kunya irin tasa ta kasa barinsa ya nuna, shiko baisan wacce idanunta ta sauk'a kansa Dakura bace, abun har mamaki yake baiwa Balaji mahaifin Dakura yanda ta rik'e karatun bilhak'k'i bayan a baya babu kalan yak'in da baiyi da ita ba kan zuwa islamiya, amma yanzu lisha nayi ta janyo Falmata sun tafi, har alla alla take tajeta taga Malam Hafizu, su Dakura harda d'inka hijabai ta raba masu gaba d'ayansu, ga wani sabon k'awancen da ya shiga tsakaninsu da Mairo...
Malam Hafizu yana gama parking Babur d'insa wayan mahaifinsa Baba Malam ya shigo masa...
Da sallama ya amsa saidai jin muryar mahaifin nasa wani iri ya sanyasa dakatawa... Lokaci guda Hafizu ke furta "Baba kana nufin yau ya farka....?"