Sashe 1
Fuska Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
[12/9, 11:24 AM] +234 810 044 6653: *FUSKA UKU*🏮
__
*01*
*©Sameena Aleeyou... ✍🏽*
*Bismillahir Rahmanir Raheem*
_*Garin Misau Jihar Bauchi*_
Zaune take saman k'aramar kujera irin wanda mata ke amfani dashi a madafi... Yanda ta rafka uban tagumi ga buta ijiye gabanta zai tabbatar maka cewa cikin damuwa take, da alama alwala take shirin yi amma ko gizau da butan gabanta bata yi ba, tayi nisa matuk'a cikin duniyar tunani....
A haka ya fito daga makewayi ya kuwa hangeta yanda ya barta nan duk'ufe gaban buta... Girgiza kansa kurum yayi ba tareda ya furta koda kalma kafin ya k'arasa gaban k'aramar randar da kansa ya d'ibi ruwa ya tada nasa alwalan... Abin mamaki har yakai ga ida alwalansa wannan baiwar Allah sam batako motsa daga tagumin da tayi ba...
Cikin tsanaki ya warware hannun rigarsa kafin ya d'au karan goge bakinsa ya saka cikin bakinsa, lokaci guda ya k'araso yanda take a zaune....
"Bilkisu..!" Shiru bata amsa ba... D'an bud'e muryarsa ya kuma yi a karo na biyu
"Bilkisu..!"
Sai a sannan taji kiran nata da yake yi....
Saida ta sauk'e nannauyan ajiyan zuciya had'i da muskutawa kana tace "Malam wai har an sauk'o daga masallacin ne...?"
Yanda ta masa tambayar yaso basa dariya amma ya d'an gimste yace "Kiyi alwala kiyi sallah idan na dawo sai muyi maganar kinji koh... Amma wllhi wllhi kinji na rantse maki ban yarda ki tafi bariki neman d'anki ba, wannan shine rayuwar da ya zab'ar ma kansa tunda shi bamu da daraja bamuda mutunci a idanunsa, na tabbata akwai ranar da zai nememu da kansa basai kin tafi nemansa ba,..."
Baikai aya ba murya na rawa ta katse sa da fad'in "Malam wllhi ni nasan ba laifin d'ana bane tsinanniyar matar nan tasa ita ta shiga tsakaninmu dashi, wllhi nasan yana son zuwa gida amma bazai iya ba sabida ta jik'a ta basa yasha, kasan matan bariki sunfi maciji guba... Malam don Allah ka min izini na fita na nemo shi, yau fah kusan shekara kenan tim rabonmu dashi...."
Shiru Malam yayi tamkar mai nazari had'i da yin gajeren murmushi kafin ya girgiza kai yace "Mata kenan, akan 'ya'yayenku zakuyi komai kuma zaku d'aura laifi kan 'ya'yan wasu ku wanke naku 'ya'yan... Shin kin tab'a sanin kalan matar tasa? Kinsan yaya akayi aka nema auren, kinsan wanda ya tura a matsayin wakili....? Duk baki sani ba, rana guda ya shigo tsakar gidan nan ya sanar damu yayi aure kuma bai buk'aci albarkan ko guda daga cikin mu ba... Sanin kanki ne tunda muka gama d'awainiyar karatunsa ya girma ya zama mutum ya tsallake k'afafu ya rabu damu,... Toh ina mai tabbatar maki kada ki kuskura ki d'aura laifi kan koma wacece ita matar nasa, wannan shine rayuwar da ya zab'ar ma kansa.. Laifina guda gata da na nuna masa da yawa, cikin sa'anninsa da suka taso tare a garin nan shi kad'ai ne ya tafi makarantar kwana na yaran hamshak'ai, kai tun daga alimantari d'insa karatu mai inganci na basa, idan baki mance ba har gona ta da shanayena na gado duk na sayar a dalilin na inganta rayuwar yaron nan amma ga sakayyan da yayi min, kar dai ki mance mahimmacin shanayen gado wajen bafillace.... Tabbas sai yanzu nake hango maganganun su Malam Dalha, shi yaro ba'a masa haka, yanda ka tarbiyartar dashi toh kuwa haka nan zai tashi maka, baisan babu ba tun tasowarsa shiyasa ya girma yana jin nauyin ya nunamu yace ga iyayen sa, na masa mai wuya tunda na turasa har k'asar waje yayi karatu ya sami abin yi.... Babu komai yajesa duniya ce tafi gabaruwa iya jima, bazan masa baki ba sannan bazan saka damuwarsa cikin zuciyata ya dameni ba, kuma kema ina shawartar ki da ki cire tunaninsa cikin zuciyarki domin hakan ne kurum zaifi maki sauk'i, mu zuba wa sarautar Allah idanu, rayuwarsa ce yayi yanda yaso da ita, duk yanda yaje yazo nan dai shine cibiyarsa kuma mahaifarsa.... Na wuce masallaci kinji liman har ya tada ik'ama, maza kema kar na dawo na sameki wajen nan...." Bai jira cewarta ba ya fice cikin sassarfa...
Ta jima tana nan zaune a wajen tana sak'e sak'en hukuncin da zata yanke gameda al'amrin, har saida taji masallaci suna raka'a na uku kafin ta murmurs tana mai jin dad'in mafitan data samo, don bazata biye Malam ba ta zauna ta zuba idanu tanaji tana gani ta haifo tilon d'anta guda ma bariki ba.....
***
*Abuja*
Cikin sanyin muryarta taci gaba da buga k'ofar tana kuka take fad'in "NANA H please open the door, please listen to me sis.... Don't shut me out again please.... Dan Allah ki saurareni....."
Daga cikin d'akin kana iya jiyo sautin k'aran fashe-fashe... Cikin kukan itama take fad'in "Just go away NANA A I hate you, I don't wanna see you ever again.... Ki fice min daga gida kuma kada ki sake zuwa yanda nake.... Burinki ya cika Ammah da Uncle SIRAJ suna fushi dani... Ki tafi bana son ganinki..."
Hannu tasa tana share hawayen da suka wanke mata fuska kafin tace "Sis I'm sorry.... I.... I didn't mean to upset you, please let me explain.. Wllhi zanyi duk abinda kika umarceni kiyi hak'uri dan Allah...."
Jin kalamanta na k'arshe ya sanyata sakin wani shu'umin murmushi tana mai duban kanta jikin dressing mirror kana tace "I you sure zakiyi duk abinda na umarceki..."
Cikin sauri ta bakin k'ofar ta shiga jinjina kai tana fad'in "Wllhi zanyi kinji pls open the door....."
Saida ta mik'e tsaye tayi rawa saman gadon tamkar mai tab'in hankali kafin ta dirk'o daga saman gadon ta nufo k'ofa....
Kallo d'aya tayi mata sanda ta bud'e k'ofar nan ta lura da yanda fuskar 'yar uwartata ta kod'e sosai alamun taci kuka, lokaci guda tayi rau-rau tana fad'in "Oh Sis ki daina kuka pls... Kinji I'm sorry, bazan sake sakaki kuka ba kinji koh...."
Lokaci guda suka rungume juna kafin suka koma cikin d'akin hannayensu rik'e cikin na juna,...
Yanda suka jeru suka zauna bakin gado zaka gane tsan-tsan kamannin da suke, basai ance maka tagwaye bane sabida tsananin kamanni da suke, saidai d'aya 'yar gayu ce ta k'arshe yayinda d'ayan gayun sam bai shalleta ba, hasalima bata iya ba....
"NANA ASMA'U....!" Cewar 'yar gayun tana mai duban 'yar uwar tata wacce itama ita take kallo....
"Kina jina, bawai bana son Uncle Siraj yayi aure bane, kinsan 'yan matan yanzu wllhi idan yayi aure shikenan mun sallamawa matar da danginta shi, kuma sanin kanki ne bayan shida Ammah bamuda kowa, gwara ni ma nayi aure inada miji, but what about you, wa kike dashi? Waye zai tsaya maki a rayuwa namiji idan buk'atar hakan ta taso,... A kullum ina nusar dake hanya but baki ganewa, nifa idan ta ni ne Uncle Siraj zai iya zuwa yayi aurensa, but wllhi har ga Allah ke nake jiyewa Sis, kinga dai irin lalurar da kike fama dashi ta rashin k'afa guda, shin kina jin a haka zaki sami wanda zai k'aunaceki tsakani da Allah... Kema kinsan saidai ya aureki kawai don babban kaso na dukiya da mahaifinmu ya mutu ya bar mana, na sani kinada kyau Nana A amma duk yanda kyaunki yake baikai na lafiyayyayar mace ba maras nakasa a tattareda ita... Nana ki auna magana na ki gani, this world is something else now,..."
Tunda ta soma magana jikinta yayi sanyi dama hakan ne yake faruwa da ita duk sanda 'yar uwar tata tazo mata da wani zance ko shawari....
A hankali ta shiga jinjina kai tana mai auna kalaman 'yar uwar tata kana tace "Na fahimceki NANA HAFSAT, kuma duk abinda kika fad'a hakan take, amma wannan dalili sam baiki yasa mu hana k'anin mahaifinmu jin dad'in rayuwarsa ba, Nana H sam nakasata bata dameni ba, kuma nasan shi aure lokaci ne kuma abincin wani guban wani, nasan Allah zai kawo min wanda zai soni ya k'aunace dukda cewa yana sane da nakasan dake tattare dani, don haka ki daina saka ma ranki damuwa sabida lalurata... Sannan Uncle Siraj went through alot, yaga iftila'i daban-daban a rayuwa, kar ki manta a baya duk macen da ya nema toh fah mutuwa takeyi, sannan kar ki mance Aunty Zulfah a daren aurensu 'yan fashi suka shigo har cikin gidan suka kasheta, daga wancan lokaci ya shafe shekaru kusan uku cikin tsananin tashin hankali da alhini, uwa uba sanin kanki ne babu abinda Ammah take so kaman taga autanta yayi aure.... Nana H nidai a gani na mu bar Uncle Siraj yayi aure idan har Allah ya tabbatar da hakan....."
Tunda ta soma magana take binta da wulak'ancaccen kallo tana huci, lokaci guda ta mik'e tsaye tana nuna mata k'ofa take fad'in "Fita.. Fita nace idan ke baza'ayi shawarin arziki dake ba...."
Bata mik'e d'inba bata fice ba sai gyara zama data kuma yi.....
Lokaci guda tamkar ta tuna wani abin ta komo ta zauna a mazauninta kafin ta sauk'e ajiyan zuciya tace "Gaskiyanki ne Sis, Uncle Siraj deserve to be happy... Babu damuwa zanje har gidansu Nadiya na bata hak'uri, amma nasan yana fushi dani..." Lokaci guda idanunta sukayi rau-rau ta kuma damk'o hannun 'yar uwar tata tana fad'in "Dan Allah Sis ki basa hak'uri kinji, make sure ya hak'ura pls kinji dan Allah...." Ta k'arashe kaman zata kurma ihu...
Lokaci guda tausayin 'yar uwar tata ya shigeta....
***
Driver na ida parking ta hangi Ayiya tsaye farfajiyan gidan hannu hard'e da k'irji tana bin motar da kallo, ga dukkan alamu dawowarta take jira, ta kuwa sha mur....
Sosai tasha jinin jikinta don babu wanda yasan sanda ta fice a gidan, bayan tasan ya zamto tamkar doka duk yanda zataje tofah tareda Ayiya ne , Dattijuwa mai kimanin shekaru 66 a duniya...
Cikin takunta na d'ingishi ta nufo yanda take...
Sam bama ta kanta Ayiya take ba tukuna, Sule dreba kawai take kallo yanda yayi parking motar cikin tsoro don yasan zai iya kwasan nasa buhun bala'in tunda ta sa masa doka bataso 'Yar Albarka tana fita ita kad'ai sabida lalurin dake tattareda ita....
"Ayiya barka da yammaci...."
Kallonta kawai tayi ba tareda ta amsa ba kafin ta k'arasa ta nufi yanda Sule ya ida parking....