← Book details Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 92

Sashe 92

Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Ummu Salma ɗaki ta shige tana ta kuka, ba ta taɓa hasaso ma kanta a aure awannan tsakanin ba, sai ga shi kaddara ta sake juya rayuwarta a karo na biyu, wayarta ma kasheta ta yi domin ba ta son ma a dame ta. Mami ma ba ta sake nemanta ba, sai dare da Daddy ya dawo ya kirata.

"Ga Sadakin ki, na ba da auranki akan dubu É—arin da kika lamince."

Daddy ya faɗa bayan ta karɓi kuɗin a farin takarda. Mamaki take yi, kenan da gaske ne?

"Allah ya ba ku zaman lafiya. Kin yi dacen samun nagartattacen miji Ummu Salma."

Kowa na faÉ—in ta yi dace amma ba a faÉ—a mata waye mijin ba, itama ba ta son sani shi ya sa ba ta tambaya ba.
Har da goro da dabino da minti duk Daddy ya taho da su, ita dai kuɗin kawai ta karɓa ta koma ɗaki ta tasa su gaba tana sharɓan kuka komai ya dawo mata sabo, yanzu kuma ina za ta je? Wata rayuwa za ta sake faɗawa? Menene makomar Hanan?

Washegari tun safe Mami da Basira suka shiga kitchen jalop din shinkafa da nama suka dafa aka saka a takeway É—ari har da matar Sunusi ta zo ta taya su aiki Ummu na ciki ba ta fito ba, ta dai fito sun gaisa da Mami, ba ta kawo dalilin auran ta ne ya sa Mamin yin Sadaka ba, da yake ta san suna yi duk karshen wata amma yau É—in na daban ne har da drink da ruwa.
Hamisu ya fita da shi a mota zai je makarantan almajirai a hayin banki zai raba musu.

Ummu abincin ma ba ta ci ba sai da Mami ta leƙo ta yi mata mgana sannan ta fito ta sha tea, ga shi dai ita ta amimce amma kuma abin duk ya dame ta. Ta yi na farko ba ta dace ba yanzu kuma ba ta san wata irin kaddara za ta sake faɗawa a karo na biyu ba.

Sannan da ta kunna wayarta kowa fatan alheri yake yi mata cikin yayyenta,  Hamma Jibo har da cewa Amarya, shi ko Hamma Mustapha wani suna ya kira ta da shi our princess
amma ba wanda ya kira sunan mijin da  aka aura mata, itama ba ta tambaya ba har Baɗɗo da suka yi waya murna take yi mata.

"Sisna, tabÉ—ijam kin samo mai zafi wannan karon. CancaÉ—i."

Amma ba ta faÉ—a mata waye ba, itama ba ta ce tana son sani ba.

"Sisna, ni fa bana son auren nan. Ban zan iya ma Baffa Gaddama ba ne."

"Sisna, ai wannan auren na musamman ne, ya doke wannan auren naki na farko, tab ai tazaran kamar tazaran kasa da sama ne, Habibun banza shi ko a hanya bai isa ya haÉ—a kafaÉ—a da mijin ki na yanzu ba wallahi."

Ummu dai ba ta biye ma BaÉ—É—o ba, ba ta son ma tana jin sunan Habibu saboda tsanar da ta yi masa.
Har Ammah da suka yi waya ba ta nuna mata wani abu ba sun dai gaisa kamar Yadda suka saba, kuma ta ji ta duk a cunkushe ba cikin walwala ba. Baffa ne ma da suka yi waya ya dinga saka mata albarka cikin farincikin da ta jima ba ta ji shi a cikin sa ba.

Sati ɗaya da ɗaurin auran ta, har a lokacin ba ta saki jikinta ba. Sukuku take, da gaske ne ta tsani aure domin ta tabbata ba komai cikinsa sai baƙin ciki da da dana sani, ta fa gwada kuma ba ta dace ba.

Amma ba ta da yadda za ta iya tunda ta amsa ma Baffa an riga kuma an ɗaura baƙin alƙalami ya riga da ya bushe.
Mami kamar murna ma take yi domin ba ta ga alamun ta damu da ganin yanayin ta ba, tunda aka ɗaura auren nan duk dare sai ta yi kuka, so kawai take yi ta samu wani dalilin da za ta sauwaƙe ma kanta wannan auren, in ta tuna auren sai ta tuna makomar rayuwanta anan gaba, ba ta san mijin ba amma ta fi karkata tunaninta da wataƙila daga can Mubi ne tunda ta ga kowa ya san shi.

Ranar Ummu ta yini  cikin nazari, duk hanyar da za ta ɓulle da ita sai kuma ta je karshe ta iske a toshe take, yini ta yi a ɗaki ba ta fito ba kamar wata mara lafiya
Hanan na wajen Basira, kamar ta san yanayinta na yau ba ta zo ta yi mata rigima ba. Tana kwance Basira ta zo tana faɗa mata Mami ta yi baƙo, mamaki ya kamata wani irin baƙo kuma? Kuma Basira ta ce yana Falo, kafin ta fita ta yi ta kiran wayar Mami ta ji ko ta san da zuwan baƙon amma wayarta ba ta shiga shi ya sa ta saka mayafin abayan dake jikinta ta fita zuwa falon Mami.
Duk a tunaninta tunda aka ce ya shigo har falo to ko daga Jimeta ko daga cikin dangin Daddy shi ya sa ta fita kanta tsaye ba fargaba.

Mamaki ya sandarar da ita lokacin da ta yi arba da ganin Hamma LamiÉ—o zaune a falon Mami yana É—auke da Hanan a jikinsa tana ta wasa da sajen fuskar shi.

Sanye yake da farar shadda, har tana ƙyalli kansa da hula amma saboda suma a saman gashin hulan tasa baƙa ta tsaya.
Ya ji shigowarta amma bai iya É—agowa ya kalleta ba.
Ummu ta ce a ranta lalle Mami na da Babban baƙo
Domin tunda ta zo gidan ba ta taɓa ganin ya zo ba sai yau.
Me ya kawo shi? Ta tambaya a cikin zuciyarsa.

"Ko kin manta Mami mahaifiyarsa ne?

Wata zuciyar ta tunasar da ita abin da ta manta. Har ga Allah mantawa take yi da Mami ce ta haifi Hamma LamiÉ—o.

"Barka da zuwa Hamma LamiÉ—o."

Ta faɗa bayan ta ɗan ƙariso falon. Da farko ta so ta yi wucewarta ne saboda Mami ta tsaya da kuma tuna ya fa taimake ta, da jininsa take rayuwa a yanzu.

"Lafiya."

Ya amsa mata, sau É—aya ya kalleta bai sake ba, wasa yake yi ma Hanan. Ta so ta yi komawarta É—aki ne domin ita yanzu neman ma kanta mafita take yi amma ganin yadda ya É—auki Hanma ya sa ta ji sanyi a zuciyarta, ko ita bai yi mata kallon Daraja ba ta ji daÉ—i da ya yi ma Hannan kallon mutumci shi ya sa
ta je kitchen ta haÉ—o masa ruwa da lemu, Daddy ba ya nan ya je Abuja tun jiya amma a yau Mami ta ce zai dawom

Har ta kawo ruwan ta ajiye ta fita falon bai ɗago ba, itama ba ta damu ba ɗaki ta koma ta yi kwanciyarta tana cigaba da sabon lissafin da ya kamata tun bayan auran da aka ɗaura mata, tunani take yi me ya sa Allah bai amsa addu'arta ba? Ita da har a masallacin Madina ta roƙesa da Allah ya sa ta mutu ba ta sake aure ba. Me ya sa kuma Kaddara ta sake buɗe mata wani sabon shafin rayuwa? Ba ma batun ba ta son mijin da aka aura mata ba, auren ne gabaɗaya ba ta so. Ta ma manta da baƙon Mami ta na ciki tana tufka tana famam warwara
Har Mami ta dawo  ba ta sani ba sai da ta shigo ɗakinta sannan a lokacin ta san ta dawo

"Kika zo nan kika kwanta Ummu?

Mamin ta faÉ—a tana kallon ta.

"Mami sannu da zuwa Yaushe kika dawo?
Ummu ta faɗa tana ɗan miƙewa zaune a saman gadon data ke kwance.

"Ban daɗe da dawowa ba. Sai kika bar baƙo shi kaɗai a falo Ummu?

"Mami to na ga Hamma ne ya zo, kin san shi ba ya son hayaniya shi ya sa na baro falon na dawo É—aki ."
Ta faÉ—a tana É—an mikewa zaume.

"To mijin ki ne, in ba ki zauna ba ai ba za ku fahimci juna ba."

"Na'am"

Ummu Salma ta faÉ—a tana kallon Mami domin sai ta ji kamar ba ta ji daidai ba.

"Ko ba ki san baƙon ki ba ne?

Mami ta sake faÉ—a tana kallonta.
Ummu ba ta son ta dire ƙasa ba sai da ta ganta a tsaye kan kafafunta.

"Baƙo na kuma?

Ta faÉ—a cikin mamaki.

"Baffa bai kira ki ba?

Mami ta sake tambaya, domin sun yi mgana da Baffa shi ya faÉ—a mata LamiÉ—on zai zo su yi magana da Ummun a tunanin ta Baffan ya kira Ummun ya sanar mata.

"Mami."

Tana ta yi magana amma ta kasa jikinta ya yi wani irin sanyi.

"Ki gyara jikin ki, ki je ki same shi."

Mami ta faÉ—i haka da sauri lokaci É—aya kuma tana barin É—akin.
Ai sai Ummu Salma ta ji kamar ta daina jin mgana ta kurmance, kamar shiga da fita haka ta ji kalaman Mami.

"To mijin ki ne, in ba ki zauna da shi ba ta ya za ku fahimci juna?

Idanuwanta sun fito waje saboda firgici da razana, in dai har ta ji daidai to Mami na nufin Hamma LamiÉ—o ne mijin da aka aura mata.

Innalillahi wa'inna ilaihirraju"um."

Ta faÉ—a a zucci da sarari lokaci É—aya ta É—ora hannu akai ta fashe da kuka.

"Ina ni ina Hamma LamiÉ—o, wallahi bana son shi."

Take faɗa tana kuka lokaci ɗaya ta koma ta zube kan gado, ji take yi kamar ta yi hauka, ina, ina za ta iya zaman aure da Hamma Lamiɗo, ai an gudu ne ba a tsira ba, sai ta ke jin kamar ta fita ta yi ta gudu kar ta tsaya, ita da ko inuwa ta minti goma ba ta taɓa haɗawa da shi ba, ta ya ya za ta iya haɗa inuwar aure da shi? Mafitan ta na ƙarshe shi ne ta samu mijin ta roƙe shi ya sauwake mata domin ba za ta iya masa biyayya ba, amma jin wai Hamma Lamiɗon ne mijin tuni lissafinta ya ƙwace. Ko burkutu ta sha ba za ta iya doguwar magana da shi ba, in tunanin ta ma ya kawo mata sunan shi ji take yi kamar ta haukace. Innalillahi ta shiga ta uku ta lalace. Ita Ummu Salama ina ita ina Hamma Lamiɗo?

Ƙarshen littafi na ɗaya.

Akwai sauran tafiya, mun gama shimfiÉ—a yanzu muka kwarari doguwar tafiya. Ga dai LamiÉ—o ga Ummu Salma, mu je zuwa domin ganin yadda tafiyar za ta kai su.
Ku biya kuÉ—in karatun ku na La shakka babu nadama a cikin wannan tafiyar in sha Allahu.

*littafin Fargar Jaji na kuÉ—i ne a manhajar Telegram akan #1k. Tura KuÉ—in karatun ku ta wannan acct É—in 9069067488 JAMILA UMAR OPAY sannan sai ku tura shaidar biya ta waÉ—anan lambobin kamar haka.*

09069067488.
08032773332.

*Yan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajojinku a cikin wannan kayattacen labarin za ku iya tuntuɓata kai tsaye ta wannan lambar 09069067488 Na gode.*

*Janafty*
*27/04/2026*
Chapter 92 · 0% Book details