← Book details Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 92

Sashe 48

Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bai amince da komawa Daura ba sai da Ammah ta saka baki sannan ya koma Daura da zama a cikin Masaurata. Gari ya ɗauka domin waɗanda suka san da auran aminttun sarkin a wancan zamanin duk sun rasu sai mutum ɗaya ne ya rage a lokacin shi ne ya ba da shaidan Lamiɗo ɗan Masaurata ne balle ma kamanninsa da kowa ya gani ba sai ya yi magana ba, kamar Maimartaba yana tashen ƙuruciyarsa.

Bai daɗe da komawa Daura ba ya kama aiki gadan gadan da kamfanin Nigerian Port Authority a matsayin matuƙin jirginsu Captain bayan ya karɓi licence ɗinsa a matsayin pilot matuƙin jirgin ruwa By Nigerian Maritime Administration and Safety Agency (NIMASA)
Sai ya zamana baya samun zama sosai amma duk salla a Daura yake yin ta saboda za a gudanar da hawan salla tare da shi, kuma uwa uba yana da wasu yan'uwan da suke uba É—aya duk da ba su tashi a gida É—aya ba amma dai yana son su tunda su É—in jininsa ne.

Sai da ya auri ƴar Sarkin Kano sannan aka na ɗa shi Yariman Daura mai jiran gado duk da abubuwan sarauta ba su dame shi ba amma Muhammad Lamiɗo mutum ne nagari mai kirki kamar mahaifinsa. In dai ya na Daura talakawa da matasa na cikin alheri yana da alheri sannan ga ƙokarin samo ma matasa ayyukan yi.
Duk da shi miskili ne mara sakewa amma kuma mutanen garin Daura suna son shi saboda yana da kyautawa. In dai ya zo Daura to tare da shi ake zaman Fada a dole sai an koya masa abubuwan da suka shafi sarauta, abin da ba su sani ba shi bai taɓa sha'awar Sarauta duk da ko bai faɗa ba mutane da dama in suka gan shi da yanayin shi sai sun ce yana da jinin sarauta a jikin shi. Sannan in dai ya zauna da Maimartaba to ba su da hira sai hiran sarauta da tarihin masaurata da sarakunan da suka gabata. Haka ma Hajiya Zaliha ko da wani lokaci suka haɗu girman matsayin shi take nuna masa, da lissafinta na cewa wata rana shi ne a kan ƙaragan da mahaifinsa ke zaune yanzu. Shi sai dai ya ji su kawai kwata-kwata baya son mulki kuma ba zai taɓa sha'awa ba, saboda mulki hayaniya ne da damuwa tare da nauyi shi kuma ba ya so.
Hajiya Zaliha(Mahma) tana son Lamiɗo sosai saboda ba ta taɓa haihuwa ba shima yana son ta ko domin yadda take ji da shi ya sakata cikin jerin mata masu muhimmanci a rayuwarsa.

Fulanin Daura da ta tsufa yanzu ba ta da abin so kamar LamiÉ—o tana ji da shi kamar tsoka É—aya a miya. Shi ko ba ya wani ta kanta amma dai yana zuwa wajenta ya zauna na wani lokaci in dai ya zo garin.

Itama in ya je wajenta haka za ta zaunar da shi tana ta yi masa hira da labarin Masarautar Daura har ya gaji da ji ya haddace. Da yana jin haushin ta akan abin da ya faru amma daga baya ya daina tun da ita kanta Mami ta na can tana wata sabuwar rayuwar da shi da Ahalin na shi duk ba sa gabanta shi ya sa ya bar komai ya wuce ya kuma rumgumi ahalinsa. Ba a sauya ma tuwo suna duk a je a dawo abin faharin shi da asalin shi garin Daura ne.

Dalilin abin da Fulani Daura ta aikata ne daga baya Fargar Jaji ya kamata ta yi nadama. Saboda haka ya sa duk wani abu da zai faru a Masarautan Daura za a sanar ma da Ammah da Baffa saboda LamiÉ—o zumunci mai karfi ne a tsakanin Ammah da Gimbiya Shahida uwar gidan Maimartaba da man duka sauran matan na shi.
Sannan Fulanin Daura yadda ta dauki Lamiɗo da muhimmanci haka ta dauƙi Ammah da Baffa. Mami ce tun da ta ce ba ta da alaqa da su haka ɗin take ba ta ma nuna ma ita ta haifi Lamiɗo ballanta wani abu ya sa a sako ta a ciki. Shima kuma ba ya taɓa nuna Mami a matsayin mahaifiyarsa Ammah ce uwar sa har gaban abada.

Lamiɗo kawai suka sani da marikan shi da suke tamkar iyayen shi, shima Lamiɗon ba ya ɗaukan kowa a matsayin iyayen shi sai Ammah da Baffa Mami dai kawai sunan ta uwa ne amma babu shaƙuwar ɗa da uwa a tsakanin su. Dalilin Lamiɗo har Hajji Masarauta ta kai Ammah da Baffa suka je suka sauke farali.

***

Ummu Salma ta kasance a wajen Ammah da Baffa a matsayin yar Auta. Ta taso cikin zaratan yayyen ta maza bakwai ko na ce takwas ga LamiÉ—o sannan ita mace, shi ya sa in dai ana maganar gata sai dai a yi kwataance da Ummu Salma.
 
Tun tasowar Ummu ta tsani karatun boko, domin kanta gaskiya ba ya ja, kusan na kusa da na ƙarshe take ɗaukowa a makaranta. Duk gori da zagin da su Hamma Kabiru ke yi mata bai sa ta gyara ba. Kuma makaranta mai tsada take yi ta Ahmadu Ribaɗo Collage a garin Yola. Amma sai a saran kuɗi ake yi kwaƙwalwar Ummi ba ta fahimtar komai har gwara ma bangaren islamiya shi ba laifi amma na bokon nan ne sai a hankali. Ita kawai karatun boko na wahalar da ita ne, duk ko yadda ba ta iya shan inuwa ɗaya da su Hamma Kabiru a cewar su daƙikiya ce ita kar  Hamma Lamiɗo  ya ji labari ita tun zaman shi a gidan su jininsu bai taɓa haɗuwa ba, wata maganar arziƙi ba ta taɓa haɗa su ba shi ba ya magana ma. In ka gan shi yana mgana to da Ammah ne ko Hamma Kabiru, tun tana yarinya ta san shi ba ɗan Ammah da Baffa ba ne saboda su suna kama da juna amma shi kamininsa na dabam ne, duk da ba ta son shi amma kuma akwai shakuwa a tsakaninta da mahaifiyar shi Mami, wacce ita ta yi renon ta bayan Ammah ta haifeta kafin auranta sannan bayan ta yi aure tana yawan zuwa Kaduna gidan Mami ta yi hutu, Mami mace ce mai fara'a sannan ita da mijinta suna ji da ita in suka je kasashen waje haka Mami za ta ciko mata jaka cike da kayan sawa na alfarma sai wanda ya gani. Ta sha zama ta yi ta mamakin yadda Mami ta iya haihuwan Hamma Lamiɗo ita ba ta ga ta in da ma suka haɗu ba, shi dabam ita dabam ita mai fara'a ce mai kirki da son Jama'a saɓanin Lamiɗo da ba shi da fara'a ba shi da son mutane sannan ba shi da kyakyawan mu'amala.

Ummu Salma ta taso ta ga Aminci tsakanin Amma da Ummin ikki shi ya sa itama Aminta ya haÉ—a ta da Aisha(BaÉ—É—o) a yayin da makaranta ya haÉ—a ta da Shamsiya(Bestie) su suna da son karatu kuma suna ganewa ba kamar ita ba tun da kuma ta fahimci ba ta gane karatu ta ce ba za ta ci a karatun boko ba, daga lokacin ta saka ma kanta tunanin daga sakandiri ba za ta cigaba da karatu ba.
Kuma haka aka yi ba yadda ba a yi ba amma Ummu Salma ta ce ta gama Baffa kuma da Ammah suka goya mata baya. Abu É—aya Ummu ta fi mayar da hankali shi ne girken-girken zamani, ta bakin Hamma Kabiru ya ce shi kaÉ—ai take ganewa.
Bayan ta gama sakandiri ta je Kaduna ta yi wattani huɗu a wajen Mami saboda tsangwaman su Hamma Kabiru akan sai ta cigaba da makaranta tun ballanta ganin kawayenta Baɗɗo da Shamsiya sun cigaba.

A can kaduna ta yi ta shiga catering School tana samun ƙwarewa  bayan ta dawo Jimeta ma ba ta zauna ba yayyenta sun gaji da magana sun ƙyale ta tun da Baffa yace boko ba dole ba ne, shi bai yi ba Ammah ma ba ta yi ba amma ba su mutu ba sun rayu saboda haka a bar Auta ta sarara. Kadunan ma da ta gudo saboda Mami ta fara zaunar da ita tana kwatance a kanta na amfanin karatu tunda ta ji haka tace za ta koma gida saboda Mami za ta iya jan Ra'ayin ta in kuma hakan ya faru ko ta shiga ba za ta iya ba gwara maganin ayi kar a fara.

Sai da ta yi zaman shekaru uku a gida ba makaranta ba ta da aiki sai girke girken zamani a gida duk abin da ta koya sai ta gwada shi tun ballantana abubuwan da take gani a waya tunda Mami ta siya mata waya Samsumg babba ta zamani, ko da yaushe tana cikin kwabin fulawa ita ce Cake ita ce donot wani abun ta yi ya yi daÉ—i wani kuma ya lalace Amma ta yi ta masifa Baffa ne mai supporting É—in ta.

Ummu Salma Bata taɓa tunanin za ta haɗu da Habib ba sai ga shi Allah ya haɗa su, wata rana ta dawo daga gidan su Baɗɗo ya biyo ta. Duk da a ganin farko ta ji ya yi mata ba ta ɗauka soyayyar da ya nema a wajenta zai kai su ga aure ba sai ga shi komai ya faru cikin lokaci. Ummu Salma da Habib sun yi soyayya kamar su lashe juna kafin aure ya nuna mata duk duniya bai so wata mace sama da ita ba, yayyenta suka yi ta mganganun cewa bai kamata a yi mata aure a lokacin ba, amma Baffa ya ce tunda ta samu miji kuma ya bincika yaron nagari ne zai aurar da Ummu sun yi adawa sosai amma kuma sun haƙura daga karshe. Cikin wattani biyar aka yi auran Ummu Salma da Habib auran ya zama abin kwatance kowa na ganin Ummu ta gama yin dace, ko bayan auran Habib ya nuna ma Duniya Ummu Salma ce duniyarsa, zaman lafiya da soyayya da ƙauna shi ya rike su a cikin wattani takwas ɗin da suka yi da aure. Duk masu adawan auren ta sun haƙura ganin tana zaune lafiya da mijinta.
Chapter 48 · 0% Book details