← Book details Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 92

Sashe 19

Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunanin ta guda ɗaya ne, yanzu duk wannan soyayya da ƙaunar da Habib ya nuna mata duk na ƙarya ce? In tana so ta aminta da mganar shi sai ta ji ta kasa ta fi gasgata da gaske Habib na son ta ɓacin rai ne ya sa ya faɗi wannan mganar, amma in yana son ta me ya sa ba ya son haɗa zuru'a da ita? Ta kwana a ƙasan cafet jingine da wardrope ba ta damu da komai ba, ita kawai fatan ta, ta buɗe ido ta ga komai a mafarki ne in kuma da gaske ne to ya kasance Habib ya zo ya ɗuka yana ba ta haƙuri ya ce duka mganganun da ya faɗa ba gaskiya ba ne, sai hakan bai faru ba har garin Allah ya waye ba ta sake ganin Habib ba, ba a ɗakin barcin su ya kwana ba sannan ko da ta rarrafa ta fita da safe ta iske shi ya bar gidan. Kukan da ta kwana yi ya taimaka wajen sake sakar mata zazzaɓi mai zafi, tana kwance tana hawaye in ta gaji ta yi kuka salla ne kawai ke ta yar da ita tun jiya ta kasa saka komai a cikin ta sai dare da ta ga za ta mutu ta sulala indomie da ruwan tea ta ci shima ɗin bai zauna ba ta amayar da shi, ruwan zafin ta sake sha shi ne ya samu zama a cikinta.

Yadda ya bar ta da ajiyan da daddare haka ya sake dawowa ya iske ta kwance a falo tana rawan sanyi. Yadda bai ce mata sannu ba itama ta yi alƙawarin ba za ta sake yi masa mgana ba sai shi da kan shi ya gano ya yi mata laifi ya ba ta haƙuri, tunanin Ummu-Salma Habib na son ta kuma zai dawo gare ta domin ya ba ta hakuri su daidaita kansu har a wannan lokacin yardan da ta yi ma Habib bai samu nakasu ba.

Tsayin kwana biyu ba ta da lafiya sannan ta warware tun da ta na shan pracetamol amai kuma da man laulayi ne ba shi da magani, a kuma kwanakin nan magana ta fatar baki ba ta sake haɗa Ummu da Habib ba, ya sauya akalan zaman su gabaɗaya. Ba ta sanin fitan shi ba ta sanin dawowar shi, sannan ya daina kwana ɗaki ɗaya da ita, ya koma yana kwana a ɗayan bedroom ɗin da daman na shi yawancin ma kayan sa suna ciki ne, kawai shi ya ce ya fi son na ta ne saboda yana da tiolet a cikin ɗakin saɓanin ɗayan sai an fito yana tsakiya shi ya raba bedrooms ɗin su guda biyu.

Da ta ji sauƙi ta fara yin abinci ta jera a saman dinning da beakfast kamar yadda ta saba sai dai yadda ta ijiye haka take ɗauka, sun kwashe sama da sati a haka tun Ummu na tunanin nadamar Habib har ta fara sarewa, ta dawo tana gaishe shi in sun haɗu da safe amma bai taɓa amsata ba, yadda ya ke yi ma a cikin gidan kamar bai taɓa sanin ta ba. Saboda in ya dawo ba ya neman ta ballanta ya san a wani hali take ciki, abin da ya faɗa ne yake aiwatar wa da man  ya ce sai ta yi nadaman ƙin bin umarninsa tun kuma tafiya ba ta yi nisa ba Ummu ta fara nadama sai dai ba ta jin za ta iya zubar da cikin jikinta, abin da ke damunta ta kasa jin haushi Habib a cikin zuciyarta da duk da irin yadda zaman auran su ya sauya. Ta kwana kuka ta yini kuka duk ta rame ta lalace ta kuma ta kasa tattauna mganar da kowa, tunanin ta da hangen ta Habib zai dawo ya ba ta hakuri ba za ta yi saurin fallasa sirrin auran ta ba, sannan tana son shi har gobe Habib na nan da wannan matsayin a cikin zuciyarta ta kasa jin haushin shi ko kaɗan a cikin zuciyarta.

Da a ce wani É—an'uwanta zai gan ta a yanayin da ta ke ciki sai ya yi gaggawan tambayan ta ko wani abu na damun ta ne, saboda yadda
Ummu-Salma ta koma, ta sake yin fari ta ɗashe ga shi tana laulayi mai zafi ba ta iya cin komai sai ruwan lipton in dai ta ci abinci sai ta amayar da shi, yini take yi a kwance kamar ruwa amma babu ruwan Habib, tana jin shi zai shigo da daddare sosai tun da zaman su ya sauya sai ya kai sha ɗaya na dare a waje bai dawo ba in ko ya dawo yana ɗayan ɗakin sai dai ta ji shi yana ta waya ba kuma za ta iya gane da wanda yake yin wayar ba. Wani lokacin sai in ta ji zai fita ne da sassafe sai ta rarrafa ta fita falo in ya fito ta gaishe shi amma bai taɓa amsawa ba har ya saka kai ya fita ba zai sake kallon ta ba.

Duniyar duk ta yi mata ƙunci ba abin da ke yi mata daɗi, kowa sai ya ji ta ɗif kamar ba ta nan Ammah duk rashin nuna kulawanta ga Ummu sai da ta kira ta, an ci sa'a ma ranar wayar na kusa da ita domin kwana biyu nan sai a hankali ko iya amfani da wayar ba ta yi saboda kasala da zazzaɓin da ta ke fama da shi.

"Ummu kwana biyu daga ke har megidan na ki mun ji ku shuru ina fatan dai kuna lafiya?

Haka Ammah ta faɗa bayan Ummu ta ɗaga wayar. Lokacin da ta amsa mata da lafiya sai da ta danne bakin ta saboda kuka take yi hawaye sun kece mata amma ta kasa iya faɗa ma Ammah wani abu. Tunanin ta Habib zai dawo zai yi nadama sannan zaman auren su zai gyaru bai kamata ta yi gaggawan fallasa sirrin gidan auran ta ba shi ya sa ta daure ta ce ma Ammah zazzaɓi suka yi ta yi ita da Habib kwana biyu shi ya sa a ka ji su shuru amma duk sun samu sauƙi.
Ammah ta yi fatan ƙara samun sauƙin su sannan suka yi sallama to shi ma Baffa haka ya kira ta yana tambayan ko tana lafiya.

"Lafiya ta ƙalau Baffa."

Ta ba shi amsa da fillanci, shima ba ta faɗa masa komai ba sannan ba ta bar shi ya fahimci wani abu ba. Mami ma da ta ji ta shuru sai da ta kira ta, itama ce ma ta ta yi zazzaɓi suka yi ta fama da shi a kwana biyu nan. Baɗɗo ma sai da ta kira ta, ta ce a online kwana biyu ba ta ga ta hau ba itama dai ƙaryan ta yi mata na zazzaɓin sai ta ce satin nan za su gama jarabawa za ta zo ta duba ta daga haka suka rabu. Abin da ya ba ta mamaki yadda Bestie ba ta kira ta ba sai da ta kunna Data sai ta ga ta yi mata mgana ta faɗa mata za ta kashe wayarta sai dai lokaci bayan lokaci za ta dinga kunnawa har su gama jarabawa, shi ya sa ba ta san ta yi kwana biyu ba ta online ba. Sannan dalilin da ya sa ba ta kira ta ba kenan.

Sun shafe wajen sati uku a haka ita da Habib ba abin da ya canza, ba ta sake tsinkewa da lamarin Habib ba sai da ta kama shi yana saka mata wani abu a cikin zoɓon da ke cikin frezer ɗin ta. Abin da bai sani ba ita yanzu ko ruwa ba ta sha ya zauna mata ballanta wani zoɓo tun wanda ta haɗa ne kafin zaman su ya lalace ta ma manta da shi. Da daddare cikin ta na ta juya mata saboda yunwa domin yini ta yi ba ta ci abinci ba, ba ta san shigowar Habib gidan ba tun da ta samu barci ya ɗauke ta sai a lokacin ta farka da agogon wayarta ta yi amfani ta duba lokaci. Ƙarfe 2:43am na dare, tana fitowa sai ta ga kitchen da ɗan hasken fitila ita da farko ma ta tsorata shi ya sa ta yi tsam, ta fara takawa salaf-salaf ta leƙa kitchen ɗin tun da ƙofar a buɗe ne daidai ya na saka wani abu a cikin zoɓon da ba za ta iya tantance mene ne ba, amma koma mene ne ba abu ba ne mai kyau tana da tabbacin haka, ba abin da zai ta da mutum cikin dare yana zuba wani abu a cikin abin sha kuma ace alheri ne.

Ba ta bari ya lura da ita ba bakin ta alaikum ta koma ɗakinta ta faɗa kan gado ta na mai fashewa da kuka matsananci, kuka take yi kamar ranta zai fita ta yi ta tunanin mene ne dalilin Habib na aikata haka? Sai wata zuciyar ta bata amsa da cikin jikin ki, tabbas ko ta amince ko kar ta amince cikin jikin ta ne Habib ya yi alwashin sai ya fidda shi ko ta ƙarfin tsiya.
Ita kuma yanzu ta ji ma tana sake ƙaunar cikin ta, ta yi alƙawarin komai zai same ta sai ta kare shi ta zame masa garkuwan yadda Habib bai isa ya matso kusa da shi ba.

washegari Habib na fita ta je ta kwarara wannan zoɓon a tiolet ta zuba masa ruwa ya wuce. In da ta sake tabbatar da zargin ta a daran da ya dawo har ɗakin sai da ya leƙa ta ya ɗauka zai gan ta a galabai ce wata ƙila cikin ya zube amma bai fahimci komai ba a fusace ya buga mata ƙofa ya fice ya bar Ummu da hawaye a fili tana tambayan kanta.

"Me ya sa Habib? Me ya sa haka?
Chapter 19 · 0% Book details