← Book details Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 92

Sashe 68

Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To ai ban ga laifin Ammah ba, itama dai Bestie ba ta yi nagana mai kyau ba duk wannan abin da Habib ya yi miki sai ta ce laifin ki ne?  Haba ko Habib ta sani ba ke ba ai ta faɗi gaskiya ballanta ta sanadinki ta san Habib ɗin, ai wallahi Ammah ta yi mini daidai ko ni ce a wajen haka zan yi mata."

Ummu ta kalleta kafin ta ce" Ku yi ma Bestie uziri kin san yanayinta da gidan su."
Baɗɗo ta taɓe baki kafin ta ce" Haba koma dai mene ai ke tata ce, in ba ta tausaya miki ta ba ki baki kan abin da ya same ki ba, bai kamata ta zauna a fuskarki tana cewa ke ce da laifi ba, kuma har tana fadin cewa ba za ki samu kamar Habib ba ni wallahi kalamanta ma sun saka ta l zube mini a idanuwana Habib ɗin banza? Wallahi sai kin samu wanda ya fi shi kuma ta jira ta sha kallo."

Ummu dai ba ta kara magana ba ganin BaÉ—É—o ta É—au zafi ta samu suka yi sallama ta tafi, ita kuma ta dawo cikin gida. Itama fa kalaman Shamsiyar sun ba ta mamaki ita ce ta farko da ta fara cewa Habib ba shi da laifi. Sannan ta yi mamakin rashin dawowarta sannan ko a waya ba ta kirata ba, ai tana da lambar Ammah.
amma ba ta kawo komai a ranta ba, Ammah na É—akin Baffa ta É—au wayarta ta kira ta har sau biyu ba ta É—auka ba, sai daga baya ta kirata tana ce mata ba ta gida ne da yake ta koma makaranta.
Sun É—an jima suna hira Shamsiya ta bata hakuri kan cewa komawarta makaranta ne ya zo a gaggauce shi ya sa ba ta dawo ba. Amma kafin su yi sallama sai da ta yi ma Ummu tambaya.

"Yanzu Bestie haka za ki yi renon cikin nan ki haife shi a ƙasƙantan ce! Alhalin uban cikin ya ce ba ya so?

"In shi ba ya so ai ni ina so. Kuma da ikon Allah zan haifi abin da ke cikina da goyon bayan iyayena da dangina"
Ummu ta bata amsa muryanta a raunane domin kuka na shirin ƙwace mata..

"TabÉ—ijam. To Allah ya kyauta."

Ta faÉ—a cikin ganin karfin halin su tunda wanda ya yi cikin nan ya ce ba ya so to me kuma za a jira da shi? Kafin su yi sallama ma wayar ta katse kamar katin ta ne ya kare. Ranar kamar an yi ma Ummu Salma fami kan damuwarta ta kusa raba dare tana koke-koke ballanta da Ammah ba a wajenta ta kwana ba, ganin ta yi kuka ba zai fissheta ba ya sa ta tashi ta je ta É—auro alwala ta fara salla daga zaune domin jiri take gani addu'a take yi Allah ya cire mata soyayyar Habib a cikin zuciyanta ko za ta samu salama.

Ba ta samu barci ba sai da ta yi sallar asuba shima ba daÉ—ewa ta tashi da ciwon kai da jiri, tana kuma karyawa sai amai kamar za ta yi amayar da hanjin cikinta, sannan da ta shiga tiolet sai ta ga jini a ruÉ—e ta fito ta faÉ—a ma Ummin ikki da ta zo gidan tarban su Hamma LamiÉ—o. Baffa baya nan ya shiga cikin gari tare da Abdullahi can harkokinsu.
Sai kawai Ammah ta ce Ummin ikki ta raka Ummu zuwa asibiti, tare suka tafi har da Adda Suwaiba da tun safe suna gidan.

****

Ƙarfe biyu saura na rana Hamma Abdullahi ya je filin sauka da tashin jirage na YOLA INTERNATIONAL AIRPORT JIMETA. da kuma motar Hamma Lamiɗo wata hilux ƙiran Toyota da alamu dai Hamma Lamiɗo na son mu'amala da motocin kamfanin Toyota.

Lokacin da suka iso gidan su Ummu ba su daɗe da dawowa daga asibiti ba, cikinta ya shiga wattani huɗu amma likita ya ce ya yi rauni ta riƙa samin hutu sannan jininta ya yi sama again, ba kuma ta samun isasshen barci. Amma dai ya rubuta magunguna sannan ya ce nan da sati uku za ta fara zuwa awo, suna son ta samu hutu sosai sannan ta riƙa cin abubuwan da za su gina mata jiki, amai kuma da kasala laulayi ne za ta bari in cikin ta ya yi girma watakila ma sai ta haihu ya danganta da yanayin ta.

Ummu Salma na kwance a cikin ɗakinta lamo akan gado tana sauke ajiyar zuciya tana ji daga falon Ammah ana ta yi ma baƙi maraba. Har da Adda Ummu Sulaim, duk tare suka taimaka aka gyara gidan girki dai Ammah ta yi a cewarta Lamiɗo na ganewa in ba ita ta yi mishi abinci ba.

Ga muroyoyin su nan har na Ammah amma ko tarin Hamma LamiÉ—o ba ta juyo ba, kuma yana falon tunda ga Ammah can na ta masa maraba kamar ta goyasa.
Da ga cikin É—akin dai ta ji na matarsa cikin yauki da yanga kamar yadda ta saba tana gaishe da Ammah da su Ummin ikki.

Barci ne ya kwashe ta daga nan ba ta farka ba sai wajen biyar saura shima ɗin ta tashi ne don kanta, Adda Suwaiba ta gani a ɗakin tana zaune tana ba ma ƙaramar yarinyar ta Mimi mama.

"Adda an yi salla ne?
"Tun É—azu. Biyar ma ta kusa."
Ta bata amsa.
Sai ta miƙe da sauri tana faɗin.
"Shi ne ba wanda ya tashe ni?

"Ummi ta ce a kyale ki likita ya ce ki huta sosai."
Ba ta sake magana ba ta shiga tiolet ta yo alwala ta zo ta yi salla. An riga an shigo mata da abincinta ta ja ta zuba tuwo É—aya a filet ta fara ci, miyar ma daÉ—inta na musamman ne saboda zuwan Hamma LamiÉ—o.
Tana jiyo muryan Hamma Abdullahi da na Hamma Abdulrrahman, har da na Ammah da Baffa amma ba ta jiyo na Hamma LamiÉ—o ba.
Sai ta yi tunanin ko har sun karisa gidan na su ne?

"Adda su Hamma LamiÉ—o sun tafi gidan su ne?

"Aa ba su tafi ba, ga shi can shi a falo suna hira da su Baban Mimi a falo, har da Baffa ma."

Ummu ta yi shuru ba ta sake magana ba.

"Balkisun kuma tana É—akin Ammah tare da hadiman ta da suka zo tare."
Ummu ta É—an gyaÉ—a kai, da man in dai za ta zo, tana tare da hadimanta.

Nan Adda Suwaiba ta fita ta barta bayan ta gama cin abinci tana son shan ruwa amma ba za ta iya fita falo ba tana jin kunya.
Sai kawai ta yi zaman ta.
Har fa mangariba duka suna gidan ba su tafi ba. Ummin ikki ce kawai ta tafi gida.
Bayan mazan duk sun fita sallan magariba itama ta idar kenan Ammah ta leƙo ta ganta saman darduma tana lazimi.

"Ke kam ba ki ji zuwan yayanki tun É—azu ba ne? Ko da yake kina ta barci."

Kafin Ummu ta yi magana Ammah ta riga ta da cewa.
"To taso ki gaishe da matar yayan naki, kafin su dawo daga masallaci."
Ba ta isa ta zille ba domin Ammah ba a yi mata wasa.
Dole ta miƙe ta bi bayanta zuwa ɗakin Ammah in da ta iske Balkisu da ya'yanta tare da Sabuwa da Anitha
Da ta gaisheta ta amsa tana kallonta.

"Ba ki da lafiya ne?
Ta faÉ—a cikin yanayin maganarta.
Ta kasa mgana, domin ba ta san me za ta ce ba.
"Uhm ba ta da lafiya ai tana ma gida ne sun rabu da mijin"
Balkisu ta yi salati cikin yanayinta ta ce. "Subhanallahi."
Nan fa Ammah ta gyara zama ta shiga ba ta labarin abin da ya faru.

Ummu ta kasa zama ganin har Sabuwa na yi mata wani kallo, Anitha ma ta kafe ta da kallo kamar ta san me ake faɗa. Sai kawai ta tashi za ta fita Beena ta biyo ta a baya tana magana ba ma ta jin me take faɗa, ba shaƙuwa da yaran ta yi ba ko a baya suka zo gidan ba ta ta kan su.

Tana fitowa daidai su Hamma Abdulrahaman suna shigowa falon Ammah.
Sun riga sun ganta ba ta da yadda za ta yi, ga Beena ta rike mata gefen hijabi tana fadin egg za ta ci.
Kanta na ƙasa ta ma kasa ɗagowa tsabar kunya da nauyi.

"Ummu kin ta shi? Na leƙo ɗazu aka ce kina barci. Sannu ya jikin?
Hamma Abdullahi ya faÉ—a
"Ba ta da lafiya ne?
Hamma Abdulrrahaman ya faÉ—a yana kallon ta.

"E sai da suka je asibiti da Ummin ikki."

"Allah ya sauwake. Sannu "
Shima ya faÉ—a yana kallonta.
"Papa."
Beena ta faÉ—a ganin babanta sai kuma ta saki Ummu ta nufe sa ta faÉ—a jikinsa.
Kamar tsautsayi Ummu ta É—ago kanta karaf sai a idanuwan Hamma LamiÉ—o da yake zaune saman kujeran zaman mutum biyu da ke falon Ammah.

*Janafty*
*FARGAR JAJI.*

*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:JamilaUmarJanafty*

"To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude"

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/L6zUax648eTERbvw8Bqyie?mode=gi_t

*17*

Sanye yake da wani baƙin yadi mara kauri domin in ka ƙura ido sosai za ka iya hango farar vest ɗin dake jikin shi ta ciki.
Ɗinkin zamani ne amma rigar ta kai har wajen gwiwan ƙafafunsa, kansa da hula amma saboda ya tara suma sai hulan ta samu matsugguni a saman gashin kan nashi, sannan gefe da gefen fuskar shi sumar ta ɗan bayyana.

Ummu ta yi saurin kauda kanta, shi da man bai nuna ma ya ganta ba, Beena ce ke yi masa raÉ—a a kunne yana sauraranta.
Ummu ta so ta yi sauri ta koma É—akinta ne amma ina ta juya za ta shige kenan kawai ta ji Hamma Abdullahi ya kira ta.

"Ummu"
Ta juyo tana kallon shi.

"Ba ki ga LamiÉ—o ba ne? Na ji ba ki gaishe shi ba ne"

Ummu ta runtse ido tana cije baki Hamma Abdullahi ya kwafsa mata, ita fa ba ta so ma ya ganta ba, ballatana ma har gaisuwa ya haÉ—a su ita a fatan ta ma har su gama zaman garin su koma ma ba za su haÉ—u ba sai ga shi tun a ranar farko Allah bai cika mata wannan manufar ba
Chapter 68 · 0% Book details