← Book details Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 92

Sashe 60

Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallon kansa kawai yake yi a madubi yana mirmishi shi kaɗai saboda yau ranar ta musamman ce a gare shi da abar ƙaunarsa. Yau ne rana ta farko da za ta gabatar da shi a wajen mahaifinta a matsayin wanda take so kuma take mafarkin aura. Gabaɗaya jin sa yake kamar yana yawo a saman gajimare saboda tsabar farinciki. Ya saka kaya sama da kala goma ba su dace da ranar yau ba, ga su nan duk ya zube su a saman gadon dakyar ya samu waɗanan na jikinsa suka dace da yanayin yau ɗin.

  Agogon fata baki ya saka a tsitsiyan hannunshi na hagu yana sake kallon kanshi a madubi yana sake yin sakin ɗan mirmishi. Ya ɗauko wani bakin booth ɗin takalmi yana sakawa kenan aka kira wayarsa tun kafin ya duba ya san ita ce domin sun yi magana da ita bayan ya fito wanka ya tabbatar mata da mintina goma zai gama shiryawa ya fito.
Sai da ya gama saka takalmin sannan ya É—auki wayar dake gaban madubin farinciki ya sake dabaibaye shi ganin ita ce ta kira shi.

"Gani nan zuwa Sweety."

Ya faÉ—a cikin wani amo bayan ya É—aga kiran.

"Kar ka bar ni na saƙe wajen jiran ka Habib."

Daga can bangaren ta faɗa cikin muryan shagwaɓa.

"Gani nan zuwa In sha Allahu."

Daga haka suka yi sallama, suna katse wayar ya turata cikin aljihun wandonsa tare da wallet ɗinsa bai tsaya kwashe kayan da ya watsar a tsakiyar ɗakin ba ya suri key ɗin motar shi da na ɗakin ya fice bayan ya rufe ƙofar ya tura komai cikin aljihun wandon sa ya sauka ƙasa zuwa haraban hotel ɗin suna ta gaisawa da ma'aikatan wajen a wattani biyun da ya kwashe a hotel ɗin ya saba da duka ma'aikatan wajen ba laifi, Tun ballanta ƴan ƙananun kyatttukan da yake yi musu, yau ma saboda yau ɗin rana ce ta musamman a wajen shi. motarsa ya shiga da yau ya kaita wanki ta yi fess yadda motar take  fess shima haka yake fes, ya fiddo kuɗin sabbi yan ɗari biyar biyar ya kira wani ma'aikacin hotel ɗin yana daga cikin masu kula da tsaftan ɗakunan Hotel ɗin sunan su ɗaya shima Habibu sunan shi, kuma in dai ya ga Habib ya yi ta masa kirari kenan shi ya sa tasu ta zo ɗaya.

KuÉ—in sun kai 20k ya ba ma Habibu ya ce ya raba shi da sauran ma'aikatan gabaÉ—aya.
Har ƙasa ya duka yana godiya lokaci ɗaya yana masa kirarin da ya saba.

"Allah ya taimake ka ranka ya daɗe Allah ya ƙara arziƙi da wadata."

Habib ya yi dariyan nishaÉ—i kafin ya ce" Amin Habibu na gode da addu'arka kamar ka san yau rana ce ta musamman a waje na."
"Allah ya kara maka farinciki da wadata Megida."
Ya riƙa amsawa da Amin kafin ya rufo motar ya daidaita zaman shi sannan ya tayar da motar ya yi riverse ya yi hon megadi ya buɗe masa get ya fita, yana tafe yana jin nishaɗi har redion motar ya kunna da wakar Auta waziri yana tafe yana kaɗa kai kamar wani kadangare.

Tun a daran ranar da ya saki Ummu Salma bai yi barci ba sai da ya gama haɗa dukkan abin da yasan mallakan shi ne gari na wayewa karfe shidda na safe ya kwashe komai zuwa mota ya bar gidan. Yadda suka rabu haka yake so alaƙarsu ta ƙare na har abada.

Hotel ya je ya kama ya saka kayan shi a ciki, tunda gidansu yanzu ba shi da mazauni kuma ba shi da in da zai je ya zauna, gidanshi da yake ginawa ba a gama ba, gidan da Ummu Salma ta yi ta mafarkin shi a matsayin ita ce za ta shige shi abin da ba ta sani ba bai kafa ginin gidan nan da sunan ta ba sannan zanen gidan ma ba zaɓin ta ba ne na masoyiyarsa ne da suka shirya sabuwar rayuwa tare, an kusa gama ginin gidan tunda yanzu tayels ake sakawa na ɗakuna da tiolets da an gama za a yi filista da fenti shike nan shi kuma a yadda yake so bikin shi kar ya wuce wata biyu saboda ya ƙosa ya mallaki masoyiyarsa sannan yana son ya samu natsuwa. Tunda har yau za ta gabatar da shi ga mahaifinta an gama mgana, da man a cikin wata ɗaya ta bayyana shi a wajen iyayenta da y'anuwanta mata a matsayin wanda take so yana zuwa gidan su zan ce yau ne za su haɗu da mahaifinta. Jin sa yake yi kamar sabon haihuwa saboda farinciki kamar bai taɓa aure ba. To kamar bai taɓa ba ne domin Ummu Salma amfani ta yi masa kuma tunda ta gama amfaninta ya fitar da ita daga rayuwarsa, sai yanzu yake jin kansa sakayau kamar bai da wata damuwa. Duk da ya ɗan fuskanci ɓacin rai daga wajen Gwaggo da Abba Alhaji Sheriff amma duk ya jure.

Gwaggo haka ta yi ta masa faɗa bayan an ɗan lafa da faruwan lamarin ya je gidan, ba shi da masaniya amma ya san labarin rabuwansa da Ummu Salma zai je musu kuma zargin shi ya tabbata. Mahaifinsa dake kwance haka ya riƙa son ya yi magana da shi amma ya kasa sai kuka hawaye na ziraro masa ta gefe da gefen idanuwansa.

Ransa ya ɓaci ya yi baƙin ciki sannan ya sake jin tsanar Ummu Salma a cikin zuciyarsa. Sanadiyarta iyayensa sun yi fushi da shi. Gwaggo ma sai da ta yi kwanaki ba ta amsa gaisuwarsa har ƴan'uwansa mata wasu sun nuna ba su ji daɗin abin da ya aikata ba shi kuma sai ya ce ai ita ce ta ci ƙwalan shi ta ce in ya cika haihuwan uwarsa da ubansa ya saketa shi ne ya sake ta. Wasu dai sun yarda wasu kuma ba su aminta da maganganunsa ba, kamar Gwaggo da jinsa kawai take yi ta san ya faɗa ne domin ya kare kansa. Haka ya yi ta zuwa Gidan Alhaji Sheriff kusan sau uku amma ba ya ganin shi ya ƙi bari ma su haɗu kwata-kwata, amma duk da haka bai haƙura ba sai ya bi ta hannun Baba Usman da lallashi da daɗin baki ya samu shi ya saurare shi, duk ya ɓata ma Ummu Salma suna a idanuwansa da cewa ba ta da tarbiya rashin kunya take yi masa shi ya sa ya sake ta kuma ma ita ce ta neme sakin, Baba Usman ne ya shiga tsakiya ya sulhutansu da Alhaji Sheriff ya kuma haɗa su waje ɗaya suka yi magana. Habib ya duka yana ta bashi haƙuri Baba Usman na kora wajibin cewa yarinyar ce ashe ta ce sai ya sake ta shi dai Alhaji Sheriff jin su kawai yake yi yasan ƙarya Habibu yake yi ya dai faɗa ne domin kawai ya samu hanyar kare kan shi.

"Koma mene ne wannan ya zama tarihi tunda ya sake ta ta koma gidansu magana ta kare. Habibu kai ba yaro ba ne daidai gwargwado kana da ilimin ka, ka san abu mai kyau da aka sin shi. To ka sani in har kai ne ka yi zalunci Allah ba zai barka ba, in ma ita ce ta zalunce ka duk Ubangiji na gani kuma zai yi ma duk wanda aka zalunta sakayya"

Abin da ya faɗa masa kenan a lokacin da ya sake rankwafa yana sake bashi haƙuri sai ya ɗaga masa hannu yana sake faɗin.
"Ni fa ba ka yi mini komai ba Habibu. Ka je kawai Allah ya kyauta na gaba."
Duk da haka bai haƙura ba yana zuwa gidan shi sannan yana kiran shi a waya har dai ya samu ya ɗan sauko daga fushin da yake yi da shi, shi da man burin shi kenan saboda nan da lokaci kaɗan amfanin su zai ta shi kuma in babu su ba zai samu cikar burin shi ba shi ya sa bai gaji ba sannan bai sare ba, Baba Usman ma duk ya siye shi da kuɗi sannan haka ya yi siyayyan kayan abinci ya kai masa, gidansu ma duk ya kashe bakin su da kuɗi suma ɗin kayan abinci ya siya musu duk da daman ya saba yi, yan'uwansa mata kuma duk ya kashe bakin su da kyauttuka har Gwaggo ma bakin ta ya yi shuru shike nan babin Ummu Salma ya kare a gidansu da zuru'an su gabaɗaya yanzu ne zai sake buɗe ma rayuwarsa wani sabon shafi.

Kai tsaye anguwar Barraks road ya nufa, ya yi parking ɗin motarsa a wani babban gidan bene mai makeken bakin get. Bai yi hon ba sai da ta ya kira ta ya ce ga shi nan a ƙofar gida sai ta ce kawai ya shigo gata nan fitowa. Sai a lokacin ya yi hon megadi ya leƙo shi kuma sai ya zuge gilsshin bangaren  da yake zaune  ya gane shi baƙon gidan ne tunda yana zuwa kuma ya san shi, har ma wani lokacin yana yi masa kyauta

"Alhaji barka da zuwa."
Bafullatanin maigadin ya faÉ—a da hausar sa irin ta fulani.

"Yauwa."

Habib ya faÉ—a yana mirmishi, get É—in ya ruga ya buÉ—e masa shi kuma ya sulala motar tasa zuwa cikin haraban gidan da ga motoci nan guda uku a haraban gidan, alamun megidan yana ciki tunda yaran gidan ba sa tuka kansu a mota sai in kin yi aure baban zai ba ki mota amma in dai kina gida direba ne zai kai ki duk in da za ki je, kuma ya koma ya dawo da ke.

Habib ya daɗe yana tunanin kamar gidan da ya zo sun fi ƙarfin shi amma in ya tuna yadda soyayyar su ta fara sai ya ji ya samu ƙarfin gwiwa da yadda abar kaunarsa ta ba shi tabbacin duk abin da suke so shi mahaifinsu ke so, kuma shi ya yarda da kan shi duk da shi ɗan talakawa ne amma yana da ilimi da dukkan nagartan da duk in da ya je za a ba shi aure.

Bayan ya daidaita motarsa a haraban gidan ya É—au wayarsa ya yi kira.

"Gani na iso haraba."
Chapter 60 · 0% Book details