Sashe 9
Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"Mu shiga Baby, ba fa Ammah ba ce."
Ya faÉ—a yana dariya Ummu ta girgiza kai kafin ta ce" Ba ka san su ba ne, daga ita har Amma halin su É—aya."
Ya dage sai da suka shiga cikin gida, matan baban su BaÉ—É—o Biyu Ummin ikki ce uwargida sai Anty Saratu, suna tsakar gida ne suna hira lokacin da suka shigo BaÉ—É—o da Ummu Habib kuma ya tsaya a sauro kafin su yi masa iso.
"Ke yanzu Ummu kin kyauta ma kan ki kenan?
Da tsohon daren nan?
Ummin ikki ta fara faɗan ta, itama kamar Amma ne ba su gani su ƙyale.
"Ummi BaÉ—É—o ce ta yi dare Habib ya ce ta jira mu kawo ta gida."
"Habib ya ce ko ku kuka ce?
Umma ikki ta faÉ—a tana hararan su, BaÉ—do ta kwaso rantsuwa tana faÉ—in" Wallahi Ummi shi ya ce na jira shi."
Wata uwar harara ta maka musu, atare Ummu da Baɗɗo suka saka dariya suna kumshe bakin su.
"Ja'iran yara kawai, to ina shi Habibun? Waje ku ka baro shi?
Jin haka yasa Ummu ta miƙe tana faɗin" Bari na ce ya shigo."
Ummin Ikki ta yi ƙaramin tsaki kafin ta ce" Ba ni hijabi na"
Hijabin BaÉ—É—o ta É—auko mata a cikin É—aki ta saka ita kuma Anty Saratu da man ta shiga ciki tun bayan da suka gaisa da Ummu da farko.
Habib har ƙasa ya duka ya gaishe da Ummin ikki kamar yadda ya saba ta amsa mishi cikin sakewa, ba su daɗe ba suka yi musu Baɗɗo ta raka su har bakin gida nan suka ci karo da Baban su Baɗɗo ya dawo shima faɗan ya fara yi da ya gan su.
"Kai Habibu ba za ka daina biye ma shirmanmun yaran nan kuna yawan dare ba ko?
Ya faÉ—a ba wasa a muryan shi Habib a ka bari da kare su Ummu.
"To ku yi sauri ku isa gida garin da kamar hadari. Allah ya yi muku albarka."
Suka amsa da Amin ya shiga gida, su kuma suka shige motar Habib ta kamfanin Toyata, Baɗɗo na ɗaga musu hannu har suka ɓace daga layin.
*****
Ammah da tawagarta ranar litini da safe jirginsu ya É—aga zuwa katsina. Ummu ma ba ta san tafiyarsu ba sai da ta ga Hamma Sadam na posting É—in hotunan shi a status a cikin jirgi a first class, shi ne ta tambaye shi ya ce tun safe suna Daura.
"Eyye Baffa ne ya biya muku kuÉ—in jirgin?
"Wani Baffa, ai wani kaya sai amale Hamma LamiÉ—o ne, na ke faÉ—a miki a rukunin masu kuÉ—i muka je katsina. A VIP muka kame, muna sauka kuma ga motocin masarauta da dogarai da yan sanda suna jiran saukan mu, suka kwashe mu da jerin convoy motoci hadaÉ—É—u, sai ga mu dai a cikin Masarautan Daura."
Duk Hamma Saddam ne ya zayyano mata wannan labarin, da man shi nan ya fi ƙwarewa.
"Ba shakka. To ina su Ammah yanzu?
"Suna can cikin gida ni ina bangaren Hamma Lamiɗo ne nan ake sauke ni, Ummu kin ga masarautar Daura? Kin ga shashen Hamma Lamiɗo? Na rantse da girman Allah ban taɓa ganin tsaruwa da kyau na masarauta kamar yadda na ga tsaruwa irin ta masarautar Daura ba"
"Uhm. Na gani."
Ta tura masa ganin yana neman ya manta itama fa ta je ta ga komai ba sai ya sake zayyana mata ba.
"Yanzu muna tare da Saleem ne ƙanin Hamma Lamiɗo, anjuma za mu je gaida Mai mairtaba Sarki"
Ba ta tambaye shi ba amma sai zuba mata labarai yake yi, gajiya ta yi ta katse shi da cewa." kai ma har can Abuja za ka je?
Ya dawo mata da amsa da cewa sosai ma a gobe za su tafi tare da tawagar matayen Sarki amarya da tawaganta suna can tun shekaranjiya.
"Allah ya ba da sa'a."
Ta rubuta mai daga nan ta kashe data, amma bayan awa ɗaya da ta sake kunnawa sai da ta ga saƙon sa
"Kin san Mai martaba Sarki na da wani ƙaton gida a garin Abuja acan za mu sauka. Har sai an gama shagulgula sai ranar ɗaurin daure da safe za mu koma Daura."
Emojin mirmishi kawai Ummu ta tura masa, ita fa shi yasa ba ta yi mamaki da ta ga Hamma Saddam ya je Jamia yana karantar aikin jarida daman ya fi dacewa da shi, shi fa duk in da ya je sai kowa ya sani posting ne kan posting har da karin bayanai, ranar ya saka status sun fi goma na ƙarshe shi ne wanda ya ɗauka tare da Mai martaba Sarkin Daura Alhaji Dr. Nasiru Muhammad Daura a cikin fadar shi yana zaune kan ƙaraga idanuwansa ne kawai ake iya gani saboda yana cikin naɗi. Caption ɗin da ya saka ne ya sa Ummu kwashewa da dariya.
"Allah ya ja zamanin ka ubanmu uban ƙasa, Allah ya ƙara maka lafiya Mai mairtaba Sarkin Daura."
Hamma Saddam na da abin ban mamaki, sawa yake yi har bargar dawakai da ya shiga sai da ya yi hoto ya saka, Ummu ta tabbatar da ba za ta yi missing komai na shagalin bikin nan ba, tun da dai Hamma Saddam ya na can ai kamar suna can ne suma.
Â
Sai ranar Jumma'a Habib ya sauke ta gida da safe kafin ya tafi wajen aiki, duk da Ammah ba ta nan amma Baffa na gida bai je ko'ina ba tare suka yi ta hira sai da ya fita zuwa sallar jumma'a, yana fita ba daɗewa matar Hamma Abdurrahaman ta zo ita da yara, Adda Ummu Sulain tare suka yini a gidan har dare, Ummu ta yi ma Baffa tuwo miyar yauƙi, da man da Amma ba ta nan daga gidajen su Hamma Abdullahi ake kawo masa abinci sai misalin tara na dare Habib ya zo ya ɗauki Ummu suka koma gida bayan ta yi guzirin tuwo saboda ɗumamen safe.
Lalle ko an sha shagali a garin Abuja, ashe su Ammah duk uwar Amarya ta yi musu anko da man shi ya sa take ta tambayan mutanen da za su zo daga bangaren Ammah. An yi mothers Day su Amma an sha kamfala da mayafi ita da Ummin ikki, Hamma Saddam ya ɗora su a status a ƙasa ya saka
"Hamma LamiÉ—o mai uwaye biyu."
Hoton ya yi kyau, sai da Ummi ta É—auka itama ta yi status, da wanda aka yi ma Ammah ita kaÉ—ai ta yi shar da ita, ita da ta tashi saka hoton sai ta yi zolaya.
"Amman Baffa"
Ta saka emojin love da rawa.
Baffa kuma ya gani dariya kawai ya yi bai yi mgana ba.
Da man Hamman Saddam ya faɗa ma Ummu Amma na ta masa faɗan wai ya yi ya tura ma tsohon ta hotunan ta. Ummu ta yi dariya sosai rayuwar auran Ammah da Baffa rayuwa ce abar burgewa da tsari, ita tana da zafi shi kuma Baffa mai sanyi ne da haƙuri shi ya sa aka zauna lafiya.
An yi Dinner na gani na faɗa abu ne masu mulki da sarauta, matan sarakuna sun zo ma uwar Amarya biki, a matsayinta na uwargidan Mai mairtaba Sarkin Daura Gimbiya Shahida, itama ɗiya take ga tsohon wazirin na garin Daura. Sai ga su Ammah a tawagan uwar Amarya suna jera kafaɗa da matan gwamnoni da sarakuna da matan ƴ'an majilisu har da matar mataimakin shugaban ƙasa, ga matar Gwamnan Jihar Katsina sannan ga bangaren uwar ango itama da na ta tawagan, matan ministoci da masu faɗa aji a fadar gwammatin tarayya.
Ammah sun yi hotuna da uwar Amarya sannan ta yi da Amaryan da ango sai kuma wanda ta yi ita da matar Hamma LamiÉ—o Dr. Balkisu Usman Bayero"
Su Hamma Saddam an saje cikin Æ´aÆ´an sarakuna da Æ´aÆ´an ministoci shima cikin É—anyar gezner irin ta masu bikin, sai da Ummu ta yi da gaske ta iya ma gane shi, lalle su Hamma Saddam an samu duniya.
Matar Hamma Lamiɗo Ummu ta shagala da kallo, matar nan akwai gayu, yar gayu ce ta bugawa a jarida ga kyau ga ilimi ga gayu, ƴa'ƴan su Biyu mai sunan Maimartaba Nasiru(Sultan) sai mai sunan Amma, Jamila(Beena) wani arnen leshi ne a jikinta da ga gan shi ka ga kuɗi, ankon Dinner ɗin ne amma na ta kalan peach ne na su Amma kuma maroon ne kalan ya yi kyau sannan da mayafin su kalan head ɗin su, Amma da Ummin ikki fa har da makeup aka sha irin light ɗin nan sun fa ba za kafacity.
BaÉ—É—o ta saka su a status ta rubuta.
"Capacity iya capacity Amma da Ummin ikki."
Babu wanda bai saka su a status ba, har Hamma Jibo, Hamma Kabiru ne ya saka hoton Amma ita kaÉ—ai ya yi caption da cewa.
"Ammah uwar Amini Lamiɗo"
Ummu na gani sai da ta taɓe baki, duk wannan bidirin da ake yi shi gogan bai san ma ana yi ba.
Ba ta da lambarsa , yadda bai taɓa nuna damuwarsa akan rayuwarta ba, itama ba ta damu dashi ba duk da ko uwa ɗaya ce ta yi musu tarbiya.