Sashe 46
Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ba yadda Baffa bai yi da kar a yi auren ba amma ba wanda ya saurare shi, dangin Gwaggo suna ganin wata dama suka samu guda tak a kaf zuru'an su, suma su Baffa Hamza haka suke gani musamman shi da yake Babba mulki da kwaɗayi sun rufe masa idanuwa ganin irin dukiyar da Sarki yasa aka aiko wasu amintatttunsa da shi a matsayin Sadakin Fatima har da gwala-gwalai, Umma(Asma'u) a lokacin itama ta goyo bayan Baffa amma Baffa Hamza bai saurare ta ba, yana ji yana gani aka ɗaura ma Fatima aure da Hakimin Daura daddare domin sirrinta auren. Auren da aka ɗaura a garin Mubi sannan anan aka saka Fatima a lalle tana kuka tunda ko sau ɗaya bata taɓa sanin mijin ba, ta dai san Hakimin Daura a saman doki kansa da rawani idanuwansa kawai ta taɓa gani tunda suna zuwa kallon hawan salla lokacin shagulgulan salla a lokacin mace ba ta ikon cewa ba ta son wanda aka bata ko ba ta so dole za ta yi hakuri ta zauna kowa faɗa mata yake yi ta yi dace a dangin su kaf daga asalin tushen su ba wacce ta taɓa samu sa'ar da ta samu, Baffa ne kaɗai bai yi farinciki ba Ammah daga baya ta saduda ta riƙa lallashin Baffa da ya yi hakuri ya yi ma ƙanwarsa addu'an samun dacewa. Da za a tafi da Fatima Daura a wani kebantttacen gidan Maimartaba da ba wanda ya san da shi za a ajiye Fatima cikin sirri, Baffa ya yi magana da ƙanwarsa ya yi mata nasihan ta yi ma mijinta biyayya amma shi dai a ƙasan zuciyarsa yana ta jin tsoro, tsoron faruwan abin da yake gudu kuma daga ƙarshe sai da ya faru ɗin
 Tun Baffa na tunanin nan da wata ɗaya zai ji wani abu game da Fatima har dai aka kwarari wattani bai ji komai ba sannan tana yi masa saƙo da cewa tana nan lafiya lau. Sai hankalin shi ya kwanta ya ɗan samu natsuwa bai sake jin ya natsu ya samu kwanciyar hankali ba sai da Fatima ta zo ganin su a Yola tare da wani dogari amintattacen Hakimin Daura ya kawo ta Fatima ta yi kyau ta yi kiba har da wayar nan ta zamani a hannunta Handset sannan ta tabbatar ma da su Amma da Baffa cewa mijinta na son ta Sarki ma na zuwa dubata amma dai ba ta zuwa ko'ina itama ba mai zuwa wajenta daga ita sai wata amintattaciyar Baiwa mai suna Zulai tare ma suka zo sai dogarai guda biyu masu gadin ta da direba, irin kayan alfarman da ta zo da su kawai ya isa ya ba su tabbacin abin da ta faɗa gaskiya ne sannan ta zo ma da Baffa da kuɗi da suturu shi da Ammah da yara ta ce daga Hakimin Daura. Baffa dai ba abin duniya ba ne a gaban shi, shi dai fatan shi da burin shi Fatima ta samu farincikin da zai dauwama. Bayan zuwan Fatima sun sake dawowa tare da Hakimin Daura mijinta sun zo yi musu sallama zai tafi wani cos na wattani biyar kasar waje kuma tare da Fatima zai tafi, Hakimin Daura har ƙasa ya duka ya gaishe da Baffa ya kuma ba shi tabbacin har iya numfashinsa na ƙarshe zai kare Fatima. A lokacin da suka bar kasar Fatima ta bar Ammah da cikin Kabiru ne itama acan ƙasar da suka je ta samu ciki kuma suna garin ba su dawo ba maganar auren Hakimin Daura ya tabbata da Ɗiyar Wazirin mai ci a lokacin dalilin haka ya sa Fulanin Daura ta tsara bikin da yana dawowa za a ɗaura aure a yi shagulgula.
Auren da ya zagaya duniya, amma Baffa bai damu ba tunda Fatima ta tabbatar masa tana lafiya babu abin da auren nan ya rage ta ko shafe ta. Ita tunda auren sirri ne yanzu ne duniya ta shaida Hakimin Daura ya yi aure suka kuma tare a wani katon bangare a cikin masarauta. Fatima ta zo taron sunan Kabiru da tsohon cikin ta in da suka haɗu da dangi daga Mubi, kowa ya ga Fatima sai ya rike baki ta yi wata kiba sannan duk in ta taka kunyanga na biye da ita riƙe da jakarta ta zama abar sha'awa a wajen dangi, tana ma Yolan ne ta samu labarin Maimartaba Sarki Muhammad Shitu ba lafiya an fita da shi ƙasar waje domin nema masa lafiya kuma tare da mijinta aka tafi, dalilin da ya turo direba ya ɗauke ta ya ma yar da ita Daura ta koma da kwana uku Allah ya yi ma Maimartaba rasuwa, mutuwar da ta saka ma suna da mutuwa mai tonon asiri, domin sanadiyar mutuwar maimartaba sirrin auran ta ya bayyana a masarautar Daura. Ranar da Hakimin Daura ya zo hankali tashe yana sanar da ita mahaifiyarsa Fulanin Daura ta saka ana bibiyansa ta gano komai saboda haka ta shirya zai saka a zo a ɗauke ta zuwa can Mubi har zuwa komai ya lafa ya fita ya barta cikin tashin hankalin da ya jawo mata gajeruwar naguda.
Daga ita sai Zulai ta haifi kyakyawan É—anta namiji mai kama da uban shi, tana ma nishin haihuwan Fulanin Daura ta dira gidan a daran tare da Mijinta Hakimin Daura.
Fatima na kwance a cikin jinin Haihuwa Fulanin Daura ta umarci ɗanta da ya sake ta a cewarta zama da Fatima zai iya yi masa cikas da hawa karagan mulki ita kuma nan duniya ba abin da take muradi da fata kamar ta gan shi ya gaji mahaifinsa Fatima na kuka yana kuma yana roƙon ta amma Fulani ta ce ya zaɓa ko daraja da ƙimar masarautan Daura, Ko auren Fatima
Ba shi da yadda zai yi anan take ya yi ma Fatima saki ɗaya sannan ko ɗan da aka haifa masa Fulanin Daura ba ta bashi damar ɗaukan gudun jininsa ba a daran ta saka aka ɗauki Fatima a mota ita da abin da ta haifa, a cikin jinin haihuwa ita kanta da tsamin naguda da jinin haihuwa a jikinta ta kamo hanyar Yola a daran ba ta je ga gidan mariƙanta ba , sannan ba ta je mubi ba Sai ta je ga Baffa da Ammah ƙarfe uku na dare Fatima ta isa ita da Zulai da wani dogari Baffa sai da ya yi hawayen tausayin Fatima. Suna kuma kawo ta ba su tsaya ba suka juya daga Umarnin Fulanin Daura bayan an basu kuɗaɗe da gwala'gwalai da cewa kar Fatima da abin da ta haifa su sake dawowa Daura har abada. Sannan su Madibbo ma sai da Fulani ta saka a ka sauya musu gari suka koma cikin garin kurfi a cewar ta, ba ta son duk wani da ya danganci Fatima ya zauna a garin Daura ba ta fatan nan gaba labarin Fatima ya fito har ya yi ma ɗanta cikas ɗin zamowar Sarki. Waɗanda ma suka sani a lokacin duk ta rufe bakin su, ta haramta musu ambaton labarin.
Tabbas burinta ya cika, Hakimin Daura Muhammad Nasiru ya gaji mahaifinsa ya hau ƙaragan mulkin Daura bayan matarsa Gimbiya Shahida ya sake auran mata uku ya cike kofa a halin yanzu mata huɗu gare shi, ita kuma Fatima tana wajen Baffa tana rayuwa cikin kunci da baƙin ciki, dalilin Fatima domin ta samu kwanciyar hankali ya so da a ce shi mai kuɗi ne da zai yi nesa da garin Yola na har abada saboda Fatima ta samu kwanciyar hankali amma duk da haka sai da suka bar Yola suka koma cikin Jimeta da zama, kuma dawowar Fatima gida bai sa ya je Mubi ya faɗa musu abin da ya faru ba daga can ne Midibbo ya sanar da su ga abin da ya faru Baffa Hamza ya dawo yana wallahi tallahi, duk dai bayan an gama jajantawa ba wanda ya sake bi ta kan Fatima ballanta halin data ke ciki.
Fatima ba ta mgana sai kuka sai damuwa ba ta cin abinci sai Baffa ya zaunar da ita yana ba ta baki da lallashi da nasiha kamar ta ji amma da ya bar wajen sai ta koma gidan Jiya. Muhammad Lamiɗo da Baffa ya yi ma shaƙika da huɗuba wajen ma bashi Nono ma sai Baffan ya tsaya mata ba domin Ammah ba sai dai Lamiɗo ya mutu ba mai kula da shi, itace ta haɗa shi da Kabiru a lokacin mutane da dama suna tunanin ko y'an biyu ta haifa tunda tsakanin su bai fi kwana arba'in ba. Ammah ta sha wahala sosai ga Fatima ita kanta kula da ita ake yi Aminiyarta Aisha ce auren ta ya mutu a can Mubi kuma ana ta magana sai Amma ta yi ma Baffa mgana ya ce ta taho ta zauna da su na wani lokaci, ko domin ta riƙa taimaka ma Amma da kula da su Lamido ga Fatima.
Ta zauna da su na tsawon shekara É—aya a wajen su Ammah ta samu miji ta yi auren ta da Babansu BaÉ—É—o Malam Sani, mutumin Jada ne shima kasuwancin siyar da hatsi ne ya kawo sa Jimeta ba jimawa suka yi aure anan kuma cikin Jimeta suke zaune Amma ta fi kowa murna Aminiyarta ta dawo kusa da ita. Haihuwan ta na fari mace ta haifa mai suna iklima shi ne dalilin da ya sa ake kiran ta da Ummin ikki.
Fatima ta sha gwargwarmaya kafin ta dawo daidai. Daga lokacin ta tsani duk wani abu da ya shafi sarauta, ta tsani har garin Daura gabaɗaya. A daddafe ta yaye Lamiɗo ta sakar ma Ammah ita kuma da taimakon Baffa ta koma makaranta a zaman ta a gidan Baffa har deperession sai da ya kamata Allah ne ya taimake ta tana da sauran kwana a gaba, zuciya da takaicin abin da aka yi mata ya sa ta ji tana so ta tashi daga Fatima yar ƙauyen Mubi zuwa Fatima mai ilimi wacce za ta nemi ilimi domin gobenta ta yi kyau.