Sashe 30
Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta ji zuwan shi lokacin tana salla ne amma yanayin da ta gan su a ciki ya sa jikin ta ya yi san yi.
"Baffa me ke faruwa,?
Ta faÉ—a tana mai zama a gefen Ummu.
"Me aka yi ma wannan ta ke rawan jiki?
Ammah ta sake tambaya tana mai kallon Ummu da har ta fara hawaye.
"Au kema ba ki sani ba?
Hamma Abdurrahaman ya tambaya yana kallon Amma.
"Mene ne? Ban sani ba"
Ta faÉ—a cikin mamaki, Hamma Abdurrahaman bai tsaya ba ya kwashe komai ya faÉ—a ma Ammah yana fada mata tana sake kallon Ummu cikin mamaki.
"Na zo na same ta durkushe a gaban Baffa kamar wata marainiya, ba ta so na ji mganar ba ne. Raina ya ɓaci sai da lokacin nan Kabiru ya yi ta cewa an yi gaggawa Baffa ko fa bincikan shi yaron ba a yi ba sosai in da an yi bincike sosai ta ina za a aura mata ɗan iska wanda ba ya son haihuwa. ? Wato in ma wajen zubar da cikin wani abu ya same ta shi ba shi da asara kenan ko?
Ya sake faÉ—a har yana ta yar da jijiyan wuya.
"Duk binciken da ya kamata a yi an yi Abdurrahaman kuma ba a same shi da wani abu na ashha ba."
"To Baffa wannan dai abin assha ne, jahilci tsantsan da rashin tunani. Tunda cikin ya shiga sai ya bar shi ta haihu can tsakaninsu za su iya tsayar da haihuwa da fahimtar junan su duk ana haka ba matsala ba ne. Amma kawai ya ce sai ta zubar da ciki da karfin tsiya wannan ya saɓa ma doka. In muka yi ƙaran shi sai ya gane ba shi da wayau"
"A'a ba za a yi haka ba."
"To Baffa me ye amfanin zama da mara mutumci? A raba auren kawai."
Da sauri Baffa ya ce" Na ce aa ko, shi ya sa ban faɗa maka da farko ba sanin halin ka na saurin yanke hukunci."
"To Baffa me kake so a yi?
Hamma Abdurrahaman ya faÉ—a cikin sarander
Ammah mamaki ne ya sa ta kasa mgana tunani take yi lokacin da Ummu ta yi ɓarin cikinta na farko yadda Ummin ikki ta ce ya damu, to yanzu kuma da ya kamata ya yi murna me ya sa zai ce ba ya so?
"Baffan ku Umaru zan kira, shi zai kira waliyin shi ya faÉ—a masa sai mu ji abin da ya kamata mu yi nan gaba."
"Baffa ya fa san da waliyin na shi ya ce sai ta zubar da ciki. Ni ina ganin a biyo da shi ta hanyar da ya biyo, ka ji fa ta ce yana azabtar da yarinya yana so ya yi mata dole."
Baffa ya tare shi da cewa" Duk da haka dai a fara sanar da su, a bi komai a hankali."
Amma ta jinjina kai kafin ta ce" Baffa ya yi gaskiya a fara sanar da su a ji su kuma na su hukuncin. Amma dai Habibu ya ba ni mamaki ban zaci haka daga wajen shi ba."
"Nima haka wallahi."
Baffa ya faÉ—a shima cikin É—an damuwa Ummu kuma hawaye ta ke sharewa ta kasa mgana.
"Ni da man na san za a yi haka. Yaro ne fa ƙarami Baffa yarinyar nan da karatunta ta cigaba amma ta na ce ta ce aure za ta yi ai ga shi nan kin fara ganin uwar da ke cikin auren."
Baffa sai da ya yi dariya Amma ta kauda kai ba ta yi magana ba.
"Ba yadda ba mu yi da ke ki cigaba da karatu ba kika ƙi, kika ce ke aure ke yar soyayya to yau duk ina soyayyar! Tun da kin samu ciki ya ce dole sai kin zubar? Kin ga wawancin da muke faɗa miki kin yi ko a wancan lokacin ko? Auran ki ko shekara bai yi a ce su Baffa sun fara sulhu tsakanin ku? Da yau karatun ki kike yi da ba ki yi kuka ba"
Ya sake faÉ—a yana kallon Ummu yadda take kuka har yana fidda sauti.
"Na so ki cigaba da karatu, na so ki yi karatu. Nawa kike Ummu? Just 24 to 25 kina da sauran damarmaki masu yawa amma kika ƙin jin maganar mu, Baffa da Hamma Jibo suka mara miki baya. Yanzu don Allah ina amfanin a fara kiran su Baffa Umru da magarnar ki? Yaron ma ba shi da mutumci in har ba zai sauke kudirinsa ba ya sake ki kawai "
Ummu ta sake jin kuka ya taso mata, domin ta san ko giwar wake ta sha ba ta isa ta ce ma Hamma Abdulrrahaman tana son Habib ba ta son rabuwa da shi ba, ta tabbata sai ya yi ball da ita shi ya sa ta yi shuru tana ta kuka shi ko yana ta faɗa da masifa Baffa ne ke tausan shi amma bai haƙura ba.
"Kaddara ta riga fata fa, Abdulrrahaman. Fatan mu dai Allah ya sa lamarin ya zo da sauƙi."
Ammah ta faɗa, ita tausayin Ummu ta ke ji. Ita mace ce sannan ƙarin tausayin ta da fatan ta kar Ummu ta fara fuskanta kaddaran aure da ƙananun shekarunta. Ita ta zauna da Fatima lokacin da kaddaran aure ta faɗa mata da shekarunta sha bakwai a duniya ita kaɗai ta san siraɗan da fatima ta tsallake kafin ta iya tsayuwa da kafafunta. Fatan ta Ubangiji ya zaunar da Ummu a ɗakin auren ta na har abada ya kuma sassauto da zuciyar Habib a kan ta. Kar Allah ya sa ta ɗanɗana zafin zawarci har abada a rayuwarta.
"Fatan da za mu yi kenan tun da mai afkuwa ta faru. Kuma bawa bai isa ya sauya zanen kaddaran sa ba."
Baffa ya faÉ—a, amma shi fa Hamma Abdulrrahaman bai yarda ba faÉ—i yake yi har da kuskuran su Baffa.
Amma ta ga Autar ta nata kuka ya sa ta shigar mata.
"Don Allah ka kyale ta Abdurrahaman ba ta ko da cikakkiyar lafiya!. Ke ta shi ki je ki ci abinci"
Ammah ta cece ta, ta samu ta bar ɗakin Baffa tana kuka zuwa falon Ammah ta faɗa saman kujera ta saki kukan ta shike nan abin da take gudu ya faru ya za ta yi ma Hamma bayanin yadda take son Habibu ta ke kuma son cikin jikinta da aurenta. Ta tabbata ba zai taɓa ganewa ba gwara Baffa shi ne zai fahimce ta da halin da ta ke ciki ba amma ba su Hamma Abdulrrahaman ba da daman yana cikin yan adawa da auran ta da Habib.
Ummu ba ta sake fitowa daga falon Amma ba har sai da Hamma Abdulrrahaman ya tafi, la'asar na yi ta yi salla ta ce ma Ammah za ta tafi da ta ce mata tun yanzu sai ta ce za ta biya gidan Ummin ikki, dambun ma ba ta ci ba ta É—auka ta ce sai ta je gida Baffa ma ya fita masallaci bai dawo ba ta tafi, Amma dai ta faÉ—a mata an kira Baffa Umaru ba a same shi ba amma Baffa ya ce zai sake kiran shi. Har haraba Amma ta raka ta, tana ta sake jadadda mata ta kula da kanta.
Gida ta koma da man dai ta ce ma Ammah za ta je gidan su BaÉ—É—o ne saboda kar ta ce ta tafi da wuri, nan ko hankalinta ne ke tashe ba ta san yadda Habib zai yi in ya ji mgana ta kai wajen waliyin shi ba, tsoro ta ke ji shi ya sa ta kasa zaman gidan sannan da fargaban kar wani ya sake zuwa Baffa ya sanar da shi abin da ke faruwa a sake sauke mata wani masifan. A waya kawai ta kira BaÉ—É—o suka yi mgana ta sanar da ita ta je gida ta faÉ—a ma Baffa.
"Gwara hakan, in manya suka shiga ciki sai asan mafita."
Ita dai ba ta ce komai ba ta ma kasa ba ta labarin karon ta da Hamma Abdulrrahaman
Ranar da Habib ya dawo tana ta jiran ko za ta ji ya yi mata wata mgana ba ta ji ba, yadda ya saba mata haka ya yi na mantawa ma da wata hallita a gidan.
Washegari Shamsiya ta kira ta, tana tambayanta yadda ake ciki , tana kuka ta sanar da ita halin da ake ciki.
"Kash. Bestie kin yi kuskure na so ki yi amfani da shawara ta kafin maganar ta kai wajen su Baffa."
Ummu ta rantse mata da cewa bata san cewa haka lamarin zai koma ba, sannan ita dai tana son cikin jikinta ba za ta iya rabuwa da shi ba.
Shamsiya dai ita tana ganin laifin Ummu ne Habib ne ke da gaskiya. Ita a ganin ta ahakan ba wani abu ba ne, normal ne. Tunda yanzu yin tsarin iyali domin taƙaita haihuwa ya zama ruwan dare.
***
A ranar Baffa bai samu Baffa Umaru a waya ba sai a washegari ya same shi sannan ya sanar da shi abin da ke faruwa.
Shi kan shi Baffa Umaru faÉ—a ya hau yi yana cewa ai wannan shirme ne.
Suna gama waya da Baffa nan take ya lalubo lambar waliyin Habibu kanin mahaifinsa Alhaji Sheriff, tun lokacin neman aure suke da lambar juna.
Yana kiran shi bayan gaisuwa da tambayan iyalan juna. Sannan Baffa Umaru ya zayyane masa halin da ake ciki.
"Wani shirme ne haka Habibu ya aikata? Shi ba a haihuwa iyayen shi suka haife shi? Kuma ya san ba ya son haihuwan yanzu bai É—au mataki ba sai da cikin ya samu? Ai ko bai isa ba "
Sun yi sallama da juna akan cewa zai yi ma Habibun waya ya ce ya zo gida ya same shi. Yadda suka yi zai kira shi, nan take ya kira Baffa ya faÉ—a masa yadda suka yi da waliyin Habibu shima suka rabu da cewa sai yadda ta yuyu in ya kira shi zai sake kiran shi.