← Book details Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 92

Sashe 44

Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Abdullahi ka ji tozarcin da wannan yaron ya yi mana? Saki uku fa ya yi ma Ummu?

Har Hamma Jibo ya ji abin da Ummi ikki ke faɗa a tare shi da Abdullahi suka saki salati cikin  firgici.
Kashe wayarsa Abdullahi ya yi yana mai karɓan takardan hannun Ummi ya fara karantawa a bayyane.

"Ni Habib Idris Mai Imani na saki matata Ummu Salma Hadi Baba saki uku, da ita da cikin jikinta bana ɓukatar su a rayuwata. Na sake ta ne saboda ni ban aure ta domin ina son ba, saboda jikinta na aure ta kuma na samu abin da nake so, shi ya sa na rabu da ƙwallon mangwaro na huta da kuda. Maganar ciki kuma sai da na ce ta zubar da shi ta yi taurin kai da a ce ta ji magana ta da ba haka ba, to ina so ku sani abin dake cikin Ummu Salma ba ni da alaqa da dashi har abada ba ni da danganta da abin da za ta haifa ballanta wata rana a neme ni saboda shi. Ni da Ummu mun rabu,rabuwa ta har abada ku ɗauka ma kamar ba mu taɓa sanin juna ba."

"Hasbunallahi wa'imal wakeel"

Ummi ikki ta faɗa tana mai riƙe kanta cikin baƙin ciki da takaici.

Abdullahi ya ma kasa mgana ji ya yi lamarin ya yi masa nauyi wannan wani irin tozarci ne, lalle wannan yaron bashi da mutumci duk yadda Abdullahi ke da saukin kai sai da ya fusata ya harzuka da wannan sakin wulaƙancin da Habib ya yi ma ƙanwarsu.

"Lalle wannan yaron ba shi da mutumci ba ɗan arziƙi ba ne. "

Ya faÉ—a yana jin wani irin zafi a cikin zuciyarsa. Baffa da Ammah kawai yake tunawa, in ya tuna da Ummu sai ya ji ya karaya, ya take ji yanzu? A wani hali zuciyarta take ciki, ya cuceta, ya cuce su sai dai Allah ya saka musu kawai.

*littafin Fargar Jaji na kuÉ—i ne a manhajar Telegram akan #1k. Tura KuÉ—in karatun ku ta wannan acct É—in 9069067488 JAMILA UMAR OPAY sannan sai ku tura shaidar biya ta waÉ—anan lambobin kamar haka.*

09069067488.
08032773332.

*Yan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajojinku a cikin wannan kayattacen labarin za ku iya tuntuɓata kai tsaye ta wannan lambar 09069067488 Na gode.*

*Janafty*
*FARGAR JAJI.*

*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:JamilaUmarJanafty*

"To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude"

https://chat.whatsapp.com/LsC7Rjmei7J6Hd11e95nNS?mode=gi_t

*11*

*TUSHE, MAFARI*.

Mafarin ya fara daga Abdullahi(AUDU BABA) bafillace haifaffan garin Mubi. ita kuma Mubi ƙaramar hukuma ce daga cikin Jahar Adamawa Yola. Garin Yola nan ne maƙyanƙyasan sa tun daga kakkannin shi dai bai san wani asalin tarihin iyayen shi ba sai da ya san su a haifaffun jahar Adamawa, wasu suna cikin yankunan dake zagaye da Adamawa kamar irin su girai, funfore, ganye da dai sauran su amma shi asalin iyayen iyayen shi a garin Mubi sukai rayuwa shima anan aka haife shi anan kuma ya yi rayuwarsa har zuwa auran shi na fari da bafillatan matarsa mai suna Asma'u.

A matsayin shi na bafillace tsantsan na gaba da baya, kamar wajibi ne ya auri bafillatana yar'uwansa sannan da yake ba karatun boko matan suke yi da wasu mazan ba to ana yi musu aure ne suna da ƙananun shekaru, in har ka ga namiji ya yi karatu to sai in har fita ya yi cirani daga nan sai ya faɗa harkan neman ilimi , shima hakan ne ta kasan ce da shi yana da ƙarancin shekaru ya yi auran shi na fari kafin ya sake yin wani auren na gani ina so.

Lokacin ya fara shiga jahohin Nigeria domin fatauci ya faɗa garin Daura na Jahar Katsina a can Allah ya haɗa shi Ummu Salma(Gwaggo) ita ɗin haifaffiyar baƙar bafillata ce yar nan garin Daura ce ta uwa da ta uba, tunda Audu Baba ya ƙyalla ido ya ga Ummu Salma ya ji duk duniya ba wacce yake so irin ta a lokacin itama shekarunta ba su wuce sha biyar ba yarinya ce ƙarama ya ɗauka zai sha wahala kafin ya same ta amma sai ga shi cikin lokaci ya samu abin da yake so, tun ballanta da Ummu Salman take son shi ta ga dogon bafillace jajir tas a tsaye jarumi kuma Sadauki tuni ta ce shi take so, su kuma iyayenta ganin duk tushe ɗaya ne sai suka aura ma Audu baƙo Ummu Salma ya tafi da ita can garin su Mubi.

A lokacin ƴa'ƴan shi da Asma'u huɗu Hamza, sai Umaru, Salihu da Sha'aibu. Zuwan Ummu Salma ya sanya suka haɗe kansu suna zaune lafiya Ummu Salma ta ɗan jima ba ta haihu ba sai da aka yi ta karɓa mata taimako wajen shekaru biyar da auran su sannan ta haifi babban ɗan ta namiji wanda Audu Baba ya yi ma huɗuba da Hadi bayan shi kuma ba ta sake haihuwa ba har sun cire rai ma gabaɗayan su sannan ta samu Fatima wanda tsakanin su da Hadi shekaru sha bakwai ne. A lokacin da aka kawo Ummu Salma wacce kowa ke kiran ta da Gwaggo akwai wata maƙociyarsu da aka yi ma Gwaggo uwar ɗaki da ita tun lokacin da aka kawo ta Daura wacce ake kira Nenne tsada saboda hasken fatan ta duk yankin a lokacin ba mai jan ta, shi ya sa ake kiran ta Nenne tsada ita ta zama kamar uwa ga Gwaggo tun kawo ta garin zuwa yanzu komai nata da na ƴa'yanta Nenne take shigewa gaba ita Nenne Allah bai ba ta ɗa Namiji ba duka ya'ƴanta mata ne sannan in ta haihu sai su yi wabi a cikin yara goma da ta haifa huɗu kawai suka tsaya mata, Balki ce babba sai Salamatu sai A'i, sannan autar ta Jamila wacce a lokacin yar shekaru goma ce to bayan Jamilan ma ta sake haihuwa sau uku suma suna yin wabi su kaɗai ne ta samu suka tsaya mata, tunda da daɗewa megidanta ya rasu ita kaɗai ce ke gwagwarmayan riƙe marayun ƴaƴan nata.

A lokacin Gwaggo tana cewa ta kama ma Hadin ta Jamila matsayin mata, tun ana ɗaukan maganar wasa har dai Gwaggo ta tabbatar da ita ba wasa take yi ba. Tun Jamila na ganin Hadi tana gudunsa har ta daina domin shi bai taɓa ɗaukan maganar Gwaggo da muhimmamci ba tun ballatana a lokacin shi ɗan gayu ne tunda yana makarantan boko, Jamila kuma karatun allo suke yi a lokacin sannan tana da wata Aminiya da suke tare tun suna yara mai suna Aisha. Gida uku ne ya raba tsakaninsu duk in da za su je tare ne sannan makarantan allo ɗaya suke zuwa iyayensu su san juna, ko kaya ne in za a yi ma Jamila sai an yi ma Aisha haka itama gidan su Aisha ba sa nuna cewa Jamila bare ce, Aminci ne mai karfi a tsakanin su tun suna yara har kuma girman su sai da Ubangiji ya saka aminta da yarda har a tsakanin ƴaƴan su.

  Jamila na da shekara sha shidda a duniya bayan ta yi saukan Allo aka saka ta a lallen aure ita da Hadi. Shi a lokacin yana da shekaru ashirin da shidda ne, kuma yana gama sakandiri amma bai cigaba da karatu ba sai dai yana yin noma sannan yana kiwo. Auren gata aka yi musu auran da har bayan shekaru masu yawa suke zaune a ƙarƙashin kulawan iyayen su a garin Mubi suka fara gudanar da kyakyawan rayuwarsu a farkon auran su Hadi ba ya son Jamila amma da tafiya ta yi tafiya sai ya ji ya gode ma zaɓin Gwaggo har bayan ranta in ya tuna da abin alherin da ta yi ma rayuwarsa sai ya gode ma ta sannan ya yi mata addu'an samun haske a cikin kabarin ta.

A shekaran auran su Jamila ta haifi yaron ta na farko mai suna Jibril ana haihuwan shi Gwaggo ta ce an samu Jibo shikenan sunan ya bi shi har girman shi, Jibo ya taso tsakanin iyaye da kakanni ne shi ya sa Jamila(Ammah) ba ta sha wahalan renon shi ita kaÉ—ai ba sunan da Hadi(Baffa) Ammah ce ta fara kiran shi da Baffa har ya kama bakin yaran gabaÉ—aya, bayan Jibo ta sake haihuwan Mustapha tana da cikin Mustapha suka saka Aminiyarta a lalle Aisha ta yi aure a garin Girai duk da ba ta son auren amma hakan nan aka kaita kuma ta zauna sai ya kasance ba a gari É—aya suke aure da Jamila(Amma) ba.

Haka dai rayuwa ta cigaba da gudana cikin farinciki, Nenne ta fara rasuwa maciji ne ya sare ta a makewayi sai dai gawarta aka iske a kwance shike nan su Ammah sun zama marayu Allah ya sa ma dukkansu sun yi aure a cikin garin Mubi shi ya sa sai maraicin ya zo musu cikin gata Ammah ta fi kowa jin mutuwar Nenne amma samun Baffa kusa da ita ya sa ba ta daɗe ba ta warware uwa uba ga Gwaggo ga Baba ita yar gata ce gaba da baya ba sa barinta ta yi kukan rashin wani abu saboda soyayya da gata. Ga ƙanwar Baffa Fatima da kusan a tare suke rayuwa tun da ba wani tserayan shekaru ne a tsakanin su ba.
Chapter 44 · 0% Book details