← Book details Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 92

Sashe 89

Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sanye take da bulawus ta yara mai kyau, kanta kuma kitson kalaba ne an kama da band ga ta dai yarinya yar kimanin shekaru biyu amma tana da suma kai da gashi ga ta fara jajir da ita amma ko kusa ba ta kama da Ummu Salma, kamaninta da komai kamanin mahaifinta ta ɗauko, wanda kullum in Ummu ta kalleta sai ta ji baƙin ciki, ba ta so ta sake cin karo da mai irin fuskar wannan mutimin ba, amma sai ga shi tilon yar da ta haifa ta ɗauko kamaninsa

"Mahma"

Ta sake faÉ—a tana sake lafewa a jikin uwar ta ta,.
"Gani nan kukan na mene ne? Ko yunwa kike ji ne?
Sai ta gyaÉ—a kanta.
"Tea Mahma."
Ta ce tea za ta sha, nan da nan Ummu ta saɓa ta a baya tana faɗin" Hau bombu yanzu na haɗa miki tea ɗin ki sha."

Nan da nan ko ta lafe a bayanta ita kuma da haka ta yi amfani ta saka ruwan zafi a wata butar a kitchen É—in tunda suna da wuta su da sai su yi sati ba a É—auke musu wuta ba koma an É—auke akwai solar ba ka gane ma akwai wutar ko babu.
Tana cikin tattara kayan video É—in ta Basira ta shigo Kitchen É—in.

"Ya Ummu da kan ki kika goya wannan yar rigimar!"

Ta faÉ—a tana dariya Ummu ta juya tana kallon Basira yar matashiya ce ko za ta girmeta bai wuce da shekaru biyu ba, itama kaddaran aure ne ya faÉ—a mata suka rabu da mijin watanni kaÉ—an da auran su, ita ce wacce Mami ta sake É—aukowa daga can garin su Daddy É—anmarke bayan sun mayar da Baraka an yi mata aure.

"Ba ruwan ku a ciki Basira."

Ummu ta faÉ—a tana sake zumkuÉ—a Hannan a bayanta.

"Yi kwanciyarki Hanan kar ki biye ta Basira."
Saboda suna yin ta Hanan kiyuwa da rigima Basira kuma faÉ—a ta yi ta janta tana saka ta kuka amma bai hana anjuma Hanan É—in taje wajenta da zanin goyo tana faÉ—in bombu.

Hanan na son goyo sosai ko domin da aka haifeta ta sha goyo ne? Lokacin Baraka nan nan ko da yaushe tana bayanta Mami ma in tana gida za ta goya ta haka ma Islam har Faruku rigima yake yi a lokacin sai an goya masa shima.

"Ke sauko ki kyale Ya Ummu ta huta, ta ho nan ki hau nawa bayan da kika saba hawa.."
Basira ta faÉ—a tana leka Hanan sai ko ta makale bayan uwarta tana kallon Basira.

"Ba ki tahowa ko?

Ta faɗa tana miƙa mata hannu kawai sai ta saka kuka tana kiran Mahmah, Ummu na dariya ta ce"Hanan ke da Basirun na ki."
Haka Hanan ke kiranta su yi ta dariya ita da su Mami Basira tun tana masifan cewa ni da na reneki ki san sunan kowa daidai amma ni basiru kika mayar da ni har ta zo ta haƙura domin ya kama bakinta.
"Ba ruwana in ta ce ba za ta sake goya ki ba."
Ummu Salma ta faÉ—a tana dariya.

Kamar kuma tana ji sai ta daina kuka ta kura ma Basiran ido tana kallonta sai ga shi da kanta ta miƙa mata hannu ita kuma ta kama tana faɗin" Yauwa Hannatuna."
Tana dariya dariya yarinyar ta bar bayan uwar tata ta haye na bayan Basira tana zillo.

"Basiruu."

"Ke ni sunana Basira ba Basiru ba."

"Basiru.."

"Kai wannan yarinyar, to ke ma Habu ba hannatu ba."

Ummu na gefe tana cin dariyanta.
"Ku je falo Basira bari na haÉ—o mata tea É—in."
"To, na ji jikinta da É—umi ya kamata ta sha maganinta na rana."
"To ta sha tea É—in sai na É—auko mganin ki ba ta yar rigimar nan ai sai ke Basira."
Ta fice tana dariya.
Basirace ta taimake ta har ta samu ta haÉ—a mata tea É—in bayan ta kawo mata ta bata ta sha, sannan wajen shan mgani sai da aka yi mata É—ure ba ta son magani tana ta kuka da rigima bayan nan Basira ta yi mata wanka ta sauya mata kaya sai barci bayan ta goyata ram a bayanta da zani.

Mami ba ta nan ta shiga cikin makaranta gidan daga Ummu ne sai Basira Faruku na makaranta sai biyar da rabi zai dawo tunda nan Al'areeb yake yi a Kaduna yana primary 6, Islam dai ana bording  zaria can FGGC BASAWA tana jss2 yanzu sai an yi hutu take zuwa gida amma suna zuwa yi mata visiting zuwa ma biyu duk Ummu ke zuwa ita da Basira da Faruk Hamisu ke tuƙasu.
Daddy kuma ba ya nan ya yi tafiya kasar Turkey ya fi sati acan.

Sai a lokacin itama Ummu ta samu ta É—an sake yin wanka ta sauya kaya wayarta ta É—auka ta shiga shafukanta tana ganin video É—in da ta yi É—azu ta fara É—ora shi a kan Youtube sai kuma nan da nan ta yi sharing É—in shi zuwa Handles É—inta na sauran shafukan sada zumumta an yi mata comments amma duk akan godiya da yabawa ne sannan da masu cewa suna gane koyarwaanta don Allah ta buÉ—e musu online class mana, itama tana so ta buÉ—e amma ba yanzu ba sai ta sake tara yawan mabiya.
Bayan ta gama duba shafukanta sai ta shiga kan whatsApp ɗin ta, tana duba saƙonni, ko wata biyu ba su yi da dawowa daga Jimeta ba tun bayan barin ta gida sai a lokacin ta sake komawa Jimeta shima ya kama dole ne Baɗɗo ce ta gama makaranta shi ne ta je mata graduation Mami ba ta samu zuwa ba daga ita sai Hanan suka tafi kwananta goma ta dawo Kaduna duk da ta yi kewar garin amma ba ta jin za ta sake zaman garin ya wuce na sati biyu ba, yanzu Ummu Salma yar kaduna ce ba yar Jimeta ba.

Hamma Saddam ne ya yi mata sako tana dubawa ta ga ya ce" Ke nifa ina Lagos."
Mamaki take yi sai yanzu ta san dalilin da ya sa Hamma Saddam ya zaɓi shiga Camp a garin Lagos.

Ashe saboda ya je ya huta a gidan Hamma LamiÉ—o ne.
Hotuna ne ya turo mata sama da goma, har da wasu ma yana driving a wata mota mai kyau da tsada.

"Ni fa har motar Hamma LamiÉ—o nake hawa yanzu"

Ta tuna mganarsu ta kwanaki da ta tambaye shi motar waye yake aro yana ta wayon gari ya ce tashi ce ashe wasa yake yi mata.
Yanzu ma hotunan shi ne a bakin ruwa kala kala.

"Ya mutanen gidan?

Haka kawai ta rubuta masa saƙon ya maka biyu domin ta san yana online, Hamma Saddam da waya kamar 5 and 6 ne.
Tun bayan barin ta Jimeta ba ta sake ganin Hamma Lamiɗo ba wataƙila Mami na haɗuwa da shi tunda ta je Jimeta sosai a wannan shekaran amma ita ba ta sake ganinsa ba kuma ba ta sake bibiyan labarin shi ba, ta dai san ya biya ma Hamma Abdullahi da Hamma Abdulrrahaman tare da matansu sun je Umra tare da Ummin ikki da babansu Baɗɗo, a shekaran da ta dawo Kaduna itama Daddy ya biya musu sun je gabaɗaya acan suka haɗe a masauƙi ɗaya ma suka sauka ta kan ji ana hiran ya yi kaza ya yi kyauta kaza amma ita dai tunda bai taɓa yi mata ba, ba ta taɓa damuwa da shi ba.

Hamma Abdulrahim ne ta ga ya saka hoton shi cikin likitoci turawa kamar yana can ƙasar waje alhalin yana Abuja yana Housemanship ɗin shi a asibitin NIZAMIYE HOSPITAL ABUJA.
Bayan ya dawo ya yi jarabawa ta Medical and Dentel council of Nigeria.
(MDCN) Sau É—aya ya yi kuma ya samu nasara.

Abdulrahim kamar wani bature daman ga shi jajir da shi ɗabi'unsa ma da komai na shi ya koma na turawa, hausa ma tana neman ɓace masa magana kaɗan turanci fillanci ko har ya fara mantawa shi da ya shafe sama da shekara bakwai a kasar Singpore.

Da ya dawo Ammah ta yi ta masifa, in suna hira ya dinga yi mata turanci.
"Buraubaka, tir da wannan kasar turawan tunda ya sa ka manta da al'adanka ka kwaso mana daɓi'an turawa."

Lokacin da ya zo Kaduna ne ya ke ta ba ma Ummu labari tana cin dariya.
Har waliman dawowarsa an yi amma Ummu ba ta je ba Har Mami taje shi ne bayan ya natsa ya huta ya zo ya ganta kwana biyu ya yi suka sha hira suka fita yawo cikin gari kafin tafiyarsa.
Tun da yanzu Ummu har driving ta koya kuma ta iya, tana tuƙa motar Mami wani lokacin.

Ummu Salma ba ta taɓa tunanin da gaske rayuwarta za ta sauya ba sai ga shi Ubangiji ya sauya mata rayuwa, rayuwar da ba ta yi hasashe ba, lokacin da suka zo Kaduna ga shi dai gidane amma ta yi ta baƙunta da rashin Sabo ba abin da za ce da Mami da Daddy sai godiya domin sune tsanin da rayuwarta take kai a yanzu. Sun kula da ita da lafiyanta da ita da abinda ke cikinta, da karfi da yaji suka yakice damuwa da tunani a zuciyanta.

Kwanan ta arba'in a Kaduna ta haihu a asibitin kuÉ—i na Garkuwa, aiki aka yi mata domin ta yi doguwar naguda, an samu nasaran ciro mata ya mace wacce ta saka ma suna Hannatu suna kiranta Hanna, Daddy da Mami su suka yi mata komai, raguna biyu Daddy ya yanka mata kuma ya shirya taron suna.
Chapter 89 · 0% Book details