Sashe 51
Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Har abada in dai maganar Habibu ne na fita daga cikin ta, amma ba wai ina nufin na fita daga sha'anin ɗan'uwa na ba ne, ba Habibu ne ya haɗamu ba. Ubangiji ne ya kawo mu duniya a mahaifa ɗaya. Zan shiga sha'anin duka yaran gidan amma ban da Habibu ai ya isa kan shi saboda haka ya je ya yi rayuwarsa Allah ya ba da sa'a."
Yana gama faÉ—in haka ya saka takalminsa ya bar gidan ya bar Gwaggo na hawaye. Haka ma mahaifin shi ke kuka daga in da yake kwance, an ya Habib zai ga daidai a rayuwasa kuwa?
***
*ZONE 3.*
2:30PM.
Har zuwa lokacin su Ummin ikki na gidan ba su tafi ba, ita Baɗɗo tana tare da Ummu a ɗayan bedroom ɗin dake kusa da na Ammah nan aka sanya mata kayanta. Daman kuma nan ne ɗakin da ta yi ƴanmatancinta kafin ta yi aure, komai yana nan Ammah ba ta kauda shi ba ko baƙi ta yi ba ta cika sauke su anan ba duk wasu littafan makarantan Ummu Salma da tarkacenta duk suna ɗakin Ammah ba ta kauda su ba. Sai ga shi Ummu Salma ta sake dawowa cikin shi a karo na biyu.
Ammah kuma suna tare da Ummin ikki tana ta É—an jan ta da magana saboda ta kwantar mata da hankali, duk da tana nuna mata ba komai. Baffa kuma tun da ya gama waya da Alhaji Sheriff ya shige É—akin sa Hamma Abdullahi ya bi shi ya É—an jima a ciki kafin ya fito ya yi musu sallama ya tafi gidan shi. Tun kuma daga lokacin Baffa bai sake fitowa ba sai da zai je sallan azahar.
Ammah kuma aikinta ta fita tana yi kamar ma ba ta damu ba, ba wanda ma ya tsaya bi ta kan ba ta damu ba domin an san ta damun. Aminan junan tare suka share gidan suka yi girki shinkafa da wake jallop mai allayahu Ammah ta kai ma Baffa na shi amma ya ce mata ba zai iya ci yanzu ba. Na su Ummu ma yadda ta shiga da shi ciki haka ta koma ta gan shi daga Ummu har Baɗɗon ba su taɓa ba.
Ummu Salma na zaune a in da ta yi salla a saman darduman tana nan dai a yadda take. Ba ta magana sai dai kallon waje É—aya kawai tunda suka zo ko tari ba ta yi ba. BaÉ—É—o ma ta kasa iya shan ko ruwa ne tana zaune a gefen gado ta yi tagumi kawai tana kallon Ummu cikin tausayawa. Ummin ikki ta zo tana ta yi ma BaÉ—É—o fada akan cewa ta matsa ma Ummu ta ci abinci.
"Ummi tun É—azu na ke yi mata mgana ba ta kalle ni ba."
Baɗɗo ta faɗa idanuwanta na tara ƙwalla.
"Ummu daure ki ci abinci kin ji ko? Kar ki manta ba ke kaÉ—ai ba ne ko domin abin da ke cikin ki."
Ummu Salma ba ta ko kalleta ba sannan ba ta motsa ba,har tea Ummin ikki ta haɗo mata mai zafi tana ta lallashinta da nasihan cewa ta sha ruwan zafi ya ɗan jiƙa mata maƙoshi kafin ta ci abinci amma kamar da dutse ake magana.
"Haba Ummu Salma kar ki ja da hukuncin Allah, Ubangiji yana sane dake, ki yi haƙuri ki sha ruwan zafin nan kin ji ko?
Har bakinta ta kai mata kofin amma ta kauda kai ba ta yi magana ba.
"Me ya sa kike haka ne Ummu? Ba fa ƙarshen rayuwarki ba ne ya zo domin Habibu ya sake ki. Ki yi haƙuri ki yi hakuri ki daure ko domin abin da ke cikin ki Ummu Salma ki sha wani abun don Allah."
Sai a lokacin ta kalli Ummin ikki da luhu luhun idanuwanta.
Ƙarshen rayuwanta ne ya zo mana. Me ya rage mata? Habib ya sake ta me kuma ya yi mata sauran ita Ummu Salma a wannan duniyan babu shi.
Duk magiya da lallashin Ummin ikki bai saka Ummu ta kurɓi ko ruwan tea ɗin ba Ammah ce da ke ƙofar ɗakin tun ɗazu tana jin duk magiyan da Ummin ke yi mata amma ba ta karɓa ta sha ba.
"Aminiya ƙyale ta. ."
Haka kawai ta faɗa ta juya ta koma cikin ɗakin ta. In ta ce Habibu zai ga daidai a rayuwarsa ta yi ƙarya tana so Allah ya wulaƙanta rayuwarsa ya farraƙa jin daɗinsa kamar yadda ya farraƙa jin daɗin ɗiyarta mace ƙwara ɗaya da Allah ya bata, ji Ummu Salma cikin kwana ɗaya ta fita kammaninta da Hayyacinta. Ita ko a matsayinta na uwa wani fata ko addu'a za ta yi ma Habibu face na Allah ya ɗanɗana masa ƙwatanƙwacin irin zafi da raɗaɗin da Ummu Salma ta ɗanɗana a dalilin shi, Allah ya haɗa shi da firgici da baƙin ciki irin kwatanƙwacin yadda ya haifar musu tare da duk wani masoyan su.
Har Ummin ikki ta shigo ta zauna kusa da ita ba ta sani ba sai da ta yi magana.
"Ta ƙi shan ruwan zafin abincin ma haka."
"Barta in ta gaji za ta sha ai ba za ta zauna ta mutu ba."
Ammah ta faɗa tana cije bakinta saboda ɓacin rai.
"Aa Aminiya ko saboda abin da ke tare da ita ya kamata ta ci wani abu. Yanzu haka tun jiya rabon ta da wani abu."
"To ba kin faÉ—a mata ba ta ji ba Aminiya? Ai tafi ki sanin ba ta ita kaÉ—ai ba ce. "
Ammah ta sake faɗa har tana girgiza ƙafa, ji take yi kamar ta rufe Ummu da duƙa ko ta huce baƙin cikin ta. Akan wannan ɗan iskan yaron da ya tozarta ta koma haka? Kawai ta yi shuru ne ba ta so ta yi magana ace ba ta tausayin Ummu. Ita a yadda take jin zuciyarta bai kamata Ummu ta sake kuka saboda Habib ya sake ta ba. Godiya ya kamata ta yi ma Ubangijinta domin bai kaddara mata rabon wahala anan gaba ba. Tunda Baffa ya karanta takardan sakin nan da kalaman dake ciki ta ji nan duniya ba wanda ta tsana sama da Habibu ta yi masa addu'an bala'ai kala kala a cikin zuciyarta da fatan ya tozarta kamar yadda ya tozarta su.
"Aminiya sai fa haƙuri yanzu sabon reno ne za ki yi Ummu kafin ta warware har ta cire abin a cikin zuciyarta "
Ummin ikki ta faɗa sanin halin Aminiyarta ta, ba ta ɗaukan reni da ɓata lokaci akan abu ko kaɗan.
"Aminiya."
Ammah ta kirata ta amsa tana kallon ta.
"Ba zan lalace akan lallashin Ummu Salma ba. Ita ba yarinya ba ce ta san illan yunwa da abin da damuwa ke haifarma gangan jikin É—an adam."
"Ba za a yi haka ba Aminiya."
Ummin ikki ta faɗa da sauri, kafin ta ɗora da maganarta Ammah ta miƙe da sauri za ta bar ɗakin Ummin ikki ta riƙo hannunta amma taƙi juyowa saboda kuka take yi ba ta so ta ganta tana kuka.
"Ki yi kuka Aminiya ko za ki samu sauƙi na fi kowa sanin ki na san yadda zuciyarki ke ciki a halin yanzu."
Ta faɗa tana miƙewa tsaye ta isa ga Ammah wacce tana ganin ta sai ta juyo ta ɗora kafaɗanta a saman na Ummin ikki ta fashe da kuka.
"Me ya sa za ta damu don ya sake ta? Da man bai dace da rayuwarta ba. Tana so ta kashe kanta saboda wanda bai san darajan ta ba? Ko so take yi wani abu ya same ta muma zullumi ya kashe mu a tsaye Aminiya?
Amma take faÉ—a cikin kuka Ummin ikki na bubbuga bayanta alamun lallashi sai da ta yi kukan ta fidda hawaye sannan ta É—ago ta share hawayenta.
"Ki kalli yadda Ummu ta koma Aminiya? In ta cigaba da zama a haka wata cutar za ta kama ta."
Ammah ta faÉ—a cikin rawan murya.
"Lallashi ba zai sa ta ji ba. Ki yi mata faÉ—a ne ki zare mata ido in ba haka ba za ta cutar da kanta sannan ta cutar da abin da ke cikin ta."
"Zan yi mata, kar ki damu ba abin da zai same ta "
Ta faÉ—a tana kallon Ammah da duk ta yi zuru zuru a yini É—aya kawai ta faÉ—a, lamarin nan ya dake ta sosai.
"Haka na riƙa yi ma Fatima a wancan lokacin. Tunda duk lallashin Baffa ba ta ji, amma da ta ga na buɗe mata wuta na fara masifa za ta yi shuru ta ɗau abinci tana ci."
Ta faÉ—a tana kallon Ummin ikki, kai ta gyaÉ—a mata kafin ta ce" Za ta warware sai a hankali Aminiya."
Kafin Ammah ta ce wani abu suka ji muryam Saddam ya shigo cikin ƙaraji yana kiran sunan Amma.
"Ammah"
"Amma kina ina ne?
Da sauri Amma da Ummin ikki suka fito falo, ita Ammah ta ma manta da yana gidan kwata-kwata.
"Saddam? Da man kana gidan?
Ummin ikki ta faÉ—a cikin mamakin ganinsa.
Bai ko damu da tambayanta ba ya kalle su ita da Ammah yadda suka ƙura masa ido da yanayin Amnma kawai ya sa ya samu tabbacin abin da Hamma Jibo ya faɗa.
"Da gaske ne kenan?
Ya tambayana yana kallon su.
"Me fa?
In ji Ammah tana kallon shi.
"Yanzu na buɗe data kawai sai ga saƙon Hamma Jibo a Family group namu wai mijin Ummu Salma ya sake ta saki uku."
Ammah ta wucesa zuwa kan kujera ta zauna ba tare da ta yi magana ba.
"Da gaske ne Saddam kai dai bari "
Ummin ikki ta faÉ—a cikin sanyin murya.
Zaro ido ya yi kafin ya ce" Da gaske ne? To ni duk ina ina hakan ta faru ban sani ba, kuma yau ne abin ya faru?
Ya tambaya cikin É—imuwa da mamaki
"E yau ne da asuba nan."
Ummin ikki ta faÉ—a kafin ta cigaba da faÉ—in" To kai kana ina ne duk ba ka ji zuwan mu ba."?
"Ummi ina can cikin ɗaki mun gama exams ina biyan bashin barci, tashi na kenan na yi salla sai na ga saƙo a group ina shiga kawai na ga Hamma Jibo na faɗin wai mijin Ummu Salma ya sake ta "
Ya gama faÉ—a yana sake duba wayarsa.