Sashe 63
Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Kan drowers É—in gefen gadon ta É—au remot ta rage karfin A.C É—in. Ta rasa yadda aka yi LamiÉ—o ke son sanyi haka da yawa daga É—an shigowarta É—akin barcinsa sai da ta ji sanyin har kasusuwan jikinta.
Shi fa ko hatta handel ɗin kofar ɗakin shi in ka taɓa sanyi ne ƙalau saboda ko yana nan ko baya nan ba a kashe A.C ɗakin 24/7 cikin sanyi yake yi, ita ta yi ta cewa sanyin ya yi yawa amma shi haka yake so duk da bai taɓa faɗa mata yana son sanyi ba a zamansu na shidda biyar ta fahimci haka, in ta zo ta ga ya ƙure sanyin za ta ɗauka ta rage ba zai yi mata magana ba amma tana barin wajen zai ƙara karfin gudun sanyi, tun ba ta fahimta ba har ta gane, daga baya sai ta fahimci haka Allah ya yi sa yana son rayuwa cikin sanyi, in ta ma tuna shi da yake rayuwa a saman ruwa ya saba da sanyi ba lalle ya yi masa illa ko cutarwa ba.
Har ta dawo ta zauna a gefen gadon saitin da kafafunsa ke shimfiɗe bai sani ba. Bargon ya ɗan yaye kafarsa doguwa fara sambal mai cike da gargasa mai yawa ta bayyana a waje, ɗan mirmishi ta yi har bakinta na matsowa wayarta ta ajiye a gefenta sannan ta saka taussaun hannayenta ta ɗago kafar tasa ta ɗora a saman cinyarta, lokaci ɗaya tana jan yatsun kafafunsa da suke wasu irin dogaye tafin kafarsa wani irin taushi kamar bai taɓa taka k
Ƙasa ba saboda yadda suke wani ja ja da fari fari kal, haka kumbunansaa kamar kumba bai taɓa fitowa ba tsabar yadda suke tas da su. Har ta gama jan yatsun na shi kuma duka sun yi ƙara, ita haka kurum tana son kafafun Lamiɗo balle ma in ta yi ta jan 'yan yatsunsa suka yi ta ƙaran nan yana saka ta a cikin nishaɗi.
ÆŠayan ta jawo daga cikin bargo itama ta É—aura a saman cinyarta itama kamar É—ayan haka ta yi mata amma ko motsi ma mallakin kafar bai yi ba duk da ta san zuwa yanzu ya san da wanzuwarta a É—akin tunda ba shi da irin nauyin barcin nan.
Gargasan kafarsa guda ɗaya ta ja da ƙarfi har sai da ta tsinke, hakan da ta yi ne ya sa ya ɗan motsa kafarsa guda ɗaya sai ta kalle shi da mirmishi a fuskarta kafin a hankali ta ce.
"Ranka ya daÉ—e ka tashi haka nan yamma ta yi "
Ta faÉ—a wani wani irin omo mai cike da aji da sanin ciwon kai
Shuru kamar ma baya jin ta, domin bai kara motsawa ba
"Tun jiya da daddare da ka shigo gidan nan kake barci har wayewar garin yau. Ba ka ci komai ba fa Ranka ya daÉ—e?
Ta sake faÉ—a tana É—an jan gargasan kafarsa guda É—aya.
Sakwan goma sannan ya iya motsawa daga kwanciyar lokaci ɗaya yana cire filon da ya rufe fuskar shi ya mayar da shi bayan shi, sannan ya miƙe a hankali kamar bayansa ya samu matssala bakinsa na ɗan motsi yana karanta adduar tashi daga barci, lokaci ɗaya kuma yana sauke kafafunsa daga saman cinyarta ya samar musu mazauni a saman lallausan cafet ɗin ɗakin.
Kafin kuma da sauri ya saka hannu yana kare fuskarshi saboda hasken waje ya É—an shigar masa ido.
"Ni na buÉ—e windows saboda haske ya shigo kaÉ—an."
Ta faÉ—a cikin sautin ta, akwai wuta amma ba ta kunna gulop ba sanin ba ya son haske sosai.Â
Miƙewa ta yi ta ɗuka a gaban shi hannu kawai ta ɗan zira kasan gadon sai ga shi ta jawo masa wani ttatausan takalmi na maza zuwa wajen kafafunsa.
Ba musu ya zura dogayen kafafunsa a ciki sannan ya yunkura ya miƙe lokaci ɗaya itama tana miƙewa sai ga ta a gaban shi yar firit. Kallon shi take yi tana mirmishi a fuskarta shima ya kalleta da idanuwansa masu ɗan girma kaɗan kafin ya ɗan rusuna su, mirmishi ya yi mata amma daga gefe da gefen bakin shi ne kawai ya ɗan motsa.
Muhammad Nasiru Muhammad (LamiÉ—o) Sannan kuma Yariman Daura, magajin mai Maimartaba Yarima mai jiran gado.
Wani irin dogon namiji ne faffaɗa, ga tsaho ga jikin murjewa ta cikakkun maza. Lamiɗo na da tsawo sosai domin ko size ɗin takalminsa 45 ne, kuma wannan tsahon na zuru'ar sarkin Jafaru ne, sarki na 11 a tarihin masarautar Daura, shi ne asalin tsatson su har kawo yanzu. Su ke da wannan tsawon kamar ƙiran samudawan farko, sannan suna da girman jiki matansu da mazan su. To Lamiɗo haka yake har ma yafi mahaifinsa Maimartaba Alhaji Dr Nasiru Muhammad Daura cika ido da ƙwarjini. Ahalinsa na Daura ba su da hasken fata sosai amma shi Lamido fari ne jajir, saboda Mami farar bafullatana ce kyakyawa, a wajenta ya ɗauko dogon hanci amma fuskarsa tana da ɗan faɗi ita kuma ta mahaifinsa ce, amma sumar kansa mai santsi da cika ta Mami ce, da yake shi ma'abocin tara suma ne gashi nan sumar ta yi yawa ta kwanta luf tana shan gyara. Sannan bakin sa yana da ɗan faɗi kaɗan zagaye da sajensa da ya zagayo har gemunsa da ya yi ɗan tsawo. Lamiɗo tun yana saurayinsa yana son tara sumar kai da barin gemu har kuma yanzu bai sauka daga kan wannan daɓi'an nasa ba.
Ko a yanzu ma gashi duk ya cika fuskarsa amma duk da haka kyawunsa da cikar zatinsa sun bayyana. Balle ma da ya fara tafiya ya bar gaban Balkisu cikin tafiyarsa ta gif gif ta cikkakun mazan duniya kallo ɗaya za ka yi masa ka shaida Muhammadu ɗan Nasiru da Fatima Sadauki ne, kuma jarumi ne yanayin sa irin na fusattatun maza ne giant masu mazantaka da ke dukan zuciyan duk wanda ya kalle su, jarumatar su ba ya ɓoyuwa, sannan suna iya rike numfashin wanda ya kalle su gaba da gaba na wani lokaci saboda ƙwarjini da haibar da baiwa ce Allah ya ba su, sannan yanayin su komai karatun mutum akan sanin hallayan ɗan adam baka isa ka fahimci yana yin su ba, ko ka ce ga abin da suke so ko ba sa so ba, irin su Lamiɗo sai zama ya haɗaku na shekaru masu yawa shi ne har za ka iya fahimtar lamuran rayuwarsu, amma ba wai don su furta da bakin su ba.
"Wanka za ka yi ranka ya daÉ—e?
Balkisu ta faÉ—a tana mai kallon bayan shi.
"E.."
Ya amsa mata cikin dakakkiyar muryansa amma cikin sanyin amo a karon farko sannan ya tura ƙofar tiolet ɗin ya shige ya rufo.
 Numfashi ta fesar tana mai sake bin bayan shi da kallo bayan ya shige. Sanye yake da bakin wando wanda iyakarsa gwiwan kafafunsa sannan jikinsa wata farar riga ce mai dogon hannu tana da botira a gaba amma bai saka boturan ba, ƙirjinsa mai cike da gargasa ya bayyana a waje kuma tasan ma dalilin da yasa ya yi saurin barin in da take tsaye saboda haka ne.
Tunda take ba ta taɓa ganin namiji mai kunya irin mijinta Lamiɗo ba
Yau shekaran su shidda da auren su tare da albarkan ya'ya biyu amma bai taɓa yarda ta gan shi daga sama har ƙasa naked ba, itama za ta yi rantsuwa bai taɓa kallonta haka ba. Da farko ta ɗauka ko ba ya son ta ne yasa yake yin haka sai da zaman su ya mika ta fahimci haka Allah ya yi shi, yana jin kunyar tsaraici shi ya sa ko kayan barci baya sakawa masu sharara, in zai kwanta sai ya saka dogon wando, da riga mai dogon hannu ya rufe jikinsa ba ya so ya fidda wani tsaraici na jikinsa duk ko da ita ɗin matarsa ce, yana jin nauyi da kunyar ta gan shi a haka, shima bai iya mata dogon kallon matukar ta fidda masa tsiraici, domin akwai wani lokacin tana da cikin Sultan suna gudanar da Sunna ta kudiri niyyar sai ta ga abin da Allah ya hallata mata. Ita da mijinta amma ace ba ta san girman shi ba, sai da ta bari sun natsa cikin harkan sannan ta kunna hasken ɗakin, ranar ta ga abin mamaki da saurin gaske ya faɗa gefenta cikin zafin nama ya jawo bargon dake gefe ya rufe jikinsa, sannan ya juya mata baya cikin wani sauti amon murya ya ce itama ta rufe jikinta. Ta daɗe lamarin yana ba ta mamaki kuma ta ji haushi har sai da ta yi masa magana da cewa ita fa matarsa ce halaliyarsa amma yana jin kunyar ta ga jikinsa, ko shima ya ga jikinta. Har ta gama maganganunta bai ce mata komai ba, bai ma sake tayar da maganar ba sai da ya tafi ne ya tura mata da saƙon cewa ta yi haƙuri daga haka bai ce komai ba kuma bai sauya ba, dole ita ta bi shi a yadda yake tunda haka Allah ya hallice shi, hallayan shi ne a haka kuma ba zai iya canza kan shi ba.