Sashe 3
Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta faÉ—a tana sake tura bakin ta gaba, ajiyar zuciya ta sauke ta fita daga nan ta koma Tiktok tana ta kalle-kalle amma tana ta duba lokaci har tara ta kusa amma Habib bai dawo ba, kuma bai kira ta ba, ta fita daga wajen da niyar sake kiran shi sai kuma ta koma cikin chart É—in ta bangaren status, kwatsam ta ga Hamma Sadam ya saka status 4m ago.
Da rawan jiki ta buɗe hotuna ne kuma hotunan ba baƙinta ba ne, duk wani ɗan Nageria dake mu'amala da social media ya san hotunan nan saboda yadda suke trending a duka kafafan sada zumunta tunda satin nan ya fara.
Amma abin da ya ba ta mamaki caption ɗin Hamma Sadam a ƙasan hoton
"Allah ya sanya alheri my Sis Badi'atu"
Baki ta buÉ—e sannan ta rufe tana sakin wata dariya.
"My Sis? Lalle ne ma to ko a yaushe ta zama sis É—in ta shi ni ban sani ba?
Ta faÉ—a a fili tana sake yin dariya hotuna ne ya saka sun fi kala biyar na Amarya Badia'tu da angon ta wato Pre-wedding pictures ne da yan zamani Æ´a'Æ´an masu kuÉ—i ke yi in za su yi aure. Hotuna ne fitattu da suke tashe a yanzu bikin sai satin sama ne amma tuni hotuna da katin shagulgula sun watsu a duniya saboda bikin na masu kumbar susa ne da masu mulki da sarauta
Duk in da ka shiga hotunan Amarya da angon ne, sai katin bikin da na Program of events ke yawo a duka manya bloggers É—in mu na arewa gabaÉ—aya.
Kallo take yi tana taɓe baki kafin ta ce a fili.
"Allah ya sa ta ma san kana yi Hamma Saddam"
Ta faɗa tana sake yin mirmishin gefen baki, sau ɗaya ta taɓa ganin ta lokacin da Ammah ta matsa mata suka je naɗin sarautan Hamma Lamiɗo a matsayin Yariman Daura. Tun a lokacin ta ga jin kai da isa a wajen wannan yarinyar, ta tabbata tusa kai ne kawai irin na Hamma Saddam ba ma a san yana yi ba. Wata ƙila Hamma Lamiɗo ya yi ma kara shima kuma tana da tabbacin bai san ma yana yi ba. Abin da ya saka na karshe a status ɗin sa katin bikin ne da shagulgulan da za a yi tun satin bikin har zuwa ranar ɗaurin aure.
ÆŠaurin aure ne kawai za a yi a masarautar Daura amma sauran shagulgulan duk a garin Abuja za a yi.
Ba ta san ta kwashe da dariya ba sai da ta ga caption É—in Hamma Sadam a kasan katin
"Family and Friends bikin gidan mu ne fa ya zo. Bikin gidanmu saboda haka ban ɗauke ma kowa ba."
Ummu-Salma tana dariya har sai da ta shaƙe, Hamma Sadam na da abin dariya wai bikin gidan su ne.! Yaushe bikin gidan masu Sarauta da masu mulki ya zama na gidan su? Bikin ɗiyar sarkin Daura ALHAJI Dr. NASIRU MUHAMMAD DAURA ne fa za a yi, za ta auri yaron mai ba ma shugaban ƙasa shawara akan yaɗa labarai, shi ne wai Hamma Sadam ke ta rawan jiki har yana faɗin wai bikin gidan su ne, gaskiya Hamma Sadam akwai tusa kai ba ƙwarjini da gayya ta masa reply akan status ɗin sa na ƙarshe.
"Ka ji Hamman nan, bikin gidanmu ma fa ka ce? Ko dai bikin gidan su Hamma LamiÉ—o?
Kamar yana jiran ta sai ga shi ya turo mata da sticker na an ɗaga wani an tika da ƙasa sannan tare da emojin nan na ɓacin rai.
A ƙasa ya haɗo da cewa.
"Bikin gidammu ne Ummu ko ke ba na gidan ku ba ne?
Kai tsaye ta bashi amsa da cewa.
"A'a wallahi ba na gidanmu ba ne Hamma."
Emojin mamaki ya turo kafin ya ce" Ammah na gefe na nuna mata abin da kika ce?
Da sauri ta ce" Rufa mini asiri Hamma bikin gidan mu ne."
Ta rubuta sannan ta tura emojin heart har da na rawa.
"Yauwa yarinya."
Ya rubuto tare da sticker na dariya, saboda haushi ba ta amsa shi ba sai ma ta kashe data ta ajiye wayar, Hamma Sadam na so ya jawo mata masifan Ammah a daren nan ba ta shirya ba, ai tana jin yadda Amma take shirya ma wannan bikin ko ita uwar Amaryan albarka. Wanda take yin abin nan domin shi wataƙila ma ba zuwa zai yi ba, mutumin da an sha yin abubuwa na daɗi da aka sin su bai taɓa zuwa ba, shi bai ɗauki zumunci ma abakin komai ba, ba abin da ya sani sai tuƙin jirgi, kuɗi kawai alhalin ahalinsa suna da tarin dukiyar da har jokokinsa ma ba za su yi talauci ba, tana da tabbacin ko rantsuwa ta yi ba za ta yi kaffara ba, ba zai samu zuwa ɗaurin auran ƙanwarsa ba shi ya sa da bai zo na ta ba, ba ta damu ba Ammah ce ta damu saboda sun yi mgana ya ce mata zai zo, a cewarsa ya ɗauka za su iso bakin gaba ne ana gobe ɗaurin aure sai kuma tafiyar ta su ta sauya tsari shi ya sa bai samu zuwa ba. Duk fa Ammah ce ke ta yawo da wannan mganar shi gogan ba wanda ya ji haka daga bakin shi. To wai wanda ko ɗaurin auran shi bai samu zuwa ba to na waye zai je? Shi ya sa ma wanda ya damu in bai gan shi a sha'aninsa ba, shi ke da kaico shi dai bai ma san kana yi ba, shi fa mutumin nan dabam yake, ɗauka yake kuɗi sune muhimmi a rayuwar nan daga naira ɗaya har miliyan goma zai iya tura maka amma kuma ba zai iya zuwa ya yi maka murna ko jaje ba shi ya sa har gobe bata taɓa saka Hamma Lamiɗo a jerin mutane masu karamci ba, ta fi saka shi a jerin mutane masu girman kai da ɗagawa.
Â
Tana cigaba da cin doughnuts ɗin ta, tana kuma kurɓan tea a lokaci ɗaya amma sai taɓe baki take yi ita kaɗai daga gani hakan yana daga cikin ɗabi'arta.
Ita fa tun wancan satin da ta je gida Ammah ta dame ta da labarin bikin nan na Daura ta ji ba za ta sake komawa ba sai bayan an gama bikin nan, domin hankalin Ammah ba a kwance yake ba yanzu sai ta ga ta je Daura an gama biki lafiya ta dawo tukunna. Baffa dai ba ruwan shi ba lalle ne ma yaje ɗaurin auran ba Ammah kuma ba wanda ya isa ya ce ba za ta je ba ai sai ranar gidan ya kwana ba lafiya. Baffa ma yasan halin kayan shi, shi ya sa ba ya ma gigin shige mata na shi addu'a ne da fatan alheri, domin in dai akan sha'anin abin da ya shafi Hamma Lamiɗo ne ko Baffa bai da ta cewa, da jikinta da zuciyarta take hidimtama wannan bawan Allah da Ubangiji ne ya haɗa wannan ƙaunar da tana tunanin ko su ƴa'ƴan cikinta ba ta nuna musu ƙauna da kula da alamuransu da muhimmanci kamar yadda take kafa-kafa da duk wani al'amarin da ya shafi Hamma Lamiɗo.
 Shi ma kuma ba ya iya tsallake umarninta komai tsaurin shi a gare shi. Da Amma kaɗai yake iya doguwar hira cikin nishaɗi, ita ce kawai take iya ganin dariyan shi har da haƙora a waje. In ba za ta manta ba lokacin tana aji biyu a matakin babban sakandiri aka yi bikin Hamma Lamiɗo, auran da a farko cewa ya yi ba ya so tunda haɗin daga kakarsa ce Fulanin Daura, Mai martaba kuma ya ce ba zai matsa masa ba, Mami kuma ta ce ina ruwanta da sha'anin Lamiɗo? A nemi uwar sa Ammah ita ce za ta iya saka baki akan mganar,
Hamma Lamiɗo da bayan gaisuwa magana ta mintina biyar ba ta taɓa haɗa shi da Mami a matsayinta na mahaifiyarsa ba, ko da za su yini waje ɗaya su kwana. Ba ma ita ba, Hamma Lamiɗo zai yi rayuwa da mutum na tsawon kwanaki amma ban da gaisuwa magana ta fatar baki ba zai yarda ta haɗa su ba. In ko ka matsa ka yi hira da shi kai ne da haushi, domin a ginshiƙe zai din ga tafiyar da kai da har sai ka yi zuciya ka ƙyale shi.
Haka ko aka yi tawagar Fulanin Daura har cikin falon Ammah, ta zauna ta roƙe ta da ta sanya baki Lamiɗo ya karɓi auran nan, da suka je suka karɓo masa ƙafa da ƙafa har wajen Mai martaba Sarkin Kano a lokacin Balkisu ba ta daɗe da dawowa daga ƙasar Spain ba, a can ta yi duka karatun ta na likitan ci. Ammah ta yi ma Fulanin Daura alƙawarin za'a yi auran nan kuma maganarta ya tabbata. Tana cema Hamma Lamiɗo in har ya ɗauke ta a matsayin uwa to ya karɓi wannan auran da cewarta da auran ko wata biyu ba a yi ba. Abin mamaki sun rufe shekara da wattani ne da aure matar Hamma Lamiɗo ta haihu, har yau Ummu-Salma na mamakin wannan abu, ka ce ba ka son aure amma kuma ana yi sai shuru, kuma ko zuwa suka yi tare ba mai gane yanayin shi. Ba za ka ce yana son ta ba, ba kuma za ka ce baya son ta ko da wani lokaci yana nan a ginshiƙen sa. Shi fa ba ka iya gane ma yanayinsa kwata-kwata, fuskarsa ba ta bayyana farincikinsa ko bakincikinsa.
Ammah kuma al'amarin ƴa'yanta kuwa sai dai Ummi ikki ta yi gaba ita tana baya, amma in dai lamarin Hamma Lamiɗo ne ba ta jira ba ta kuma sakawa a yi mata, ita ce da kanta take yi masa komai, tun tana ƙarama ta shaida Ammah ta fi hidimtama Hamma Lamiɗo fiye da su ƴa'ƴanta na cikinta tun tana damuwa har ta saduda ta sare. Ta taɓa tambayan Baffa me ya sa Ammah ta fi son Hamma Lamiɗo akan kowa a gidan nan?
"Sabo da shima É—an ta ne Ummu Salma. Nima ba ki ga ta fi son shi a kaina ba?