Sashe 66
Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ummu Salma ta rushe da kukan da take ta riƙewa. Ammah ta duka a gabanta lokaci ɗaya tana dafa kanta.
"Ki yi hakuri Auta kin ji ko?
Sai Ummu ta gyaÉ—a mata kai amma kukanta ya kasa tsayawa.
"Mu kan mu muna cikin damuwar abin da ya faru, amma yanzu mu damuwarmu taki ce Auta. In ba ki kwantar da hankalin ki ba, muma hankalin mu ba zai kwanta ba. Samun kwanciyar hankalinki shine farincikin mu da mu da yan'uwanki gabaɗaya, tunda dai ba mu isa mu sauya abin da ya faru ba, to gwara mu taru mu yi haƙuri gabaɗaya mu fauwalla ma Allah duka lamuranmu da sannun komai zai wuce sannan kuma zai yi miki sakayya in sha Allahu "
Duk wannan dogon nasihan da Ammah ke yi mata ba ta ji ba kuka kawai take yi har da gunji.
"Yanzu shike nan Habib ya rabu da ni har abada Ammah?
Ta faɗa lokaci ɗaya tana kallon Ammah idanuwanta suna masu zubar da ƙwalla.
"Shike nan Habib ya rabu da ni. Shike nan ya gama da ni Ammah?
Amma ta yi kasaƙe tana kallonta cikin takaicinta. Ba ta son ta yi ta ma yaro magana yana yi mata taurin kai.
"Ammah ina son Habib. Ina son na sake rayuwar aure da shi. Wallahi ina son shi, na kasa mantawa da shi sai na ke ganin kamar tunda ya rabu da ni har abada ba zan sake farinciki ba Ammah."
Ta ƙarishe faɗa tana mai sakin wani marayan kuka mai fitowa da shessheƙa
Ammah da takaici ya ƙume ta, ture ta ta yi kafin da sauri ta miƙe tana faɗin" Ke kam dai an yi sakara Ummu, wallahi in da kin san yadda na tsani sunan yaron nan da baki yi gangancin ambaton shi a gabana ba. Haba don Allah yaron da ya yi miki wulakanci ya tozarta ki kike ikirarin har yanzu kina so saboda ba ki da zuciya Auta?
Ta faÉ—a lokaci É—aya tana balla mata harara.
Ummu ta danne kukanta sanin halin Ammah yadda ta fusata sai ta iya kai mata duka ma in ba ta yi wasa ba.
"Yaron da tunda ya sake ki bai sake waiwayoki ba, ba ruwan shi da ke ballatana yadda kike rayuwa, cikin dake jikin ki ma bai damu da shi ba ballatana ke, amma saboda wawanci ke kina nan kina kuka kina cewa wai kina son shi, to Allah ya tsine ma wannan son Ummu ba shi da albarka tunda bai tsinana miki komai ba sai tozarci da wulakanci"
Yadda Ammah ta harzuƙa tana ta faɗa ne yasa Ummu tana hawaye ta ce" Ki yi haƙuri Ammah."
"Ke kika sani wannan kuma ruwanki ne, ki yi hakuri ki rumgumi kaddaranki, ki sani yanzu rayuwarki ta sauya ki rika tuna Habibu a matsayin wani darasi ne wanda ya shuɗe daga rayuwarki, sannan ki riƙa tuna ba ke kaɗai ba ce nan da wani lokaci za ki zama uwa. Abu na ƙarshe kuma ki zauna ki yi ta kuka da damuwa kar ki yi farinciki a kan wanda har abada bai san kina yi ba sannan bai damu da rayuwarki ta cigaba ko ta tsaya ba. "
Ammah ta gama faɗa tana barin wajen zuwa kitchen ta bar Ummu na kuka wurjajan lokaci ɗaya tana faɗin" Ki yi haƙuri Ammah."
Ammah na jinta ta yi mata banza takaici duk ya kumeta, tana jin baƙin ciki in ta ga Ummu Salma na kuka saboda wannan yaron mara mutumci, wanda bai san kana yi ba har da cewa wai tana son shi, Allah ya tsine ma wannan soyayyar domin su kansu iyayenta bata amfanesu da komai ba.
Nan Ummu ta bar ma Ammah gyaran wakenta ta shige ɗaki ta kwanta a saman gado ta cigaba da rusan kuka kamar ranta zai fita kowa yaƙi ya fahimceta, kowa ya kasa gane yanayinta.
Ko za ta manta da komai ba yanzu ba, wataƙila sai an ɗauki wani lokaci su yi mata uziri su gane yanayinta har gobe mafarkin Habib take yi sannan tana begensa ba laifinta ba ne laifin zuciyarta ne da ta kasa tsanar shi har yanzu.
Ranar yini ta yi kuka fuskar duk ta yi ja, idanuwana sun tasa Ammah ba ta sake bi ta kanta ba ko abincin da ta shigo mata da shi cewa ta yi in ta gama dama ta tashi ta ci in ba ta ga dama ba ta cigaba da kuka saboda wanda bai san tana yi ba, ba ta sake bi ta kanta ba ballanta ta lallasheta. Ita ce don kanta ta haƙura da kukan ta sauko ta ci abinci jin cikinta na ta murɗawa, su Baffa ba su dawo a ranar ba sai washegari da rana, Ammah kuma ba ta sake mata magana ba, tun bayan gaisuwan safe, itama sai ta kama kanta ta daina kuka amma a ƙasan zuciyanta dankare take da damuwa.
Da ta je gaishe da Baffa idanuwanta ya kalla kawai ya fahimci ta yi kuka.
"Auta har yanzu dai ba ki daina koke-koken nan ba?
Sai ta kasa yi masa musu, tunda gaskiya ya faɗa shuru ta yi kanta na ƙasa tana wasa da gefen hijabin jikinta
"Har yaushe ne za ki kai kina wannan kukan Auta? Kuka fa ba zai yi miki magani ba sannan ba zai taɓa dawo miki da abin da kika rasa ba. Hakuri da tawakwalli shi ne mafita ki samar ma da kanki lafiya ki bar zuciyarki ta huta sai gangar jiki ta amshi canjin ki Auta. Juna biyu kike da shi halin da kike ciki zai iya shafar abin da ke cikin ki, in hakan ta faru kuma kema kina cikin matsala, faruwan haka kuma daidai yake da muma kin saka mu cikin damuwa Auta"
Tunda Baffa ya fara magana ta fara hawaye.
"Ki yi hakuri Auta ki yi tawakalli. Ubangiji yana sane dake, shi ya haɗa ki da Habibu a karon farko, kuma da saninsa ya raba ku, in kina yin haka sai ki yi masa bultulci, ki sani in kika yi hakuri Ubangiji mai rahama ne mai jinƙai, watakila ya yi ma rayuwarki wani kyakyawan canji anan gaba. Canjin da zai goge miki dukkan wani bakin cikin da kika taɓa shiga a rayuwarki."
"Ka yi hakuri Baffa."
Ta faÉ—a cikin kuka tana toshe bakinta da hijabin hannunta.
"Ka yi hakuri Baffa, in sha Allahu na daina."
Ta sake faÉ—a cikin kuka.
Baffa ya ji daɗi ya jinjina kai kafin ya ce" Allah ya sa Auta. Ina fatan Ubangiji ya sake sauƙaƙa miki."
Ta amsa da Amin a hankali tana mai sharan ƙwalla ta jima a ɗakinsa yana ta yi mata nasihan kafin ta koma ɗakin Ammah.
Ammah ko sai da Ummu ta bar É—akin Baffan sannan ta shiga tana faÉ—an cewa Ummu Salma ba ta bukatar lallashi, in ba ta bayan gida aka fito mata ba haka za ta zauna tana neman kashe kanta saboda wanda bai san tana yi ba.
"Jamila."
Baffa ya kira sunanta, ta kalle shi amma ba ta yi magana ba.
"Ki yi haƙuri da Auta, don Allah ki yi haƙuri da ita domin a halin da take ciki tana bukatar lallashi da ban baki ba faɗa ba."
Ammah ta yi shuru ba ta yi magana ba.
"Na san kina ƙoƙari amma don Allah ki ƙara kin ji ko?
Ya sake faɗa yana riƙo hannunta guda ɗaya.
"Ba ki ce komai ba.'
Ammah ta yi jim kafin ta ce" Baffa cewa fa take yi wai har yanzu tana son yaron nan wai kuma tunda ya rabu da ita ba za ta sake yin farinciki ba,"
Ammah ta faÉ—a cikin takaici in ta tuna maganar sai ta ji zuciyanta na zafi.
"To ai wannan sai a hankali Ammah, a sannu sannu duk za ta manta da komai. Ke dai kawai ki É—an bata lokaci."
Ammah ta ɗan ɓata rai kafin ta ce" To Baffa wani irin so kuma! Kalli fa wulaƙanci da tozarcin da ya yi mata amma ita har yanzu son shi take yi?
Baffa ya yi mirmishi kafin ya jinjina hannunta a cikin na shi yana fadin" Ina ruwan zuciya Ammah, ba laifin Auta ba ne bata da alhakin sarrafa zuciyarta. Amma lokaci ne wallahi tallahi za ta manta da komai, watakila sai dai in ta kalli abin da ke cikinta bayan ya fito duniya ta iya tuna da shi"
Ammah ta yi shuru tana kallon shi sai ya gyaÉ—a mata kai kafin ya cigaba da faÉ—in" Na baki tabbacin haka, ki dai kawai ki É—an kara mata lokaci."
Sai Ammah ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce" Shike nan Baffa Allah ya ba ta dangana."
Ya amsa da Amin yana faÉ—in" Ko ke fa matar Baffa"
Ammah ta yi mirmishi ba tare da ta yi magana ba.
Fita ta yi zuwa kitchen ta shako wani ƙaramin faranti da kulolin abinci sai ruwa da kofi ta kai ma Baffa yana ci suna ɗan taba hira kaɗan kaɗan ita kuma tana gefen shi tana yi masa fitita da mafici tunda ba wuta sun ɗauke.
"Baffa gobe fa su LamiÉ—o na hanya."
Kai ya É—an jinjina kafin ya ce" Na ji Abdullahi na maganar shi zai je fillin jirgi ma ya taho da su."
Ammah ta washe baki tana faÉ—in" Haka ya ce mini, Baffa LamiÉ—o fa ya fi wata biyar rabon shi da garin nan"
"Zai yi gaskiya."
Ya faÉ—a yana kai cokali bakin shi cike da shinkafa da wake jallop.
Ammah ta cigaba da faÉ—a masa ta kira Ummin ikki ta faÉ—a mata gobe za ta zo ta taya ta girkin da za ta yi musu na tarba.
"To ke ki bari surukan ki su zo su yi girkin mana."
Da sauri Ammah ta ce" A'a LamiÉ—o ya ce na yi masa tuwon shinkafa miyar zogale. Kuma kasan in bani na yi girki ba yana ganewa."
Baffa ya kalleta kawai ya yi É—an mirmishi.
"To uwar LamiÉ—o."