← Book details Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 92

Sashe 17

Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya faɗi haka sannan ya raɓa ta gefen ta ya bar falon, nan ƙasan cafet Ummu ta durƙushe tana mai fashewa da kuka, ji take yi kamar ba ita ba zuciyarta na zafi kirjinta wani abu ya tokare mata da ya kasa wucewa kuka  ya sake kece mata, tunani take yi ko Habib ya fara shaye-shaye ne yau wata ƙila ya sha wacce ta fi karfin ƙwakwalwarshi shi ne ta faɗa masa ba daidai ba, amma ta ya ya zai ce ta zubar da cikin jikinta cikin sunna ba ta taɓa jin maganar da ta ruguza zuciyarta kamar wannan mganar ba, me mganganunsa suke nuna mata! Me ya sa ta ji zuciyarta na yi mata rawa akan Habib? Me ya sa yau ya sauya mata? Me ya sa zai yi haka?

Kuka take yi kamar ranta zai fita, tana kuma dafe cikinta da ta ji wani kaunar shi na ratsa jinin jikinta, tun tana gida ita mai sha'awar yara ce duk in da ta ga yaro sai ta ji da man na ta ne, ɓarin ta na farko kuka ta dinga yi sai da Ummin ikki ta yi ta lallashin ta. Ammah kuma faɗa ta dinga mata da cewa ba Allah ne ya ba ta ba, sai ta yi haƙuri shi zai sake ba ta wani, to ga Habib na faɗin da man ko cikin bai bare ba za a zubar da shi, an ya yana cikin hayyacinsa kuwa ita ce fa Ummu-Salma da ya ke so kamar ransa, ita ce matarsa da ya ke burin ta zama uwar ƴaƴan shi, me ya sa yanzu zai zo yana wasu mganganu?

Ta kasa gano dalili, ta fi tunanin wani abu Habib ya sha da ya birkita masa tunani amma a cikin hayyacinsa ba zai ce ta zubar da gudan jininsu ba. Wataƙila zuwa da safe zai dawo hayyacinsa ya ba ta haƙuri ya fahimci kuskuren da ya yi, ita kuma za ta yafe masa ta rufe mganar nan har duniya ta naɗe ba wanda zai ji

"Habib na shaye-shaye ne?

Wata zuciyar ta tamabaye ta, ko ba ya yi wataƙila dai jiya ya fara haka ta ba ma kanta amsam yunwa ta ke ji, amma ta kasa iya saka ma cikinta komai anan saman cafet ɗin ta kwana sai gabda asuba ta koma ɗaki, ta iske Habib na ta barci sai ta lallaɓa ta kwanta a gefen shi tana sauke ajiyar zuciya idanuwanta sun kumbura saboda kuka da man ita mai saurin kuka balle ta samu dalili, cikin lokaci barci ya kwashe ta duk da kanta na ciwo ba ta tashi ba sai da ta ji ƙaran ruwa a banɗaki sannan ta san asuba ta yi. Habib ne ya fito sanye da jallabiya ko kallonta bai yi ba ya saka hula ya fita zuwa masallaci.
Ita kuma daƙyar ta lallaɓa itama ta shiga tiolet ta ɗauro alwala ta zo ta ta da salla.

Ta idar kenan Habib ya shigo jallabiyan jikinsa ya cire daga shi sai ƙaramin wando ya koma ya kwanta. Ita kuma sai da ta gama addu'o'in ta sannan na nannaɗe darduman ta ijiye ta tare da hijabin nan saman side drower na gadon. Habib idanuwansa biyu yana latsa wayarsa yau asabar ba fita aiki.

"Ina kwana Noori."

Kamar bai ji ba sai da ta sake maimaitawa sannan ya amsa da lafiya kamar ba ya so har yana juya mata baya.
Ajiyar zuciya ta sauke ko a cikin Sujjadan ta sai da ta roƙi Allah ya dawo da hankalin Habib jikinsa ita fa a tunanin Habib ba ya cikin hayyacinsa ne.

Gefen sa ta koma ta kwanta tana cigaba da saƙe-saƙe.
Saboda rashin barcin da ba ta yi ba ya sa ta ji barci na shirin fizgan ta sai dai me? Kamar a mafarki ta ji Habib ya matso kusa da ita, yana shafa ta sai da ta yi mirmishi a fili a tunanin ta Habib ya dawo hayyacinsa ne tuni ta zage ta bashi dukkan halin kai, da a ce Ummu ta san manufar Habib a kanta da ko sama da ƙasa za su haɗe ba za ta sake ba shi jikinta ba.

Da safiyar ma da ta ɗumama musu taliyar ya ci sai ta dafa musu ruwan tea suka haɗa da shi, kuma a gida ya yini bai fita ba duk da bai sakar mata fuska ba amma in ta yi masa mgana zai amsa sai dai ba cikin walwala ba, sai dai yinin nan da ya yi a gida Ummu-Salma ta gane ba ta da wayau ita ya yi ta moruwa ita kuma jin daɗi take yi a tunanin ta ya bar wancan mganar ganin bai sake yi mata ba, har wani zumuɗin ba shi haɗin kai ta ke yi yana ta murzanta ko tausayi ba shi da shi a kanta alhalin a daran ranar ma ta ci abinci kenan ta amayar da shi duka kuma bai saka ya ɗaga mata ƙafa ba. Haka ma washegari a gida ya yini sai da yamma ya samu fita shima bayan duk ya gana sakar mata gajiya, Ummu ba ta damu ba tuni ta manta da mganar Habib a tunaninta ya dawo cikin hayyacin sa ya bar mganar, tun da kuma ta ga yana cin abincinta sannan yana neman ta a shimfiɗa sai ta yi tunanin addua'nta ce ta karɓu Habib ya dawo cikin hayyacinsa. Shi ya sa ma ba ta yi mganar da kowa ba hatta Bestie ko da ta kira ta a ranar lahadi suka daɗe suna magana tana ta tambayanta.

"Bestie kina dai lafiya ko?

Ita kuma ta ba ta tabbacin lafiyan ta ƙalau, a tunaninta ta rufe mganar ba wanda zai ji.
Sai dai abin da ba ta sani ba Habib zai yi silan tarihin auren ta da shi zai zama abin tunawa gare ta da ahalinta na har abada.

Abin da ba ta sani ba game Habib, ko ta manta ya ce lokaci ya ba ta. Wataƙila yana jiran cikar wa'adin kwanakin da ya ɗiba mata ne"

****

Monday.

Tun a daren jiya da zazzaɓi ta kwana da asuba ma sai da ta yi amai amma a haka Habib ya neme ta, ta fara jan jikinta da wannan rashin tausayin da Habib ke nuna mata. Za ta gama yin Amai amma sannu Habib ba zai ce mata ba.

Yadda ya ke son ta ta É—auka tare za su yi wannan laulayin amma sai ta ga aka sin haka.
Ya ganta kwance cikin bargo tana rawan sanyi amma ya ce ta tashi ta sama masa abin karyawa, haka nan ta tashi tana makyarkyata ta fita zuwa kitchen buredi ta gasa masa a ovean ta dafa ruwan zafi ta so ko ƙwai ta soya masa amma ta kasa sai ta haɗa masa da sauran cake ɗin ta yi bai ida ƙarewa ba.  Ba ta ma tsaya ba ta koma ta kwanta shi kuma sai da ya ci ya yi nak sannan ya fita ba tare da ma ya yi mata sallama ba.

Haka Ummu ta yini kwance da zazzaɓi sai can zuwa yamma ne ta ji sauƙi tun da ta sha paracetamol komai babu a cikinta ruwan lipton ta dafa ta sha sannan ta yi wanka ta ji ta ɗan samu sauƙi. Shi ne ta rarrafa ta yi ma Habib friederice mai nama tunda ba ta da hanta, abin ya ba ta mamaki ganin da wuri yau ya dawo tun kafin isha'i
Sai da ya ci abinci sannan ya fita sallar isha'i kafin ya dawo Ummu ta sake yin wanka duk da ta na jin kamar zazzaɓin zai dawo mata tana jin sanyi-sanyi.

Sai ta saka wata doguwar riga ta haÉ—a da rigan sanyi saboda ta fara rawan sanyi. Komawa ta yi ta kwanta ta rufa da bargo saboda har kanta sara mata yake yi, Habib na dawowa ya biyo ta har cikin É—akin ganin ta a kwance bai sa ya yi tunanin ba ta da lafiya ba kawai sai ya saka hannu ya yaye bargon da ta rufa da shii.

A kasalance Ummu ta É—ago tana kallon shi.

"Ta shi mu yi mgana."

Ya faÉ—a a kausashe.

"Noori ba ni da lafiya zazzaɓi na ke ji."

Ta faɗa cikin rawan sanyi tana ƙoƙarin sake jan bargon ta rufa ya fizge cikin mamaki ta kalle shi kafin ta samu damar magana ya tare ta da cewa.

"Kin manta da maganar mu ne?

Gaban Ummu-Salma ya faÉ—i ras!. Cikin rawan baki da na jiki ta ce. "Wa ta maga na."?
Ta faÉ—a cikin mutuwar jiki, maganar cikin ne! Kar dai a ce Habib bai manta da mganar nan ba, kar dai a ce yana kan bakan shi.

"Kin manta ne? Mganar da muka yi da ke ranar. Da man kwana uku na ba ki ki yi tunani ki yanke shawara, yau kuma cikon kwana uku shi ya sa na ce ki ta shi ki faÉ—a mini matsayar ki "

Ummu ta ji kanta ya sake sarawa da ƙarfi da man kaɗan kaɗan yake ɗan sara mata. Maganar Habib ya sa ta ji kamar gefen kanta zai cire kallon Habib take yi cikin mamaki da gaske ya ke yi?

"Me kika yanke? Za ki zubar ko a'a?

Ya faÉ—a yana mai kallonta.

Ummu ta runtse ido kafin ta buÉ—e tana mai dafe kanta.

"Habib wai da man da gaske kake yi?

"Wasa na ke yi miki?

Ya katse ta a fusace.

"Na É—auka ba ka cikin hayyacinka ne."

Ummu ta faɗa masa ido cikin ido saboda tana so ta samu tabbacin lafiyan Habib ƙalau.

"Au kin É—auka na fara shaye-shaye ne?

Ya faɗa cikin riƙe haɓa, ita kuma Ummu sai ta ma yar da kanta a saman fito ta ma kasa magana mamaki take yi wai da gaske wannan abin da ke faruwa da gaske yake faruwa!

"Ummu-Salma."

Ya kira sunanta ta amsa ta na mai sake É—agowa a lokacin ita gani take yi wasa ne ba gaskiya ba ne abin da ke faruwa.

"Kin ga wasa a magana ta ne?

Shuru ta yi masa ba ta yi mgana kawai sai ta ji ya daka mata wani matsanacin tsawa har sai da ta firgita

"Na ce kin ga wasa a magana ta ne Ummu-Salma."
Chapter 17 · 0% Book details