Sashe 47
Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daga SS1 ta fara karatu sannan tana zuwa lesson haka saboda taimakon kanta tunda daga sama ta faro karatun kamar ba za ta iya ba domin ta sha wahala kafin ta fara ganewa ko za ta sare sai ta ba ma kanta ƙwarin gwiwa ta cigaba. Ta zana jarabawa kuma ta ci sai ga ta da taimakon Baffa ta samu gurbi a Federal Collage of Education Yola Jimeta. Saboda ma ta yi karatun a cikin makaranta take zama sai bayan wata ɗaya take zuwa ganin su Baffa Lamiɗo ko tun da ta yaye shi ta sakar ma Ammah ta ce ta bar mata shi halak makal a matsayin ɗan ta. Shikenan ta koma kamar ba ita ta haife shi ba shi ma yadda ba ta ta kansa shima Ammah ya sani a matsayin uwa tun yana ƙarami. Fatima ta mayar da hankalinta a kan karatunta da taimakon Baffa.
Bayan ta gama NCE ba ta zauna ba ta nemi gurbi a jami'ar Maddibo Adama University, tun a lokacin tana Federal University of Tecnology.
Shima saboda nisa a garin Girai jami'ar take can take zama a hostel sai ta samu hutu take zuwa gida kuma tana karantar Biology ne. Fatima ta saka kanta da cewa za ta iya ta yi dakiya ta yi naci kuma Allah ya taimaketa ta cika burin ta.
****
SHEKARU TALATIN DA SUKA SHUÆŠE A BAYA.
Bayan shuɗewar wasu shekaru Talatin a baya Rayuwa ta daidaita. Tunda Baffa harkokinsa sun buɗe ya yi arziƙi da kasuwancin sa na siyan tsoffin ƙarafa yana siyarwa sannan shekaru goma a baya ya fara haɗawa da siyar da motoci tun haɗuwarsa da Alhaji Isa Ɗan marke bazamanfare mai siyar da motoci wanda ke da kamfani a garin Kaduna sun daɗe suna kasuwanci kuma dalilin shi Baffa ya samu alheri masu yawan gaske. Baffa ya gina katon gida a anguwan Zone 3 in da iyalansa ke zaune har yanzu.
Shima Alhaji Isa Ɗanmarke a dalilin Baffa ya samu matar aure. Ya auri Fatima tana da shekaru talatin da biyar mai kwalin karatun Degree da masters a lokacin. Matarsa ta rasu kuma ba su taɓa haihuwa ba yana ganin Fatima a gidan Baffa ya ce ya yi mata Baffan kuma ya bashi domin a lokacin shi ke da alhakin aurar da Fatima da duk itama tana da haƙƙi tun da ita bazawara ce. Fatima ta auri Alhaji Isa ta kuma tare a gidan shi dake Kaduna. Suna kuma yin auran ta ɗora karatun ta na PHD a jami'ar Amadu Bello dake Zaria wato ABU ZARIA.
Tana cikin kuma karatun ne ta samu ciki ta haifi yarta mace Islam(Fatima) bayan ita sai da ta gama karatu da shekaru biyar sannan ta haifi Faruk(Umar). Tun bayan barowan ta Daura ba ta sake komawa ba amma su mutanen Dauran sun neme ta daga baya saboda LamiÉ—o.
Baffa kuma ya tara zuru'a sai son barka. Hamma Jibo ne babba wanda ya yi karatu har matakin Master mazaunin Abuja da iyalansa shekarunsa na haihuwa 40.
Sunan matarsa Nauwara da yaran su huÉ—u, Saudat, Jamila(Amma) sai yan biyu Hassan da Hussaini sai Isma'il.
Sai Hamma Mustapha shima ya yi karatun boko har matakin Degree yana garin Gombe tare da iyalansa yana aiki da hukumar ruwa(Water resourses) shekarunsa na haihuwa 38.
Sunan matarsa Aisha(Momi) ya'yansu uku Fatima(Mahma) Zainab sai Hadi(Baffa).
Sai Hamma Kabiru shima ya yi degree a kan medical lap, yana aiki da asibitin Federal hospital Jalingo. Shi kuma shi da LamiÉ—o suna cikin shekaru na 35 ne.
Sunan matarsa Safinatu yaran su biyu, Muhammad da Yusra, kuma a can Jalingon yake zaune da iyalansa.
Sai Hamma Abdulrrahman lauya ne mai zaman kansa yana zaune a garin Jimeta shekarunsa 33. Matarsa Ummu Sulaim da ya'yan shi biyu duka mata. Mariya da Jamila(Mimi) sai Hamma Abdullahi tare suke kasuwanci da Baffa shima ya yi karatun Boko ya karanta harkan kasuwanci shekarunsa 31 babu nisan haihuwa tsakanin a duka yaran Amma.
shima yana zaune da matarsa Suwaiba da ɗansa ɗaya Umar(Maddibo) sai Hamma Abdulrahim shi kuma yana can ƙasar singphore yana karatun likitan ci, ɗan kimanin shekaru 29.
Wanda Hamma LamiÉ—o ya É—auki nauyin karatun na shi.
Sai Hamma Saddam wanda ke karatun mass com a jami'ar ATBU BAUCHI yana aji uku, tsakanin Saddam da Auta Ummu wata ashirin ne.
Shi yana cikin shekaru na 27 ne. Sai Auta Ummu Salma wacce iyakar ta sakandiri ta tsaya aka yi mata aure.
Zuwa lokacin rayuwa duk ta yi kyau, a can Mubi ma Baffa Hamza ya rasu haka ma Umma(Asma'u) a gidan su Baffa yanzu Baffa Umaru ne Babba duka kuma a gidan su ke zaune da Æ´a'Æ´ansu da iyalansu, su dai ba su bar Mubi ba suna nan a cikin ta amma dai Baffa da iyalan shi suna zuwa Mubi akai akai in an yi wani abu Amma ma tana da zuru'a a can tun da su Umma Balki sun tara iyalai masu yawa a can Mubi É—in. A nan kuma ita da Ummin ikki ne suka tara iyalai, sai son barka Ummin ikki ta aurar da matan ta huÉ—u, iklima, Saratu, mai sunan Amma Jamila, sai Binta sannan kaltume da BaÉ—É—o(Aisha) su ne yanzu a gabanta ita Allah bai ba ta namiji ba amma Mallam Sani ya kara aure amaryan ta haifa masa maza uku. Amintansu da Ammah sai ma abin da ya yi gaba sai dai duk amintan dake tsakanin Ammah da Ummin ikki Baffa da Mallam Sani ba sa Aminta sosai amma suna da kyakyawan alaqa da juna sai dai ba kamar Aminta da shakuwa irin na matan su ba
Abin da Mami(Fatima) ba ta sani ba shi ne tun Lamiɗo na ƙarami Mahaifin shi Maimartaba Sarkin Daura Alhaji Dr Muhammad Nasiru na tura kudaɗe duk wata domin hidimarsa a ɓoye ba tare da kowa ya sani ba sannan duk in da Baffa suke yana sakawa ana bibiyan su
Da shawaran ƙanwarsa mai bi masa Hajiya Zaliha(Magajiyar Sanda Mata) kuma ita ke auran Madakin masarautan Zazzau, tun faruwan lamarin ita ce kawai ta nuna rashin kyautawar Fulanin kan abin da aka yi ma Fatima. Amma sauran duk sun goyo bayan Fulani a wancan lokacin. Ita ce ta bashi shawaran ya nemi in da Fatima take domin gudan jinin dake tsakanin su, ya sani Fulani ba yadda za ta yi domin Ubangiji mai haɗawa ya riga ya haɗa danganta a tsakanin shi da Fatima ta sanadiyar Lamiɗo.
Tunda ga haihuwar Lamiɗo har girman shi da komai da komai Marmartaba yana da labarin komai sannan shi ya saka a ka samo masa lambar asusun bakin Baffa yana tura masa kuɗi, a saƙon da ya taɓa tura masa na farko ne ya yi bayanin kan shi sannan ya roƙi Baffa da cewa kar ya ce ba zai karɓi kuɗin ba, har abada ba zai taba karɓan Lamido daga hannun su ba, shi ko Baffa daman ko bai roƙe sa ba, ina shi ina ma yar ma da sarki kuɗi kuma ko ya ce zai karɓi Lamiɗo ai ba shi da ta cewa ba zai iya ja da masu mulki ba, shi ya daɗe da yafe komai da man sanadin Fatima ne, yanzu kuma Fatima ta samu komai na rayuwa kuma yawancin mutanen da suka yi ruwa da tsaki a kan auran ba sa raye. Hatta mariƙan Fatima na Daura sun rasu da daɗewa amma dai har yau akwai wasu daga cikin ahalin Gwaggo a garin Daura Baffa dai kan tura musu saƙo amma shima ba zuwa yake yi kamar yadda Fatima ta tsani garin haka shima ya ji ya fita kan shi gabaɗaya.
Mami ba ta san Maimartaba ke ɗauke da nauyin Lamido ba sai da ya tafi ƙasar Malesia karatu a lokacin Baffa ya sanar da ita komai saboda ta san ba shi da kuɗin da zai kai Lamiɗo waje domin ya yi karatu kuma kaf cikin yaran ba a kai kowa ba sai shi. Ta sha kuka tana faɗin ita har abada ba ta da alaqa da waɗanan mutanen Baffa ya nuna mata ita ko ke da alaqa da su, tunda akwai jininsu a tare da ita. Da ta yi bore Ammah ta ce ba ruwanta tunda daman tuntuni ta ce ta bar mata ɗan, jin haka yasa ta cire bakin ta akan Lamiɗo da man kuma ba saka bakin take yi ba.
Rayuwa ta gangara har Lamiɗo ya gama karatun shi na degree da Master akan Nautical Sceinces a jami'ar Akademi laut Malaysia. Ya samu ƙwarewa da horo kan tuƙin jirgin ruwa kuma lokacin ne Fulanin Daura ta buƙaci Jikan da ta juya ma baya tun a farko. Saboda duka ƴa'yan sarakunan da ta aura ma Maimartaba ba su ba ta jika namiji ba sai mata ita kuma tana so zuru'an ta su ƙare a zamowa sarakuna ne shi ya sa ta ɓullo da maganar nemo Fatima da abin da ta haifa shi kuma da man Maimartaba yana neman dama ne sai ga Fulanin Daura har falon Ammah tare da manyan ƴa'ƴanta mata
ta duka tana ba ma su Baffa haƙuri, Baffa ya ce shi ya daɗe da yafewa Fatima za ta roƙa gafara. Mami kuwa ta ƙi yafe musu har sai da Fulanin Daura ta je har falonta a gidan mijinta dake garin Kaduna. Dalilin mijinta Alhaji isa ya sa ta yafe ma Fulani da ɗanta amma game da Lamiɗo ta ce ba ruwanta a ciki ta nemi Baffa da Ammah sune iyayen Lamido. To shima dai Lamiɗon ya yi taurin kai duk da daman ya san ba Baffa da Ammah ba ne suka haife shi ba. Maimartaba na zuwa Jimeta a ɓoye Baffa ya kai masa Lamiɗo ya gansa sannan da yana Malaysia yana zuwa ganinsa tare da Hajiya Zaliha(Mahma)
A haka ne sabo ya shiga tsakanin su kuma Maimartaba da kansa ya zaunar da LamiÉ—o ya bashi labarin duk abin da ya faru shi ya sa ya fi jin haushin Fulanin Daura.