← Book details Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 92

Sashe 39

Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ka yi hakuri Alhaji na ka ne fa ba yadda za ka yi. Don Allah ka dawo ka zauna zai ji maganar ka in sha Allahu."

Gwaggo ta faÉ—a cikin tausasawa Baba Usman na ta ya ta.

"Sai hakuri Alhaji, kai Habibu ka yi magana ka ba shi hakuri tunda ba ka da gaskiya."

Habib ya tura hulan kansa baya yana shafa gaban goshin shi yadda yake jin zuciyarsa a lokacin kamar ya buɗe idanuwana ya ga Ummu Salma ya fara ƙwallo da ita ko zai wuce takaicin shi.

"Ka yi haƙuri Abba ba zan ƙara ba."

Ya faɗa yana ƙasa-ƙasa da kansa kamar na gari.
Da ƙyar ya dawo ya zauna yana faɗin" Ni da na ce na cire hannuna ya je can ya yi duk abin da ya ga zai iya ai ya girma zai iya tafiyar da rayuwarsa yadda yake so."
"Ka yi hakuri Alhaji. Habibu duƙa ka ba ma baban ka hakuri."
Gwaggo ta faɗa tana kallon Habib, ko ba ta ce ba dole zai rankwafa ya ba shi haƙuri saboda kar nan gaba ya ce ba zai shige masa gaba wajen auren masoyiyarsa ba.

"Ka yi hakuri Abba kuskure ne hakan ba zai sake faruwa ba"

Habib ya faɗa yana sauke kansa ƙasa sai da ya yi ta ban haƙuri sannan Alhaji Sheriff  ya sassauto yana faɗin" Duk fa wannan  faɗan da ka ga muna yi maka Habibu don muna son ka ne, muna son rayuwarka ta zama abin sha'awa da ƙwatan ce"

"Sosai. Kuma wanda ba shi da na gaba ai shi ke da kaico."

Baba Usman ya faɗa shima. Shi dai Habib yana ta basu haƙuri kansa a ƙasa.

"Ya rage na ka Habibu. Sai ka shirya ko gobe ne ka je gidan surukan naka ka ba su hakuri sannan kar mu sake jin wata magana ta sake tasowa. In hakan ya faru Habibu zan cire hannuna akan ka wannan karon."

Alhaji Sheriff ya jaddada  masa, ya kuma amsa masa da cewa zai yi abin da ya ce sun daɗe suna yi masa faɗa da nasihu, ya yi kamar yana ji nan ko a kasan zuciyarsa shi kaɗai ya san abin da yake saƙawa an kawo gabar da ba zai iya kauda kai ba tunda ya ce in gaji da ƴarsa to ya dawo masa da ita, ai ko zai dawo masa da ita, da man duk ya nuna alamun haka sune ba su gane ba. Sai goma saura ya bar gidan duk da tun yana can ake ta kiran wayarsa da turo saƙo bai duba ba sai da ya fito daga gidan ya ɗau hanya sannan ne ne ya duba wayarsa.

Da man ya san ita ce saboda sun yi da ita yau zai je wajenta amma bai samu zuwa ba, Ummu Salma ta ɓata masa kyakyawan daran sa, amma hakan ma ya yi yau zai yada ƙwallon mangwaro ya huta da ƙuda.

"Habib wani abu ya faru ne?

Saƙon da ya buɗe kenan bayan tarin kiran da ta yi masa bai amsa ba yana gaban su Abba.

"Za ki iya aurena nan da wata biyar ?

Haka ya rubuta ya tura, ba daÉ—ewa ko sai ga shi an turo masa da amsa.

"Me zai hana? Ni da man kai nake jira ni nawa matsalan mai sauki ne Habib."

Mirmishi ya yi shi kaÉ—ai kafin ya sake yin rubutu ya tura.
Saboda haka har gefen titi ya gangara ya yi parking É—in motar shi.

"To ki shirya kin kusa zamo wa Amaryan Habib in sha Allahu."

Yana gama turawa sai ya saka wayarsa a Aeroplane mode saboda ba ya so ta dame shi da tambayoyi abin da ya sani É—aya ne a wannan daran zai yakice Ummu Salma daga rayuwarsa da ita da cikin jikinta har gaban abada ba ya fatan a sake danganta shi da su, zai fara sabuwar rayuwar da ya tsara ma kansa nan da wattani biyar.

Tabbas kaddara ta riga fata. Da man zanen kaddaran su in ya fara tare to Ubangiji bai yi hukuncin labarin na su zai kamallah a tare da juna ba.
Ummu Salma da Habib za su rabu a wannan  duniya amma kuma za su sake haɗewa a wata sabuwar duniyar.

*littafin Fargar Jaji na kuÉ—i ne a manhajar Telegram akan #1k. Tura KuÉ—in karatun ku ta wannan acct É—in 9069067488 JAMILA UMAR OPAY sannan sai ku tura shaidar biya ta waÉ—annan lambobin kamar haka.*

09069067488.
08032773332.

*Yan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajojinku a cikin wannan kayattacen labarin za ku iya tuntuɓata kai tsaye ta wannan lambar 09069067488 Na gode.*

*Janafty*
*FARGAR JAJI.*

*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:JamilaUmarJanafty*

"To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude"

https://chat.whatsapp.com/LsC7Rjmei7J6Hd11e95nNS?mode=gi_t

*10*

*10:12pm*

Ƙarfe goma da mintina sha biyu Habib ya shiga falon gidan shi, da ƙishin ruwa ya dawo shi ya sa yana shigowa falon bayan ya kunna hasken wuta.

Da yake Ummu ta kashe komai kafin ta kwanta Kitchen ya zarce yana neman ruwa a firiza amma babu ruwa sai wani guda ɗaya pure water da ya gani a saman kantan kitchen ya ɗauka sha, ya manta bai bar komai a gidan ba, ruwan bai ishe shi ba amma haka nan ya haƙura har zai fita sai ya leƙa store bai yi mamakin ganin kayan abinci ba, daman dalilin da ya sa ta nace ta ƙi tafiya saboda iyayenta sun kawo mata kayan abinci ne tunda daman ta ji daɗin kai shi ƙara wajen iyayenta.

Da gangan ya kwashe kayan abincin shi ya kai gidan su, a tunanin shi ai ba za ta zauna ta mutu da yunwa ba, in ta ga babu komai za ta koma gida ta sanar ma da iyayenta halin da ta ke ciki, su kuma kafin ma su kira shi zai aika mata da takardan sakinta, amma saboda maita da rashin zuciya ba ta tafi ba sai ma aka kawo mata kayan abincin saboda dole ne sai ta zauna a gidan shi, to ya gaji shima zai sauwaƙe ma kan shi ne, gida da man na haya ne kuma shekara ɗaya ne kuɗin hayar kuma na shekaran ya kama gidan saboda biyan buƙatan shi ya kuma samu biyan buƙatan shi to ba zai damu domin ya bar musu ragowan kuɗin hayar ba. A gidan kansa  zai gina wata sabuwar rayuwar da ya tanada shi da abar ƙaunarsa.

A fusace ya fito daga kitchen ɗin ya shiga ɗakin da ya ke kwana ya nemo takarda da biro, yana fitowa ƙofar ɗakin da Ummu ke ciki ya shiga bugawa cikin sauri sannan da ƙarfi kamar zai ɓalla ƙofar sannan lokaci ɗaya yana kiran sunan ta.

"Ummu Salma."

"Ke Ummu Salma."

Ya ke faɗa da muryansa a sama lokaci ɗaya yana cigaba da buga ƙofar da karfi.

Kamar a mafarki ta ji bugun ƙofar domin har ta fara barci kanta ke ciwo saboda kukan da ta sha, sai ta sha pracetamol tana idar da sallar isha'i ta kwanta cikin ikon Allah barci ya kwashe ta da man wani lokacin tana samun yin barci a farkon dare amma in ta farka ne yake da matukar wahala ta samu nasaran komawa, wata rana ta tashi ta yi salla wata rana kuma ta yi karatun Qur'ani wata rana kuma ta yi kuka. Yau ma da wuri ta samu barcin amma bugun ƙofar da Habib yake yi ya katse mata barcin nata kuma a daidai lokacin daman mafarkin Habib ɗin take yi wai ya kira ta yana yi mata mgana ita kuma ta ɗuka har ƙasa tana bashi haƙuri har ya tashi zai tafi ta riƙo kafarsa amma ya juya ya ture ta a cikinta ta faɗi, sai ga jini na bin ƙafarta shi ya sa bugun ƙofar da mafarkin da ta yi suka samar mata da tashi a firgice tare da fargaba mai tsanani.

"Ba za ki buÉ—e ba! Ke Ummu Salma."

Ta ji muryan Habib yana magana, ta sake figicewa cikin gigita ta sauko daga kan gadon da take kwance, ta ma manta da hulan kanta da ya saɓule bayan ta kwanta sai da ta nufi ƙofar sannan ta shafa kanta ta ji ba ɗankwali ga shi kan ya yi datti goron kitso har ya ɓace saboda daɗewa, saboda ba ta kitso take yi ba.

"Wai ba za ki buÉ—e ba? Na san fa kina jina."

Habib ya sake faɗa kuma yana cigaba da buga ƙofar, yadda jikinta ke rawa haka zuciyarta ke rawa domin ba ta san da abin da Habib ya zo a daran nan ba amma dai tafi tunanin abin da ke kawo shi wajenta ya zo nema jikinta, in shi ne kuma ya zo ga shi nan har sai ya gaji.
Saboda saurin ta buɗe kofar har tana neman faɗuwa rigar jikinta ce ta harɗeta ta kusa kaiwa ƙasa sai da ta riƙe gefen wardrope ɗin dake ɗakin. Hannnunta na rawa ta murza key ɗin dake jikin ƙofar ta buɗe ɗakin, Habib ya tsaya yana kallon ta cikin bacin rai.

"Ni za ki mayar É—an iska kina ji ina kiran ki kina yi mini shuru?

Kanta na ƙasa ta ce" Ka yi haƙuri ban ji ba ne"
Ta ɗauka abin da ya saba kawo shi yau ma shi ya kawo shi ya sa tana gama bashi haƙuri ta juya za ta koma ciki.

"Ki same ni a falo."

Ta ji ya faɗa ta juya cikin mamaki shi kuma tuni ya bar wajen, zuciyar ta amsa na rashin sanin dalilin kiran Habib amma ba ta yi ƙasa a gwiwa ba ta bi bayan shi zuwa falon, jikinta ya yi wani irin sanyi ne lokacin da ta ga Habib zaune kan kujera mai zaman mutum biyu ya harɗe kafafunsa kamar wani basarake ga littafi da takarda a hannun shi har da biron rubutu.

Kasa ƙarisowa ta yi ta tsaya cak daga nesa tana kallon shi cikin bugawar zuciya, me Habib zai yi da takarda da biro? Allah ya sa ba abin da zuciyarta ke saƙa mata ba ne, in ko haka ne da ta ce ita yau Ummu Salma ta shiga uku ta lalace rayuwarta ta faɗa cikin mawuyacin garari, gararin da har abada ba za ta iya fita daga cikin sa ba.

"Malama ki ƙariso kin tsaya mini a saman kaina "
Chapter 39 · 0% Book details