← Book details Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 92

Sashe 10

Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har Adda Nauwara matar Hamma Jibo ta je Dinner ɗin ita da su Saudat, tun da suna garin suma sun yi kyau da ya ke Hamma Jibo shima ba daga nan ba ɗan gayu ne sosai, matarsa ma yar gayu ce haka ma ƴaƴan su. In suka zo hutu Jimeta ba sa yin hausa wa junan su yaran su yi ta turanci wata rana da Saudat ta yi ma Ammah mgana da turanci yini ta yi faɗa tana cewa ita za a nuna ma iskanci to ko uban ta nan ya girma ita da Baffa hausa da fillanci suka koya masa ba ta son tsirfa da iyayi, kar a sake yi mata turanci a gida gargaɗi aka yi ma Hamma Jibo da Adda Nauwara, da cewa ba su ko ya ma yara fillanci ba sai wani turanci yaren da ba na su ba. Ammah fa  Ƴa'ƴan Hamma Lamiɗo ba su jin hausa daga uwar har uban da turanci suke yi musu mgana gwara ma Hamma Lamiɗo shi yana yi musu hausa da fillanci wani lokacin amma uwar sai turanci amma har yau ba a ji Amma ta yi faɗa akan haka ba tun da Hamma Lamiɗo ne, shi kuma Hamma Lamiɗo shalele ne a wajen Ammaj ba ya laifi.

Ranar da aka yi Dinner sai wajen ɗaya na dare Ummu ta kwanta Habib ya gaji da jiranta ya kwanta ta kafa ta tsare tana kallon abin da ke kwana a garin Abuja a wani ƙayattacen hall, an sha Dinner sai wanda ya je ya gani su ɗin ma dake gida sun gamsu da Dinner ɗin ta masu mulki da sarauta ne. Maƙawan arewa sun hallarta kowanne mawaƙi ya baje na shi kolin, irin su Ali jita, Naziru sarkin waƙa, Nazifi Asnanic, Auta MgBoy, Auta waziri, Salim smart, Ɗan musa da sauran su ko wanne da irin karin waƙar shi ga amarya da ango sun kuma sha kuɗi, domin miliyoyi ne ke tashi da dollars, wannan daren dai Dinner ɗin ce ta dinga trending a kafafen sada zumunta ita dai ko alama bata nuna ma tana da alaqa da masu bikin ba.

Sai washegarin ranar asabar aka É—aura aure a masarautar Daura, Hamma Kabiru ya saka hoton Hamma LamiÉ—o.
Sai da Ummu ta kau  da wayar daga fuskarta saboda tsoratar da ta yi, sanye yake da uniform ɗin su na matuƙan jirgin ruwa
Farar riga da baƙin wando fuskar shi ce ta ba ta tsoro, ta yi gargasa gemunsa ya yi kamu uku, kansa gashi ya cika ya yi yawa babu kyan gani.

"Amini a bakin aiki."

Haka Hamma Kabiru ya saka, sai da ta je hoton gaba sai ta ga ya saka wanda ya yi gyaran fuska ya rage gashin fuskar da na sumar kan amma ba sosai ba.

"Amini ya yi gyaran fuska."

Wataƙila Hamma Kabiru ne ke wahalar posting ɗin Hamma lamiɗo, shi ko ba ta da tabbacin yana saka shi, duk dai kowa ya shaida akwai aminci a tsakaninsu fiye da kowa ma, Hamma Lamiɗo mutum ne da bai cika bayyana ƙarfin alaqar sa da ko ma waye a zahiri ba, fuskar shi ba ta fallasa sirrin zuciyarsa.

Kullum a ginshiƙe za ka gan shi,  fuskar nan kamar yana cikin wani damuwa a kame in ma ka samu ganin shi kenan, mutumin da a shekara bai wuce sau ɗaya
yake zuwa ganin gida ba. Duk da yana da tamƙamemen gida anan garin Jimeta, sai ya yi rabin shekara a rufe wani lokacin a shekara sau ɗaya yake zuwa in an yi wani abu ne sau biyu sai dai yana yin sama da wata a Jimeta in ya samu hutun karshen shekara wani lokacin shi kaɗai ya ke tahowa matar tashi sai aiki ya yi mata sauƙi sai ta biyo shi ita da yara, daga nan ne suka wucewa Daura can ma wani alkarya guda ne da sunan bangaren Hamma Lamiɗo.

Aikin su na yana da tsauri, Captain ne shi ma'ana matuƙin jirgin ruwa ne. CAPTAIN M.N. MUHAMMAD.
Yana aiki da kamfanin Nigerian port Authority jiragen dake jigilan mutane da kayan masarufi shi ya sa suke daÉ—ewa a saman ruwa
Babu ƙasar da ba sa zuwa ta kogi sai su yi wattani sama da shidda a saman ruwa ba su shigo gari ba, sun fi ma saurin dawowa gida in sun ɗauko kayan masarufi.
Shi ya sa suma kan cika fuskar shi wani lokacin sai sun zo bakin gabar wani garin ne suke samun damar yin wani abu, hutu ko bai wuce na awanni huÉ—u ba ka ci abinci ka kwanta kana tashi ka koma bakin aiki, sau tari shi ya sa ba ya kiran waya da rana sai cikin dare ko asuba, wani lokacin ma sai a yi kwanaki ba a samu wayar sa ba.

*littafin Fargar Jaji na kuÉ—i ne a manhajar Telegram akan #1k. Tura KuÉ—in karatun ku ta wannan acct É—in 9069067488 JAMILA UMAR OPAY sannan sai ku tura shaidar biya ta waÉ—annan lambobin kamar haka.*

09069067488.
08032773332.

*Yan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajojinku a cikin wannan kayattacen labarin za ku iya tuntuɓata kai tsaye ta wannan lambar 09069067488 Na gode.*

*Janafty*
*FARGAR JAJI.*

*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:JamilaUmarJanafty*

"To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude"

https://chat.whatsapp.com/BxcTrVcz7GoIDzbqZTpIxF?mode=gi_t

*03*

Daga Daura bayan an gama ɗaura aure Abuja aka sake dawo da Amarya tunda anan ne ƙayattace gidanta yake a cikin jerin gidajen masu kumbar susa da faɗa a aji a ƙasar gabaɗaya. A ranar aka yi buɗar kan Amarya a gidan iyayen ango, tab an yi ɓarin miloyoyi wajen buɗan kan Amarya kamar kuɗi ba matsala ba ne a wajen su,  shi kan shi Ango dangin Amarya sun fanshe shi da miloyoyi, Matar Hamma Lamiɗo miliyan biyu ta fanshi kan Ango a madadin ita da Mijinta Yariman Daura, Muhammad Nasiru Muhammad Daura(Lamiɗo).

MC da aka gayyato domin gabatar da program É—in ta kacame da guÉ—a tana yi ma Balkisu kirari.

"Takawarki lafiya Uwargida kuma Amarya a gidan Yariman Daura. Muhammad Lamiɗo ke ya zaɓa ke ma shi kika zaɓa, ɗiyar masu sarauta kike kuma Yariman daura ne mijin ki, sannu ƴar sarki matar ɗan sarki, uban ki sarki mijin ki ma zai yi sarki in sha Allahu, kuma za ki haifi Sarki da ikon Allah
Sannu likita bokan turai, uwar Sultan kike sannan ke ce kika haifi Beena. Na gaishe da sarauniya Balkisu, na gaishe da Matar Yariman Daura takwarki lafiya Gimbiya Balkisu Zinariya."

Sai dai kawai aka ga ta saƙa ma MC ɗin kuɗi a hannunta waje ya ɗau tafi Ummu ranar ba abin da ta yi sai faman bin shagulgulan bikin nan, matar nan ta Hamma Lamiɗo hadaɗɗiya ce ranar ma shigar lafaya ta yi, ta saka wani material gangariya daga ganin shi ya ba ma wasu nairori baya.
Tabbas ta cancanta domin zinariya ce.

Duk da Hamma Lamiɗo ba gwanin ta ba ne, ita ma matar tashi wata doguwar mu'amala ba ta taɓa haɗa su ba, amma dai ita a karan kanta tana yin matar saboda yar gayu ce mai kyau ce mai kama da model ce, ga ƴaƴan su farare gwanin ban shawa'a in ka ga rayuwar wasu sai ka yi tunanin wataƙila su suka zaɓa ma kansu, to komai na rayuwa na duniya sun same shi a hannu, suna yadda suka ga dama da shi.

Ita kanta irin mijinta ne ba ta samun zama, a ƙiyasin kirgin Ummu Salma sau biyu Dr Balkisu ta taɓa zuwa gidan su zuwa na musamman da ta kwana fiye da ɗaya.

Akwai zuwan da ta yi bayan auran su da Hamma Lamiɗo, to bayan shi ta yi biyu haihuwan matar Hamma Kabiru da yake wannan Aminin shi ne ta zo, sai wani zazzaɓi da Ammah ta yi mai zafi har ta fara sambatu hankula sun tashi, kowa ya ɗauka Ammah lokaci ya yi ashe zafin ciwo ne, suna Abuja lokacin kafin ta koma Lagos da zama ta zo duba Ammah, a lokacin Sultan na ƙarami to bayan shi
Yanzu daga baya tana biyo shi in ya zo hutun karshen shekara, tunda sai ya fara sauka a Jimeta ya gama kwanakin sa a nan suke wucewa Daura.

Daga ita har mijin nata suna yin wuyar gani, hutun na shi kuma a shekara sau É—aya ne, in salla ne ma baya daÉ—ewa za su fara sauka nan Jimeta su yi kwana biyu daga nan su wuce Daura saboda wasan hawan salla akwai ma sallolin da aka yi yana can bakin aiki bai ma samu zuwa ba.

Duk da itama tana da halin É—agawa da ji da kai bai damu Ummu ba, ita dai bata ba ta haushi sannan tana burgeta ,hankalin ta bai kwanta ba sai da aka gama shagulgulan bikin nan sannan ta bari waya ta huta daga hannunta ta samu ta kira Ammah a waya ta gaisheta sama sama ma suka yi mgana tana cikin hayaniya ta ce za ta kirata ba kuma ba ta kira tan ba. Sai ta kudirta cewa in Ammah suka dawo za ta je har gida ta yi mata sannu da zuwa.

****

*NO. 224 NDC QUATERS. KADUNA NAGERIA.*
*9:47AM*

Da sassarfa take sauko wa daga kafar bene lokaci ɗaya hankalinta na kan agogon I.wacth ɗin dake maƙale a tsitsiyan hannun ta na hagu,  lokaci take dubawa domin tana da aji ƙarfe goma da rabi na safiya yau ɗin nan

Falon ƙasa ta sauƙo da yake shuru ba ka jin motsin kowa, farar mace ce doguwa mai ɗan kaurin jiki, tana sanye da wata gold ɗin atamfa mai ruwan ganye shi yasa mayafin jikinta ma da takalminta haɗe da jakan dake hannunta masu kalan ruwan ganye ne.
Hannayenta da zobban gold guda biyu da a warwaro suna ƙyalli, haka wuyan ta wani ɗan kunnen gold ne da sarƙan shi mai kyau da yarari.
A ƙiyasin shekarunta ba za ta wuce 52 ba sannan ba za ta gaza ba, amma a kallon farko za ka fahimci mace ce mai ilimi da gayu.

Sake duba lokaci ta yi, kafin ta ɗago kanta tana sake nazarin ƙayattacen falon mai kama da aljanar duniya. Falon babba ne domin saitin kujeru ne sama da guda huɗu saboda tsabar girman falon.
Zama ta yi kan É—aya daga cikin kujerun falon lokaci É—aya tana sauke jakar hannunta daga gefenta.

"Baraka."

"Baraka."
Chapter 10 · 0% Book details